Breaking News

KWARATA 16

🅿 ------ 16

                Bandai ji komai ba , 71 , 29 babu damuwa zamu rama muma...   ___```^^=°°---  Basarwa nayi tare da d'auke fuska ta daga dubansu, mutum dai bai isa yazo har gidana ya dakeni ba, kallon banza ko maganar banza mutum yamin wadda batamin ba wallahi ina da Lamba3 d c o zaici k'aniyar mata....


         A daidai lokacin da suka iso gabana maganar zuci ya k'are, Amisty ce tace wurinki fa muka zo kina yi kamar baki ganmu ba, saida na gama kallesu tsaf sannan nace sannunku da zuwa tare da mik'ewa zan shiga d'aki dan d'auko musu tabarma...

      Gaba d'ayansu rufa min baya sukayi suma suna k'ok'arin shigamin d'aki, ja nayi na tsaya tare da tambayarsu ina zasu je ? Amisty tace ciki zamu shiga ? Murmushi nayi tare da cewa kuyi hak'uri ku jirani ni bana kai mata cikin d'akina...

       Hafsa zatayi magana Amisty ta dakatar da ita, kallonsu nayi tare da cewa barta ta fad'i cikinta, Amisty tace barta kawai d'auko mana kedai, munafikin murmushi nayi tare da juyawa na shige cikin É—aki, domin ita Amisty tasan wace ce ni, tabarma na d'auko nazo na shimfiÉ—awa banza nace su zauna...

        Dukansu zama sukayi lokaci É—aya, su A ` i da Saude Nana da Karima duk suka taso suka dawo Æ™ofar É—akina, nima zama nayi tare da cewa meke tafe daku ne ? Na Æ™arasa maganar tare da kauda kaina gefe É—aya....

Amisty tace Sultana ke kikace mu sameki gida ! Kallonta nayi tare da cewa sai akayi ya ya ? Amisty tace ai shine muka zo ! Kallon tantiran mata nayi sannan na maida hankalina wurin Amisty nace da Allah daga yau idan zaki zo wurina kidai min kwashe kwashe , da sauri Amisty ta kalleni sannan tace haba Sultana mi yasa haka kuma ?

     Kai tsaye nace kinsan bana san munafirci kuma ban tare da munafikai, waccan bak'ar yarinyar da kika gani na nuna Hafsa budurwar Dikko sannan naci gaba da cewa gaskiya aminci take da mak'iya na saidai ta zab'a ni take so ko su A ` i , murmushi Hafsa tayi tare da kallona sosai ni kuma na d'an gyara zama yanda zan d'aukar mata hankali sosai, saboda ina so na rabata tarayya dasu A ` i idan ina tare da Hafsa suma suna tare da ita riÆ™a zugamin ita zasuyi har su hanani na cimma buruni tunda na lura ita Hafsa doluwa ce kuÉ—inne kawai ba wayau sai tsabar neman matan bala'e. Kwazzaba tasa har bata iya tantance kifi bata gane kwad'o,

     Cikin ruÉ—ewa Hafsa ta fara magana irin ta "ya "yan masu kuÉ—i, kin gane Sultana nifa ba abokaina bane kawai gaisawa mukeyi sai kuma wata huÉ—É—a tamu data haÉ—amu amma ba komai tsakaninmu gaskiya,

Ɗaure rai nayi tare da cewa nifa ba abinda ya haɗaku nake so na sani ba cewa nayi kawai ki faɗa ni zakiyi abokiya dani kibar su A ` i ko kuwa su A ` i kika zaɓa, Hafsa tace haba aike tawa ce kuma ina tare dake, murmushi nayi tare da cewa magana ta ƙare mata tacewa mijinta shege...

        A ` i zatayi magana nace dakata malama ta bakin gulbi, ki taka sannu da lafiya kafin insa a É“atarmin dake cikin garin nan, nuna yawan su Amisty nayi tare da cewa nan da kika gansu duk dalibai na ne, zan fara basu karatu daga jibi idan Allah ya kaimu, na kafa Æ™ungiya ta mai take kwarata duk wacce kika gani anan mabuÆ™aciya ce, zan haÉ—a ne zanba mace namiji idan an sallami mace zata fiddani, zan haÉ—a mata da mata amma a tafiyata ban tafiya da taron banza,  sabbin É—alibai ku na É—aukeku kyauta basai kunyi register ba, amma daga ba yanzu ba duk wacce zata shigo cikinmu saita ajiye dubu talatin kuÉ—in register haƙƙina neman maza da mata masu abun hannunsu....

        MiÆ™a hannuna nayi tare da cewa duk wanda yake tare dani ya É—ora hannunsa a saman nawa, kowa É—ora hannunshi yayi harsu Nana matan aure ba'a barsu a baya ba, ku É—auki alÆ™awari babu cin amana , gaba É—aya suka amsa munyi alÆ™awari bazamu ci amana ba, nace kuyi alÆ™awari zaku zama É—alibai masu biyayya, munyi alÆ™awari zamu zama É—alibai masu biyya nace idan kun samu ina nan ko bana nan zaku ajiyemin nawa kason, shima suka maimaita, sannan nayi addu'a tare da neman Allah yasa albarka a cikin wannan Æ™ungiya tamu mai albarka wanda nayi ma laÆ™abi da KWARATA saboda dukanmu lalatacci ne ,

       Bayan an gama nace tou kowa ya tashi ya tafi nima zan fita inda fuskar jama'a take na samu gida na siya idan kuÉ—ina yakai, idan basu kai ba kuma zamu kama shago, wannan shago zai zama nan ne kowa zataci gayu da safe taje ta zauna, yayin da zamu kafa Æ™aton allonmu ya kalli al'umma, za'a rubuta a gaban shagon ko gidan tambarin KWARATA idan ma baka iya ba kazo za'a koya maka.

        Zamu rubuta a jikin takarda mukai kuma a buga mana su da yawa, ni zanbi manya ofisoshi da kasuwa da kuma kamfaninika da inda "yan siyasa ke zama saina zabo mana manyan alhazawa sai mu raba musu, duk wanda ya gani ya karanta dama ga number wayata nan a jiki, ku kuma kuna shago kunsha wanka kunayi kuna Æ™ara powder da jagira ina binku ina muku wanka da turare, da mutum yace zaizo zance ya iso akawai kaya a Æ™asa, yana shigowa ya ganku wayyo shikenan labari zai canja salo, ni kuma ina da wata dabara É—aya amma bazan faÉ—a muku ba saboda karuwa bata da amana,

     Nana tace tou mu da muke da aure fa ? Kallon ta nayi Æ™asa da sama sannan nace duk iskanci da kukeyi keda A ` i sai yanzu kika tuna Allah ? Tsoki nayi tare da cewa tunda na lura kema kinasan duniyar sai in É—aukeki aiki ki riÆ™a sharewa kina gogewa, ke kuma Karima idan mijinki ya barki zan zuba miki kayan mata da maza na gyaran harka duk wata zan baki dubu biyar ko anyi ciniki ko ba'ayi ba, amma idan mijinki ya barki fa.

      Tun kafin in rufe bakina Karima tace koma bai barni sai naje wallahi, dubu biyar fa ? Ina nan kullum zaune gida naira hamsin ma wahala take min , kuma Sultana ki rubuta a jikin takarda duk wanda zaizo ya taho da kaza kinga idan anci an rage ai muma zamu maida miyanmu.....

        Kallon Karima nayi sannan nace kazar Lbura'uba, an faÉ—a miki kwartancin wahala zamuyi ? Kudai kuyi ta addu'a a samu bakin titi, addu'a sukayi tayi Allah ya taimaka ya bada sa'a, daga Æ™arshe dai kowa ya kama gabanshi, nima na kulle É—akina na fantsa ma cikin gari...

        Ina bakin titi tsaye naji wayata tana ta kururuwa dan haka dole na dakata, fiddota nayi na duba dan ganin mai kirana, Lamba 2 wato Bello kenan, É—auka nayi tare dayin sallama, bayan ya ansa na gaishe shi, bai ansa gaisuwar ba yace ke Uwar masu gida hotuna na gani ?

      Amma ai ka gane ko waye a jikin hotunan ko ? Eh nine , tou kuÉ—i zaka bani naira budu É—ari biyar nan da gobe idan Allah ya kaimu idan kuma kace babu sai ina watsa su duniya kowa ya kalla kyauta.... ÆŠanka da matarka da abokanka duk suna kwance a saman gado zasusha kallo abunsu...

         Sirikinka da surukarka zasusha kallon siriki tsirara... Tou nabarka lafiya, ina faÉ—in haka na katse kiranshi, ina duba yanayin samun mutum kafin na yanka mishi haraji, Bello baida ko sisi kuma baida wata sana'a data wuce caca, kuma caca ba kullum akeyinta ba, gashi kuma na sace kuÉ—aÉ—anshi kaff da na gani a mota ba damuwa na bane nidai kuÉ—i kawai, ina gama waya da Bello na kira lamba3 wato d c o, mai girma É—an sanda yarinyar jiya ce, Maryam Sultana Aliyu Binna, ya garin ? Haka nayi masa bayani bayan ya É—auki wayata....

         Hajiya ya kike ? Lafiya qalau kana ta ina haka ne ? Yace naje ganin gida ne baby, cikin salon cuta na kwantar da murya Æ™asa Æ™asa nace kuma "yar laÉ“ai maimakon ka kirani inyi rakiya ? Murmushi yayi sannan yace wallahi nima tafiyar bazata ce wife ina ce bata lafiya, tou lallai wannan kuwa da sa'a take wace ce ita, dan bansan abinda wife in take nufi ba, dana dangantata da mace saboda naji yayi magana da sunan jinsin mace ne, yace wife itace ba lafiya,

       D c o yace matata nace, danshi yanda yake kallon wayewa ta ya É—auka wata shegiyar baturiya ce, danaji yace mata nace ai shine nace wannan tana da sa'a, da kaji kuma nace wace ce ita ina tambayarka amarya ne ko uwar gida ?

     D c o yace ai mata ta É—aya ce, nace tou yayi kyau yaushe zaka dawo ne ? Zan dawo amma sai ta samu sauÆ™i, to Allah ya sawaÆ™e ya bata lafiya, d c o ya amsa da amin mukayi sallama.....

     Lallai duk yanda akayi wannan matar tashi tasan damarta ne, idan ta riÆ™e d c o sosai taya zamu samu wani abu a wurinshi ne to ? Wato ita munafika nufinta ita É—aya zataci ? Taci gidansu bari dai d c o in ya dawo bata Æ™ara ganinshi dan ubanta ba rashin lafiya ba ko mutuwa tayi sai anyi jana'izarta baije ba....

       Napep na hau na nufi gidan Alhaji marenin wayau na, tsoho ya tsufa amma zuciyar bata mutu ba, buÉ—e na samu gidan dan haka na banka kaina tsaye na shiga, babu dawakuna ko guda É—aya duk an fitar dasu an share gidan Æ™wal gwanin burgewa, sai cire yana akeyi ana wani kakkaÉ“e kakkaÉ“e get in gida sai wanke shi akeyi ana goge duk inda yayi Æ™ura....

       Cikin masu sharar na tamabaya lafiya ko Alhaji ya tashi ne ? Yace lafiya qalau bai tashi ba ubangidan shi ne zai dawo gobe, tsoki nayi tare da cewa shine ake ta wani share share ? Yace Eh , Dikko ko ? Na tambayi yaron yace Eh ai ance ma ya iso yana Abuja ko zasuyi me ne ne ? Amma dai naji ance jirgin safe zaibi yaje kano akwai abinda zasuyi sannan zai shigo katsina....

 Jinjina kai nayi sannan nace tou shi ina Alhajin ne ? Ai sun tafi kano taroshi, daga nan har kano suka tafi su taho dashi saboda tsabar basu da aikinyi ? Yaron yace ai ba rashin aikinyi bane ba hajiya duk abinda kika ga sunayi dan sun san zasu samu, Alhaji fa baya saida fari baya saida baÆ™i kiwon dokuna yake amma kiji irin dukiyar dake gareshi, sun san suna samu da D ---K É—in ne shi yasa suke laÆ™afe dashi, da yana nan da baya nan kuÉ—i suke samu kamar tashin hankali...

     Tou zan tafi kawai mayi waya dashi, jakata na buÉ—e nayi ma yaron alheri godiya yayi tayi tare da cewa Allah ya kareki ya Æ™ara arziÆ™i hajiya ubangiji yasa kifi haka Allah ya Æ™ara lilka darajarki ngode sosai. Ban saurareshi ba nayi waje abu na,

     Gida na koma saida nayi sallah isha'e sannan na fara nazari akan Alhaji abinda zance masa kawai ya bani mota da gida sai in fita daga harkarshi, dan ni duk inda zanji Æ™amshi ko labarin sunan D ---K na tsani wurin tsakani da Allah bana san Dikko na tsani rayuwarshi wallahi, amma idan har Allah yayi min cikakken arziÆ™i saina wulaÆ™anta ma Dikko rayuwa,

      Wani irin baÆ™in ciki naji yana tasomin hawaye ya cikamin ido na abinda ya faru tsaÆ™anina da Dikko ya dawomin sabo fil a zuciyata, zuciya ta tace min Æ™aryane baza a fita daga harkar Dikko ba sai na halakashi, kamar mai aljannu lokaci guda na burkuce nayi nayi na saita kaina amma na kasa wuÆ™a na É—auko tare da kwarara wani irin ihu nace wallahi saina kashe ka........ Na Æ™arasa maganar cikin kururuwa.

      Duk wanda ke gidan nan babu wanda baiji ihuna ba, da gudu Nana da Karima sukayo É—akina amma banda su A ` i saboda yau da wuri suka tafi gida. Lokacin da su Nana suka shigo duk na yanyanki wasu wurare na jikina da wuÆ™a, abin ya tada musu hankali dakel suka riÆ™eni suna tambayata waye Sultana kallon Nana nayi cikin kuka nace wallahi saina kashe shi gobe zai shigo katsina bana ko Æ™aunar jin irin sunanshi a rayuwata....

        Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shine abinda Dikko ya faÉ—a a daidai wannan lokacin tare da janye ruwan dake gabanshi, hankalin kowa yayo kanshi tare da tambayar lafiya ranka ya daÉ—e ? Dafa Æ™irjishi yayi tare da cewa gabana ke faÉ—uwa babu gaira babu dalili.

         Duk kusa dashi suka matsa suna mishi sannu, kallon babban yaronshi yayi sannan yace maza kiramin gida, É—aukar waya yayi ya kiro dadyn dikko, babu É“ata lokaci dady ya É—auka D --- K babu ko gaisuwa yace Dady lafiyanka qalau kuwa ? Murmushi Dady yayi tare da cewa mi kuwa zai sameni ? Bayan ina nan zaune cikin iyalina muna farin ciki saboda zuwanka ! Dikko yace Dady karka É“oyemin dan Allah miye ? Dady yace tsaya ma kaji, saida ya haÉ—a Dikko da kowa yayi magana sannan yace kaji ko ?

Ajiyar zuciya Dikko yayi kamar wanda yasha kuka ya ƙoshi sannan yace kawai haka nan naji gabana yana faɗuwa, Dady yace saboda zaka ga ganni ne, kayi ta addu'a Allaah ya tsare kuma kayi bacci da wuri, jinjina kai Dikko yayi tare dayi ma Dady sallama suka ajiye waya....

     Dakel su Nana suka lallasheni nayi shiru, Karima tace inyi ta addu'a don Allah sharrin shaiÉ—an ne, nace tou amma har yanzu ban daina baÆ™in ciki ba, saida suka tabbar hankalina ya kwanta sannan suka tafi bayan sunsha fama na faÉ—a musu ko waye naÆ™i faÉ—a musu...

     Suna fita na rufe É—akina nayi addu'a na kwanta bacci,

        Da safe kuwa misalin 12:45pm na fara gwagwaÉ—awa Alhaji kira, bawan Allah banda zufa babu abinda yake haÉ—awa, idanuwanshi sunyi jajir saboda tsabar tashin hankali duk wanda ke wurin saida Alhaji ya bashi tausayi duk da babu wanda yasan abinda yake damunshi, amma banda Dikko dakeyin kyakkyawan murmushin dake fito masa da tsananin kyawunshi, da yasan yanda yakeyin kyau idan yanayin murmushi daya dawwama yanayin fara'a, duk da ko baiyi murmushi ba yana da kyau sosai gaskiya, taunar rainin hankali yake ma cingom in bakinshi sannan yace wai har yanzu ta hanaka ka huta ne ?

      Kamar Alhaji yana jira yace Eh ranka yadaÉ—e, Dikko yace bani ita, Alhaji yace ai kiran ya tsinki, É—aure fuska Dikko yayi sannan yace kirawo min ita...............