Breaking News

KWARATA 50

🅿 ------ 50

         Cike da farin ciki ya juyo , amma me ? Sai yaga Jiddah tsaye ta zarge hannuwan ta , wayoyinshi ya É—auka sannan ya tunkaro ta dan ta hanyar da zaibi ya wuce ta tsaya , cike da kissa tace haba Yaya daga dawowa kuma ina zakaje haka da daren nan ? Inda raina yake so zanje , haba Yaya gaskiya haka an shiga haƙƙina , kallon raini wayau yayi mata tare da cewa a haba ? Umm gaskiya
ina so mu kwanta mu huta duk gajiyar jirgi tana damuna , ta ƙarasa maganar tare da san kwanciya a jikinshi , zamewa yayi da sauri ya karkata ya fice daga ɗakin.

       Ni kuma bayan nayi sallah isha'e tunanin duniya yazo ya tokaremin zuciya , ikon Allah wato ita rayuwa haka take , Mamy bata taÉ“a tunanin mutuwa ba kwata ² a "yan wa'annen lokuta , hawaye ya gangaromin daga cikin idona nace shikenan anyi zamaninta an gama , duk saÉ“awa ubangiji da tayi saboda samun duniya kuma Allahn ya yaddar mata ta samu kuma ta tara , amma ta tafi ta barshi domin ansa kiran mahaliccin ta , 

      Me ake ma haÉ—ama a duniyar ? Bayan babu wanda yazo dashi kuma babu wanda zai tafi da komai , anan aka samu kuma anan za'a tafi a barshi , haba mata meke ruÉ—armu a cikin duniya ?

    "Yar uwa ko kunyi yar jejeniya da mala'ikan mutuwa ga lokacin da zaizo miki ? To kisani mutuwa bata sallama bata jira sai kin gama sharholiyarki wallahi zata iya riskarki a duk yanayin da kike ciki , ba ruwanta da kina aikata alheri ko akasin haka , ya ubangiji ka karÉ“i rayuwarmu muna masu aikata alkhairi ka sada mu da aljannar ka dan darajar fiyayyen halitta S. A. W , am3n.

    Gadai Mamy nan an tafi neman duniyar amma an haÉ—u da mala'ekan mutuwa a hanya , kai ubangiji kasa muyi kyakkyawan Æ™arshe , ko waye ma ya haÉ—a Mamy da wannan ibilishin ?

      Ƙarar wayata naji a gefena a firgice na juya inda take na miÆ™a hannuna na É—auko , lambar Dikko naga ta bayyana a saman screen in wayata , ajiyar zuciya na sauke da sauri na É—auki wayar tare da miÆ™ewa tsaye na karata a kunnena ,

     Sai sauke wani irin wahaltaccen numfashi nakeyi mai nuni da nasha wahala , cikin muryarshi maisa natsuwa yace har kin fara bacci ne ? Kukana ya Æ™ara kwacewa ban bashi ansar tambayar shi ba nace shine ka tafi ka barni.... ?

       Murmushi yayi mai sauti cikin murya mai kashe jiki yace in dawo ne ? Da sauri nace Eh , dariyar mugunta yayi yace An mata taji a jikinta tou fito gani nan Æ™ofar gida , da gaske ? Na tambayeshi sai kin fito zaki tabbatar da haka , da sauri ya ajiye wayata nayi waje da gudu ,

    Dikko yana tsaye ya jingina da mota ya rungume hannayenshi a guje na isa inda yake tsaye da niyar in rungumeshi , a wayance ya matsa daga saitina ni kuma na É—an sassauta gudu na saboda na iso ina ganin ya kauce nima na basar na rumgumi mota ,

      Kauda kanshi yayi gefe tare da cewa ya kike ? Nima juya mishi baya nayi ina wasa da Æ™asa da babban É—an yatsana na Æ™afa nace aini dana san kaine ma da ban fito ba , buÉ—e mota yayi ya shiga yana cewa ai dan nasan dama idan nine baza ki fito ba shi yasa nace miki ga Dikkonki ya dawo , ya Æ™arasa maganar a daidai lokacin da yake zama a mota , 

      Juyowa nayi dan a tunani na tafiya zaiyi , murmushi yayi yace ba tafiya zanyi ba banajin daÉ—in tsayuwar ne shigo mu tafi , da sauri na zagaya na buÉ—e mota na kame a gaba , ina rufe murfin motar ya taka motar muka shiga gidan dawakan shi ,

      Kusa da motar daya bani yayi parking , ajiyar zuciya ya sauke tare da riÆ™e sitiyarin da duka hannayen shi biyu yayi miÆ™a cikin yanayin gajiya tare dayin hamma yace An mata na gaji wallahi yayi maganar cikin murya mai ladaftar da zuciya ,

        Murmushi nayi amma banyi magana ba , dan idan inajin muryar Dikko sai inji tawa wata iri shi yasa ban cika magana a gabanshi ba , wayarshi ke ringing dan haka ya É—auketa daga gefenshi daya ajiye yana cewa tou fa , karkace kaina nayi ina kallon fuskar shi yayin da hasken wayar ya haskaka fuskarshi dan duba mai kiranshi waya ,

      ÆŠan kallo yayi mai kyau yayin da idanuwan shi ke duba daga saman wayar zuwa Æ™asa , zai É—auka yace nifa bana san kallo da yawa , ki daina kallona haka nan tunda bakya so na , a dai² lokacin daya É—auki wayar yana cewa inajin ka ,

      Tou haka yace kuma ? A , a gaskiya bana kusa kawai kuje idan na dawo Ashiru zai tattaro minsu , ba komai fa kawai kaje abunka , to yayi kyau , ya kashe wayarshi ,

    Bayan ya gama wayar ya juyo ya fuskance ni sosai yace An mata mi yasa kika bar mota tayi datti bakya hawanta ? Nace haka nan , hmm tunda bakyasan Dikko motar da ya baki ma bata burgeki ko ? Nace tana burgeni mana kuma ai nahau ta ma , Dikko yace haba An mata ai da kin hau wannan motar da naji a jikina , zansa a wanketa a daren nan ko baki so na ki hau motar nan don Allah inji daÉ—i kuma ko bakida inda zakije gobe kiÉ—an hau ta ,

    Nace tou , yace yawwa ngode sosai , bayan wani lokaci kuma ya sake kallona yace An mata wai dan Allah mi yasa kike da kunne Æ™ashi ? Mi yasa bakyajin magana ? Nace me kuma nayi yanzu ? Bama kisan abinda kikayi ba ko ? Nace Eh , jinjina kanshi yayi yace yanzu ina amfanin irin rayuwar da kika koyama kanki don Allah ? Kullum baki da aiki sai É—aukar tsiraicin mutane ,

     Idan an taroki nan sai ki koma nan kina rayuwa kamar baki da kwalwa a kanki , shiru nayi banyi magana ba , cikin É“acin rai yace ki kiyayeni ranar da nima zan miki tsirara in miki irin abinda kike ma mutane , bana san É“acin raina akan ki saboda fushi na baida kyau idan har nace zanyi miki hukunci dai² da irin abinda kike aikatawa lafiyayen duka É—aya zan miki ki mutu , cike da É“acin rai nace tou ni yanzu waye kuma nayi ma vidio ,

         Æ˜anÆ™ance idanuwa yayi yace Baban Mardiyya dama shine baÆ™in cikin da kike cewa zaki dasa mata a zuciya ? Ki bari bana so , nace tou , sake maimaitawa yayi cewa bana so ׳ idan kuma kuma kika sake zakiji babu daÉ—i , nace tou , 

      Hararata yayi cikin salon so , yace to me kuma akayi miki kikayi kuka naga fuskarki duk sai a hankali , ban bashi ansa ba na canja maganar da tambayarshi wanda ya faÉ—a mishi nayi ma Baban Mardiyya vidio ? Cikin lallausar murya yace babu ruwanki da wanda ya faÉ—amin idan nace bana san abu kawai ki bari idan baki so mu É“ata , a É—an zuciye nace tunda baza ka faÉ—amin ba bari in tafiyata , hannuna ya riÆ™o yace yi haÆ™uri An mata , tou faÉ—amin , yace ni bana san É“acin ranki Al 'Ameen ne ya faÉ—amin , gaskiya An mata Al ' Ameen bai jitu dake ba kullum burinshi ya nemo aibunki ya faÉ—a a gidanmu duk da kince bakya so na ina so ki zama mai mutunci a idon "yan uwana da kuma iyayena kinga idan aka tashi bada labari cewa za'ayi Æ™awar Dikko bata da hali mai kyau ni kuma kinga ai bazanji daÉ—i ba ko ? A kunyace nace Eh , yace tou da Allah ki baryin abu mara kyau duk ki barbaÉ—awa "yan baÆ™in ciki yaji a ido ya Æ™arasa maganar yana kashe min ido É—aya na dama , nace tou ,

    Tada motar yayi yana cewa bari in ajiyeki haka nan kar ace kin É“ace , a dai² lokacin daya fara tafiya a hankali , yau da natsuwa yakeyin tuÆ™i yana Æ™ara jamin kunne na daina shiga sabgar kowa nayi rayuwata ni É—aya idan banji bari ba kuma zanji hoho a jikina , a Æ™ofar gida ya ajiyeni yana cemin idan Allah ya kaimu gobe zai dawo , nace tou Allah ya kaimu ya kuma hutar da gajiya , ya ansa da amin ni kuma nayi cikin gida da gudu , murmushi yayi ya wuce cikin farin ciki ,

Yau zuciyarshi ta ƙara tabbatar mishi da akwai soyayyar shi a zuciyar An mata tunda har tasan idan ya daɗe bai zo ba idan yazo zata zo da gudu ta rumgume shi , kuma yace ko tana so ya dawo tace Eh , babu abinda ya kawo haka idan ba soyayya ba , yau kam yana cikin farin ciki.

      Washe gari sai 9:30am na fita daga gida domin zuwa wurin jana'izar Aunty Mamy dan naji ance 10:00am za'ayi mata sallah domin kaita gidanta na gaskiya , doguwar hijabi nasa mai hannu ta saukar min har Æ™asa mai ruwan jinin kare , dake ina da haske sosai sai hijabin ta matuÆ™ar martabamin fuskata , babu abinda na shafa domin yau ranar ta jimami ce , makullin mota na É—auka nayi gaba abuna ,

      Ina fita naga su Amisty suma sunsha nasu hijaben cikin mota suna tahowa , ganin zan shiga gidan dokuna yasa Amisty tayi parking dan ganin abinda zanyi , a natse na shiga da jakata a hannuna saboda riÆ™on wayoyin zaimin yawa a hannu ,

       A gidan na iske Dikko da kayan training jikinshi ya cire takalma rufaffi ya jiye a gefenshi ya naÉ—e kafafuwan wandonshi , silifas ne a Æ™afarshi É—orowo { Yellow } masha Allah shine abinda na furta lokacin da na kalli Æ™afarshi , hutu dajin daÉ—i ya tabbata a gareta har wani hurhurun haske takeyi tsabar tasha madara ta Æ™oshi "yar gayun Æ™afa da ko mai ba'a shafa mata sabar hutawa , ga wani gargasa ya sauko saman Æ™waurinshi "yan yatsunshi masu kyau dan dani keda Æ™afafuwan shi babu abinda zaijamin saka wasu takalmi idan ba irin silifas in daya saka a Æ™afarshi ba domin yafa burge ,

       Yana gani na ya tashi tsaye ya tare da É—auko takalman daya ajiye a gefenshi ya tun karo inda nake yana cewa ina zaki tunda asuba haka ? Nace rasuwa akayi , Allahu Akbar Allah Allah ya sawaÆ™e , nace ba rashin lafiya ba mutuwa , yace Ey ai na sani ina nema ma ahalin gawar sauÆ™i ne , Allah ya kiyaye hanya nace amin , biyoni yayi bai sake magana ba shima ya nufi wurin motarshi ya buÉ—e but in mota ya watsa takalman ya rufe ya shiga motarshi nima na shiga wacce ya bani wanda yau itace ranar farko da zan fita da ita ,

      Tasha wanki tayi kalar É—aukar hankali , saida na shiga harna sauko daga inda na ajiyeta shima ya sauko yana cewa mintuna 15 na baki ki dawo , tsayawa nayi nace ya kuma minti 15 sai kace kai ka aikeni ? Ban aikeki ba amma wallahi kika wuce lokacin da nace saina É“ata miki rai za'a faÉ—amin lokacin da kika dawo ai , haba wai mi yasa kake yin haka ne ? Ki wuce lokacin da nace miki sai kiga dalili , cikin hayani nace aure na kakeyi da zaka tsaramin yadda zanyi rayuwata ne ?

Murmushi yayi ba tare daya kalleni ba yace ai da ina aurenki babu abinda zaisa na barki kije gaisuwar wacce aka kwakwale ma ido tirr ya ɓata baki tare da ficewa ya barni cikin mota kamar sakarai.

        Da sauri na kalli agogo naga 10:19am , kenan zan dawo gida 10:34 ? Gashi kuma har naci minti 1 , ina da sauran minti 14 yaushe naje har nayi musu ta'aziyya na dawo ? Tsoki nayi kamar kar naje wata zuciyar tace kije kawai kina É“ata lokaci ,

        Da gudu na fito daga gidan kamar zan tashi sama , su Amisty suka rufowa motar baya dan a tunaninsu Dikko ne a ciki , lokacin da suka fito bakin titi tuni na É“ace musu ko Æ™urata basa gani , hanyar da motar tabi ta wuce suka gaza gano ta ina motar tabi ta wuce ,

      Da nasan haka hawan motar nan zai jawomin tashin hankali wallahi da ban hauta ba , ni kuma na hauta ne kawai dan Dikko yayi farin ciki saboda tayi wata huÉ—u da "yan kwanaki da bani ita amma ban taÉ“a hawanta na fita sai yau ,

      Ina isa Æ™ofar soro har an dawo daga kai Mamy dandazon mutane kamar Æ™asa gaskiya Mamy tayi jama'a a hankali na shiga mutane suka riÆ™a darewa suna bani hanya duk wanda ya kauce saiya bi motar da kallo kowa ya Æ™agara yaga Dikko ya fito dan nace muku lokacin daya siyo motar anyi ihunta a gari duk garin katsina wannan motar Dikko kaÉ—ai keda ita ,

      Daga Qerau zuwa Æ™ofar soro minti biyu kacal ya kaini shima dan nabi a hankali dan motar tana da tafiya sosai , nabar gida 10:20 , na iso Æ™ofar soro 10:22 harda parking da nayi , manyan mutane suka fara yayyaÉ“e motar dan cikawa Dikko sheda ba'a iya gane waye a motar saboda gilashin motar duhu gareshi , wa za'a gani ta fito daga motar ? ÆŠiyar É—an caca ,

     Tunda na fito kallo ya koma sama a dai² lokacin dasu Amisty suka iso , banbi takan kowa ba na É—auki jakata na wuce jama'a suka bini da kallo yayin da surutu ya fara tashi Æ™asa² danni taron mutane baya hanani tafiya kuma bai ruÉ—ani bai firgitani haka kuma yawansu basa gigitani kuma banayin tafiya inji kamar zan harÉ—e na faÉ—i ,saida nakai gaf da zan shiga gidan Mamy naga Bello , kallona yayi Æ™asa da sama yace wai Sultana ce haka bakya ko gane mutane ? Murmushi nayi tare da cewa ya za'ayi lafiya ta kasa gane mai bata damuwa ? Magana ce na faÉ—a masa ina faÉ—in haka na shige abuna na barshi da dogon nazari ,

         Gidan mutuwar sai koke ² akeyi yayin da tabarmin zamar gaisuwar suka rarraba kashi ² , dangin Mamy da tasu , sai dangin mijinta makota sai kuma wasu lafiyayun karuwai suma sunyi nasu mazauni , ahalinta na farawa ta'aziyya sannan "ya "yanta , sai dangin mijinta , ko inda karuwan suke ban kalla na miÆ™e zan fita wata mata tacemin nan zaki zauna ke ?

     A dai² lokacin dasu Amisty suka shigo gidan , miÆ™ewa nayi banyi mata magana ba , tace ke Sultana take ko wa ? Ta tambaya , aka ce mata Sultana , tace nan ne mazaunin mu , juyawa nayi da niyar feÆ™e mata uwa saidai banda isashshen lokaci dan ina so nayiwa mijin Mamy ta'aziyya , ina Æ™oÆ™arin fita matar ta biyoni ta cakumoni ta baya tana cewa akace ina zakije ? Baki ga inda karuwai suke zaman gaisuwar su ba ? Ban mata magana ba na fiddo wayata daga cikin jakata nace ki duba zaki ga an rubuta Sultana itace lambar wayata ,

       Kallona tayi sosai kuma kome tayi tunani Oho sai ta sakarmin hijabi ba tare data anshi wayar ba , É—an gajeren murmushi nayi da gefen bakina na juya na fito ba tare dana sake mata magana ba , a Æ™ofar gida nayi ma mijin Mamy ta'aziyya da "ya "yanta maza Bello kuma sai kallona yake , murmushi nayi mishi na miÆ™e shima ban mishi magana ba ,

       Tunda na fito daga barandar Æ™ofar gidan Mamy ake nunani nice nazo a motar Dikko ,  wasu kuma na cewa ni karuwa ce amma meya haÉ—ashi dani bayan baya harkar mata , wasu kuma na cewa É—iyar É—an cacar nan ne shege mashayin giya ya haifo wannan kyakkyawar , wani yace ai yarinyar shegiya ce tana burgeni domin tanayin karuwancin cikin tako ne , kowa dai da abinda yake faÉ—a akaina abundai babu daÉ—in saurare ,

        Murmushi mai ciwo nayi yayin dana tunkari mota ta , wato shi karuwanci babban tambari ne da baya gogewa har "ya "ya da jikoki kayi Æ™oÆ™ari ka zama na gari domin gori akan karuwanci ciwo gareshi yau mutane da sun san zasu taÉ“ani su kwana lafiya inajin dasai sunci ubana kafin na fito , mota na shiga na karce duk wanda bai ga zuwa na saida yaga fita ta ,

      Wuta ² na iso anguwarmu , a Æ™ofar gida naga motar shi , lokacin 10:33am kai tsaye inda na É—auko motar na maida ta , lokacin dana fito ban sameshi ba kenan yazo da kanshi yaga lokacin da zan dawo ? Da sauri na wuce cikin gida dan inada abinda zanyi ,

       Wuri É—aya naje da mota amma yau gari magana ta kawai akeyi wata karuwa take tare da É—an gwamna ta gama dashi ta tsafeshi har ya bata motar daya siyo ta miliyoyin kuÉ—i , duk inda ka saÆ™a a gari Sultana É—iyar É—an caca kafin wani lokaci kuma hotuna na sun fara yawo a social media da motar dana hau É—iyar É—an cacan da yafi ko wane É—an caca sa'ar rayuwa ,

      Al ' Ameen kuwa tuni yaje ya samu mahaifiyar Dikko ya faÉ—a mata halin da ake ciki dan yaga Dady yayi sanyi , Momy kuwa tayi zafi har ta wuce tafasashshen ruwa , matar Dikko data zo gaisheta itama ta cika ta kawo wuya , tace ma Al ' Ameen ya bari Dikko ya tafi a kamo Sultana zata Æ™agi azabar da zata bata , Al ' Ameen yace ai ko yanzu ina iya kawota , Momy tace kudai bari yabar katsina dan koni baya so kamar yadda yake san mayyar yarinyar nan ,


        Wane dalili yasa Dikko ya matsamin nahau motar daya bani yau ? Tabbas dan yasan za'ayi magana ne kuma haka yake so dama kowa yasan ina tare dashi shima yana tare dani dan idan babu wata alaÆ™a dani dashi mai girma me zai haÉ—ani da motar shi.... ?

        Yau kuma idan akwai wanda yafi Jiddah baÆ™in ciki bai wuce Momy ba kuma sun tanadin shaglin partyn wulaÆ™anta ni , Jiddah bata Æ™ara jin takaici ba saidai Dikko ya tura Ashiru ya maida ita gida , tace bata komawa , koda Ashiru ya faÉ—awa Dikko tace bata komawa cewa yayi ya barta idan ta gaji ta koma da kanta ,

     Tunda naje gidan rasuwa ban sake komawa Dikko ya hanani , sai yau sadakar 3 yace inje amma yau mintuna 10 ya bani , Umar ya aiko ya kawomin kuÉ—i in bada sadaka idan naje , kuma har yanzu yana gari bai tafi ba saboda kullum rana muna tare , 

       Ina ta shiri zan fita saiga Ummu Affan wai tazo min gaisuwa , bayan ta gama ta'aziyyar tacemin ashe kuma sai kikayi mota ? Murmushi nayi ban bata ansa ba naci gaba huÉ—É—ar gabana kenan ba gaisuwar ta kawota ba dan kawai taji labarin mota , saida na gama shirina kaf nace tou zan rufe É—akin , tace tou bari in tafi idan kika dawo na dawo , fita tayi nima na fita na rufe É—akin .

      Ina fita naga Baba zaune a tsakar gida duk yayi wani kalar ban tausayi , nace Baba baka lafiya ne ? Kallona yayi yace wallahi Mamana gabana keta faÉ—uwa , nace miya faru ne ? Yace nidai nayi miki alÆ™awari nabar caca har abadan duniya nace Eh Baba , yace tun daga ranar da mukayi maganar dake da na saka motarki a caca wallahi ban sake zuwa koda wurin caca ba haka duk abokai na bana tare dasu tun ranar ban sake shan giya ba haka kuma ban sake neman mata ba ,

     Nace to yanzu meya faru ne ? Yace abun ya dameni ne tun ranar da nayi wannan maganar idan na kwanta bacci sai inga wani mutum tsaye a gabana yana cewa idan baka koma caca ba ajalinka ne zaici gaba da fuskantar ka , ka koma caca kaci gaba da neman mata kasha giya idan ba haka ba zamuyi maka kisan wulaÆ™anci domin zaka lalatamin duk wani tsari na ,

     Shine nace bazan koma ba , jiya itace rana ta Æ™arshe daya bani kuma yace yau idan banje gidan caca ba wallahi kasheni zaiyi , murmushi nayi nace Baba kenan wannan ai duk shirmen bacci ne , yace Mamana ba shirme bane da gaske ne dan har sunanki naji an kira a mafarkin yace shine ya toshe miki rayuwa wai ya rufe Æ™walwarki a bakin mataccen kwaÉ—o , dariya nayi sosai nace ji wani magana Babana ni na tafi saina dawo ,

       Saida na fita daga anguwarmu zuciyata ta fara tabbatarmin da ba shirme bane , maganar Baba abin dubawa ce da tunani iri ² na isa gidan rayuwa , ban jima ba na fito bayan na basu kuÉ—in da Dikko ya bani duka ban rage komai ba ,

      Jiki a sanyaye na dawo gida ban samu Baba ba , dan haka na shiga É—akina kaina sai juyawa yakeyi , wayata na É—auka na kira Dikko kaf na rattafa mishi abinda Babana ya faÉ—amin , yace baya nan yaje kano amma idan yayi magrib zai taho in Allah ya yadda , nace tou don Allah daka dawo kazo wurina , yace insha Allah An mata ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru sai alkairi , nace tom saida ya kwantarmin da hankalina sannan ya kashe wayar ,

       Ina gama waya da Dikko wayar Mamy ta fara kuka , da sauri na É—auki wayar ba tare dana san mai kirana ba , ina É—auka nace Hello , mai magana a waya tace Mamy na samu duk bayanan da kike buÆ™ata , kila bata san Aunty Mamy ta rasu ba , akwai wani kwaÉ—É—o da aka rufe gawarshi a kwalbar lemu kuma gawar kwaÉ—on saida aka zuba kwata a cikinta , akwai bokan dake gyara aikin kullum amma yace abu ya warware komai zai iya faruwa tunda har Binna ya fita a caca ,

       Anyi Æ™oÆ™arin juya al'Æ™amin tsafi ya sauka akan yarinyar da kike magana bokan yace sai ta tsallake sallar isha'e da asuba idan har batayi su ba tana dai cikin tsarki ba jinin al'ada ba itace zata maye gurbin ubanta , yarinyar tana da addu'a gaskiya kuma bata wasa da sallah , kiyi sauri yanzun nan suka kira Binna zasu kashe shi.... Kwalbar da akayi asiri gata a hannuna , amma kiyi gaggawar zuwa gidan........ Ihun matar naji ina ta hello ׳ amma cikin wahaltacciyar murya tace kiyi gaggawa zuwa bayan gidan caca acan za'a kashe Binna ni kuma zanci da sauran....

       A firgice na fara kiran wayar Dikko amma sai akacemin a kashe take , wayar Babana na fara kira sai ringing take amma ba 'a É—auka , wayyoni Allahna na sake faÉ—awa wata rayuwar , me yasa Dikko ya kashe wayarshi ? Su waye suka kirashi ya fita ? Me akayi ma wacce nake magana da ita a waya ? Wayyo Allahna rayuwa me yasa zakiyimin haka ne .....⁉ 😭