WAYAFI SONTA 4
WAYAFI SONTA ?🌺
WANNAN LABARIN NA KUDINE...gamai bukata zata biya naira 300 kachal ta karanta " tahanya mafi sauk'i Zaki siya Zaki tura kudin ta account number 0089110527 suwaiba Hussaini zakirai access bank... saikiyi screen shot kituro shaidar kin biya ko kuwa kituro MTN ta wannan number na 300" 08100084251
WAYAFI SONTA ( mmn fareesa)
naira 300
Induka kakeso naira 400 ne
kachal...masu bada kati suyi mgn a wannan number 08100084251....
Inkinsan Zaki fitarmana da
books karki siyasa....
Free page
p4
Murmushi Mai ciwo Inna tayi
had'e da nuna husna ta dubi Umar tace yimana bayani dangane d ita.....da mamaki
Umar yace bayani Kuma Inna?" baba yace Kai dakata! karka maidamu bamuson
me mukeyibane...narigada nagama mgn ita zaka aura....tokodan sbd sune zainab ke
kuka cewar Maryam tana kallon Umar?" dafe Kai Umar yyi had'e da cewa Wai
meke faruwa ne kusanar Dani me wadannan marrassa tarbiyyar sukazo yi anan gdn
??" Inna tace sunxo akan aurenka da itane....najah tayi saurin Jan hannun
husna tace zomuje....Umar yace bbu inda zakuje munafukan ALLAH sainaji me
kukazo kuka cewa iyayena" kafin nadauki mataki.... yafad'a Yana had'e
Rai...baba yace Kai saurara mana dg abin arziki inzainab ka aura uwarme zaka
k'aru dashine?.... Inna ta girgiza Kai kawai tafara korama Umar bayani.....cike
da mamakinsu yake kallonsu....kafin yace...wlh duk k'aryane Inna ,yadube su
yace dake da y'ar tayaki kanfe din duk zaku gane kuranku...wawaye Dana aureki
gara na mutu bbu aure har k'arshen rayuwata"aini kinmun tsufa dubeki
dallah sannan abin nan dakikayi har media saina yad'ashi sbd yazama iznah
gamarasa tarbiyya d kunya irinki....ke ahaukanki iyayen k'warai zasu yarda
d'ansu ya aureki....yah isah haka mlm inkafasa yadata baka k'aunar ALLAH Kuma
saikaga Mai zai biyo baya wlh! Bbu abinda zai gani sai alkhairi...cewar Inna
tanama baba kallon gargadi... yyinda d baba duk jikinsa yyi sanyi yarasa abin
cewa har husna d najah suka fice bayan Umar yamusu tas....shima yanufi gdnsu
zee dan xuwa ya rarrasheta yabata hkri.
Inna ta dubi baba tace wlh kacanza Hali sbd
son abin duniyar ka yyi yawa har kana neman zubda girmanka danamu da yayanka
Dan sbd kud'i kaci amanar zumunci...na tabbatar mahaifin zainab bazaiki bawa
Umar zainab ba sbd yaga Mai kud'i.... sallamar baffa sule( kaninsu baba) yasaka
Inna yin shiru....tana murmushi tace sannu da zuwa mutanen abuja yyi murmushi
yazauna kan kujerar tsigunne dasu husna suka tashi...suka gaisa....Inna na
tambayarsa Mai dakinsa yace lfy
qlau...nan suka hau fira Dan rabonsa d kaduna kusan wata7 kenan acan abuja yake
kasuwancinsu shekaran sa 12 da aure har yanxun matar Bata haihuba...********
Koda zainab ta shiga gd"
parlourn mama ta nufa " tazauna kan kujera ta had'a Kai da gwiwa tacigaba
da kuka...
Mama dake rabon abincin Rana
duk tana hankalce da ita" byn ta idarne ta biyota cikin d'akin t zauna
gefenta had'e da cewa kewai lfy Zaki shigo kina kuka tun d'azun meke faruwa
ne??" Cikin shashsheka tace bbu komai!
Mama ta tabe baki had'e da
cewa nasan be wuce tsaninku d umarba,Kuma nasan bazaimiki komai ba" k'ila
wata kika gansu tareko?" Dan nasanki dazafin kishi y'ar ficiciya
dake...nifa mama bbu komai! Uhumm kikace ba,aidama ana yin kuka Dan
dad'iko?" To Bari kiji ba'a nmj haka! Kuma nmj mijin mace 4 be garama ki
sassautawa zuciyar ki wlh ,Danko bayan ya aureki in ALLAH yace zai k'ara aure
dole yak'ara Koda kuwa baya son matar....koni nan dakike gani kinsan kishiyata
basonta ubanku yakeyi Amma dayake matar mutum kabarinsa saigashi taja raayinsa
ta hanyar surkulle ya aureta gashi harda zuria atsakaninsu to wlh kibi ahankali
sbd shi nmj... sallamar Yaya Umar tasaka mama yin shiru...ta amsa yashigo
yazauna suka gaisa ta fice dg parlourn.,,,,
Kusada zainab yadawo yazauna ahankali ya
janye hannunta data rufe fuskarta dashi ,cikin taushin murya yace haba zee! sbd
wata banxa can Zaki zubar mun da hawayenki masu tsada da...fisge hannunta tayi
tana maka Masa harara tace malam sakeni.... murmushi yyi Yana kallonta yace in
ank'i sakekinfa?wlh zainab banida wata alak'a da yarinyar nan ki yarda
Dani...baza a yarda d'in ba ainaji komai da suke fad'a itada k'awarta saika
hanzarta tura magabatanka tunda baba yace yagama mgn ita zaka aura....Wai
mekike fad'a hakane zeetah ? Kinsan halin baba karsaka maganar shi aranki har
ta b'ata Miki Rai kiyi hkri Dan ALLAH
" wlh banason husna tazone dama Dan ta hargitsamun family ne" akan
abinda yafaru kwanaki to ko yanzunma nazageta da gargad'arta karta koma zuwa
gdnmu...inta sake mezaka Mata?" Duk hukuncin da zeetah ta yanke shi
zanmata... yafad'a Yana murmushi had'e da sake Mata hannu yasaka handcheef
yagoge Mata hawayenta ,kafin yace kin hak'ura?" d'aga Masa Kai tayi alamar
eh"yace sai kinyi murmushi tukum sannan Zan yarda....kallonsa tayi suka
had'a ido...atare sukayi murmushi... adedenan Kuma khalifa yashigo da plate din
wake da shinkafa da Miya da latuce ya ajiye gaban Umar,yace gashi Yaya"
kafin yafice..
Umar yajawo abincin yace
nasan bakici abinciba ko? Tace eh...yamotsa yadebo cokali guda yakai bakinta...bbu
musu ta karb'a ! Tare suka cinye abincin suna dariya tamkar wani Abu be faru
ba....ta rakosa suna asoro saiga baffa sule....yakallesu yyi murmushi yace love
birds...suna dariya suka gaidashi d tambayarsa anty mariya matarsa yace lfy
qlau,kafin yashiga ciki Dan gaisawa dasu mama...Umar yarubi zainab yace kikoma
ciki anjima da dare zandawo naka miki d' inkunan nan kinjiko"" to
shikenan nagode Yaya saika dawo ALLAH ya yatsare" Yana murmushi yace ameen
my real one...Kamar yadda Umar yace haka kuwa yadawo da dare...awaya yakira
zainab dan yasan goggo haule tana tsakar gd tun yau itake girkin dare...sai
k'amshi ketashi ajikin zainab " bayan tasaka doguwar riga ta atamfa
ajikinta ta Dora karamin mayafi tasamesa zaune kan dadduma asoron gdn ga fitila
ya kunna"sallama tayi cikin siririyar muryanta ,ya amsa Yana cewa sannunki
da zuwa gimbiyya ai shanyar dakikayi t bushe, yafad'a cikeda tsokana" tayi
y'ar dariya ta zauna agefensa tana cewa Ina wuni ?" Ya amsa da lfy lau
y'anmatana!yana bud'e ledar hannunsa yace duba kiga d'inkunan kigani sunmiki ?" Tana murmushi tace namasan sunyi "Dogayen
ruguna ne kala3 biyu na material guda ta atamfa sai hijab kala2...d'aga kayan
take tana yabawa cike da d'okinsu da nuna jin dad'in ta" yakafeta d
Ido...Yana murmushin jin dad'in yasakata farin ciki...cikeda zumud'i tace Yaya
Ina zuwa tayi cikin gdn da kayan...tasami mama kan tabarma zaune d khalifa suna
Shan iska tayi saurin azamata kayan gabanta tana cewa mama duba ki gani Yaya
yamun.
Tafad'a cike da faraa...fuska
sake mama ke duba kayan tace Masha ALLAH gsky sunyi kyau" kingode ALLAH
yasa ki kashe d kanki....uhumm dabaa San asalin angulaba dasai ace dg masar
take duk mace Mai rokon nmj Bata daraja wlh...cewar goggo haule cike da nuna
tsantsar hassadarta k'arara...mama tayi murmushi tace oh ALLAH ya shirya
mutumin dake shiga abinda beshafeshiba....yo ai gara wacce zata roki saurayi da
wacce zatace tanason saurayi yace bayasonta....tahad'a asiri yasota adole...gum
goggo haule ta yi d bakinta Dan batasan mama zata Fadi hakaba ..( inbaki yasan
abin fad'a besan Wanda za'a maida mishiba)
Zainab kuwa soro ta koma suka
cigaba da firarsu da yah Umar har 10:pm tukum sukayi sallama....
*********
Sanye zainab take da yunifoam
na islamiyya ajikinta"gaba d'aya yau tarasa meke damunta ?" Batajin
dad'in jikinta ga faduwar gaba datake yawan ji, sannan duk taji batasan
fita...wayarta spack 2 da Yaya Umar yabarmata kyauta ta dauka tayi calling
D'insa... salamu alaikum gimbiyya yata !ta amsa cike da shagwaba tace Yaya
nikazo karakani islamiyya ! Murmushi yyi yace wato yau sarauta kkji kenan
ko?" Kina raina ,inatunaninki kika Kira" nigashi dinkin mutane
nakeyi"to shikenan tunda d'inkin yafini. Matsayi agunka"maida wukar
gimbiyya wasanake bara nazo sai muje ko?" Yauwa Yaya ta fad'a tana murmushi
ta yanke wayar....befi 10 minit ba" yakira ta fito su wuce...
Kallonta yyi byn tafito dg gd yace INASONKI
zainab! Dan ALLAH innamiki laifi kiyafemun kinji?" Arikice tace banganeba
Yaya?" Kamar ya nayafe maka?" saikace Wanda zai mutu har kaja gabana
yafad'i...uhum zeetah ai basai Wanda zai mutu keneman yafiyaba...inaso kimin
Abu 2 arayuwa zainab" cike da mamakin kalamansa tace kamar me? na 1 karki
manta dani arayuwarki na2 kimun addua...gsky Yaya kabari kamar Wanda zai mutu
sokake katayarmun da hankali,nima ai INASON KA! tafad'a cike da kunya.....kafin
ta juyo Dan ganin Mesa yaki mgn,taga wata bak'ar mota ta nufota da gudu....da
sauri yah Umar yature zainab dake gabansa tafad'a bayan wasu yara,itada yaran
suka fad'a kwatar dake bayansu... shikuma motar ta bankesa yyi sama yafad'o
k'asa...atake motar tabargun atsiyace....yah Umar na kwance cikin jini....
arikice zainab ta fito dg cikin kwatar kamar mahaukaciya ta nufesa da
gudu,tarike Masa hannu... alokacin har mutane sun taru agun....cikin kuka tace Yaya!
Tana kallonsa" Yana wani irin nishi yamatse hannunta" yyi murmushi
cike da azaba yace INASONKI zainab! ALLAH ya Baki Wanda...be Ida fad'a ba
yarik'a kalmar shahada....atake Rai yyi halinsa....mutanen dake tsaye Gurin
sukayi kabbara suna cewa ALLAH yakikanka bawan ALLAH! Arazane zainab ke
kallonsu ta tashi tsaye tana girgiza Kai had'e da sakin wata gigitacciyar k'ara
ta dafe Kai sbd yadda taga duniyar na juyamata...atake ta sulale k'asa su
mammiya....ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ Kuyi hakuri haka yafaru badaga gareni
bane...
Share
BY MMN FAREESA🖊️
