Breaking News

KWARATA 33

🅿 ------ 33

           Tafiyar Dikko babu jimawa Nana ta shigo take faÉ—amin mai gidan dokuna yazo nema na amma ance bana nan...

    Tsoki nayi ban bata ansa ba , tsintsiya ta É—auka taci gaba da share É—aki , ni kuma jakata na É—auko na buÉ—e ina kallon abinda nake fesawa mutum ya tafi bacci , jijjigashi nayi bayan naji sauran abinda ya rage na mayar a jaka ina mai addu'ar haÉ—uwa na da iyayen su Hafsa...




     Maganar Babana naji a tsakar gida yana cewa duk iya Æ™warewa munafircinku na gano ku baÆ™aÆ™en munafikai , wato duk lokacin da kukaji motsina sai ku kashe wayoyi ku É“oye kar nace ku bani kuÉ—i kuce babu , idan naji babu zansa wayoyi suci kasuwa , dan ku bani kuÉ—aÉ—en , lissafo duk yayuna yayi masu waya cewa kowa ta kawomin wayarta dukanku ancemin har face buk kukeyi , kuma na gani da idona dan babu wacce banga hotonta a cikinku ba...

     Cike da damuwa suka fara fitowa Babana yana zaune a saman kujera kowa sai ta bashi ta koma É—aki cike da É“acin rai , bayan ya gama tattare wayoyin kaf ya kira babban yayanmu yace maza kasuwar tsaitsaye ka siyar min dasu , da guda² yake bashi wayoyin tare da faÉ—a masa adadin farashin da yake so a siyar da ko wace waya...

Shima Yayanmu cikin fargaba yace Baba ai duk kuɗin daka faɗa baza'a siya a haka ba , wata irin harara ya zabgaga mishi tare da cewa wannan kuma damuwarka ne , kai tunani ya rage ma yadda zaka siyar danni duk kuɗin dana faɗa su zaka kawomin a ko wace waya na faɗa maka , yana faɗin haka ya miƙe ya nufo ɗakina...

      Da sauri Nana ta ajiye tsintsiya saida tayi masa sannu da zuwa ta fice daga É—akin , bayanta yabi da kallo zuciyarshi tana Æ™isima mishi wasu abubuwa , amma bai ansa sannu da ta masa ba...

       Gefen katifa ya zauna kusa dani cike da soyayya irinta mahaifa yabini da kallona mai tattare da tsantsayar soyayya , murmushi nayi nima ina kallonshi nace Babana baka da kuÉ—ine ? Murmushi yayi bai bani amsa ba , nima murmushin na sakeyi kamar yanda yayi sannan na jawo jakata ina cewa ni ina da kuÉ—i bara na baka...

     Ansar jakar yayi tare da rufeta yana mai cewa nifa ina da kuÉ—i Mamana kinsan mage kota Æ™oshi sai ta hari Æ™wari , ajiye kuÉ—inki anjima zan Æ™aro miki wasu , ajiye jakar yayi a gefena sannan yace Mamana tun kuna ku hamsin da bakwai har yau an wayi gari kun zama ku sittin ciff,

Tsoki yayi tare da kauda kanshi gefe yace tirr , wallahi da za'a tambayeni abinda nake so a musanya min da tulin "ya "yan nan ke kaɗai zan cire a cikinsu sauran a mayar min dasu daga motocin hawa sai ƙayataccin gidaje , ita kuma matar malam bahaushe ita dai burin ta kawai ta tara taron "ya "ya ita dai a mutu kawai taci gado , tou ban ajiye ba kuma bazan ajiye ba duk wacce ta haifi "ya "yanta taji da abunta ni babu ruwana...

      Uhum Babana kenan mugunta kamar mai tsaron gidan yari , wato karya nema ya ajiye idan baya duniya a ci gado , hmm halin Babana saishi kallo nabi shi dashi ga wayyen mutum kisan boko É—an gayu mai buÉ—ewar ido yana da ilimin boko mai zurfi amma saboda tsabar baÆ™in ciki ko aikin gwamnati bayayi , tunda yaga ana ruguwar haifar mishi "ya "ya ya daina aiki ya koma caca...

Kallona yayi yace ki ɓoye sirrin mahaifinki koda bana faɗin duniyar nan , ki zama maimin addu'a bayan mutuwa ta ɗaukeni daga kusa dake , ki nunamin soyayya irin wacce nake nuna miki Mamana , ina miki soyayyar da duk duniya bana ma kowa irinta , banajin kunyar kowa idan nayi abinda ban kyauta ba amma Allah ya sani inajin kunyarki Mamana , babu wanda ya isa yasa nayi ko na bari amma idan har kika hanani na hanu , labarin waye Binna kuwa zan faɗa miki ne saboda abinda ya faru dake wanda ba'a san raina hakan ta faru ba , kuma ki yafemin na roƙeki ya haɗa hannayensa biyu tare da ci gaba da cewa kuma bazan sake tafiya na barki ba , ya ƙarasa maganar yana mai min kyakyawan murmushi ....

      RiÆ™e hannunshi nayi tare da cewa kayi alÆ™awari ? Jinjina kai yayi yana murmushi yace nayi miki alÆ™awari , nima murmushin nayi tare da cewa nima nayi maka alÆ™awari Babana bazan taÉ“a tafiya na barka ba , yayi Allah ya albarkaci rayuwarki Uwar masu gida , da amin na ansa tare da gyara zamana , shima gyara zamanshi yayi sannan ya fara....


      ALIYU MUHAMMAD BINNA...

    Shine cikakken sunan da kowa ya sanni dashi , BINNA laÆ™ani ne dana sakawa kaina shi bayan na shiga harkar wasan caca , dalilin binna kuwa saboda tsabagen neman asiri irin nawa , BINNA a binne kenan , dan da anyi magana kaza bazai yuwu ba , zance a binne shi kawai , tou idan nace a binne sai mutane suka fara ankara da abinda nakeyi dan haka sai nayi waiwayen damisa na zama Binna kawai dan É“atar da mutane lissafinsu , sunan yana firgita kowa haka kuma yake bawa kowa tsoro duk wanda yaji ance BINNA.... tou binna abin tsoro ne abun firgici tashin hankali ne ga duk wanda yasan Binna da irin rayuwar da nakeyi...!

      Malam Muhammad shine mahaifina , Maryam wacce Æ™auye yasa ake kiranta da mero itace mahaifiyata , matan malam 2 mero da sahura , mahaiyarmu itace Æ™arama kuma dake ta daÉ—e bata samu aihuwa ba , ita kuma Sahura dama tuni ta kwankwatso É—iyanta goma sha shidda , hmmm Babana yayi tare da cije haÆ™orashin na gefen dama ya karkace leÉ“unansa sukayi sama , jinjina kai yayi sannan yaci gaba da cewa "ya "ya sha shidda saboda haÉ—ama sai kace wata kaza , dan tun kafin a auro Mero tuni Sahura tayi haihuwarta ta gama...

Mu talakawa ne na abin musali , kaf zuri'armu ba'a taɓa samun mutumin daya mallaki kaza biyar ba , kaf kauyen Ƙarara babu mutane masu talaucinmu , bamu gaji arziƙi ba kuma babu wanda yayi shi , kowa dai yanashan azabar talauci yadda ya kamata ,

     Malam kuwa wutar talauci data isheshi ya rasa inda zai saka ransa saiya fara aikin tsubbanci , kuma sai Allah ya tallafa mishi domin idan yayi aiki kamar yankan wuÆ™a wuyar dai kafin yayi ne kawai , cikin Æ™anÆ™anin lokaci sunansa ya fara ketawa yana zagawa kunnen jama'an duniya , yayin da mutane suka fara kiransa mai gobe da nisa...

      Nanfa harka ta buÉ—e dan Allahn yace masa zama , tun abun bai fita ba har mutane suka fara shigowa daga cikin birni suna zuwa wurinshi , a tsabibincin nasa fa yakai maÆ™ura kuma shekarar arziÆ™in nasa ya tsaya kalmar zama da Allah ya yaddar masa taci gaba da tabbata akanshi....

      Malam fa ya fara tara abun duniya , liÆ™afa taci uban ta da , dan malam ba mutum bane mai rowa dan haka jama'a suka fara saÉ—aÉ—owa zuwa gidanmu cin arziÆ™i , cin nan 3 a yini tou fa idan mutum yazo zaici ya É—inke har yayi guziri , shi yasa gidan namu kullum ya koma kamar wani gidan biki ko suna...

A lokacin da Mero ta samu cikin farko Sahura kuwa tace ina wuta ta jefata , nan ballin asiri ya fara tashi jefe² tahana mahaifiyarmu zaman lafiya , da ta samu ciki sai ya É“are , ciwon yau daban na gobe daban , abun dai babu daÉ—i ,

      Su kuwa malam ba abinda ya damesu da harkar da iyalinsu ke ciki burinsu kawai sudai a kawo musu , kullum matan malam basu da aiki sai wanke alluna , ana haka dai har Allah yasa Mero ta samu cikina , tunda Sahura ta lura Mero tana da ciki taci gaba da wurgago subbancinta , haba ina harta isa ? Allah yace saina zo asiri baya tasiri a wannan lokaci sai hukuncin Allah...

    Har Mero ta haifeni cikin wahala take da musibar rayuwa , tunda na sako Æ™afa duniya dama azababbena aka haifoni , da rana zansha baccina har in gode Allah , amma da zaran an kira sallah magrib na fara kwarara ihu har garin Allah ya waye babu wanda ya isa ya runtsa idonshi kona second a gidan nan saboda kuka na , a haka akayi suna Allah ya cidani da Aliyu , ina wannan masifafen kuka da an kira asubahi kuma zanyi bacci , malam kuwa saida ya rubuce yace abani insha maganin kuka duk ranar da aka bani rubutu kukana sai yafi na jiya , har malam ya haÆ™ura ya daina rubutu ana bani...

    Haka Mero ta haÆ™ura taci gaba da rainona duk wanda ya ganta yasan tana tattare da damuwa , tabi ta soye tayi baÆ™iƙƙirin saboda tsabar rashin kwanciyar hankali , dana fara zama kuwa idan ta zaunar dani zan fashe da wani irin ihu mai firgici wanda dole saita É—aukeni ta goyani , nadai zama fitinanne ta ko wane sashi ,

      Dana fara rai rafe kuma É“arna harta Æ™eta , duk abinda yake na Mero bana É“atawa amma daga ba ita ba duk abinda na gani saina tadashi aiki , Sahura tace iskanci kesa nakeyi É“arnar tunda nasan abun uwata bana É“atawa , da nayi mata É“arna sai tayita dukana maimakon inyi kuka sai inyi ta dariya...

    Abun fa ya fara tayar da kowa hankali , har aka yayeni a nono , iskancina kuma sai abinda yayi gaba , tun ina É—an firiri na , na iya tsakalo fitina saidai idan ban fita ba , masu kawo Æ™ara kuwa haka zasu jero layi , wasu a biyasu wasu kuma a basu haÆ™uri...

    Shekarata 3 Mero ta sake samun ciki , amma har ta haifeshi Allah bai sanar da Sahura ba , tashin hankali wanda tayi ba kaÉ—an ba , amma bata da yanda zatayi dan duk wanda yazo baya komawa sai idan Allah yaso...

     Ranar suna data zagayo aka sakawa jariri suna Muhammad , wanda ake kiranshi da Æ™arami , ku kuma kuna ce masa Baba Æ™arami , haka dai akaci gaba da cakwakiyar rayuwa , har Allah ya kawo wata mace matar wani attajiri malam yayi mata aiki , bayan buÆ™ata ta biya shine ta siyawa malam gida anan cikin garin birnin katsina , a anguwar Æ™ofan marusa , daga nan muka tattaro mukayo birni !

      Shekarar mu biyu da dawowa birni Mero ta ansa kiran mahaliccinta babu jinya haka kuma babu ciwon kai bare na hannu , nasha kuka kamar zan mutu na rashin mahaifiyata , wanda Sahura ko a kwalar rigarta , 

Bayan anyi kwana 3 da rasuwar Mero Sahura ta samu malam ta kitsifa masa ita bata iya zama dani ga iskanci ga rashin kunya ta taɓani ace dan uwata bata raye take azabatar dani , saidai ya raba mana wurin zama ,

Ba tare da nazarin komai ko tunani ba , yace in bar mishi gidanshi dani da ƙarami , haƙuri na bawa malam akan ya bari saiya kamani da laifi , amma fur ya ƙeƙashe idanuwanshi saina bar mishi gida , ina ƙoƙarin barin ɗakin malam Sahura tace sai inzo in tafi da ɗan uwana dan so take gaba ɗaya fitina ta fitar masu daga gida , a lokacin shakarar ƙaramin 2 da wattanni , ni kuma ina da shekara biyar da "yan watanni , haka malam yayi mana korar karnuka , ina kuka na ɗauki ƙarami muka fita daga gidan ,

Ina ɗauke da ƙarami na shiga cikin gari , duk wanda ya ganni ɗauke dashi zaice na mayar da yaron nan bana iya ɗaukarshi , ko sauraron mutane banayi bare na basu ansa , tafiya nakeyi har aka kira magrib , ni kuma a lokacin na isa wata anguwa ita Gambarawa....

    Bakin wani shago na zauna na sauke Æ™arami dake ta zabgaga kukan gajiya da yunwa , bayan na zaunar dashi naje na É—auko buta da wani ya gama alwallah ya ajiye na bashi sauran ruwan daya rage yasha , bayan yasha na matsa wurin mai shagon da yake Æ™oÆ™arin buÉ—ewa ya dawo daga sallah nace Baba da Allah ka taimakamin da sadaÆ™a zan siyawa yaro abinci yaci ,

    Cikin hargowa yace ai sai ka buÉ—e ka É—auka mishi É—an barauniya , dama irinku ne masu sacewa mutane abu idan basa nan , wata irin kwanya yaimin tsakiyar kaina harsai da nayi tunanin kaina ya huje , dariya nayi tare ce masa ka nunamin inda zan É—auka , kuÉ—i ya fiddo daga cikin aljihunshi kwaci ² shege É“arawon banza , kallonshi nayi sannan na duma ma kuÉ—in wawa , kaf kuÉ—in na kwace na ruga na cicciÉ“i karami nabi lunguna ba tare da nasan gari ba , 

       Biyoni yayi da gudu yana a tara É“arowa , Æ™arami kuma sai kuka yakeyi saboda ya wahala , ganin jama'a na ketowa daga hanyoyi da dama yasa na samu wani zauren gida na sake na rufe bakin Æ™arami sautin kukanshi ya daina fita...

     Dube ²n su sukayi basu sameni ba saboda haka suka hakura kowa ya kama gabanshi , saida na tabbatar babu kowa sannan na fito naje na samawa Æ™arami abinci yaci muka bar anguwar Gambarawa a daren na dawo Qerau da zama....

    Haka rayuwa taci gaba da tafiya , ni na saka kaina makarantar allo kuma na samu gidan aiki , gidan aikin suka sakani makarantar boko , haka dai na haÉ—a abu goma da ishirin , ga karatun allo ga boko ga gidan aiki ga rainon Æ™arami ,

    A daddafe dai nayi ta dafa rayuwar kuma ban sake zuwa wurin malam ba kuma daga Qerau zuwa Ƙofar marusa babu wani nisa ,

      Shima Æ™arami daya isa sakawa makaranta boko gidan aiki na suka sakashi , kuma tare dashi mukaci gaba da aikin gidan , daga baya ma suka bamu wurin zama a cikin gidan ,

     Na gama secondry sch Bello ya shigo cikin rayuwata , gidan Æ™awar matar da muke zaune gidanta itace take aikena gidan Æ™awarta gidan kuma a maÆ™otan gidansu Bello ina zuwa idan aka aikeni nan ya ganni ya liÆ™emin , yana zuwa gidan da muke zaune yana yini wani lokaci ma har kwana yakeyi , ya shigeni sosai abota mai girma ,

   Makarantar gaba da secondry tare da Bello muka fara nidai nayi karatu kuma na fito da sakamo mai kyau yayin da Bello ya faÉ—a harkar mata , a lokacin kuma Æ™arami yana secondry sch aji biyar , bayan na gama degree aka fara neman min aiki , yayin da ni kuma nake neman Æ™ara faÉ—aÉ—a ilimin nawa...

       Har wannan lokaci banje wurin malam ba , kuma malam bai nemeni ba ni kuma naÆ™i nemansa dan dama ni nasan inda yake , saida naci gaba da karatu na , na faÉ—a harkar wasan caca daga nan duk lissafi ya jagulemin , dan duk wannan kangarar da nayi a baya tana da dalilinta kuma a gaba zaki ji ta , dan bayan na baro gida naÉ—an samu natsuwa , amma shigowar Bello rayuwata yasa na ida Æ™wacewa......