WAYAFI SONTA 3
🌺WAYAFI SONTA ?🌺
WAYAFI SONTA ( mmn fareesa)
naira 300
Induka kakeso naira 400 ne
kachal...masu bada kati suyi mgn a wannan number 08100084251....
Inkinsan Zaki fitarmana da
books karki siyasa....
Free page
p3..... cike da mamakin k'aryar
da Musa yasharara mama ke kallonsa Baki bud'e....bata sare da lamarinba.saida
taji goggo haule nacewa,ahto innayi mgn ace ga munafuka kak'i yarda inacikin
bayi inajin yadda take aibatasa.... innalillahi wa inna ilaihir Raju un! Mama
tafad'a had'e da kallon baba tace narantse da ALLAH Wanda yabusamun Rai Kuma
gunsa zankoma wlh duk abinda suka fad'a malam ba gsky bane!iya abinda nasani
zainab ta shigo a guje ta b'uya bayana"inabtambayarta lfy Musa
yashigo....ta Ida sanar Masa yadda akayi....mlm yadubi zainab yace ke gayamun
mekika Masa?"
Zainab taja numfashi tace wlh
baba antasomu islamiyya na mance littafina husnul Muslim gun saratu
kawata,saina natuna ,yanagunta nafasa zowa nan nabita gdnsu" asoron gdnsu
Mai duhu nasami Yaya Musa da yayarta harira " hannunsa cikin hijabinta
Yana....ya isa cewar baba Yana watsawa Musa wani mugun kallo" kuka goggo
haule ta saka Wai mama da y'arta sunhad'a Baki sunyiwa d'anta sharri...baba
yace dama dalilin biyokin kenan zaidaka dankingansa?" Zainab tace
eh...baba yadubesa yace kasameni adakina kaida uwarka...bejira amsarsuba yanufi
dakinsa... goggo haule ta dubi mama d zainab tayi kwafa had'e da cewa insha
ALLAH saikunshiga kuncin rayuwa keda 'yar Taki...mama tayi murmushi tace ba
bakinkiba! duk abinda yafaru damu "munyi Imani damacan ubangiji yarubuta
zai faru...
**********
Haka rayuwa tacigaba da
kasancewa wataran da dad'i wataran sai hakuri"zainab da Umar kullum kwanan
duniya k'ara son junansu suke d Kula d junansu" insunyi fad'a su shirya
"ahaka har Umar yakammala krtunsa yafara service"yyinda zainab tayi
SSCE inta"bayan aurensu da Umar saita Ida karatunta nason Zama Yar
jarida...Umar anan kd aka samarmasa yyi service nasa...hakan yasa Yana gd Koda
yaushe "sannan Yana dinkin Mata"( telane)
Sanye take cikin areviant gownt "
Tasha attachment yazubo Mata har baya"sai kamshi take zubawa"gefenta
naja ce itama taci wanka"parking husna tyi tana yatsina "ta zuge
glass d'in motar tana k'arewa gdnsu Umar da zainab kallo ,kamar yadda jiya da
dare aka kawota har k'ofar gdn aka nuna Mata , kasancewar itama anan kaduna
take" shine yau tadawo Dan Fara cin manufofinta akan Umar...zainab dake
doso layin ,tun dg nesa ta hango wata arniyar mota tayi parking agaban
gdnsu...har zuwa lokacin da husnah tafito dg motar tacire faskeken glass d'in
fuskarta tanawa naja mgn...daidai lokacin da zainab ta iso zata shiga gd da
markade ahannunta " wata faduwar gaba zainab ta ji ganinsu husna dakumjin
muryarta tanawa naja mgn"sak muryarta ta yarinyar datace ita buduwar yah
Umar ce....Amma sai bata sake kallonsuba ,tayi saurin shiga gd ,tasami mma
gaban murhu ta ajiye Mata markad'en,tana cewa bara na dawo mama" mama tace
kada kiyi nisa kinsan bansan yawace yawancen da bbu dalili...gdnsu yah Umar
zainab ta shiga ta lab'e zaure tanajiyo maganar su Inna da husnah...bayan
wucewar zainb su husna suka shiga gdnsu Umar" naja sai wani yatsina fuska
take had'e da toshe hanci...sallama sukayi ,Inna dake fama da hura wuta ta amsa
musu "tana kallonsu da mamaki Dan tasan badai k'awayen Maryam bane (yarta
ta5) Dan tasan sun wuce ajin Maryam azatonta ko wni gu suke nema...maraba ta
musu had'e da Basu kujeru y'an tsigunne suka zauna suka gaisa...Inna na lura da
yadda suke k'arema gdn kallo da yadda naja ke toshe hanci...kafin tace yara!
Meke tafe daku,ko wani guri kuke nema??" amm mama ba haka bane,cewar naja had'e da da nuna
husna tace wannan sunanta As'ma'u y'ar
gdn Alh mukhtar dalah...Inna ta zaro Ido sbd tasan mukhtar dalah Yana
cikin manyan masu kudin kaduna...najah tace to shine suke makaranta guda d Umar
na nan gdn jininsu yahadu danata sosai suna son juna shine dg baya yace Wai
tahakura auren gd za'amasa...Inna ta dubesu Dan tasan dama makarantar da Umar
yake gwamnati ke biyamasa sbd k'okarinsa...subasuda halin sakashi kodaba ba
takudiba.. Inna tace shi Umar din yafad'a muku haka?" Eh cewar najah had'e
da cewa to yanzun ita Kuma babanta yabata damar ta fito da Wanda takeso ,shine
tasanar Masa Umar ne zabinta "to yace Umar yaturo bayan sun Gama service
nasu sai ayi auren...ayanzun zai canza muku gd yabawa Umar mota da kud'i yaja
jari....Da sauri Inna tad'agawa naja hannu had'e da cewa ya isa! nasan waye
Umar...Amma kiramunshi awaya kice yazo inajiransa....najah takalli husna ta
kiftamata Ido...abinda Basu saniba Inna duk tana hankalce dasu...kafin suyi mgn
baba yafito dg d'akinsa Baki washe duk maganar dsukeyi yaji komai...da sauri
suka rusuna suna gaidashi...ya amsa jiki na kirma had'e da cewa Ina surukar
tawane acikinku?"
Najah na murmushi tanuna husna tace gata
nan baba...yyi murmushi yace Masha ALLAH insha ALLAH Muna nan tafe ayi mgn sbd.....haba mlm miye hakane Wai?" Zaka
biyewa yara kana mgn dasu....iya nan zainab ta iyaji" zuciyar ta namata
nauyi kirjinta na buguwa fatanta duk abinda suka fad'a k'aeyane sbd tasan waye
Umar...saidai inta tuna kalmar hausawa dasuke cewa nmj beda tabbas! Saitaji
gabanta yafad'i....hawaye masu zafi suka wanke mata fuska...ta juyo sbd ta tafi
suka had'a ido da Maryam kanwar Umar...da sauri Maryam tace lfy zainab kike
kuka ??" Girgiza Kai zainab tayi batace komai ba tajuya d gudu ta fice....
Maryam ta fita itama Dan Kiran Yaya Umar dake shago yazo yaji meke damun zee...
Baba kuwa kallon Inna yyi
yace Ina ruwanki ?" Kirabu Dani...kafin yadubi naja yace ai tunda
tanasonsa bbu komai dama yarinyar da zanmasa auren gd da ita itama d'iyatace
Dan haka sai abawa wani dama yafito
acikin masu sonta....Inna ranta yakai k'ololuwar b'aci cikin b'acin Rai
tadubesu had'e da cewa Kai yara kubar gdn nan tun muna girma da arziki nafadamu
ko?"baba yace bbu inda zasu sai Umar yazo anyi mgn...da sauri husna da
tund'azun bata mgn tace ah ah baba bara mu wuce munyi mgn da Umar awaya kaidai
kamishi mgn da kanka... tafad'a cikin rudewa sbd bataso Umar yazo yasameta
agdnsu yji bayanin dasuka zo dashi itada naja...kud'i najah ta fito dsu kusan
dubu50 Yan dubu dubu tamik'a baba....hannu na rawa yamik'a dan k'arba.....inhar
kkabawa mahaifina k'azaman kudinki ya rik'e sainamiki abinda yafi Wanda namiki
askul.....d sauri suka juyo su duka sukaga Umar tsaye Maryam na bayansa data
kirasa......
Share
