WAYAFI SONTA 6
P6
gd zainab ta shiga ta yiwa
mama bayani tana hawaye! Mama tayi godiya had'e da saka albarka ,kafin ta Adana
kud'in har baba yadawo..... xainab ta bud'e alk'ur'ani Mai girma tana karantawa
saratu k'awarta ta shigo d'akin da sallama abakinta" ta zauna gefen zainab
harta idar 'ta ajiye alk'ur'anin ,tad'akko book d biro ta rubutawa saratu cewar
Hamza yazo da abinda yabada... kasancewar itada saratu basa b'oyewa juna komai
k'awayene na ku'd d k'ud..saratu tayi murna sosai da saka albarka....da Abba
yadawo mama tabashi kud'in yagani "yyi godiya....hakan yakasance duk asibitin da baba yaji labari ko
wani Mai bada magani Alan lalurar zainab sai anje ,Amma bbu sa'a aciki"duk
abinda suka mallaaka Saida yak'are akan ciwon zainab"duk masu taimakawa
sunayi bakin iyawarsu.
Amma abin sai hakuri...
zainab ta fauwala ALLAH al'amarinta tasan komai da saninsa hakan Kuma na
aka'ddararta" malaminsu na islamiyya yyimata nasiha sosai ,yace tacigaba
da zuwa islamiyya ana karatu da ita tunda naji...hakan yasa aka mayar da ita
skul tana zuwa part time,tunda tanaji ,inma exam za'ayi zata rubuta... Gaba
d'aya Abba ,mama ,Inna dasu Maryam tausayin zainab suke,yau kimanin wata 4 da
rasuwar Umar Amma kallo guda zakayiwa zainab kasan tana cikin damuwa! Tayi Rama
,sai tak'ara haske,fuska bbu walwala ga bbu mgn ,danma yanzun sbd Takoma
islamiyya da skul yasa damuwar cikin Kashi 10
3 yaragu,Amma kullum jin mutuwar Umar take tamkar sabuwa,in anyi wani
Abu yasa ta tunasa,saitaita kuka ,duk sallar dazatayi saita Masa addua....
Zaune take tana gurza kubewar
da mama tasakata sbd batasan ganinta
zaune tana tunani....ahakan baba yashigo" cike da tausayi yake kallonta
,tamkar yyimata kuka,yanajin tausayinta sosai ,Amma bbu yadda ya iya da ikon
ubangiji,yaso afita da zainab k'asar
waje to Amma bbu halin hakan , sannan shi mutum ne dabaison zuwa neman wani Abu
gun mutum yafiso yanema agun ALLAH! Mutane sun bashi shawara akan yanemi
taimako gun masu kud'i"akan afitada da zainab k'asar waje"Amma yace
bazai iya ba... ahankali baba yace
zainab sannu da aiki kinji! ALLAH yyimiki albarka ya albarkaci rayuwarki yabaki
ladan jarabawarki..... murmushi tayi ta na d'a hannu sama,shima murmushin yyi
Dan rabonda yaga tayi murmushi tun kafin Umar yarasu.... biscuits da cheewingum
da chocolate yafito dasu dg aljihu yamik'a Mata....akan idon goggo haule! Gsky
mlm baka adalci agdn nan! Sbd ALLAH saika rik'ason Kai Dan ita k'adaice mace
agdn nan kana bata Abu,bakaba isah ,Kuma k'anintane....cewar goggo haule ta
rik'e k'ugu...Wai miyasa kk hakane?" Ke yanxun bazakiji tausayin taba
kodan halin datake ciki"isah dakike maganar k'anintane ,ince ga khalifanan
k'anin isane Kuma banbasaba"kirika' Abu da lissafi,duk ranar da kk koma
mun mgn akan abinda yashafi zainab zanbaki mamaki Dan sai ranki yab'aci da
uwarta zakiyi kishi bada itaba....cewar baba Yana shigewa d'akin sa...mama ta
girgiza Kai tacigaba da gyara wutar tuwo datake tukawa... zainab kuwa dama ta
Saba da hakan ,kullum sai goggo haule ta yi abinda zai b'ata Mata Rai ko sakata
tuno Yaya Umar..
*************
Bayan shekaru 3....
Haka dama akace kwanci tashi
asarar Mai Rai.... zainab na nan bata warkeba! da larurarta, sannan tagama
karatunta dukda ansha wahala da gwagwarmayar rayuwa,...gaba d'aya tasake kyau
ta murje dukda batadawo da walwalarta ba,sbd rashin masoyi akwai d'aci,amma
tarage yawan damuwa sosai,bbu ruwana da kowa asalima inzata fita nik'eb take
sakawa , sannan duk Wanda yanuna yanasonta tun askul bata kula shi,dg baya
insungane tanada larura Basu dawowa ,akwai wani Bashir dayasota dukda tana
bebiya, amma ita be mataba! hasalima, soyayyar bata gabanta" wannan
karatun data Ida da kyar ,tanaso tasami aiki dukda tasan da wuya adauketa aiki
Bata mgn...gefe guda Kuma aminiyarta saratu tayi aure... zainab dama can batada
yawan k'awaye Dan batasan raini" tafiso ta tsaya matsayinta na
talaka... sukansu iyayenta abin sai
hkri wadatar bbu ba kamr daba,danma Yaya Ahmed (Yayan zainab babban D'an mama)
Yana aiki agdn Mai ,Yana taimakon baba sosai Dan yanzun haka baba Yana gd bbu
sa'a,kud'ad'en jarinsa dasukayi saura yabiyawa zainab su amakaranta,yanzun haka
abinda Ahmed yabada kowace ke cikawa tayi girki ranar girkinta"yyinda duk
girkin goggo haule sai tayi mita,dukda cewa yanxun Musa yanada adedeta
yanasamun kud'i Amma saidai yabata ,baya taimakon baba! Sauran yarnta Kuma
akwai masu shaye shaye sai autanta dake SS 2 yanxun...kullum buri. Zainab ALLAH
yabata abinda zata taimakawa Iyayenta musammun mahaifinta...
Babane kwance k'ofar d'akin
sa" Yana waya da Baffa Sule akan Yana hanya zasuzo shida matarsa anty
mariya...bayan yagama wayar yadubi goggo haule dake wankin Kaya, kasancewar
mama bata nan ammusu haihuwa"yace Kinga haule ajiye wankin nan ki aza
abinci ga sule da matarsa nan ahanya zasuzo!...batace komai ba,ta ajiye ta nufi
gun baba ,tace to kawo kud'in muga me yadace asiyo a aza.....hannu yasaka a
aljihu yafito da wata dari biyar da mama zata fita tabashi Dan tasan goggo
haule keda girki,zata iya masifa tace bazata rantaba...awulakance ta dubi kudin
Taki karb'a"had'e da cewa banganeba gsky?" Wannan abin yafara isata,
yaza'ace Ina aure Kuma Ina ciyar da kaina? Be yuyuwa,yanzun haka Ina binka dubu
da d'ari bakwai kak'i biya to wlh bazan rantaba,nagaji....kiyi hkri ki ara wani
Abu kihada da wannan d'ari 5 d'in lokaci na tafiya"inkuma bazakiyiba to
kibari, wannan halin danike ciki ALLAH ne ya azamun...kadai azawa kanka,wacce
kayi Dan ita ,Kuma bbu riba tana nan yadda take...cikin tsawa yace wace irin
wawiyar macece ke?" Kafin tayi mgn zainab ta fito fuska bbu walwala da
kud'i dubu2500 ta mikawa baba tana Masa nuni Yana goggo haule kud'in ta1500
datake binsa ,yabata 1K tayi girki...yayi shiru kafin yace Ina kika Sami kud'i
zainab?" Nuni ta Masa da kakanta mlm yabata 5K ,tabe Baki goggo haule tayi
had'e da karbe kudin... zainab kuwa
khalifa ta aika bacin ta rubuta Masa abinda zai siyo Mata...bayan
yakawo! Furace da nono da yogurt sai indomie da kwai,ta tada wuta ta aza kafin
ta dama furar tasaka acikin fridge din mama
D'an k'arami dake parlourn...Tana xuba indomie d'in taji sallamar baffa
sule d anty mariya...da gudu tazo ta rungume anty mariya tana murmushi"
cikin sakin fuska anty mariya tace zee y'anmata! Kink'ara girma" kafin ta
gaisheda baba da goggo haule dake ta tab'e Baki" tanufi bayi tayo
alwallah,suma su baba suka wuce masjid"
Bayan anty mariya ta idar da
Sallah, zainab ta xubo Mata indomie da kwai" da fura a jug...kafin takaiwa
baffa sule dashigowarsu kenan sundawo dg masjid...baba yyi murmushi yace ALLAH
yyimiki albarka zainab yabaki ladan karrama bak'o kinji...tayi murmushi. Kafin
ta ajiyewa baffa sule agabansa Dan tasan baba bayacin indomie...furar ta
dibarwa baba ta kamasa" baffa sule yyi murmushi yace oh zainab nada
hankali wlh " inajin tausayin yarinyar nan,dama Yaya mak'asudin zuwana
akantane gsky! Baba yace banganeba?"
Baffa Sule yace kasan
kwanakin baya kafin Umar yarasu naso karb'an zainab ta dawo guna "alokacin
Kuma naga yadda suke son juna basa Yi nesa da junaba!baba yace eh nasan da
hakan! Baffa Sule yace gsky Yaya inason zainab ta dawo gummu abuja kaga
bantab'a haihuwaba ,gdn danike Kuma bbu yara... sannan hankalinta zai kwanta
tarage tunani da kewar Umar insha ALLAH zakayi farin ciki da zamanta guna
,Yaya, xainab nada hankali d nutsuwa had'e da tarabiyya,nasan zamuji dad'in
Zama da ita"Kuma insha ALLAH akwai wata hospital dazan ruk'a kaita
acan,ba'asan inda ake dacewaba....baba yyi ajiyar zuciya yace to shikenan sule
ALLAH yasa hakan shi yafi alkhairi" Amma bara mamanta tadawo inji ta
bakinta ,dakuma ita zainab d'in"
Baffa Sule yace to
shikenan...
Anty mariya kuwa tare da zainab
sukaci abinci suna firar kurame ,wata Kuma zainab ta rubuta Mata,gaba d'aya
tausayinta yakama anty mariya,fatanta ALLAH yasa iayayen zainab subasu ita
ruk'o dukda zainab ba yarinya bace"anzun shekaran ta19_20...Cike da jin
dad'in yadda zainab ta tarbisu baffa sule baba ke fira ,Yana kallon goggo haule
dake kirgi"
Girkinda sai bayan la'asar
akagamashi"su baffama sukace sunkoshi"goggo haule ta tab'e Baki had'e
da cewa yak'ara auki....Koda dare ma ,mama data dawo tayimusu jallop rice sukaci"
Babane zaune ad'akinsa suna
mgn da baba akan tafiyar zainab Abuja" Yana Mata bayani tayi shiru tana
nazari... yyinda goggo haule ke lab'e bakin kofa tana sauraronsu ,sbd yau
girkintane " taga Kuma baba yakira mama..mama taji ajiyar zuciya tace naji
bayaninka ! amma bara na Kira mlm( mahaifinta) nayi mezaice?" To shikenan
rakiya ALLAH ya zaba abinda yafi alkhairi....cewar baba yyinda mama
kefita" sukaci Karo d haule dake lab'e! Girgiza Kai mama tayi had'e da
cewa Wanda yyi nisa bayajin kira!
Duk bayanin dayakamata mama tayiwa
mlm tamasa awaya,yakuma bata goyon baya d'ari bisa d'ari had'e da fatan
alkhairi ga rayuwar zainab d'in,dukda yaso ace zainab aure tayi sbd shine
darajar mace,to Amma komai nada lokaci,yakuma ce aturo Masa ita yabata addu'oi
yamata nasiha...washe gari mama ta sanar da baba yadda sukayi da mlm, baba yaji
dad'i sosai " kafin yasanarma baffa sule cewa subari sai gobe saisu wuce
tukum in zainab tagama kimtsawa...
*********
Zainab Tasha kuka jin Wai
Abuja zata koma da Zama , Iyayenta zasuyi Mata nisa ,ga lalurarta,wato zata
sake wata rayuwa"ALLAH sarki Yaya Umar da yanzun suna gdnsu sunyi
aure....tuni mutuwarsa tadawo Mata sabuwa"yyinda mama da anty mariya ke
rarrashinta da cewa inbataso bbu tilas tayi zamanta anan kadunan... girgiza Kai
tayi sbd zainabu yarinya ce me biyayya".
Koda taje gdnsu mama gun mlm
yamata nasiha maishiga jiki,yabata ADDUA kafin tadawo tasami mama ta had'a Mata
kayanta masu darti ta wanke matasu tas dukda masu dattin basuda yawa" gdn
saratu k'awarta taje sukayi sallama ta karb'i number in saratun dukda cewar
yanzun batada waya,wayarda Yaya Umar yabata ta siyar da ita da dadewa tabawa
mama kud'in taja jari...
Gaba d'aya adaren ranar
zainab batayi bacciba"sbd zulumi da fargaba , musammun inta tuna cewa gdn
dasu anty mariya take ,banasu bane,Kuma basu kad'ai bane..ga faduwar gaba da
takeji...washe gari duk Wanda
yakamata zainab tayi sallama dashi tayi ,kafin suhau hanyar Abuja itasu anty
mariya.... yyinda zuciyar zainab cike da tausayin Inna( mahaifiyar Yaya Umar)
sbd sadda zasutafi sai kuka take alamar ta tuna Umar da yanzun ya auri zainab
d'in"....
Basu isoba sai byn Sallar azahar "suka
shigo wata had'add'iyar anguwa"kallo guda zaka Mata kasan ta masu hannu da
shuni ne....wani gd had'ad'd'e suka nufa me get fari ...suka shige bayan anbude
musu get..abinda yafi bawa zainab mamaki ganin gdn zagaye yake da jami'an
tsaro(police)byn sunfito , baffa sule yatsaya gun jama'ar Gurin suna
gaisawa" yyinda zuciyar zainab ke bugawa har anty mariya taja hannunta
sukabi wata hanya dazata sadasu part d'in su...
Bayan sun Yi wanka da Sallah
,sukaci abincin da aka aikomasu dashi dg cikin gdn...kafin baffa sule yawuce
masallaci sbd sallar la'asar" yyinda anty mariya ta Kira mama tasanar Mata
sun sauka lfy...kafin ta dubi zainab tace tashi muje part d'in mutanen gdn
dukda sunsan mundawo.. zainab ta tashi dukda aranta bataso zuwaba Amma Yaya ta
iyane?" Tabi bayan anty mariya suka
nufi part d'in.... y'ar tafiya ce sukayi kafin su iso gun wata
had'add'iyar rumfa atsakiyar rumfar ga kujerunan na hutawa da canter
table"sau daya zainab ta kalli gun ta dauke Kai"anty mariya ta
k'wank'wasa k'ofar ,kafin ta murda' suka shiga cikin babban parlourn gdn...wani
k'amshi yadaki hancin zainab,ta lumshe ido"
