WAYAFI SONTA 19
Page 19
Marigayi Umar ta tuno alokacin da ya bata wayarsa shi yahak'ura"Fatanta ALLAH ya jik'an sa rahama" bazata gusheba Gurin yimasa addua sai tabar numfashi...
DSP kuwa asace yaketa kallon zainab batare data saniba" yakuma fahimci"cewa tana cikin farinciki,dakuma tuna wani Abu marar dad'i....muje ko!cewar DSP Yana bud'e motar"zainab tayi ajiyar zuciya tafito ahankali tana k'arewa wurin kallo... azuciyarta tace oh dama haka station d'in nasu yake?"
DSP yabita da
kallo"kafin yace yau gaki a police station ko?" Saina saka
arufemunke! Yafad'a Yana murmushi....itama murmushin tayi had'e da cewa Kai ka
Fara baccin hjy tace maka amanah" hakanefa Kuma, yafad'a suna tafiya jere
gwanin shawa'a....
Gaba d'aya sai kallo yadawo
gurinsu"anata k'us k'us,wasu nacewa ai k'anwarsa ce wacce akayi kiddnaping
d'in ta.wasu nacewa ah ah wacce zai aura ce...Sarai DSP ya lura da kallonsu da
akeyi ,amma ko ajikinsa ,sai office ma ya nufa zainab na bayansa"
Wani sanyayyen k'amshi yadaki
hancin ta" ta lumshe Ido ....komai agyare tsab acikin office d'in
nasa..kujerar dayake Zama yanuna Mata had'e da cewa" come & sit down
pls!
Zama tyi tana kallon files
d'in dake kan table d'in gabanta"
Telephone yalatsa yakara
akunne"kana Ina ne?"ok jonamun CTV camera dg cell d'in zuwa office
d'ina....ajiyewa yyi,yajawo wata loka, yafito da wata k'atuwar big borm
,yab'are had'e da tsotsa yagutsira"yadubi zainab daketa kalle kalle da
dube dube" hii my friend! Kallonsa tayi yamik'a Mata big borm d'in Kisha
kinji?" Girgiza Kai tayi"daure fuska yyi bece komaiba! da sauri ta
karb'a tasaka ad'an tsukakken bakinta!wasu chacoolate ne yasake fitowa dasu ya
ajiye agabanta"
Kafin yyi swech off d'in
plasma d'in dake jikin bango...atake wasu mutane su 2 suka bayyana jikin
akwatin tv d'in... zainab ta maida hankalinta akan tv d'in"wasu k'atti ne
suka fito ta wata k'ofa da sanduna sukafara duhumar mutum 2"rintse Ido
zainab tayi had'e da cewa Inna lillahi! Pls kasaka amusu mgn sudena
dukansu.....kallonta yyi hankali kwance bbu wani tausayi a idonsa"yace
jiyane akamusu dukan ai!amma kincika tsoro dakuma tausayi"kauda Kai tayi
ta Dena kallon tv d'in tace pls Yaya haidar ni gd zanje dama haka kukeyi
astation d'in?"taf ai bbu inda zakije yarinya"turo baki tayi cike da
shagwaba tace basai nakira hjy ba ta turo amayar Dani gd"dawace wayar
kenan?"cewar DSP Yana kashe tv d'in...
Da wayarka Mana "
Wayoyin nasa duka yamik'a
Mata had'e da cewa inkinsan pass word d'in kicire saiki kirata....kallon
wayoyin takeyi batayi mgn ba"yanzun tashi muje ki rakani "d'age
kafad'a tayi alamar bazata jeba! Ok sarkin tsoro saiki jirani,inkinji bacci ki
kwanta,ga wayoyina nan...bejira cewar ta ba yafice had'e da rufeta acikin
office d'in...shiru tayi had'e da yin latse latse awayarsa ko zata iya gane
password d'in"amma ta kasa"ga tata wayar ,Amma sim card d'in be fara
aikiba!
Chacoolates d'in tashigaba
Tasha , yyinda kujera ke juyawa da ita ,ta lumshe ido cike da
nishad'i...Ringing d'in wayar sa tasakata bud'e Ido!kallon screen d'in wayar
tayi taga bak'uwar number! d'agawa tayi had'e da karawa akunne batayi mgn
ba....haba Yaya haidar! Kasan yau zanzo bakaje kad'akko niba,and'akkoni Kuma
nasamu baka nan ,bacin kasan sbd ganin ka yasani zuwa hutun ko?"wani miyau
Mai d'aci zainab ta had'e"ga faduwar gaba dataji sbd jin tamkar tasan
muryar yarinyar dake mgn!hellow! hellow!! Kayi shiru kobaka jina ne nasake
Kira?"ba me wayar bane...cewar zainab cikin fushi,murya adake! Wacece
ke?"kibari sadda naga damar barinsa amsa Kiran mutane saiki tambayesa
yasanar Miki wacece ni agurinsa... zainab bata jira cewarta ba takashe
wayar...tana tunanin inda tasan me wannan muryar amma bata ganoba...
Ahankali DSP ya bud'e k'ofar
ya murdo yashigo"da sallama , zainab wacce harta fara bacci ta tashi tana
kallonsa" shima ita yake kallo"murya can k'asa yace tashi muje
nakaiki gd... kafin tayi mgn ansake Kira da number d'in d'azun...kallon wayar
yyi" yaja tsaki had'e da rejecting d'in Kiran sbd yasan wacce kekira"
zainab kamar tamasa mgn saikuma taga beshafeta ba,duk k'asan zuciyar ta taji
dad'i sosai dayyi rejecting d'in Kiran..
Tashi tsaye tayi ta d'auki kwalin wayarta
tace muje to!
Kema kin gaji da zaman
ko?"
Eh Mana " ni abinda
nagani d'azun yatsaya mun arai,irin wannan duka haka...uhummm danbaki Saba
bane" cewar DSP Yana bud'e k'ofar suka fice...
Yana gaba tana biye dashi suka shigo cikin
parlourn"hjy da bak'uwar zaune kan kujera... sallama zainab tayi cikin
siririyar muryanta" hjy ta amsa fuska asake tana cewa gsky kun
jima,ainazata sai dare kudawo... murmushi zainab tayi had'e da cewa muma Fara...yyinda
DSP fuskarsa adaure sbd ganin bak'uwar'' yace hjy sannu da gd" hjy tace
yauwa!
D'ago Kai bak'uwar tayi"
sukayi Ido hud'u da zainab...zaro Ido zainab tayi tana kallonsu HUSNA! Yyinda
DSP dake zaune kan hannun kujera ke lura da yanayinsu" yalura zainab
namamakin ganin husna, yyinda husna ke yima Zainab kallon bataso sun haduba
dakuma rashin gsky dake tattare da husnar sbd ganin zainab d'in...saidai hjy
batama luraba,idonta na kan TV..
Tashi tsaye DSP yyi zai
wuce....Yaya haidar! Shine bazaka mun mgn ba ?" Katsaya mugaisa. Acikin
nidake waya kamata yagaida wani?"cewar DSP cikin ko inkula..hmmm Dole kace
haka Mana tunda nakira wayarka wata ta d'aga nasake Kira kak'i d'agawa
ko?"
Eh hakane yagd dasu
momy??" Cikin yatsina tace lfy lau"
Kallon zainab yyi wacce tayi
kasak'e da kunne tanajin maganarsu ,amma inkallonta zakayi saika dauka tv d'in
da gske take kallo..
Zainab bara naje nadawo ki
gyaramun d'aki na! What? Haba Yaya haidar gani zaka bawa wata ta gyara maka
d'aki! Cewar husna cikin fushi...dsp
batare da yakalleta ba!
yabawa zainab key d'in yafice dg parlourn...
Husna tayi kwafa had'e da
kallon hjy wacce uffan batace ba.. wacece wannan Kuma hjy"tafad'a tana
nuna zainab" hjy ta dubeta"tace nan gdn take itama , sannan diyar alh
ce mahaifinta k'aninsa ne,banasan fitina dg zuwanki ,kina jina?"
D'aure fuska husna tayi
batace komai ba... yyinda zainab ketunani kusan shekara4 da rasuwar yah uwar ai
ya isa ace husna tayi aure sbd ko acan baya yah Umar ba girmar husna yyiba,
ak'alla yanxun husna tayi 27oh 28 years...tashi zainab tayi batare data sake
kallon direction d'in da husna ke zaune ba...tanufi part d'in su DSP...
Tayiwa bedroom, toilet,
parlournsa gyara ba nawasa ba,tayi kusan awa d'aya da wasu mintina...tana
turare d'akin yashigo da sallama,ta amsa fuska asake"tace sannu da zuwa
"yauwa zainab sannu da aiki"yafad'a Yana karewa parlourn kallo,kafin
yazauna kan kujera Yana maida numfashi...kagaji da yawa ko?" Eh wlh"
Kaje ga ruwa can na had'a
maka kayi wanka!to angama ranki yadad'e nagode...hararar wasa zainab tayi Masa
tana murmushi"
Kafin yatashi yanufi k'ofar
bed room d'in sa"saikuma yajuyo ahankali yakalli zainab wacce itama fitar
zatayi" ahankali yace inaso duk
abinda yarinyar nan bak'uwa zatayi karki biye Mata pls"to shikenan
zankiyaye...batajira cewar saba tafice..
#########
Da dare misalin k'arfe 8:45
zainab ce tsaye akitchen tana dafa indomie, yyinda DSP ke zaune kan kujera Yana
kurb'an coffee d'in da zainab ta had'a Masa...juye indomie d'in tayi tnata
turiri"tana kokarin kashe gas d'in husna ta shigo bbu ko sallama!dg zainab
har DSP yi sukayi tamkar basu ganta ba!
Zainab tasaka fork biyu cikin
plate d'in ta ajiye kan table d'in dake gaban DSP,kafin ta ja kujera ta zauna
" cike da shagwaba tace pls Yaya bissimillah! Uhum nasanki da cin yaji beyi
yajiba?" Eh Mana...keeee! Samun wuri tusar asuba kina nufin tare dashi
zakici ko meye?""cewar husna tana huci.. Bbu Wanda yace Mata
kanzil" k'asan zuciyar zainab fal farinciki sbd dama dan husna ta ji
haushi tace suci tare..
Fork d'in yasaka ,itama tasaka
suka Fara ci...wani mugun kallo husna ke binsu kafin ta fice...tana cin
alwashin Dole tayiwa zainab gargadi na k'arshe akan DSP sbd yarinyar nashiga
hancinta da k'udundune....
Husna na fita zainab tayi
saurin Jan plate d'in tana cewa to wacce kaci tayi Aiko?" Tunda tayi na
maka.
Kallonta yyi sbd yagane dan
ta k'untatawa husna tace suci tare...yakuma lura akwai wani Abu tsakaninsu da
juna,amma zai bi komai ahankali...cikin cool voice yace hmmm aikuwa yarinya
Baki isaba ,dg yanxunma tare zamu ruk'a cin abinci...gwalo ta Masa ta fice da
gudu dg kitchen d'in...
Duk abinda tasan al'adartane kafin ta kwanta
Saida tayi,kafin ta musu addua itada elham" sannan ta kwanta da tarin
tambayoyi fal aranta gameda husna..shin meyasa husna ta nuna alamar rashin gsky
data ganta?" Meyasa hjy tayi sauyin xance tace ita diyar alh ce?"
Wata zuciyar tace sbd gudun kada zainab ta wulak'antaki ko yimiki gori! Sannan shin dsp nason husna
kokuwa husnar ke haukanta??""murda'k'ofar akayi da k'arfi aka turo
husna ce ,tamkar anjehota batabi takan rufe k'ofar ba " tafara mgn cikin
gadara had'e da izzah! Umarni nazo nabaki ba shawara ba ! Kifita harkan Yaya
haidar! Kokuwa kibi d'an uwanki inda yatafi..zaro Ido zainab tayi had'e da dafe
k'irji! Tace mekike nufi da fad'in hakan?"
Dariyar rainin hankali husna
tayi kafin tace Ina nufin Umar yayanki,Wanda yake Miki son daba yayiwa
kansa" meyasa kikeson had'a hanya Dani?" Bacin mu basa'anin juna
bane?"tadalilinki ne Umar yatsaneni yagayamun maganganu masu zafi da
ciwo...hakan yasa ni alwashin rabaki da duniyar ,dg baya nadawo rayuwar Umar
,inhar na auresa sannan Zan d'andana Masa azabata!
Saidai kash" lokacin da
nataho da mota me bak'in glass atsiyace Zan tashi dake! Sai Umar yatureki kika
fad'a kwata,shinabi takansa,dukda naso kada hakan yafaru amma bbu yadda zanyi
tunda kinada rabon kwana.....Nina kashe Umar nakuma kashe banza bbu yadda
za'ayi Dani sbd ku matsiya tane..gsky na yadda ke jahila ce ta karshe tunda har
kike ikirarin kin kashe Rai! To bari kiji kashe yah umar dakikayi bazai tashi
abanzaba insha ALLAH dukda kina ganin anyi wasu shekaru... maganar DSP kuwa
dakike ikrarin inrabu dashi ko?" To barikiji befi 4 month aurenmu
dashiba....kutumar uba! Cewar husna arud'e.... k'arar dasukaji had'e da hasken
flasha yasakasu yin shiru...da sauri husna ta nufi k'ofar da tabari bud'e,kafin
ta iso anjawo k'ofar da k'arfi anrufe....
