Breaking News

KWARATA 72

🅿 ------ 70

          A rayuwarka babu abinda ka sani sai zafin kai , doke² , É—aure fuska gaka mahaukaci ga aljannu kamar iccen tsamiya ni taurin kai , kai kuma zuciya talauci da arziÆ™i basa zama wuri É—aya dole idan É—aya yazo to É—aya zai tafi , hawaye ne ya gangaro daga cikin idon Dikko bayan ya tuno maganganun da An mata ta jefeshi dasu , murmushi mai yagar zuciya yayi tare da kallon kanshi
a madubi yana mai sakeyin murmushi wanda har saida kyawawan haƙoransa suka bayyana.

        Wai nine mahaukaci ? Duk dana faÉ—a miki lalurata amma shine kikemin gori wai aljannu kamar iccen tsamiya kwantar da fuskarshi yayi saman sitiyarin mota a bayyane yace bani ne na É—orawa kaina ba Æ™addara ne kuma haka yazo rubuce a cikin Æ™addarar rayuwata , É—ago kanshi yayi yaci gaba da kallon gabanshi dan tuÆ™i yake kuma har yanzu baije inda zaije ba , yaci gaba da addu'a ya ubangiji ka bani lafiya ka yaye min wannan lalurar ka bani haÆ™urin rashin An mata , goge hawayen daya zobo mishi yayi yana ci gaba da cewa wai duk girmana ni nake kuka wa mace , macen ma An mata ashe dama bata so na , wani irin duka ya kaima sitiyari a hayaniyance yace ni kika yaudara ? Nidai kika yaudara bazan taÉ“a yafe miki ba An mata kuma Allah bazai barki ba saiya min sakkayya ya Æ™arasa maganar hawaye na rigangato wurin fitowa daga cikin kwarin idanuwan shi.

      Har ya isa goruba ranshi a É“ace addu'arshi É—aya Allah yasa kada wani ya hawoshi a dai² wannan lokacin da yake cikin É“acin rai dan duk wanda yazo yana cikin wannan yanayi zafa a samu matsala , aljannu kamar iccen tsamiya ya maimaita a dai² lokacin da yayi parking , yanayin parking Yazeed ya fara gani ,

       Fita yayi daga motar cikin tsananin É“acin rai fuskar nan a haÉ—e , Yazeed yana ganin Dikko ya taso cikin girmamawa ya miÆ™awa Dikko hannu , bai anshi hannu ba yace ya akayi ? Cikin rawar murya Yazeed yace DK don Allah wani abokina ne aka kama wata Æ™awarshi ta gayyaceshi zuwa gidanta sai mijin ya dawo ya ritsatsu dan Allah kayi magana yana sabon gari police station ,

(pls mai yasa bakwa mana click akan ads)       Wani irin munafikin kallo Dikko yayi ma Yazeed , a hanzar ce Yazeed yaja baya yana kallon Dikko , tsoki Dikkon yayi ya fara tafiya Yazeed yabi bayanshi Dikko kuma yana magana cewe , baku da aiki kullum an kamaku wurin neman mata , nima yau an kamani na kasa fitowa , banyi maganin damuwa na bare inyi ma wani nashi , ina cikin É“acin rai ka kama gabanka tun kafin in fara Æ™wallo dakai....

       DK ka duba lamarin nan don girman Allah kayi wani abu akai matsalar babbace , da sauri ya juyo yace kai........... Ka wuce fa , ganin idanuwan Dikko ba'a launin daya saba ganinsu ba yasashi juyowa da sauri ya dawo baya yana tunanin halin da abokinshi yake ciki.

       Matsala ce ta neman duniya shi abokin nashi yana da wata buÆ™ata akan wasu harkokin shi nayau da kullum shine malaminshi yace sai ya samo maniyin matar aure kuma saiya nemi matar a gidan aurenta a saman gadon da mijinta yake kwanciya da ita , a jikin hankicif kawai ake so a gogo sperm in shikenan zance ya Æ™are , amma zai dawo zuwa anjima idan Dikko ya sauko , zuciyarshi tace a , a kawai kaje wurin Sultana a gabanka zatayi masa waya a wuce da damuwar nan , kai tsaye Yazeed gidansu Sultana ya nufo !

        A halin yanzu zuciyata ta cika fal da Dikko , muradina shine naga na haÉ—u dashi maganar gaskiya so nake na kasance dashi domin inajin Dikko kamar wata runduna ta tsagin rayuwata idan har na bari Dikko ya tafi na shiga3 na tawa ta Æ™are , fashewa nayi da wani irin kuka a toilet nace ina sanka ׳ mutumina.....

      Sai ihu nakeyi a toilet babu mai jina saboda gidanmu cike yake da mutane "yan kawo lefe , kuma gashi gobe idan Allah ya kaimu É—aurin aurena wanda za'a É—aura 2:00pm idan Allah ya kaimu , saida nasha kukana har na gode Allah na fito daga toilet ko mai ban shafa ba na saka kayana , wayata na É—auka na fara kiran wayar Dikko ,

Ɗauka yayi amma baiyi magana ba , cikin kuka nace Dikko gobe ne fa ɗaurin aurena , Ey ai kin faɗamin jiya da daddare ko kin manta , a , a ban manta ba ƙara tuna maka nayi fa , ina sane ban manta ba , to baza kayi wani abu ba ? Wani abu kamar me ? Shiru nayi ina kuka na kasa magana , Dikko yace Allah yasa alkairi ya baku zaman lafiya ina tayaki murna sosai yana faɗin haka ya tsinke wayarshi....

       Wani irin ihu nayi wanda ya jawo hankalin duk wanda ke cikin gidan sukayo É—aki wurina kowa yana tambayata lafiya ? Kamar baÆ™uwar mutane haka naci gaba da kallon mutane É—aya bayan É—aya cewa ya akayi ne ? Munji kina kuka ne , murmushin Æ™arfin hali nayi cewa ba komai ni ba kuka nake ba wani abu ne ya faÉ—amin a ido , kowa Allah ya sawaÆ™e yayimin sannan suka fita.

        Hijabi na saka na fita wurin Sultan dana baro a mota yana zaman jirana , dakel na Æ™aÆ™aro farin ciki na isa wurinshi amma yanzu ban shiga motar ba a waje na tsaya , ki shigo mana , a , a , haka yayimin , bawan Allah ko murmushi baya gajiya dashi yace kodai naje na barki ki huta ne ? Cike da zumuÉ—i nace Eh , tada motar yayi yana cewa zan anso miki kayanki kinsan jiya mukayi dasu , godiya nayi masa tare da mishi addu'a Allah ya tsare hanya dan na matsu ya tafi wurin Dikko nake so naje , ina tsaye a wuri harya fita daga gidan yana fita motar Yazeed yana shigowa .{{{}}}

       Inda Sultan ya É—auke motarshi a wurin Yazeed ya ajiye nashi tare da sauke gilashin gefenshi An mata wurinki nazo , ai na sani tunda na ganka gidan nan dama nasan saboda nine kazo , to dan Allah ki shigo wani wuri zamuje muyi magana naga gidanku cike da mutane , babu wani jayayya ko tambayar ina zamuje na zagaya na buÉ—e mota na kame a gaba Yazeed yaja muka bar gidanmu!

      Iyalin Dady suna cikin tashin hankali da damuwa dan tun jiya suke neman Dady babu shi ba labarinshi kuma wayayonshi duk a kashe suke , saÆ™o da lungu nemanshi ake amma babu wanda yaji ko É“irÉ“ishin inda yake , cikin kuka Momy tace saika tafi ka saÆ™e duk ka tashi hankalinmu ? Ka tafi babu bankwana shin wai kana ina ne ?

       Wani irin gumji Dady keyi bayan an É“anÉ“are Dikko dakel daga jikinshi yace baza ku faÉ—amin gaskiya ba ko ? Bello da wahala tasashi ya koma wata siffa daban tsakanin ranar daya yayyanki Sultana da wuÆ™a zuwa yau yace ranka ya daÉ—e wallahi shine yasa ni , yayin da shi kuma Dadyn yake cewa Æ™arya Bello ke masa shine Dikko ranshi ya É“aci yacicci ubansu yana cewa bazasu faÉ—a masa gaskiya ba suna masa wasa daa hankali ko ? Ya Æ™arasa maganar yana Æ™ara kaiwa Bello halbi a baki.

      Cikin kuka Bello yace wallahi bani bane shine , Dady yace wallahi Æ™arya yakemin shine tunda shi ka kama da wuÆ™a kuma shi idonka ya gani ya yayyaka mata a jiki ni misali idan ma har zanyi kisa zan faÉ—awa wani ne ? Koshi sakaraine baisan shari'a ba ? Me yasa da nace yaje ya kashe ta baije ya faÉ—awa hukuma ba ? Ko zan hura wuta nace masa ya shiga yaje ya faÉ—a ? Idan har ka duba wannan abun kasan duk Æ™arya ne sharri kawai yake nemana dashi bansan abinda nayi masa ba !

      Bello ganin Dikko yaÉ—an so karÉ“ar uzirin Dady yasa yace to ranka ya daÉ—e tunda naga kanshi ya sani baisan nawa ba kuma naga yana Æ™oÆ™arin fita ni ya barni a ruwa bara na buÉ—e maka gaskiyar abun yadda shike....

     Labari tiryan² Bello ya zayyanawa Dikko kuma ya Æ™ara da cewa kuma kwalbar da ita matar taje ta É—auko yanzu haka tana hannun shi , wani irin ihu Dikko yayi yace saina kashe ku.............. Wayyo , wai...... Wai , wai Allahna , kai........... Wai , saina kashe ku wallahi kaine ka mayar min da matata daÆ™iÆ™iya ko ? Zai fara duka su Ashiru suka danneshi Æ™asa dakel saboda ai har yanzu akwai munafirci a maganarsu abinda su suka fahimta kenan , ya akayi kwalbar ta dawo hannun Bello bayan shi yace wata tazo ta É—auki kwalbar kuma an bada ita wa wani malami ? Shi malamin ya akayi yasan Bello kuma ya bashi kwalba ? Dole bazasu bar akashe su Bello ba Sultana ya kamata a nemo kuma a nemo inda matar data É—auko kwalba take , bayan ankai Dikko Æ™asa Ashiru ya koma mota da gudu ya É—auko magani har yanzu Dikko zubar da yaranshi yake duk girmansu duk Æ™arfinsu tuni tsoro yasa Dady suma shiko Bello yayi fitsari baisan adadi ba , sunga bala'e da masifar daya girmi nasu , dakel aka sake kai Dikko Æ™asa aka zuba mishi magani dole tasa ya É—auke....

       Fiddoshi sukayi suka kaishi mota aka sake kulle su Bello sai mai gida ya dawo , Bello kuma maimaita kalmar matata kawai yakeyi , har yaushe Dikko ya auri uwar masu gida ? Lallai akwai bala'e É—iyar Binna zata zama matar É—an gwamna ? Surukar gwamna ? Sam wallahi abinda bazai yuwu ba kenan an É—aura auren ko kuwa ? Wannan ansar ita ya kamata na fara sani farko kenan ,

     Kwance zariyar wandon shi yayi ya matsa kusa Dady yayi masa fitsari a fuska , nan take ya farko , É—aure wando yayi yana cewa zaune fa bata Æ™are ba matarka ba Æ™awar matar gwamna bace ba ? Cikin jin haushi Dady ya tashi ya kama Bello da kokowa yana cewa ni zaka zubawa fitsari ? Bello yace kai da Allah dan ka farfarÉ—o akwai sauran rina a kaba fa , saida suka caku suka rabu da kansu , cikin wahaltuwa Bello yace kaji wani aikin kuma ko ? Tou idan baka sani ba É—iyar Binna ta zama matar É—an gwamna ,

     Da sauri Dady yasa hannunwan shi biyu ya goge fuskarshi tare da yarfarwa , yace aure ? Ta auri Dikko ? Yayi maganar yana fiddo duk girman idanuwanshi , Bello yace ba kana can ka suma ba yace matata kuka mayar min daÆ™iÆ™iya yace duk saiya kashe mu , Dady yace sam ba'ayi aure ba , Bello yace idan ba'ayi ba kenan ai zaice budurwarshi , tunda kuma anyi sai yace matata , Dady yace idan anyi auren nan saina rabashi idan kuma ba'a É—aurashi ba babu ubanda ya isa ya daurashi duk cikar faÉ—in birnin garin katsina....

        An mata kin fito da wayarki ? Yazeed ne yake tambayar Sultana ko wayarta yana hannunta bayan ya samu Æ™ofar wani gida yayi parking , E na fito da wayata na bashi amsa , An mata dan Allah ki kira DK kice masa yayi waya a sakar min abokina , daga ina za'a sakeshi ne ? Yana sabon gari police station kamashi akayi , laifin me yayi aka kamashi ? Gonar wani ya aura kuma ya samu damar tattare kaf amfanin gona , to ya akayi harya tsaya aka kamashi ? Yankin ya shiga ba ita matar tazo nashi yankin , kaima Yazeed wannan ai ganganci ne , Eh An mata amma dan Allah kiyi ma DK magana yasa a sakeshi , murmushi nayi mai ciwo nace Yazeed zanyi masa amma me yasa wai suke san fasiÆ™anci da matan aure ne ?

Mafi yawancin matan auren sune suke miƙa kansu wa mazajen waje ta hanyar ɓoye kawunansu su masu aure ne , kowa da irin matsalar dake shigar da ita bariki da aurenta , wasu rashi ne na talaucin abinda zasu ci ko sha , wasu kuma rashin basa samun gamsuwa ne wurin mazajensu , wata kuma tana da komai babu abinda ta nema ta rasa kawai ra'ayi ne ,

      Tou su mazan me yake sa suna neman matan waje bayan ga nasu matayen a gida , gyara zama Yazeed yayi cewa mafi yawan mazan waje masu neman matan aure suna nemansu ne saboda matsalolin matansu na gida , wasu kuma suna neman matan aure ne saboda neman wani abu na samun duniya , me yasa dole sai a matan aure ake san samu ne ? Duba girman aure kuma ki tuno daraja wacce Allah yayi masa duk wanda ya É“ata matsayi da darajar aure ya halaka , nidai kira DK a fiddoshi , kayi haÆ™uri Yazeed gaskiya ni halin yanzu bana tare da Dikko , me yasa ? Haka nan na fita daga rayuwarshi ne dan ina so nima ya fita tawa rayuwar , wai miye tsakaninku ne ? Murmushi nayi a zuciyata nace anzo wurin , kallon Yazeed nayi cewa to kai a naka tunanin meye tsakaninmu ?

      Wata "yar munafikar dariya yayi yana cewa muje kawai na maida ke gida yanzu banda lokacin magana dan hankalina baya kwance amma zamuyi magana daga baya , yayi maganar yana taka motar muka tafi , saida muka isa gida sannan mukayi magana dukanmu , Yazeed yace zai kawomin wata Æ™awarshi matar aure ce amma tana wasan danbe , kinsan miye danbe ? Ya tambayeni ? Nace masa a , a , Yazeed yace aiko yadda kike hakan nan kika shiga harkar danbe abin zai miki daÉ—i zaki taka matakai masu girma zaki fito duniya zata sanki kuma sai kinfi Æ™arfi DK wallahi ,

      Murmushi nayi tare da cewa in banda abinka taya zan iya raba fili inyi wasan danbe da Æ™atti majiya Æ™arfi ne ? Murmushi Yazeed yayi cewa ba irin waccan danben ba , kawai kidai kije zan turota tayi miki bayanin yadda danben yake , fita nayi daga motar ina cewa Allah yasa tazo lafiya , da amin ya ansa ya fita gidan da gudu lallai yana tare da damuwa , bin bayan motar Yazeed nayi da kallo nace É—an raini kenan kamar yadda nake kallon kaina a madubi haka nake kallon inda ka nufa , murmushi nayi tare da tinkarar hanyar shiga cikin gida da sauri.

    Ina shiga palo Inna na fara gani ta kame saman kujera an wani waye an goge ta fito cikakkiyar hajiya ga haÆ™orin makka tasha kuma wallahi yayi mata kyau sosai , da gudu na ruga na rungumeta na fashe da kuka , cikin jin kunya take Æ™oÆ™arin rabani da jikinta tana kallon idanuwan mutane ita a dole sai tayi alkunya irin tasu ta fulani , ke saukar min a jiki cikin kuka na sauka ina kamo hannunta cewa Inna zo kiji , da yanayin tausayi ta kalleni ta taso kuma ta biyoni , É—akina muka shiga muna shiga na rufe Æ™ofa na sake É“arkewa da kuka nace Inna nidai tsakani da Allah bana san auren nan.....

      Cikin tashin hankali ta kalleni tace Sultana ki rufamin asiri wannan maganar ma ki barta tun farko , ni gaskiya bazan barta kawai kice wani abu na rantse da Allah bana aurenshi nidai bana sansa kawai biyayya nayi ma Kawu nayi tunanin zaicemin ko ina da wani da nakeso amma sai bai tambayeni ba , Inna tace aiko dai ko zaki mutu wallahi auren nan babu fashi ni zaki tona ma asiri dan ubanki , kinsan bakya sansa uban wa yace tun farko kika amsa musu , bakisan halin mutanen ba kina wasa da sha'aninsu ko ?

        Cikin hayani nace nima kina wasa da nawa sha'anin bari in fita na faÉ—a musu bana san Sultan , Sultan in banza Sultan in wofi , wani irin wawan mari Inna tayimin , kamar zan hau bori nace wallahi bana auren Sultan saidai ki kasheni , to na yadda saidai ko ki mutun , aiko bana mutuwa zanje na faÉ—a musu bana san Sultan tunda ni ba tsoronsu nakeji ba na tunkari hanyar fita zan buÉ—e Æ™ofar É—akin , fizgoni tayi ta maidani saman gado ita kuma cikin damuwa ta buÉ—e É—akin ta fita ta kulle da makulli ta waje , da gudu na sauka daga gado naje jikin Æ™ofar naci gaba duka ina cewa bana so ׳ wallahi ,

      Inna kuwa palo ta koma ta É—auki wayarta ta kira Dikko , yana É—auka ta fita waje bayan sun gaisa tace da Allah na dawo kazo ina san ganinka idan baka komai , lafiya dai Mama ? Ya tambayeta , gaskiya ba lafiya Sultana tana so ta sake tado min wata fitina da "yan uwana , bayan an tsayar da ranar aurenta duk kwanakin da suka wuce batace ta fasa ba saboda Allah saida taga gobe²n nan É—aurin aurenta Dikko tace ta fasa ? Na rasa ya zanyi duniya Allah yayi ma Sultana taurin kai , murmushi Dikko yayi tare da cewa me ne ne matsalar ? Nidai kazo yanzu²n , zanzo idan anyi isha'e , a , a Dikko yanzu dai , gani nan zuwa........

      Cikin Æ™anÆ™anin lokaci Dikko ya iso Inna tayi  masa jagora har É—akina , Dikko yana da raini tsabar rainin shi duk mutanen dake palon ko É—aya babu wadda Dikko ya gaishe da , haka ya wuto su yana musu kallon Æ™yankyanmi fuskar nan haÉ—e kamar hadarin tsakar dare har É—akina , ina kwance saman gado ina ta kuka dan na gaji da bugun Æ™ofa har na koma na kwanta.

      Bayan sun shigo ne naji Inna tace ina zuwa ta fita , shi kuma ya shigo cikin É—akin har bakin gadona kuma bai cire takalmin Æ™afarshi , kallo É—aya nayi masa na juya mishi baya naci gaba da kuka , jawoni yayi daga saman gadon na fizge na koma na kwanta , cikin rarrashi yace zo inji waye ya taÉ“amin An matana ? Taho ya miÆ™o hannunshi , saukowa nayi daga saman gado naje kusa dashi na tsaya , kallona yayi sosai sannan ya kamo hannuna na dama ya É—ora saman kafaÉ—arshi ya riÆ™e tsakiyar bayana yace kallarni yayi maganar yana murmushi , kallonshi nayi ina kuka , wai me ne ne ? Dikko ya tambayeni , kwanciya nayi saman Æ™irjinshi nace bana sansa , ke yar raini bana so kinaji na ? Kinga zaki tayar da hankalin Mama kiyi haÆ™uri kinji jaruma ta ?

     Dikko nidai bana sansa don Allah nayi maganar cikin kuka sosai ina mai É—agowa na kalleshi , Æ™arya kikeyi da bakinki kika faÉ—amin kina sansa kuma na tambayeki yayi miki kika ce min yayi sai yanzu kice kin fasa ? Baya yuwuwa wallahi duk wanda ya tsaya miki sai an É—aura auren nan kuma babu gudu babu ja da baya , wallahi ko na tafi kika sake cewa bakiyin auren nan zanzo in tafi dake goruba jawoni yayi a jikinshi sosai sannan ya shafa bayana da lallausar hannushi yana cewa zakiji a jikinki , da sauri ya É—agani jikinshi jin ana shigowa.

      A dai² lokacin da Inna ta shigo tana ta faÉ—a cewa ai dama nasan duk yadda akayi Sultana tana da maziga ashe wai wani tsinan yaro ne É—an mara mutunci take tare dashi , kusa dani ta matso ta yayyanka min mari tana cewa meya haÉ—aki da Dikko É—an iska yaron da baya ganin kowa da mutunci garin nan , ke banda kike jaka marar tunani duk wulaÆ™anci da tozarcin da Dikko yayi muku kin manta ? Tou idan kin manta ki tuna saida Dikko ya haramta muku mazaunin gida , gararin rayuwa wane ne bakuyi ba sanadin shi ? Ki rasa abokin tarayya sai mutumin da silarshi kika yanki tikitin shiga karuwanci , sassauta murya tayi cewa ban san Dikko na tsaneshi matsashi mai É—agawa da baisan darajar kowa ba , yau da zanga Dikko dasai na É—auki wuÆ™a na soka mishi a ciki ya mutu tsabar wutar Æ™iyayyar shi dake ci a cikin zuciyata ,

     Kin samu za'a rufa miki asiri wawiyar banza a aureki amma da yake ke jakace har kike tunanin zaki ce kin fasa idan banda ma Allah yasa Sultan É—in mai imani ne an faÉ—a miki zai iya aurenki ne ? Tou Allah ya rufa miki asiri ma yaso ki a haka da duk katsina kin rasa mijin aure , wayata taje ta É—auko ta kawo ma Dikko tace ka duba cikin wayar ka ganomin lambar É—an gwamnan ka kirashi yanzu²n nan ka rabashi da Sultana...

      Daga ni har Dikko kallan kallo muke ma juna , cikin jarumta Dikko yace Mama ke baki san Dikko ba ? Ina fa zanso sanin lalataccen yaron nan , to amma waye yace miki yana tare da ya nuna ni , Sultan yake faÉ—amin yanzu yace ko rashin lafiyar da tayi Dikko shine yake kwana da ita kirawoshi....

      Kallona Dikko yayi sannan ya kalli Inna yace ai ba buÆ™atar kiran shi , me yasa ne ? Inji Inna , saboda Dikko tuni yazo , yana ina ne ? Nine *DIKKO* kuma nine *DIKKOn* da kike nema........... Gani nazo!



CLICK ON THE ADS PLS