Breaking News

KWARATA 37

🅿 ------ 37

       Gayu mutanen Allah shine abinda na furta a lokacin da naga shagalin dake cikin food flarks , murmushin jin daÉ—i nayi wai duk ni É—aya zanji daÉ—i na , miÆ™ewa nayi tare da komawa da baya cikin farin ciki na faÉ—a saman katifa zanci daÉ—i yau zanyi kalaci da farfesu , ga doya ga farfesun "yan ciki , wannan daÉ—i da hawa tsaunin rayuwa har haka ? ÆŠaga Æ™afafuwana nayi sama ina musu shangululu tare da rumgume duka hannaye na a Æ™irjina cikin farin ciki nace wallahi madarar ma duka zan juyeta...


      Wani irin ihun farin ciki na kurma wanda har na waje saida sukaji ni , da sauri na sauko daga saman katifata naci gaba da aiki dan gani nake idan na tsaya wanke baki a iya shigowa aga kamar na gama a fita dasu ,

   ina ci ina kaÉ—ai kai tare da addu'ar rayuwa ta É—auremin da irin wannan daddaÉ—an kalaci , naci komai kuma komai nasha nayi hamdala ga ubangiji da ya bani aron lumfashi ya bani baki da ciki da lafiya kuma ya ruboto min wannan babban rabo da alÆ™amin kudarar shi...

      Ina gamawa na tattara komai na fitar palo , labulayen dana ciro na É—aura na mayar dasu mazauninsu na gyara , saman katifa na dawo tunda dama nayi wanka cike da farin ciki na lumshe idona na tafi duniyar bacci.........!

    Tashin hankali a gidan su Sultana , cike da farin ciki Baba ya shigo gida ya dawo da kuÉ—in shi cike da aljihu domin a daren jiya shi ya lashe maÆ™udan kukaÉ—aÉ—en da aka zuwa a wasan caca , Æ™ofar É—akin Sultana ya nufa kai tsaye yana cewa Mamana kin ganni sai yanzu ?

      Kowa yayi cirko² domin "yan gidansu Sultana tun jiya suka dawo da labarin É“atanta , kowa dai yana cikin jimami da tashin hankali , Baba kuwa bayan ya shiga É—aki shiru² bai fito ba dan a tunaninshi Uwar masu gida tana bayi ne...

     Zama yayi har ya gode Allah , komi Uwar masu gida takeyi ai ta isa ta gama ta fito gajiya yayi da zama ya fito tsakar gida yana cewa ina Mamana taje ne ? Shiru kowa yayi ya kasa magana , bin kowa yayi da kallo yanayin fuskar su ta nuna akwai wani abu daya faru , bayan ya gama kallon kowa yayi magana cikin karyewar zuciya cewa ina Mamana...... Take ? Ya Æ™arasa maganar yana mai bin bango ya sulale ya zauna Æ™asa a hankali ,

     Maman Fa'iza ce tace mu saka Sultana a addu'a domin yanzu ba abinda take buÆ™ata sai addu'armu mu dage da roÆ™on Allah har ubangiji ya bayyana mana ita domin Sultana dai ta É“ata , lokaci guda zufa ta É“arkewa Baba ya tsurama wuri guda ido kamar mage ta É—ana tarko , bayan wani lokaci kuma yace haka zakimin Mamana ? Haka mukayi dake ? Wannan shine sakamakon alÆ™awarin ? Ina kika tafi ne ? Inajin babu jimawa mukayi magana dake baza ki taÉ“a tafiya ki barni ba , shine kika tafi kika barni..... ? 😭 hawaye ya gangaro mishi daga cikin idonshi , daga nan yayi na wani mawaÆ™i da yace ayye mata a Æ™ame Æ™am , tou Baba shima ya Æ™ame kamar wayar da tayi hucking....

Tunda na kwanta bacci babu abinda ya dameni kuma bana wani tunanin komai haka kuma banga komai ba a cikin mafarki na , bacci na nakeyi cikin natsuwa da kwanciyar hankali , sai da aka kira azahar na farka nayi sallah bayan na gama na watsa ruwa na koma nayi kwanciyata amma ba bacci nake ba !

     Gidan shiru kamar babu kowa ciki sai Æ™arar iska irin mai tahowa da Æ™asa , a hankali sanyi ya fara saukowa irin mai shiga Æ™ashin nan , zuwa bayan la'asar sanyi ya sauko sosai wanda yasa mutane suka fara saka rigunan sanyi,

     Ni kuma da banda rigar sanyi ina cikin bargo na duÆ™unÆ™une , ga azabar yunwa da nakeji na rasa inda zan saka rayuwata , har akayi magrif babu wani labarin abincin rana bare in saka ran na dare zaizo , nasha ruwa har nayi fitsari bansan adadi ba , tun ina daurewa har na fara Allah ya isa a zuciyata...

      Tunda nayi magrif ban tashi daga inda nayi sallah ba ina zaune na zabga tagumi kuma ni ba addu'a nakeyi ba , ina cikin wannan tunani naji Æ™arar buÉ—e get murmushin jin daÉ—i nayi nasan Dikko ne kuma yazo da abinci , tabbas abinci yazo ya kawomin , cike da murna na leÆ™a ta window kuma wallahi shiÉ—in ne , sanye da tsadajjiyar baÆ™ar rigar sanyi mai kyan gaske da burgewa tana da farin zif daga gaba , an zageye wuyan rigar da farin ado amma ba irin na mata ba ina ganin dibara ce dan kar rigar ta lalace daga saman wuya , sanye da shuÉ—in wando da takalmi baÆ™i amma ba rufaffu bane maÉ—auri gare su kamar sandals , hannun rigar ya É—an naÉ—eshi zuwa guiwar hannu , kanshi babu hula kuma fa gaskiya yayi kyau dake baida Æ™iba ko kaÉ—an amma yana da tsayi daidai burgewa bana zarce misali ba...

     Al ' Ameen ke É—auke da kulolin abinci shi kuma waya yakeyi , ina ganin sun tun karo Æ™ofar shigowa palon nayi sauri na kowa saman abin sallah na kalli gabas ,

      Suna shigowa shi Al ' Ameen ya kunna musu kallo , maimakon ya kawomin abinci sai kawai suka zauna sukaci gaba da kallon kwallo , har akayi isha'e suna zaune kamar asara suna kallon kwallo , inajin maganar Dikko lokacin daya shiga É—aki mai kallon wanda nake ciki yana cewa bari inyi sallah dai , tsoki nayi tare da cewa andai ji kunya sallah a gida , nima tashi nayi nai sallah dan ina da alwallah ...

     Har na gama sallah banji Dikko ya fito ba , kuma naji palon ya fara cika da maza ga dukkan alamu kila gidan dai matattara ce ta maza , tunani na farayi karfa su cinye abinci ban samu ba , tashi nayi na fita É—an madaidaicin palon na zauna ina jiran fitowar Dikko idan ya manta da ina nan tou ya ganni ya gane ina nan ,

     Tunda na zauna Æ™arar motoci ke shigowa , hayaniyar sai Æ™ara sama takeyi maza surutu ga magana babu natsuwa , nafa daÉ—e ina zaman jiran Dikko bai fito ba , kuma bana so na leÆ™a babban palon bansan ko su waye a wurin ba , na haÆ™ura da niyar komawa É—akin da aka ajiyeni naji dai bazan iya kwana banci komai ba yunwa nakeji kamar zan mutu wallahi , dawowa nayi kai tsaye na shiga É—akin ,

     Da sauri ya kallo Æ™ofar dan yaga waye yake shigowa yana zaune saman abin sallah , murmushi yayi ganina tare da cewa An mata miye ? ÆŠan suÉ“aro baki nayi ina wasa da yatsun hannuna nace dama , sai kuma nayi shiru , É—auke kallonshi yayi daga gareni yace dama me ? Shiru nayi na kasa magana , shima bai sake magana ba yaci gaba da latsa counter , naci uwar mintuna sha biyar Dikko bai sake kallona ba kuma bai sake magana ba ,

     Saida ya gama abinda yake ya É—auke abin sallar daga inda yayi sallah ya É—ora gefen gado , zuwa yayi zai wuce ya fita dan yayi kamar ma babu ni a wurin ,

     Ya kusa fita nace yunwa nakeji , yi yayi kamar baiji abinda nace ba ya fice abunshi , biyoshi nayi a lokacin har ya kusa fita daga palon  ya shiga babban palon , nace da Allah nace maka yunwa nakeji nayi maganar a tsiwace , naji ya faÉ—a tare dayin gaba abunshi ,

      Tsoki nayi cikin É“acin rai na koma É—aki ina gunguni , shi kuma daya koma kallonshi yaci gaba dayi , sai ihu sukeyi "yan iska kamar mahaukata , amma bana tunanin Dikko yana wurin dan har yanzu ban jiyo maganarshi ba , duk wanda aka ci su sai kuji hayani ta Æ™ara sama , sai gaddama da magana cikin faÉ—a² ,

       Sai yanzu naji dariyar Dikko yana shigowa cewa ko gobe da fansar kura saidai garin da babu awaki , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya nace ashe kaima ka iya karin magana ? A dai² lokacin daya shigo yana dariya ,

     ÆŠaure fuska nayi kamar ina cikin yanayi damuwa , ko kallonshi banyi ba ya É“atamin rai ni zai zubowa abinci a gaban bainannasi hmm , ga abinci ya faÉ—i maganar a daidai lokacin da yake ajiyewa a gabana , kauda kaina nayi na tura abincin na Æ™oshi ...

    Murmushi yayi tare da É—aukar abinci zai fita , nace kai nifa wasa nakeyi bani nan nayi maganar tare da nuna mishi ya maidoshi gabana , banza yayi ya fice daga É—akin da sauri na tashi nabi bayanshi amma kafin in fito harya fice ya koma cikin abokanshi yana dariyar mugunta , a ranshi yace daga yau sai kiyi hankali ni ban iya wasa ba kuma ba'amin wasa ,

Wannan rana saidai na kwana da yunwa nasha kukana har bacci ya É—aukeni bansan lokacin da suka tafi ba , 

     Koda safe dakel nayi sallah saboda yunwa duk jikina ciwo yakeyi kamar nayi aikin Æ™arfi , bayan na gama sallah na daddafa nayi wanka , na canja kaya sannan na koma bacci , 

     Yauma da asibiti ya fara , ya lallashi matarshi kamar yanda ya saba , yau ya samu ya lallaÉ“ata tasha ruwan tea , ya kuma sake tambayarta damuwarta dai tayi masa zurfin ciki har yanzu , dan haka bai wani damu ba ya wuto wurina ,

      Yau shi É—aya yazo babu Al ' Ameen kuma kai tsaye ya shigo É—akin , bayan ya ajiye kayan da yazo dasu ya kunna fitila yana cewa anya ma kinyi sallah ? Tashi ya faÉ—i maganar tare da yaye bargon dana lulluÉ“e , juyawa nayi na kifa kaina saman katifa saboda haushi ya bani jiya sosai ,

        Yauma bakijin yunwa bara in tafi , ya faÉ—i maganar tare da É—aukar kwandon , cikin fushi nace abinci banza gare ka , ko an faÉ—a maka yunwarshi nakeyi muma gidanmu sau 3 a rana akeci ka tafi na Æ™oshi nasan yunwa baza ta kasheni ba an girma ba'asan an girma ba ,

      Dariya yayi tare da zama gefen katifa yace wai nima irin wasan jiya nake miki amma ke naji kalaman naki zafi garesu ai kema da sai kiyi shiru kamar yanda nayi shiru jiya , sai kace dai kina jirana ? Cike da jin haushi na tashi zaune ina cewa jiranka nakeyi kamar yadda ka zanemin rayuwata haka zan zane taka rayuwar babu gudu babu ja da baya ba abinda ke cikin zuciyata face É—aukar fansa akan ka ,

    Murmushi yayi tare da gyara zamanshi sannan ya É—aure fuskarshi babu wasa a tare da ita ya fiddo siffofinshi masu tayar da tsikar jiki da saka fargaba yace ke har gobe yarinya ce , amma ki sani ya nuna ni tare da ci gaba da cewa wannan tsarin tamkar sautin radio na ne , na Æ™arashi na rageshi yadda nake so , kiyi haÆ™uri burina kaÉ—an ne amma sanin ya kamata na yana da Æ™arfi , ban iya ba kece kika koyamin kinsa na zama kamar wani sakarai sai biye miki nake ina Æ™ananan maganganu kamar mace , dakamin tsawa yayi tare da zaro idanuwa sannan ya sassauta maganar shi zuwa sauti mai kama da raÉ—a yace ki kiyayeni kafin na baki hukunci a karo na biyu , azabar yau sai tafi ta jiya zafi , ina nan kuma namijin ne .... 🤫 ya Æ™arasa maganar tare da É—ora É—an yatsanshi a saman bakinshi yace shitt ya rufe maganar da fiddo idanuwanshi da suka É—anyi ja...

     Jiki a sanyaye na koma na kwanta , ba tare daya kalleni ba yace tashi muyi break , da sauri na tashi naje na wanko bakina da fuskata nazo na zauna kusa dashi cikin ladabi , shine da kanshi ya zuba komai amma tea É—in a kofi É—aya ya haÉ—a kuma da kofi É—ayan mukayi amfani yana sha ya bani insha in miÆ™a mishi , cokali ma É—aya mukayi amfani dashi , 

       Ba wani damuwa a tare dashi ko kunya ko irin yaji babu daÉ—i haka dai , tsakaninshi da Allah hankalinshi a natse yake , har muka gama da kanshi ya tattara komai ya mayar a kwandon ya É—auka kwandon ya fita , ya daÉ—e sannan ya dawo ya kwanta a gefen katifa ,

     Wayarshi ya ciro yace zo kiga in nuna miki "yan uwana , matsawa nayi kusa dashi amma ni ba kwanciya nayi ba zama nayi , É—ago kanshi yayi tare da bani wayar na riÆ™e a hannuna yana wuce hotuna , wannan itace wance wannan kaza ce dad ina ne kinga momy kinga wannan itace nake bi mawa , tana aure a gari kaza , haka dai yayi ta wucewa har yazo kan Sadiya yace wannan kuma matata ce....

      Kai kalmar namiji yace matata kalmar tana da girma da matsayi , matata saida na maimaita a zuciyata sannan nace ban Æ™aunarta har abadan duniya na faÉ—a a zuciyata , kallona Dikko yayi tare da cewa tayi kyau ko ? Ban sani ba nace masa , baiyi murmushi ba kuma baiyi dariya ba yace kada Allah yasa ki sani "yar rainin hankali ,

      Cike da É“acin rai nace dakai da matarka duk kune "yan rainin hankali munafikai dukanku , tsareni yayi da ido tare da cewa kishi ko ? Ya Æ™arasa maganar yana nunani da san yayi murmushi amma ya haÉ—eshi , tsoki nayi tare da cewa hmmm Allah ya sawaÆ™e min niko waye zanji kishin a cikinku kai ne ko ita ?

     MiÆ™ewa yayi tare da cewa tunda baki son na tayaki fira zan tafi , bazan dawo anjima ba Al ' Ameen zai kawo miki abinci , idan Allah ya kaimu gobe lafiya ki shirya da wuri dan bana san tafiyar rana , yana faÉ—in haka yayi gaba abunshi....

       Abinci rana da dare duk Al ' Ameen ya kawo min , yau babu wanda yazo kallon kwallo ni É—aya a gida bayan naci nasha na koma na kwanta tare da addu'ar Allah ya kaimu gobe lafiya !

      Da safe tun kafin in tashi bacci Dikko yazo , shi ya tasheni tare da ajiye uniform a gefen kati yace maza jiranki nakeyi , kallon kayan nayi sannan na kalli Dikko da yasha manyan kaya hada babbar riga hular kanshi kuwa sai sheÆ™i takeyi saboda sabinta ko wanki ne ? Koma dai miye sai ka kalli kanka a ciki kayi sakace , kallon Æ™afarshi nayi nan ma komai yaji gemu ma dai yasha gyara yana nan dai da jan hankali da yakeyi , gaskiya Dikko haÉ—aÉ—É—en namiji ne mai tafiya daidai da zamani , ga kyau ya gayu uwa uba iya saka sutura , Dikko nada burgewa ...

      Katse min tunani yayi da cewa kin tsaya kina kallona ! Kiyi maza jiranki nakeyi , yana faÉ—i maganar yabar É—akin , cikin kuka na nufi toilet nayo wanka sannan nayo alwalla nazo na fara gafatar da sallah asuba da banyi ba akan lokaci , bayan na gama na shirya cikin kayan makaranta ina kallon kaina a madubi na fashe da wani irin kuka wanda har sai da gaban Dikko ya faÉ—i...

       Da sauri ya shigo É—akin fuskarshi É—auke da damuwa yace a mota zakiyi kalaci , shi a tunaninshi yunwa nakeji , cikin kuka nace ni wallahi bana san makaranta haba Yaya Dikko me yasa zakamin haka abin kunya a ganin a makatanta yanzu , 

       Wani irin kallon rainin hankali yayi min daga sama zuwa tsakiya ta yace lallai yarinyar nan kin rainani nine Yayan naki.... ? Baki da hankali ma da Allah ni wuce mu tafi munatane na jirana , hannu na É—ora saman kai ina cewa dan girman Allah ka kyaleni wallahi bazan sake ba , cikin kwantar da murya yace muje tun kafin kiji babu daÉ—i , 




😭 hijabi na saka nabar kallabin a katifa nayi waje , abun kunya shi ya ɗaukomin kallabin wai hada jakkar makaranta saboda ci baya , waini zan koma makaranta , ina gaba yana bayana har cikin mota , ni kaɗai na shiga baya ya wurgomin jakar da kallabina ya rufe ƙofar ya shiga gaba , Al ' Ameen yaja muka fita daga gidan , kuka naci gaba dayi ina ma katsina kallon ƙauna , tafiya akeyi sosai dan Al ' Ameen yakai mota maleji wurin gudu , kuka na ya ƙaru lokacin da naga an ibi hanya tafiya da gaske babu fashi....... !