WAYAFI SONTA 8
p8
Adedenan Kuma Alh mahamoud
(mahaifinsu) yyi sallama da sauri elham ta matsa gunsa had'e da rik'e Masa
hannu , tace Abba kaga uncle yadaki anty zainab...tsab acikin kunnan hjy dake
nufo parlourn.. da mamaki Abba yace to amaryar dg dawowata za'a matsamun da
surutu ,wacece Kuma zainab?"hjy ta iso tanama alh sannu da isowa had'e da
Kama hannun elham tace Ina haidar d'in yake?" bangan shiba granny! cewar
elham tana janye hannunta sbd hango dadinta (faruq) datayi! Tanufi gunsa.. hjy
tabi alh part d'in sa..
Elham ta ahagwabe fuska had'e da fadawa
jikin faruq tace daddy kaga uncle yadaki anty zainab,Kuma tanada kirki,Dan
ALLAH Daddy muje karakani inrarrasheta har kuka tayi!surutunki yyi yawa ke Ina
kika santane?" gdn anty mariya take ko...ok yanzun ga sweets da chacoolate
naki dana Miki tsaraba...to daddy Ina na anty zainab?"oh ita ai babbace
ko?" Kaga daddy tanada kirki har goyani tayi nayi bacci mukayi
Sallah,shine wannan uncle d'in zaidaketa...in uncle yajiki zaimiki bulala bbu
ruwana...to daddy yanzun muje anemo anty zainab muga ta Dena kukan , tafad'a
tana cin chacoolate nata" Kinga kibari sai anjima yanzun abinci zamuci
yunwa nikeji...kafin elham ta yi mgn...k'amshin turaren haidar yacika
parlourn... murmushi faruq yyi had'e da tashi yyi hugging na d'an uwansa ,Yana
murmushi yace Yaya barka da dawowa! Murmushi shima yyi yace yauwa! ALLAH Yaya kayi
duhu taf! Uhum aiyau nadawo ko?"uncle Ina tsarabata? cewar elham tana
rik'e ma haidar hannu"yyi murmushi had'e da sab'arta akafadarsa yace sai
munje mota... uncle anty zainab tana can tana ku... I'm toking to you kika koma
mun maganarta Zan zaneki! Stupid yafad'a fuska atamke had'e da ajiye elham din
yanufi dinning area... faruq yadubi elham yace kidaina Kinga har zakuyi fad'a
da uncle ko?" Turo baki tayi had'e da ficewa dg parlourn...faruq yqwuce
dinning area shima ,yyi serving dinsu suka Fara cin abinci....saiga Alh da hjy
sun iso...nan haidar yagaishe da hjy ta
amsa fuska a d'aure,sbd tanason sanin me zainab tayi Masa yadaketa ,tasan elham
inbata ganiba ,bazatayi mgn ba!
amma bara yagama cin abincin zata
tambayesa"
hjy da kanta ta zuzzubawa mijinta komai suna
fira yanaci,kasancewar suntashi cikin wayewar Kai dakuma ilimin boko, Kuma dama
atare suke cin abinci tun tuni...bayan sun idar
ne! Haidar na goge hannunsa ,yace hjy akwai sauran alkubus d'in nan a ajiyemun
anjima naci dukda banacin abinci da dare,amma naji yyi dad'i sosai?" Wani
kallo hjy ta Masa had'e da cewa wacce kadaka itace tayi maku alkubus d'in
,saikaje ka tambayeta..sbd kasan innayi ni gaddama yakemun...shiru haidar yyi
had'e da daure fuska ,yace amma hjy yarinyar nan batada d'aa tazo ta bangajeni
bazata bani hakriba saita wuce! yafad'a cike da bacin rai"inda nasan ita
ta girka bazanci ba! Ko yanzun kana iya amayarwa ai! Ya isa Wai wacece ake mgn
akantane?" Cewar alh, Faruq yace y'ar aiki ce ko ,amma ai hjy dabaki
jajibotaba wlh saikace kin manta abubuwan dasuka faru abaya...hjy ta kallesu
one by one..kafin tace to inkungama fadan iyayena Kun bani dama nayi mgn?"
Murmushi alh yyi...kafin haidar yasassauta murya yace kiyi hkri hjy dan ALLAH!
To wannan yarinyar ba y'ar
aiki bace,tanada gata da galihu da ilimi na zamani dana mahammadiyya,da
Kuma iyaye kamar kowane d'a...saidai
ALLAH ya jarabeta.... tasanar dasu labarin zainab had'e da cewa Iyayenta
sunbarta gun sule ta zauna na wani lokaci kodan k'uncin dake ranta ya ,yaye...
yarinya ce me d'aa da tarbiyya zuwanta gdn nan dg jiya zuwa yau nagane
hakan..... sannan haidar karage zafin zuciya Ina gayamaka,Inka Saba mu'a mala
acan station da mutane Kuna dukansu itafa macece ,matsayinka na hukuma zata
d'aukeka marar adalci.... sannan meta maka harka daketa?" Fuskarsa adaure
yasanarmusu...kafin alh d hjy suce inyaganta yabata hakri.... HAKURI fa
kukace??" Faruq da haidar suka had'a baki gurin cewa...banza dasu hjy tayi
tabi bayan alh daya tashi ,tana cewa inkafi k'arfin bata hakurin Toni zanje nabata....sbd
be kamata mamana taji wannan abinba duk da nasan da k'yar ne zainab ta sanar Mata....
Zainab kuwa tana dafe da
kunci hawaye na zuba tanufi part d'in su
Kafin ta Ida isa ta tsaya gun wasu flours
tazauna ,tayi tagumi ,tana kuka azuciyarta tana jin haushi da tsanar wannan
mutum dabashida sanin darajan dan Adam..dan kawai ta bigesa bisa rashin sani
zai Mata haka! Insha ALLAH bata koma zuwa part d'in inba hjy ta kirataba,Kuma
bazata gayawa kowa dan tasan su anty mariya bazasu ji dad'i ba.
Inkuma makamancin hakan
yafaru to saidai tabar musu gdnsu...bazata d'auki wulakanci ,besan ko wacece
itaba kawai zai mareta dan tashigo gdnsu ,dg dawowarsa.... lallai mutuwa Mai
tonan asiri.... ALLAH ya jik'an yy Umar ,mutuwa ce taja Mata...tashi tsaye tayi
ta gyara hijab nata sosai ta rufe Mata fuska...zata juya ta tafi tajiyo muryar
elham...
Da sauri elham ta fad'a
jikinta tace anty zainab kiyi hkri Dan ALLAH aidama uncle mugune , to nagayawa
Abba d granny zasuyi Masa duka.. zaro Ido zainab tayi jin elham tace tasanarwa
hjy, hannunta ta Kama tana Mata alamar taje gatanan zuwa....itadai elham bata
ganeba sai d'imi taketa yi....dg karshe zainab ta nuna Mata hanya,ita Kuma ta
wuce part d'in su...bbu kowa a parlourn da sauri ta shige dakinta ta wanke
fuskarta,ta zauna kan katifar....tana tunani...shigowar anty mariya yadawo da
ita haiyacinta....anty mariya tayi murmushi tace oh zee kina gun hjy abinki
ko?" Kije kici abinci to! Zainab ta girgiza Kai... alamar bazata ciga!
Anty mariya tace nan gabanmu
akwai islamiyya asabar da lahadi,danike zuwa
baffanki yace zai sakaki ciki... zainab tayi Mata alamar to...kafin anty
mariya tace gobe insha ALLAH zamuje asibitin mugani sudubaki..... zainab tayi
Mata alamar to.....
Haidar kuwa tabbas maganganun
hjy sunyi tasiri sosai azuciyarsa ! Sai yanzun yaga rashin adalcinsa na
marinta!amatsayinsa na hukuma,zata iya kiransa azzalimi komarar adalci..saidai
dayake miskilane be nuna hakan afuskaba. amma gsky shi bazai iya bata hakuri ba
,danbbu wacce yataba yiwa laifi balle yabata hakuri Kuma bazai Fara
akantaba!yasandai astation in ankawo k'ara Yana shiga maganar yasansanta
tsakanin masu rigimar yabasu hakuri...da wannan hujjar yawatsar da maganar
zainab...hjy kuwa da dare da kanta taje part d'in su anty mariya tasami zainab
ad'akinta tana karatun kur'ani,hjy ta zaunah...,byn ta idar hjy tabata hakuri
akan abinda yafaru tsakanin ta da haidar, had'e da mik'a Mata ledar hannunta!
Zainab ta yiwa hjy alamar bbu
komai yyi hakan acikin rashin sani, tana nuna Mata tana murmushi had'e da yiwa hjy
godiya....bayan fitar hjy zainab ta duba,taga kayane areviant gownt masu kyau
kala 5 da mayafansu sai kayan kwalliya da turare guda2" tashi tayi taje
tanunawa anty mariya! Cike da jin dad'i anty mariya ke yaba kayan had'e da cewa
da safe intashiga zata yiwa hjy godiya....
******************
Yau kimanin satin zainab biyu
a Abuja kuma Masha ALLAH gsky bbu laifi tana ganin canji sosai arayuwarta ,sbd
hjy d elham najanta ajiki ,Kuma tanasakewa dasu ,hakan na rage Mata damuwa
sosai,gefe guda satin da yawuce tafara zuwa islamiyya dukda tayi sauka amma
ance ilimi kogine... sannan sunje asibiti an azata kan magani dukda ancazesu
kud'i da yawa...tunda haidar yamareta batakoma yadda sun haduba duk alokacin
bata kalli fuskarsa ba. tasansadai a photo shida faruq! Duk lokacin datasan
suna ciki to hjy ta Aiko akirata bata zuwa ,shikansa Mai gdn sau daya suka
tab'a gaisawa dashi Kuma Bata kallesa ba! Hjy kuwa ta yadda da zainab sosai sbd
ta lura yarinya ce da abin duniya baya gabanta batada zalama ko had'ama sau dayawa
zatace Mata ta d'ibi kaza da kaza,amma bazata d'ibaba sai inbata akayi shima
wani lokacin zatace bazata ciba...hakan yakarasa hjy jin zainab ta burgeta...
Sanye take da jallabiya maroon colour,tayi
rolly da mayafin"fuskarta bbu kwalliya rabon datayi make up harta manta,
dukda haka tayi haske tayi kyau had'e da yin frash. ..ta nufi part d'in hjy sbd
hjy t Kira anty mariya awaya cewa zainab ta je Tana kiranta...
Murda'k'ofar tayi ,taji
gabanta yafad'i sakamakon jin motsin elham da daddynta.... yeeeeee daddy! gama
anty zainab d'in nan. da gudu elham ta fad'a jikinta! Zainab ta rungume ta
had'e da d'agata sama tana dariya har fararen hakoranta suka bayyana d
wushiryarta.... faruq yakafesu da Ido ,Yana mamakin yadda elham tayi saurin
sabawa da yarinyar,Kuma yasan elham batasan zuwa gun Wanda bata saniba... elham
tace anty zainab Kinga daddy nah ! Shima yanada kirki yafi uncle kirki,kidinga
gaidashi inbakinki ya warke zai ruk'a siyomiki kayan dad'i... zainab cike da
kosawa da surutun elham narashin kan gado ta rabata zata wuce dan shiga
parlourn hjy.elham tace bazaki gaida daddy naba,kobakinki be warkeba??"
Zainab ta saki kallon faruq caraf suka had'a ido taji faduwar gaba"dauke
Kai tayi fuska bbu walwala sbd taga Yana wani Shan k'amshi...tad'aga ma elham
Kai tawuce kawai... elham ta kalli faruq tace daddy kaga anty zainab tayi
tafiyar ta batagoyaniba! Tabe baki yyi had'e da cewa kuka sani...bin zainab
elham tayi... faruq ya lumshe Ido Yana girgiza k'afa.... zainab kuwa byn sun
gaisa da hjy ,tazauna tana yiwa hjy kitso...har elham ta shigo
