WAYAFI SONTA 16
Page 16
*India*
Tun acikin jirgi zainab ta Kama kanta" duk abinda aka bata bataci...yyinda Dr Kamal da faruq ke lura da ita!
Koda suka sauka ak'asar , straight hospital suka nufa , kasancewar Dr Kamal yasani sbd anan yake aiki ,byn wasu watanni yaje gd...hutu yadawo..... zainab dai sai kalle kallen ta takeyi ,tana mamakin Wai yau itace a India...tabbas tayi k'auyanci "Amma à zuciyar ta!d'aki 2 akabasu! Zainab 1 sai su2 guda..Cikin ikon ALLAH byn anbinciki zainab aka azata kan magani!
Yyinda faruq Yana waya da
mutanen Abuja suna jin labarin komai har zuwa yau ,da ake Shirin shiga da
zainab d'akin aikin...
Tsaye zainab take da rigar da
ake sawa in za'a shiga aikin..Dr Kamal na gefenta , kasancewar hardashi za'a
Mata aikin...faruq kuwa Yana zaune yanata kallonta ganin yadda dukta damu
,idanunta cike da k'wallah! Kiyi hakuri zainab insha ALLAH za'a samu nassara
kidaina jin tsoro"kinji?" Cewar faruq Yana kallonta!
Kamal yadubesa yace Ashe
kaima kalura da tana cikin damuwa?" Eh wlh Yaya Kamal!
Zainab dai na saurarensu har
suka gama surutunsu ,sukajira sauran doctors d'in aka shiga da zainab cikin
theater room d'in...
Alhmdllh Masha ALLAH! anyi aiki cikin
nassara dukda zainab dai Bata mgn amma doctors sunce ,bada anyi aikinba zata
Fara mgn". sun azata kan magani, yyinda zainab jikinta yyi sanyi azatonta
ko dai bazata sake mgn ba!
Shikansa faruq yarasa me
zaicewa su hjy da anty mariya da ke kiransa danjin Yaya da nassara
Ko Babu?"sai dai yace
musu ai zainab d'in nagun doctors tukum su saurara....
Ayau yakama su zainab zasu
tafi gd Nigeria" yyinda zainab jikinta yake asanyaye "har yawo faruq
yace Mata suje" waidan taga gari ,tarage damuwa da kad'aici...amma fafur
tak'iya"
Suna zaune acikin jirgi! Wayar Kamal tayi
ringing yad'aga! Naji yace Muna hanya ai! Eh wlh har yanxun" pls karka
damu komai zaizama normal insha ALLAH... Dg faruq har zainab kallon Kamal kawai
sukeyi" yyinda suke mamakin to dawa yake waya Wai?"
Saidai tambayar sa b
ahuruminsu bane musammun zainab ma...
Koda suka sauka driver d'in
DSP ne yazo yad'aukesu !
Dg faruq har zainab kowa
gabansa faduwa yakeyi"akan rashin nasarar aikinta...da wannan tunanin
sukazo gd....jiki asanyaye zainab ta fito dg mota tabi bayan faruq suka shige
waiting parlourn gdn...da gudu elham tazo ta rungume zainab tana dariya had'e
da cewa I miss you so much anty zainab?"granny tace bakinki ya warke
ko?"girgiza Kai zainab tayi hawaye na zuba afuskarta...da sauri faruq
yajanye elham hjy ta taso takama hannun zainab suka zauna gefen kujera "
Ahankali hjy tace Masha ALLAH
zainab karki karaya duk Mai nema gun ALLAH baya karaya"nassara nazuwa
tunda likitoci sun tabbatar insha ALLAH zakiyi mgn to damuwar me zakiyi?"
D'azun munyi mgn da mamanki ,nama nuna Mata kunacan India sai sati nasama zaku
dawo! Nasan uwa da k'ulafucin d'anta "nasan ta k'agara ,sanar Mata yanzun
hankalinta zai tashi zainab!
D'aga Mata Kai zainab
tayi...kafin hjy tayi mgn anty mariya tashigo" tazauna gefen kujera tanama
zainab sannu da zuwa had'e da nasiha... k'amshin turaren sa taji yadaki hancin
ta!da sauri zainab ta d'ago"sanye yake da farar shadda riga da wando"
rigar batakai gwiwa ba,kansa bbu hula yasha gyara sai salki yake"fuska
atamke kamar kullum"da sallama suk shigo shida amininsa Dr Kamal!
Had'a ido sukayi shida zainab"
tanamamakin ganinsa da manyan kaya"atake zainab ta had'e Rai had'e da
wurgomasa harara! Sbd tunawar datayi dan maganganin daya yab'a Mata aranar
dazasu tafi..dukda k'udirinta nan na barin gdn in ankwana2..
Cike da mamakin yarinyar DSP
yazaro Ido had'e da nuna Mata kansa" alamar shita harara?" Bbu kunya
zainab ta d'aga Kai"
Hakan Kuma yafaru akan idon
kamal dake rusunawa suna gaisawa da hjy" yyinda dsp yak'i Zama parlourn
sbd jin haushin zainab" dukda yyiniyar Zama....part nasu ya wuce...bayani
sosai Dr Kamal yyiwa hjy gameda matsalar zainab yakuma kwantar Mata da
hankali....kafin yatashi yabi DSP...
Zaune yasamesa kan kujera ya'aza k'afafun
sa kan center table" Yana girgiza su idonsa arufe"Zama Dr Kamal yyi
agefensa,yyi gyaran murya had'e da cewa my man how fer?"
Guntun tsaki yaja had'e da cewa bbu komai
kasan sha'anin aiki!...dariyar rainin hankali Dr Kamal yyi had'e da cewa ranar
nike jira yau gashi tazo wlh!
Harararsa dsp yyi "yace
mekake nufi da zancenka?"
Eh abinda Nike nufi kanason
zainab yarinyar nan" koka yarda ko karka yarda Amma wlh kana mugun SONTA!
Inbason ta kakeba ,minene abin kabiya Mata kud'i amata aiki Amma ka b"oye
kace Alh ne yabiya dukda nasan halinka inkayi taimako bakasan asani"sannan
meye dalilin ka nayawan kirana gameda jin lafiyarta,dakuma nuna tsantsar damuwa
akan ba'ayi nassara ba ???"sannan yanzun aparlour Ina lura daku Kuna
tsokanan juna!
Kagama labarin k'aryan?"
Cewar DSP Yana yatsina fuska..murmushi Dr Kamal yyi yace nasan zakace abinda
yafi hakama,tunda baka tab'a son wata mace ba ,saidai Kai asoka! Da alama itama
tana sonka...dallah malam in wannan surutun banzar yasaka kabiyoni kayi
gaba"baka Kuma canka daidai ba,ni banasonta,kawai dai na tausaya Mata akan
kiddnaping d'in ta da akayi sbd ta tseratar da mahaifiyata da duk duniya nafi
so da k'auna...bacin hakan bansan komai ba,zankuma yimata hukuncin hararata
datayi... yafad'a Yana tashi tsaye yashige bedroom dinsa...
Murmushi Dr Kamal yyi sbd
yafi kowa sanin halin DSP ! Hakan yasa dg shi dai saif suka d'aine abokansa na
k'ud da k'ud suma suna hakuri dashine....tashi tsaye Dr Kamal yyi yace ALLAH
yakyauta....yanufi k'ofa da sauri faruq yyi baya jikinsa asanyaye sbd yaji duk
maganar da yayansa da amininsa sukayi...Koda Kamal yahansa bekawo komaiba yyi
Masa sallama yawuce...
***************
Yau kimanin kwana 3 da
,dawowar zainab dg India!Zaune suke itada anty mariya" suna fira dukda
zainab nacan duniyar tunanin labarin da anty mariya ta bata Wai DSP ne yabiya
Mata kud'i aka fiddata waje....gaba d'aya jikin zainab yyi sanyi" sai
yanzun take Dana sani da nadama akan abinda tamasa rannan, sannan bata mance
lokacin da yatarbe kunu yak' onasa sbd ita! Gsky bata kyauta" Dole taje
tasamesa tabashi hakuri kawai....hawaye taji sunxubo Mata afuska...da mamaki
anty mariya tace ke lfy kike kuka?"
Wai zainab bazaki k'ara
hakuri ba! Kinsan me ALLAH ya tanadar Miki?
Girgiza Kai zainab tayi!
kafin tawuce d'aki Jim kad'an ta dawo da paper ahannunta ta mikawa anty
mariya....karb'a tayi had'e da karantawa" Baki kyautaba zainab meye dalilin
ki na hararar babban mutum kamarsa ?" DSP ba yaro bane wlh inda auren wuri
aka Masa yahaifeki ," dudu shekaranki20 shikuwa 40 years garesa! Zaro Ido
zainab tayi"azuciyarta tace nadauka be wuce 34 years haka...kije kibasa
hakuri nagaya Miki ,inkuma kinason yamiki kallon marar kunya da tarbiyya to!
Tashi zainab tayi tama anty mariya sallama ta koma part d'in su hjy....
B'angaren faruq kuwa tunda yaji firan Dr Kamal da DSP ,yyi dogon nazari da hangen
nesa"wato Ashe shine ke yawan Kiran Kamal yaji ya jikin zainab, sannan ya
lura inyaganshi tare da zainab yake d'aure fuska! Yatuna lokacin da yadakko
zainab sadda aka yi kiddnaping d'in ta" Yana rik'e d hannun,,Kuma suit
nasa ajikinta! Tabbas yayansa nason zainab" Dole yahak'ura ya yakice zainab
dg ransa,Amma harga ALLAH ya na SONTA da k'aunarta!Amma bazaiso macen da
yayansa kesoba,sbd yalura shi har yanzun DSP be yarda son zainab
yakeyiba"saidai k'arshe irin wannan soyayyar tafi zafi da wuyar rabuwa
,dakuma illah...inkuma suka had'a kansu to zasu buga love! Dole yahak'ura da
ita kawai! Yana k'aunar d'an uwansa dabeda kamarsa aduniya" dg yanxun
zaikoyi mgn da ita bbu murmushi ko wata mgn dake nuna Yana SONTA!saidai kawai
agaisa...
Wanke wanke takeyi tana
atsaye a kitchen!tana cikin wanke wuk'a cike da tsautsayi ta yanke....
innalillahi! Ta furta afili" waininayi mgn?" Cewar zainab Akid'ime
tana zare Ido Dan son tabbatar wa! Alhmdllh Alhmdllh!! ALLAH nagode
maka....Nike mgn da bakina ni zainab?
SaiKace nafarki" tafad'a tana d'aure
yatsanta da wani k'yalle....aje kayan wanke wanken tayi ta fito dg kicin d'in
tana murmushi.... adedenan Kuma DSP ya shigo waiting parlourn gdn....suna had'a
ido da ita!ya k'ara tamke fuska ,yabi tagabanta ya wuce....YAH HAIDAR! tafad'a
cikin siririyar muryanta....da sauri DSP ya juyo Yana kallonta cike da mamaki
saidai bai nuna afuskaba sbd tsabar miskilanci"saikuma yatunada Kamal yace
zatayi mgn insha ALLAH to yaushe tafara maganan?"
Juyawa yyi yayi tafiyar
sa....waigawa tayi taga bbu kowa da sauri tabi bayan sa....
Murd'a k'ofar tayi ta shiga
baya parlourn" knocking d'in k'ofar bed room d'in tayi sau 2"afusace
ya bud'e sbd bemayi zaton itaceba,azatonsa wanine cikin security d'in dake
bakin get! Dg shi sai farar vest da wandon yunifoam, kasancewar Yana cire rigar
tayi knocking...Koda yaga itace sai ya k'ara had'e Rai yace lfy malama?"
Kallo d'aya tamasa tadauke
Kai.... ahankali tace Yaya haidar kayi hakuri Dan ALLAH bazan koma
ba"kayafemun...yamutsa fuska yyi yace akanme zanyi hakuri?"kinmun
wani abune?" Inma kinyimun to fad'a mun naji"zainab azuciyarta tace
gsky mutumin nan akwai son yarfa mutane....Kai duk'e tace na harareka ranar da muka dawo dg India!
Murmushin gefen Baki yyi kafin yace meye
dalilin ki na hararata ?" Ni sa'ankine?"ah ah pls kayi hakuri...bazan
komaba!
Kinason nahakura ne?" Da
sauri tace eh"
