SAMEEHA C
*_🧕SÂMÊÊHÂ🧕_*
*_(C)_*
Kafin Sameer ya qaraso inda SÂMÊÊHÂ ke zaune tini SÂMÊÊHÂ ta miqe da sauri ta shige bayansa tana maida numfashi da qyar, hannunta yakamo tabayan yace.
Samee na meke faruwa ne? ,umm ummm wani abu naga gani ya gifta tanan da jella yanzu yanzu Sameer Dan Allah kamai dani wajan Umma Ni nafasa auran gaba daya tasaka kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro jikinsa yajanyota,Kinga ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki anan mudin Ina tare dake bagani kusa dakeba ko in duduba ki gani,A a,ta furta cikin sauri jikinta sai kyarma yake tana waige²waige,janyota Sameer yasakeyi suka koma Kan kujera suka zauna suna duban junna sun dau tsawon lokaci ahaka babu Wanda ya tankawa wani SÂMÊÊHÂ ta Dan saki jiki kadan ganin Sameer na kusa da ita hakan yasashi miqewa da zummar zuwa ya rufe musu qofa ya dawo.
A duqun²qunne Sameer yasami SÂMÊÊHÂ duk ta takure jikinta waje daya Kamar wace za'a dauke Sameer yasaki wani murmushin Jin dadi Wanda ya bayana fararan haqoransa me dauke da siririyar wushirya, qarasowa yai daf da SÂMÊÊHÂ tana qoqarin ja da baya ya miqa mata hannu cikin sallon soyayya da begen junna.
Taso na taimaka Miki kinji Sarauniyar mata ta ki samu ki watsa ruwa ki kwanta kiyi baci mai dadi Kinga duk kin gaji dayawa,,magana yake cikin sallon shagwa6a SÂMÊÊHÂ tace""Aa ni bazanyi ba nariga nayo nawa tundaga gida,zaro Ido yayi hade da fadin.
Au dama in mutum yayi wanka baya sakeyi Samee bazan yardaba wankan gidan Umma daban na gidan Sameer daban kinga kin gaji idan kin watsa Zaki ji dadin baci duk jamma'a sun gajiyar mun dake plsssss..... Mana taso na rakaki sai na tsaya aqofa ki kammala mu dawo tare ko tsoron ne haryanzu Bai sakar min Samee naba,sake noqewa tayi jikin kujera kamar zata shige ciki tana girgiza Kai alamar bazatayi ba Sameer ya 6ata rai yana,"""tunda bakya so to ki tashi mukoma bedroom Dina ni saina watsa a dakin, ta kuma girgiza kai akaro na biyu ba shiri ya nufota gadan gadan yana murmusawa,, aiko sai kinje dolle Wai ni banace karkizo min da wannan kunyar takiba ko saina nuna Miki Ni din Dan farin ne Sameer na gama fadin haka ya sunkuce SÂMÊÊHÂ kamar 'yar baby sai bedroom dinsa tana ta mutsu mutsun kwacewa daga hannunsa,shigarsu dakin keda wuya jikinsu gaba daya ya kar6i wani baqon al'amari Wanda yarikita nutsuwarsu da tunaninsu hade da faduwar gaba adai dai lokacin da Sameer yasaka qafarshi cikin dakin ba shiri ya saki Sameeha daga hannunsa ta fadi qasa tikkk kakeji ta bugu da gefan gadon dake cikin dakin Sameer ya sulale qasa awahalce Yana maida numfashi da qyar saboda juyawar da kansa keyi, rintsa idanuwansa yayi ya budesu alokaci guda ya hangi wani qaton kwazazzabon Rami agabansa mai mugun duhu da zurfi Wanda ke qara ruftowa Yana matsowa inda Sameer din ke kwance,qoqarin ja dabaya yakeyi ganin Ramin na kusantoshi qafafuwansa sun gaza motsawa daga inda yake kwance gaba daya sun shanye ga wata qara dake barazanar fasa dodon kunnansa Nan take ya summe awajan idanuwansa suka kakkafe samma,tabangaran SÂMÊĒHÂ kuwa Duk yanayin da Sameer ya shiga haka SÂMÊÊHÂ ta kasance sai dai ita cikin wani qaton daki ta tsinci kanta Wanda Bata ganin farkonsa da qarshensa ita dai kwance take atsakiyar dakin qasusuwan jikinta na motsawa Kamar zasu bar sassan jikinta Dan azaba ga wasu irin mucizai manya manya masu fuka fukai dasuka zagaye Sameer dinta dake kwance agefe Yana gunjin ihu da naiman taimakon Sameeha duk San fasa Kai suna furzar da dafin dake fita daga bakinsu Sara suke kaiwa Sameer ta ko Ina Yana ihu Yana ambaton SÂMÊĒHÂ SÂMÊĒHÂ tai taimakeshi gashi ta gaza motsawa daga inda take bare ta kawowa Sameer din dauki fuka fukansu suka bude suka fara janshi sama suna wata iriyar qara mara dadin ji da sauraro SÂMÊÊHÂ tayi qoqarin ambaton Allah Amma hakan Sam Bai samuba saima 6amewa da bakinta yayi alokacin ko motsashi bata iyayi ga jikinta duk amace ko yatsa takasa dagawa sai wasu siraran hawayen dasuke bin gefan idonta har mucizan sukayi samma da Sameer Sameeha na kallo sai qarar kururuwarsa daya cika cikin dodon kunnanta ahankali hankalinta ya gushe ta summa a wajan itama.....
★★★★★★★Yau kam tunda Safe Momy ta umarce duk wasu masu aikin gidan da kowace taje ta hado inata²inata zata gansu idan sun karya kummalo dakanta yau tashiga kicin ta sarafa abincin da zasu karya dashi na Sameer da sameeha ta zuba afilas ta shirya komai cikin kwandon jera abinci ta nufo sashin nasu da kanta da kwandon brfs ahanunta sai taku take dai dai da dai dai harta qaraso qofar part din, Danna qararrawar dake mane agefan qofar Momy tayi cikin abinda Bai wuce sakanniba qararrawa tafara qara,qarar qararrawar yasa Sameeha saurin bude Ido ganin inda ta tsinci kanta yasata miqewa zaune da sauri tana waige²waige.
""Shin ya akai nagani anan?waye ya maidoni nan ko dai mafarki nakeyi ya Allah kasa abinda nagani ba gaskiya bane mafarki nake............idanuwanta suka sauka akan Sameer dake kwance agefe Yana bacinsa kashir6an hankali kwance murza idonta tashigayi tabbas idonta biyu amma......tayi saurin Kai hannu da zumar ta6ashi qarar qararrawar tasake kadawa ahankali ta zamo daga gadon tana duban Sameer da jikinta kayan da aka kawota dashi din dai sune ajikinta"Shin Mai yake Shirin faruwa Dani ne ni SÂMÊĒHÂ ta furta chan Kuma ta dai kauda tunanin datake tayo qofar Dan budewa taga waye hannu tasa jikin mukulin qofar ta murda tayi sororo tana qif qifta da Ido Kamar munafuka.
Momy ta gani tsaye da kwando ahanunta da sauri tayi qas da kanta tana duban hannunta tace.
Ina kwana.
Lafiya Lau my Sameeha ya baqunta.
Shiru Sameeha tayi duk ta dabar barce kunya ta kamata Momy tayi murmushi tace.
Ungo wannan brfs dinku ne Naga alama yanzu kuka tashi ma idan kun kammala kicewa My son kusaman a fallo Ina jiranku Dan Allah kici abinci Naga Kamar kin fada kinjini ko,Kai SÂMÊĒHÂ ta gyada ta kasa dagowa suyi Ido biyu da Momy wani bala'in kwarjini Momy tayi mata magana ma takasa maida mata tsoronta da kwarjininta yasa Sameeha ke jinta kamar wata yarinya qarama 'yar shekara(4)😳,Hannu biyu tasa ta amshi kwandon har Momy tayi nisa Sameeha ta kasa miqewa daga bakin qofar ji take kamar agaban Momy take,tashi Sameer yai daga baci ko Ina najikinshi na ciwo shiru yai Yana nazarin abinda yake Masa yawo cikin qarqashin zuciyarsa Amma bisa zahiri yakasa tantance meye shi din,, Sameeha,,ya furta afili ya juya gefe da gife Bai tozali da Sameeha ba gashi dai kayan dasuke jikinsa stl yanzu ma sune ajikinsa meya hanshi chanzawa shida yasan jiya sunshigo dakin tabbas danya Yi wanka su sauya kayan jikinsu Amma meya hanashi yin wankan?tambayar da ba amsa ya jefawa kansa, ahankali ya miqe yafara duba inda Sameeha take,kaf dakunan saida ya shiga Babu Sameeha babu dalilinta Jin wani motsi yayi afalo alamar akwai wani awajan agauce ya nufo Fallon Yana Rana idanu,zaune take aqofa aduge takasa Koda motsawa daga inda take Sameer yaqaraso hade da Kai hannunsa Kan kafadar ta ya dafa bayanta.
Samee.
Na'am,ta amsa masa tasamu damar juyowa gareshi jitayi kamar ankwanceta daga daurin da akayiwa qafafuwanta dasuka kasa tashi😳 Sameer ya dubeta.
Me kikeyi a bakin qofa kika zo kika zauna anan Samee.
Kaga,ta nunawa Sameer kwandon abincin,'Momy ce takawo Mana tace idan mun gama karyawa tana fallo tana jiranmu Dan Allah muje yanzu muji abinda takeso muyi mata Kar mubari tayi ta jiranmu har ranta ya 6aci,bayani takewa Sameer kamar wata doluwa Sameer ya numfasa ya tallafo Sameeha da hannunsa daya,dayan Kuma ya dauki kwandon yace.
'Taso muje muyi wanka mu shirya Kinga bamaje mata ahaka ba ko karyawa bamiba zatayi mun fada nabar 'yar mutane da yunwa Wai ya akai nayi baci jiya ko kaya bamu sauyaba.
Shiru gaba daya sukayi acikin zuciyoyinsu tabbas abinda yafaru adaran jiya na Nan Amma azahirin gaskiya abun na neman kaucewa daga bakunansu duk kansu sun kasa sanar da junna abubuwan daya wakana cikin mafarki ne ko a zahiri.
Duk wani shiri sun gabatar dashi Sameer dakansa ya hadawa SÂMÊĒHÂ ruwa tashiga (bayi)tayi wanka atamfar da zatasaka shiya fito mata dashi sannan yafada bandakin danya Bata waje ta kintsa ganin duk ta takure jikinta kunya da tsoransa sun bayana afuskarta,da hanzari tayi gaggawar shiryawa ta fito Fallon Dan shirya (dining)da duk abinda zasu buqata naci Sameer na shiryawa adaki,hadaddan wani yaddi yasako kalar daya daga cikin kalolin jikin atamfar Sameeha yaddin ya amsheshi yai Masa kyau sosai matuqa gaya abinka da kyan angwanci yafito da kyansa da 'yar yarintarsa yasami Sameeha tsaye tana hada musu brk,fas tana ganinsa tayi qasa da sauri da murmushi afuskarta ganin kyan da angwan nata yasha tace.
""Barka da fitowa hasken farin wata Sha kwallo,da murmushi ya fara aika mata kana ya furta.
Ai idan kaga wata to lalai zakaga Zara Sameeha ke tadabance acikin mata nadade Ina godewa Allah daya bani mace Mai hankali da ladabi da biyayya Mara son abin duniya Ashe duk dagewar danayi akanki ba banza ba ke kyautace daga Allah nasan nayi dacan mata mai kyaun suffa da zuciya ki zauna yau Ni zan ciyar da matata da wannan hannayen nawa Kamar dai jiya Amma fa nima sai kin ciyar Dani da kyawawan hannayenki masu albarka ki fara kwasar ladanki tun daga yanzu ba wata kunya.
Kash gashi hannun nawa ciwo yakeyi Samee,ta qarshe maganar cikin zolaya.
Ko zai cire sai an bani ahaka Kinga idan ma ya fita ta hanyar samun lada ya cire saina baki nawa.
Amma ai.......Kinga Sai fa kin ciyar da Dan jaririn mijin Nan naki ko Zaki Kira Umma,harara ta jefawa Sameer tace.
Au zolayata kake Allah zan fasa.
Ya haquri samee na kina fasawa Ina saka miki kuka.
Qato dakai.
Lalalalalalalala Ni dinne qato........Sameer ya bare baki Yana kukan qarya idonsa Sameeha ta faka ragowar kazar data dako musu daga oven ta dumama tazari cinya guda daya qatuwa ta Danna Masa abaki charaf ya Kama hannun Sameeha da hannunsa yana kokawa da cinyar kaza a baki,kunya ce ta dabaibaye Sameeha tafara qoqarin kwacewa tana dariya shima Sameer dariyar yake ya qara riqeta gam Yana zolayarta ahaka cikin nishadi da Jin dadi suka karya tsaf suna hira a tsakaninsu Sameeha ta Dan saki jiki da Sameer sosai sukasha soyyaya akan tebir din cin abinci.
“““““Fallon baki duk masu aikin suka taru maza da mata suna jiran Momy ta qaraso,Mai girki da mai goge goge sai Mai share harabar gidan daban ruwa wa fulawowi da mai wanki da guga harda Mai gadi da dan'aike wato Mai cefane kowa kaganshi kulle yake da 'yan kayansa Yana jiran hukuncin da Hajiya zata bada gaban kowa na dukan 3-3, shigowa tayi tasha kwaliya kayan jikinta ba qaramin amsarta sukayi ba ga wani dadadin qamshi da giftawa tayi sai yadaki hancinka sai wani basarwa take tana hada Rai kamar wace aka aikowa da saqon mutuwa,kushin taje ta zauna adosane tafara kada qafa tana duban kowa dai dai dasukayi tsuro suna jiran Mai zata furta, numfashi taja kana tace""""""
""Nataraku ne badan komai ba sai Dan sallamar wasu daga cikinku,babu wanda ya 6atan ko yayi abinda yakarya dokata daga cikin dokokin Dana shimfida muku illa wata dama Dana samu yanzu da zan amfani da ita acikinku akwai wa'yanda zamanmu dasu yazo qarshe badan komai ba sai Dan zamansu atare dani bazai amfaneni da komai ba Dan haka zan sallameku kuje gaba ko Allah yasa ku samu wani gidan aikin ku cigaba nidai nawa ya qare daga yau,Momy ta qare da duban wani dattijo.
Baba Mai gadi Allah yasoka baka daya daga cikin muta Nan da zan sallama Ina fatan zaka tashi ka koma bakin aikinka.
Godiya nake Hajiya Allah yaqara girma da daukaka,baba Mai gadi yamiqe da qullin kayansa ya fuce daga dakin.
Jalolo kaima baka daya daga cikin Wanda zamansu yazo qarshe agidan nan katashi kabani waje,,.
Da girman kujerarki Hajiya badai mutum da aljan ba Nan gani Nan Bari maqiyanki faddawanki masoyanki Adama mahassadanki ahagu godiya nake farar tumfafiya jalolo yamiqe yafita Yana Mai fasawa Momy kai.
Duban balla Mai wanki da guga Momy tayi kamar zai fashe da kuka tace.
Bala.......Hajiya tuba nakeyi ayi mun aikin gafara Babu inda zanje in rufawa kaina asiri da yarana sama da gidanki Hajiya ki taimakeni yadda Allah yataimakeki ki rufan asi............Kai dallah rufe min baki anan Bala wani irin gaggawa ne haka bakajira abinda zai fito daga bakina ba kacika mun kunne da haushi ko dadin surutunka zai hanani zartar da abinda zuciyata ta ayana ne.
Tuba nake Hajiya kaina bisa wuyana duk agigice nake wallahi.
Kasani sarai bana Son ban-badanci idan nace zanyi Babu Wanda ya isa ya hanani koya sakani katashi kaban waje ka koma mazauninka Kar in qara bude baki katsomomin wannan dagajajjan bakin naka kagane.
Na gane hajjaju Godiya nake Hajiya Allah shi qara girma ya Raya zuri'a,Bala ya miqe yabar dakin.
Tafa dakai da ladi da suwaiba Ina Mai baku haqurin Gama aiki agidan nan badan kun 6atan kona gaji dakuba nariga dana sanar daku Babu wani amfani dazakuyi yi mun idan kuna tare dani Dan haka kowane zan bashi (1000k) yaje yaja jari kudin sallama idan Kuma kunsami wani gidan kwa iya cigaba da aikinku.
Gaba dayansu sukayi godiya tabbas kudin da Momy tabasu shiya wanke tabon da zuciyarsu ta samu tun sanda Momy tasanar dasu su hada kayansu ba yanda suka iya mai gidan ta sallamesu hade da kudi masu yawa bazasuga qosawarta ba ko rashin adalcinta ahaka sukayi sallam da sauran ma'aikatan kowane yayi hanyar garinsu Yana jimamin rabuwa da gidan daula duk rashin mutuncin 'yan gidan zakaci Mai kyau kasha Mai kyau ka kwanta amai kyau har Wanda ke kusa dakai ya dandana........
*SHIN MAI MOMY TAKE NUFI DA SALLAMAR MAI SHARA DA GIRKI DA BAWA FULAWOWI RUWA?.*
*MAI YASA TAKE NEMAN SAMEER DA SAMEEHA?*
*SHIN MAFARKI SUKAYI KOKO A ZAHIRI NE?*
*_By,Mmñ @ff@ñ✍️_*
