YAU DA GOBE 29&30
🅿️29&30
Wannan shafin nakine kyauta ummu sultan🥰👍💖
.....suna fitowa wayarsa tayi ringing"ta katse wani Kiran yasake shigowa.ajiyeta yyi fuska ahad'e yace Allah yasa kikoma yunk'urin guduwa kigani!wayar yaciro dg aljihun wondonsa.sake bin Kiran yyi sbd ta tsink'e... subahanallahi!; to shikenan gani nan zuwa insha Allah... yafad'a Yana kashe
wayar"kafin yamayar da ita aljihu.yaciro key d'in d'akinsa ya dubi sumayya dake zaman dole kan kujera ya wurga Mata shi"Yana cewa ki gyaran komai very neat"kimun lunch"kinji ko bakijiba?"shiru kawai tayi tana share hawayenta...yaja tsaki yafice da sauri..Duk abinda yadace Saida tayi komai. tamkar yadda takeyi abaya"
Saidai zuciyar ta acunkushe take"tana tunanin minene makomar aurensu ?"
Duk inta tuna yarabata da martabarvta saitaji tamkar ta had'iyi zuciya ta mutu sbd haushi da takaici... musammun inta tuna da yawan matan dake samun kulawa agun mazajensu adaren farkonsu"amma ita nata Daren farkon ga yadda yazo Mata..
Saida ta idar da girkin ta jere komai a dining table"ta wuce tayi wanka"bayan ta shirya tadanci abinci sama sama"kafin tasaka hijab da nik'eb ta Kira driver awaya, cewar ta shirya yafito da mota gatanan zuwa..
Basu gama loctures ba sai 6:pm"lokacin data iso gd"gab da magrib...yanayin yadda taga parlourn yasa tagane me gdn yadawo..bed room d'in ta kawai ta wuce tayi Sallah"kafin ta fito zuwa kitchen had'a dinner..
Koda ta idar ta kwashe kayan d'azun ta jera na yanzun..hakan yyi daidai da shigowar sa parlourn" ko inda yake bata kallaba.tqna idarwa tayi wucewarta d'aki...gogan kuwa tab'e baki yyi"ya iso dining area d'in....
Washe gari cikin farin ciki ta farka sbd yau zataje taga mama da twin's datakejin byn mama bbu Wanda takeso sama dasu aduniya....bayan ta Gama had'a musu breakfast ta shirya"sanye take da doguwar rigar lace yellow.tayi kyau Masha Allah"kallo d'aya zaka mata kagane tana cikin farin ciki"Yana zaune Yana break fast hankalinsa kwance."kujera taja ta zauna"had'e da cewa Ina kwana?"batare daya kalletaba yace kirik'e abarki"yaushe rabon da kigaidani?"cike da mamaki take sauraren sa"tunda tazo gidan wata2 kenan Bata tab'a gaidashi ya amsaba amma Kuma har zaice haka?"
dama in angaidakai kana amsane?"
Bansaniba! shiru kawai tayi tana had'a tea"ganin Yana k'ok'arin tashi tace maganar tafiyar na shirya... ashek'e yakalleta"sbd ganin yanzun dududu befi karfe 9 nasafeba"na lura kwana 2 nan kanki na rawa zan saita mikishi"kokuwa sbd abinda yafaru kike hakan? Toni sai5pm natsara tafiyar...nikuma yanzun na shirya"Dan kayi hakuri naje driver yakaini"da karfe 5din sai kaje...hakan be munba"kina nufin wazai Miki garki da gyaran d'aki na...batace komaiba har yagama yyi tafiyarsa d'akin sa"bayan ta idar da breakfast ta gyara Gurin"da bed room d'in ta ,ta wuce d'akin sa"sbd ganin yafita,ta binciko keys d'inta daya karb'e...takuma Sha alwashin bazata yi girkinba dagyara d'akin saidai yakasheta...chat taitayi"sai bayan taji yunwa Tasha comflax da Madara tayi Sallar azahar ta d'auki Jakarta ta wuce part d'insu ummi sbd yadda ta tsara dg can su wuce gdn mamanta...
Da sallama ta shigo cike da nutsuwa"zarah dake tsakkiyar parlourn azaune ga plate na d'an wake agabanta yaji kayan had'i"ta amsa fuska cike da fara'a"Zama sumayya tayi suka gaisa"kafin tace ummi fa?"yanzun ta shiga wanka "muci abinci anty sumayya... murmushi sumayya tayi had'e da cewa ah ah nako...ai wlh baki isaba!saikin cisa Kona Dena zuwa part d'inki"zarah tayi saurin katse Sumayyar.
Matsawa tayi sbd itama tanason Dan wake mutuminbtane"sunaci suna korawa da siro..gab dazasu cinye sumayya ta zare hannunta tace nagode anty zarah nak'oshi...hakan yayi daidai da isowar ummi cikin parlourn"zarah tace hmmm gsky yakamata kisaki jikinki nanfa gdnkune!ummi data zauna tace 'yata sannunki da zuwa !kwana 2 kindena lek'owa mu gaisa"sumayya na murmushi tace aikuwa lfylau ummi Muna jarabawa ne shiyasa"Allah sarki Allah yataimaka!cewar ummin...bayan sun gaisa " ummi tace yaune zakuje gdn Abbanku ko?" Tace eh "mma sai karfe5" ummi tace ainazata yini zakiyi acan?" Sumayya dai tana murmushi batace komaiba..
Ummi kuwa ta fahimci tabbas Aliyu ne yace sai karfe5".girgixa Kai kawai tayi tana tunanin sai yaushe Aliyu zai canza?
Sundade suna fira abinsu...dg baya zarah ta kunna kallo kasancewar week end kowa Yana gd...wata k'atuwar mage aka hasko atallar wani firm dasuke kallo sumayya ta rintse idanunta had'e da Wai Allah!zarah tayi dariya had'e da cewa tsoronta kikejine?"
Sumayya tace aini Kinga "mage k'adangare,tsaka Ina mugun tsoronsu wlh...musam... maganar ta mak'ale mata sbd hancinta daya shak'i k'amshin turaren Dr safana!
Maida k'ofar parlourn yyi ya rufe"kafin yyi sallama can cikin mak'oshi!kallo d'aya zaka masa kasan ransa ab'ace yake...sbd dawowarsa kenan dg asibiti!sbd ammishi Kiran gaggawa"yakwaso yunwa da gajiya yazo yasamu dining wayam"gashi bata nan "azatonsa ko gdn abban ta tafi"wata zuciyar tace Masa ko tana part d'in su ummi?"hakan yasa yanufo nan.
Satar kallon sa sumayya tayi aikuwa suka had'a ido yamata wani mugun kallo daya saka hanjin cikinta juyawa...saidai duk ummi na ankare dasu...zarah tace Yaya wani waje kaje bacin yau week end?"banza yyi Mata yadubi sumayya fuskarsa amatukar daure yace ke tashi kiwuce ki koma can...cike da tsoro sumayya jikinta ke rawa sbd tasan yabata umarni batayiba"damma sauk'i ta d'auke keys d'inta"koba kyajine?"yafad'a ad'an tsawace...tashi tsaye tayi! sumayya koma ki zauna! Cewar ummi fuskarta a'daure tana kallonshi"Dr safana sosa Kai yyi" sbd idonsa ya rufe ya manta da ummi na nan" ahankali yace to Amma ummi saitazo nan tayi zaune ga gidanta ! Intayi bak'i fa?"inbakin sunzo sai akirata anan taje ko?"ince ba yau kace zakuje gdn Abbanku ba?"eh ummi yaune.to saikabari dg nan kuje can d'in"in kundawo Takoma sashenkun... shikenan mutum bazaiji kad'aici yamasa yawaba yad'an fito"yaushe rabonta da nan d'in ma saifa yau!nama lura inba makaranta ba Bata zuwa ko Ina..cewar ummin tana kallonsa"sbd ta lura sumayya na mugun jin tsoronsa"bece komai ba yafice.sumayya taja ajiyar zuciya"
Koda yafita abind azaici yanema"kafin yaje masjeed yyi sallar la'asar"kafin yadawo yyi wanka ya shirya cikin riga da wando na ash colour din shadda"da hula sai agogonsa na fata itama ash"sai k'amshi ketaji ajikinsa...yyi kyau naban mamaki ga haske da yyi ,sbd jin dad'i d hutu...afito sak a agonsa..lolx
Tsaki yaja sbd yatuna bayada da number inta"dasai yakirata kawai su wuce"dole ya koma sashen ummin"bbu kowa a parlourn"d'akin zarah ya nufa "acan yasame su itada zarah da alama Sallah sukayi"zarah nataje Mata gashinta tana cewa gsky anty sumayya kinfini gashi Masha Allah...kallo d'aya yamasu yad'auke Kai "Yana mamakin yawan gashinta"shi wlh jiya daya gani azatonsa attachment ne tasaka"bece komai ba yajuya"hakan yasa zarah tayi murmushi had'e da cewa antynmu daura d'an kwali ga sweet heart d'inki najiranki"nasan Yayana da aji"Kinga bazaiyi mgn ba"Dan ALLAH kicanza manashi... murmushi kawai sumayya tayi batace komaiba...ta d'aura dan kwalinta"ta gyara gyalenta had'e da rataya jikkarta akafad'arta...Masha Allah"duk batayi k'iba ba"Amma tayi kyau ta k'ara haske da wayewa"Inka kalleta zaka d'auka budurwace.... Sumayya tadubi zarah tace pls muje kirakamu can d'in...zaro ido zarah tayi had'e da cewa rufan asiri karkijamun gun Yaya Dan ALLAH kije karkiyi laifi...da sauri sumayya ta fice"aparlour tasameshi suna mgn da ummi"da alama fad'a take mishi sbd tayi shiru dataga Sumayyar...cike da girmamawa Sumayyar tace ummi zamu tafi"to sumayya Allah yatsare kugaida mutanan gdn"tana murmushi tace zasuji da kyau...fita yyi..yabar Sumayyar suna mgn da ummi...kafin itama ta biyosa a parking space...Yana hakimce gdn baya"ga driver yashiga mazauninsa.
Ahankali ta bud'e marfin motar ta shiga Cike da tsoron abinda zai Mata sbd tasan ba k'yaleta zaiyiba akan laifin tana kin Masa girki da gyaran d'aki.
Bayan ta shiga "tasaci kallon sa"fuskarsa tamkar hadarin gabas"Yana tab'a hannunsa data ciza ranar firs night d'insu.
Har yak'ame Yana sab'a"wani farin ciki taji"ko banza itama ai ta k'untata mishi!
Dr safana kuwa haushi da takaicin abinda tamasa Yana a ransa yabarta sudawone..bbu Mai mgn har suka iso" yanayin parking tayi maza zata bud'e...karki fita! yafad'a atakaice.
Fita driver d'in yyi...kafin yace ke kura sarkin cixo" kinunawa Abba komai normal !wani kallo tamasa kafin tace Allah zakaji tsoro ba mutum ba!laifi2 kenan"yafad'a Yana fitowa dg motar"itama ta fito tana tab'e baki...gab da ita yatsaya"yakamo tattausan hannunta yasaka anashi...dg shi har ita Saida sukaji wani shock"malam kacimun hannu na!banza yyi Mata yajata suna tafiya"dg nesa inkagansu zaka d'auka love birds ne sbd irin dacewar dasukayi da juna"Yana cab'o Mata mgn saika zata fira sukeyi... straight part d'in hjy jamilah yanufa da ita" sumayya taso k'inxuwa sbd kada suci Mata mutunci agaban sa...cak ta tsayar d tunanin ta sbd hango jidda da tayi tafito dg part nasu..hakan yasa ta turje...tana cewa nika cikamun hannuna"ke wlh ranki zai b'aci"aizamu koma inda muka fito ko?"yafad'a Yana janta...da gangan tafad'o ajikinsa tasaki kuka nashagwaba "sbd ganin jidda na kallonsu cike d mamaki tana zaro ido"cikin b'acin rai da kunar Rai jidda ta koma da sauri... yyinda safana yature sumayya Yana cewa wlh kikazo hannuna Zaki gane bakida wayo"nafiki iya pretending d'in"batace komaiba"steel Yana rik'e da hannunta sukayi sallama parlourn gdn...Abba Yana zaune kan kujera ga drinks kqn center table dake gabansa "Yana duba jarida"Yana d'agowa yagansu.. wani murmushin farinciki yasaki had'e da cewa Masha Allah ga yarana...hakan yyi daidai da fitowar hjy jamilah d jidda" sbd jiddan taje tasanar Mata gasunan...kallo d'aya hjy jamilah ta musu tagano suna cikin farin ciki" gabanta yafad'i...Zama tayi tana kallon su..Dr safana yaduk'a tare da sumayya da har yanzun hannunsu na cikin na juna"suka gaida abban "ya amsa yana cewa sumayya ya kuke bbu dai wata damuwa ko??"matse Mata hannu Dr safana yyi"hakan Kuma akan idonsu hjy jamilah da jidda"sbd yadda suka maida hankalin su akansu"awahale tac e lfy qlau alhmdllh Abba bbu damuwa!
Masha Allah haka akeso"Dr safana dasai yanzun yalura dasu hjy jamilah"dg inda suke yace umma Ina wuni?"lfy ta amsa tana musu wani mugun kallo"Dr safana bedamuba sbd yasan halin ta"sumayya ma tace umma Ina wuni?"Ashe kin ganni?"to rik'e gaisuwarki kije gun uwarki kigaidata"ke marar kunya y'ar dad'i miji ko?"kunshigo rik'e da juna ku nuna bakuda kuny.... sumayya kuje part d'in mamanki"my son nan zaka barta sai anjima ko kadawo?"fuska asake Dr safana yadubi sumayya yace baby kinyarda sai anjima ko?"gyada kanta kawai tayi"atare suka mik'e tsaye...hjy jamilah baki bud'e tabisu da kallo...jidda tasaki kuka had'e shigewa ciki aguje...Abba yatab'e baki had'e da cewa Allah yashiryeku...
*************
Suna fita yacikata bece komai ba"itama sharesa tayi tana mamakin pretending d'insa"
Koda suka iso part d'in mama "twins ne da Mai rainansu ,bayan sun gaisa da ita sumayya ta karb'i yaran tana murnan ganinsu"yyinda Dr safana yyi zamansa kan kujera tamkar baya a parlourn"
Bed room d'in mama ta nufa "tasameta tana waya da gudu ta fad'a jikinta"kashe wayar tayi"tana hararar Sumayyar kafin tace kewai bazaki girma?"tana murmushi tace nayi missing naki mama wlh!hmmm kekadaice tafe ayanzun?"ah ah nidashi ne?"wake nan?"mamar ta tambayeta tana hararar ta.turo baki tayi had'e da cewa Yaya Aliyu yana parlour"mama su mazaffar sunyi wayo wlh"nabarsu gun Mai rainansu...tashi tsaye mama tayi tasaka hijab tace kije ganinan mugaisa to kawai tace ta fice.. ahankali tazo ta zauna gefensa kan 2 seeter"muga wayarki!abinda yace kenan"mezakayi da ita?"bazaki bayarba"fito da ita tayi dg hand bag d'in ta,ta Mik'a Masa"adedenan mama tayi musu sallama ta shigo"fuska asake tace sannu da zuwa Aliyu ya hanya?"kansa ak'asa yace alhmdllh Ina wuni mama?"lfy qlau..ysu umminku?"duk suna lfy..Masha Allah ta fad'a tana barin parlourn sbd kawaici d kunya...duba wayar yyi yaga bbu password.numbers yasaka yyi Kira..atake number ta ta shigo wayarsa"ajiye Mata wayar yyi"bece komai ba fice"tab'e baki tayi had'e da shigewa bed room d'in ummi..sosai ummi taji dad'in ganin sumayya sbd taganta ayanayi Mai kyau ,Kuma da alama sun Fara samun jituwa itada Aliyu"kayan Mata da kayan k'amshi ummin ta Bata"bayan tamata nasihar taita hakuri da rayuwa Kuma tayi biyayya.itadai sumayya jin mama kawai takeyi tasan sbd batasan irin zaman dasukeyi bane...Saida sumayya taci abinci ta koshi"tasake karba'an twins...Saida aka Kira magrib tukum taba Mai rainansu su tayi Sallah..
Ana Gama isha'i"wayarta tayi ringing"taga bak'uwar number"d'agawa tayi"ahankali tace assalamu alaikum!ke kifito karki b'atan lokaci...kit yakashe wayar"kallon mama tayi tace zamu tafi Yana waje.mama tace
To shikenan Allah yatsare"
Fitowa tayi aparlou sukaci karo da Abba Yana murmushi yace zaku wuce ko sumayya?"tace eh Abba! kud'i rafar yan200 20K kenan yafito dasu yabata"ah ah Abba kabarsu"karb'a Mana"yafad'a fuska bbu wasa"karb'a tayi tana godiya ta fice...farin ciki fal aranta"rabon data rik'e kud'i tun kafin aurensu da Dr safana"ko skul zata bebata ko bicika saidai yasaka akaita"inma tana buk'atar wani abu sameera ke siya Mata har credit"bata tambayar Dr safana yabata kud'i ba. ko Kuma shi yabata" betaba bataba"tasan bbu abinda tarasa Amma Kuma akwai lalurar YAU DA GOBE...
Tama d'auka yatafi"Saida ta fita get ta hangoshi"a driver sit"front sit ta bud'e ta shige..bece komai ba yaja motar"itama kanta tamayar bakin hanya har suka iso gd...
Bayan tayi wanka ta wuce kitchen sbd ta had'a tea kawai Tasha"keee!da sauri ta d'ago kanta"Yana tsaye bakin k'ofar kitchen d'in"yace inkin gadama kidafamun shayi sai indomie 2 k'wai 3 nabaki 30 minit Ina parlou...bejira cewartaba yafice"tabe baki tayi had'e da cewa"iyayi kawai narasa meye abin dole sai yasani girki?"tafad'a rai b'ace"dole ta kunna gas 2,cikin minti25 ta Gama"shayin ta juye a flux"indomie tasaka atire...takaimasa yana zaune kan kujera Yana latsar laptop d'insa"
Ajiyewa tayi kan carpet"Takoma ta dawo d drinks d cups..kizo ki fifitamun da zafi fa"da mamaki take dubarsa"shikuwa Yana kallon 💻.
Kitchen ta koma ta fito da plate na roba"sannan t k'ure iskan fanka"tazo tacigaba da fifita wa"can Kuma yace dallah kije ansakaki aiki kina kallona"batace komaiba ta tashi sbd yanzun tasaba da wulak'ancin sa.
Saida yyi kat ,tukum yyi wanka ya kwanta saidai me?wani irin feeling yaji Yana taso mishi"lumshe ido yyi Yana tuna first night d'insu"
Tashi yyi yanufi bed room d'in Sumayya"Yana murd'awa yajita arufe...
Share
By mmn fareesa