HABIBI DA'IMAN 101-120
*page 101~105*
Sannan dake cewa so kake ka aureta yanzu don kanason kazama sanadin warkewarta kamanta da aikin kane? Don nasan ko yanzu hutunka ya kusa k'arewa"
Wani irin d'aci yakeji cikin bakinshi, zuciyarshi natafasa
data haddasa jin zafin da yakeji a jikinshi, dakyar ya iya bud'e bakinshi
"zan'iya barin aikina saboda khadijah" sannan yamik'e yatafi badon
yana ganin gabanshi ba don har yana bangaje Rafeeq batare da yasani ba
Shigowa yayi yazauna, Uncle d'in yagaya mashi duk abinda
Jiddan yace dangane da auran khadijah dayake son yayi cikin weak d'innan
Neman mafita kawai yake halboma rayuwar Jiddan don yana
tsoron tarihi ya maimaita kanshi don wannan karin idan akace za'a hanashi
auranta, tabbas zasu haifama kansu D'A mara ido
Ajiyar zuciya ya safke "toh kai Uncle mekace game da
haka?"
"ina ganin kamar yaya bazai amince ba shiyasa nace yayi
hak'uri da batun auren yarinyar yanemi wata kawai ya aura, in auren
yakeso"
Girgiza kai Rafeeq yayi "wallahi Uncle nike tare da
Jiddan tunda wannan k'addarar tafad'a mashi, ina tsoron halin dazai jefa kanshi
ciki idan aka hanashi aurenta akaro na biyu, duk da nasan iyayenta dakyar su
amince, toh amma halin da zasu shiga za'a duba"
"to amma bank'i zancenka ba don gaskiya kafad'a, saidai
abinji shine mahaifin Jiddan"
"karkaji komai kabarni da Abba nasan yadda zanyi na
fahimtar dashi, Momy kuma kasan batada matsala kan maganar"
Nisawa yayi yace "toh Allah yashige mana gaba, kushirya
zuwa anjima muje wurin mahaifan khadijah muji abinda zasu ce kafin in sanarda
yaya abinda ake ciki"
"toh shikenan Uncle bari ingaya mashi"
Tund'azu take matsa mata da zancen school duk tarasa yadda
zatayi mata ta fahimta, tunaninta ne yakatse jin yadda tadage tana kuka saboda
tana son komawa skull
Dafata tayi tace "khadijah" shuru tayi tana
saurarenta, kafin daga bisani ta cigaba dacewa "inaso kinatsu ki fahimci
abinda zangaya maki" d'aga mata kai tayi alamar tana saurarenta
"khadijah kin dad'e baki da lafiya hakan yasa muka dakatar da karatunki
har abokan karatunki suka gama, bakiji nace maki Jiddan zaitafi wurin aikinshi
ba? Kinga kenan kindad'e kwance baki da lafiya, don haka inason kicire damuwar
komawarki makaranta yanzu har muga abinda Allah zaiyi"
Wani farin ciki taji ance Jiddan na aiki, kafin damuwa mai
tsanani ta lullub'e kambun zuciyarta wanda yayi sanadin jefata cikin kwaryar
tunanin da saida Mama ta fiddota ta hanyar fad'in "khadijah kinaji
nakuwa?"
Daga kanta tayi sannan tace "wace irin rashin lafiyace
nayi da harta d'auki lokaci maitsawo irin haka?"
Nunfasawa Mama tayi kafin tabata amsa "kindad'e acikin
hali na ciwo wanda yayi sanadiyar tab'a kwakwalwarki da kuma rashin gani"
batasan lokacin da
wasu zafafen hawaye kebin fuskarta wanda Mama keta k'ok'arin share matasu ta
hanyar lallashinta dayi mata nasiha komi yasamu bawa mujarrabi ne daga gareshi,
tare da k'ara lurar da'ita kan d'aukar k'addara maikyau ko akasinta
* * *
Tabbas dagaske idan khadijah ta farfad'o daga wannan
gushewar tunanin na tah, me zatace dangane da soyayyarshi da kuma aurensu, idan
ya aure ta tana cikin wannan halin?, wani gutsure ne na zuciyarshi yace kasan
bazata tab'a k'inkaba don ko kaita keso, rawa yaji zuciyarshi nayi daya tuna
yadda ta firgice sanadiyar mutuwar ss abinda yak'ara jefashi cikin kokwanton
cewa anya khadijah bata shafe shi cikin babin rayuwar taba?
Tsayuwar da motar tayi shiyayi sanadin tsayawar tunaninshi,
fita sukayi su duka ukkun tare dayin sallama a harabar gidansu khadijah
Abbansu khadijah ne yafito tare da amsa sallama ganin Jiddan
da Rafeeq saidai wannan karon harda bak'uwar fuska yasa yayi masu iso zuwa cikin palourn saukar
da bak'i
Bayan sungaisa Uncle ya gabatar mashi da kanshi a
matsayinshi na kawun Jiddan tare da tambayar jikin khadijah
Gyara zama yayi yacema mahaifin khadijah "Jiddan ne
yazo mani da babbar magana nason aure khadijah, shiyasa nima banyi k'asa a
gwiwa ba nazo nema mashi tun da addini bai haramatan hakan garesu ba shiyasa
nazo naji tabakinku"
Nisawa Abbansu khadijah yayi sannan yace "bazan yanke
hukunci ni kad'ai ba don haka bari in kira abokina kuma mahaifi ga tsohon
mijinta" nan take yakira Daddy ya shaida mashi yana neman shi
Duban Uncle d'in yayi yace "bari akawo maku ruwa kafin
zuwan Alhaji" Bayan yashiga yayi ma Ihsan umarni datakai ma bak'i ruwa
yakuma shaidama Mama kawunsu Jiddan ne yazo
Miyan bakinshi ne yakatse baisan sadda yahad'e shiba har
saida Jiddan ya waigo ya kalleshi saboda jin k'arar "kwat" da yayi
A hankali tazo ta'aje masu kayan motsa baki batare data
kalli ko suwaye ba tagaidasu sannan ta tafi
Kyarma yaji zuciyarshi nayi a hankali batare da kowa yasan
yayi maganar ba yace "oh Rafeequ be strong mana"
Shigowar Daddy tasa kowa ya maida hankalin shi kan sallama
da yakeyi, don lokacin har Abbansu khadijah ya dawo bayan Mama tasanar dashi
cewa khadijah bata da magana sai yaushene bikinta da Jiddan?
Bayan Abbansu khadijah ya fayyace ma Daddy komai kan
buk'atar dasu kawu sukazo da'ita
Daddy ya cigaba da cewa "Ni aganina wannan bawata matsala
bace tunda shi yana sonta a haka kuma itama rashin d'aura matashi yana iya
jefata cikin wata matsalar, duk da munsan abinda muke shirinyi yana da hatsari,
musamman lokacin dazata tuna komai yaya makomar aurensu take a wurinta? To amma
idan kukayi la'akari da lokacin data auri suleman bashi takeso ba Jiddan d'in
takeso, biyayya ce kawai yasa ta aure suleman ta zauna dashi lafiya"
Ajiyar zuciya Abbansu khadijah yayi yace "toh shikenan
na amince Allah yasa haka yafi zama alkhairi"
Murmushi Uncle yayi don yaji dad'i ba kad'an ba sannan yace
"muna neman wata alfarma da a d'aura auren cikin satinnan"
Abbansu su khadijah yace "badamuwa duk yadda muka yanke
da 'yan uwana zakuji ni"
Godiya sukayima junansu kowannen ya wuce gida banda su
Rafeeq dazasu gaisa da khadijah
Zaune suke a palour, sai ganinta sukayi tana dafa bango tare
da kiran sunan Jiddan, da sauri yatashi yarik'o hannunta yace "pls
andeejanah kidaina tahowa ke kad'ai kada ki fad'i"
Cikin shagwab'a ta turo baki "Dama da ban lafiya harka
gama karatunka kana aiki shine baka gayamani ba?"
D'an langab'e kai yayi alamar yayi laifi yace "i'm
sorry nayi laifi" dariya tayi "toh yaushe?" ya fahimci metake
nufi yasashi cewa "cikin weak d'innan" shidai Rafeeq yagaji da yadda
suka manta dashi shiyasa ya katsesu ta hanyar cewa "khadijah ina sister
d'inki?"
Juyawa tayi inda takejin sautin muryashi tace
"Ihsan" "eh" "tayi bacci" ba haka yaso ba sai
ganin bayadda zaiyi yasa ya fiddo wayar yabata yace "ta mantata a mota
dazu da muka dawo asibiti" da haka yatashi ya fita ya basu wuri
* * *
Yanzu ya za'ayi yaron nan yace wai bazawara kuma wacce bata
da hankali bata gani zai aure, koda yake kawun nashi daya biye mashi shine
babban mai laifi suma iyayen nata basa tunanin abinda zaije yadawo idan ta tuna
duk abinda yafaru a rayuwarta"
Momy ce tadafashi cikin sigar lallashi "haba Abban
Afnan kamanta irin wahalar da mukasha a baya? Ko kamanta halin da yaron nan ya
shiga wanda har yanzu bawai warkewa yayi ba, gaskiya bana tunanin idan muka
hanashi auranta a karo na biyu zamu samu kwanciyar hankali, idan a wancan
lokacin muna da hujja a yanzu banajin muna da'ita koso kake murushe rayuwarshi
mu binneta da kanmu, kada mukasa yi... "
Bata idaba kukan da take tarewa ya kufce mata saboda ko
cikin 'yayanta Allah yasani tafison ta gina rayuwar Jiddan don yazama uba ga k'
annenshi tunda ita jiddah mace ce hasalima yanzu a k'ark'ashin wani take, da
sauri tafita don batason mijin nata yaga halin data shiga
Zaune yayi a inda tabarshi yana tunanin magangunanta gaskiya
ne danko jiya bayan k'anin nashi yayi mashi bayanin yadda sukayi da iyayen
khadijah, ya kira jiddah itama har kuka take akan kada yace zaihana k'aninta ya
auri wadda yakeso
Wani b'angare na zuciyarshi ke gaya mashi kada yazama mai
cutar da gudan jininshi tunda su iyayenta sun amince meye nashi na hanawa?
Da wannan tunanin yasamu yasaita zuciyarshi inda tafi
rinjaye akan....
Mrs Abdul Sule
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITED BY HALIMA Mk*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
*page106~110*
*L*umshe idanuwanshi suke yana tunani saboda bashi ke
driving d'inba kamar daga sama yaji muryar Jiddan na cewa "kana sonta
kagaya mata mana"
Bud'e idanuwanshi yayi yanajin wani irin nishad'i naratsa
k'ok'on ranshi yace "itace na dad'e ina nema" da mamaki ya kalleshi
yace "kamarya?"
Da sannu Rafeeq yafara bashi labarin yadda akayi yaganeta
har yazuwa yanzu da yakejin bazai iya rayuwa babu itaba, dariyar mugunta Jiddan
yafara mashi shikuwa Rafeeq sakin baki yayi yana kallonshi saboda yana son
yatuna yaushe rabon da yaga yana dariya irin haka, saida yayi ta isheshi sannan
yad'agama Rafeeq gira d'aya yace "guy amma ka raina ni"
"kamarya yafa" "inason ya kanason
k'anwa" saramashi Rafeeq yayi tare da cewa "sorry yaya jamilun
Jiddan" hararar shi yayi yace "niko" tare da nuna kanshi
Kashe mashi ido d'aya Rafeeq yayi yace "friend"
yace "For Ever" kasancewar wannan ce sararsu insun kad'aice su
biyu,d'aya yace friend d'aya kuma yace for ever
Bayan sunci abinci sun huta saiga Abba yashigo dayake Momy
na wurin shima sai yasamu wuri yazauna
Gyaran muryar yayi yace 'Jiddan naji komai daga wurin Uncle
d'inka saidai a gaskiya... Tsayawa yayi da maganarshi yana kallon cikin idanun
Momy, hakan ya tabbatarma Jiddan Abbanshi bai amince da buk'atarshi ba
Wani irin tsalle zuciyarshi tayi a hankali yafara jada baya
iskar dake d'akin tayi mashi zafi inda harshen wutar dake babbaka cikin
zuciyarshi ke k'ok'arin tabo kwakwalwarshi don a dole ta bashi amsar meyasa
k'addara da tsautsayi suke zama abokan gaba a rayuwarshi da khadijah,
Kullum fad'a suke inda k'addara ke k'ok'arin wajen ganin ta
rabashi da khadijah kuma tana samun nasara saboda tsawon mizaninta ya wuce na tsautsayi
dake yunk'urin had'ashi da khadijah.
Baisan ya akayiba sai ganinshi yayi a d'akinshi wannan ne
yatabbatar mashi da aikin k'afafunshi ne
A hankali ya tsugunna saboda k'afafunshi sun kasa d'aukar
nauyinshi, sai kuma yayi zumbur yatashi yana neman wine d'inshi don kuwa ya
manta nan ba Abuja bane
Dasauri Rafeeq yaje yarik'e k'afar Abba yana fad'in
"Why? Why? Why? Abba kasan halin da Jiddan zaishiga idanka hanashi aurenta
ko don baka da cikakken sani akan rayuwar da yashiga baya, nasan baku saniba
don dagani sai Mujaheed mukasan Jiddan nashan giya duk saboda sanadin khadijah
na tabbata idan kuka hanashi wannan karin ba abinda zai hanashi neman mata,
Haba Abba! Haba Abba!! Kaduba kagani ya akeson rayuwar shi tak'are"
Tsoro ne da fargabar abinda Rafeeq yafad'a ya k'udundune
zuciyar Momy da Abba, a hankali cikin nadama Abba yafara cewa "baku tsaya
kuka saurareni ba daga kai harshi kuka fassara abinda zanfad'a da zarginku
saboda kunsama ranku bazan amince ba, alhali tunkan kuzo nagama shawara akan amincewa
ta
Juyawa yayi da niyyar yima Momy magana sai yaga bata wurin
hakan yatabbatar masu tana d'akin Jiddan, suma tashi sukayi suka nufi can
Zaune yake yarasa inda zaisa kanshi Momy sai bubbuga
bayanshi take tana kwantar mashi da hankali, amma ina bayajinta danko yariga da
yayi nisa
Sallamar da Abbanshi yayi ce tasashi d'agowa suka had'a ido,
kafin yakauda kanshi gefe
Wuri Abba yasamu yazauna sannan yace "baka fahimci
abinda zanfad'a maka ba kayi tunanin k'i amincewata, abinda baka sani ba tunkafin
kuzo na amince, dama maganar inda zaka ajeta da yanda zakayi da aikinka nakeso
inji?"
Sai yanzu yaji yasamu damar yin kuka kafin yatashi ya
rungume mahaifin nashi don yakasa cewa komai saboda farin ciki ya tabbata
wannan karin bazai rasa khadijah ba
D'agowa yayi daga jikin Abban yace "thank you
Abba" Murmushi Abba yayi yace tunda khadijah tazama farin cikin ka dole
muma mu sota don haka kaje kafara nema maku visa k'asar da zaka fita da'ita don
nema mata lafiya, nikuma da kawun naka kabarmu da komai na bikin, inyaso sai
rubuta takarda ka aika wurin aiki don naji Mujaheed yace cikin satin nan zaku
koma"
Wayyo Allah dad'i kamar ya mutu don farin ciki yace
"Dama sunsa bani da lafiya nagaya masu any time zan'iya koma check up
india, to yanzu kaga shaida masu kawai zanyi"
*** *** ***
Wai haryanxu laila bazaki hak'ura da Jiddan mukoma Abuja
ba?"
"Ashanty kenan, wallahi bazanyi zuwa kaduna a banza ba
tunda ance yana katsina ni kuma har katsinar zan bishi donko dukiyata zata k'are
akanshi, nidai muradina in mallakeshi to magana tak'are"
Kashe mata ido d'aya Ashanty tayi irin na gogagun 'yan
bariki sannan tace "ina tare dake k'awata har sai buriki yacika na
mallakar Captain Jiddan"
Kuyi manage bayawa
Mrs Abdul Sule
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITED BY HALIMA Mk*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
Wannan shafin naku ne:
Safiya kabir{mum Iman}
Rahina Ali{sirrin mu mata}
Rahama Muh'd sani{Garkuwa fulani}
Maman suraya{HABIBI DA'IMAN FAN'S}
Queen sarah
Mrs Jmoh
Halima kangiwa
Aisha Bala Saulawa
Aisha Bala Shu'aibu
#Anatare😘
*page111~115*
*A*n d'aura auren khadijah da Jiddan ayayin da komai ya
daidaita su Ihsan sun koma school cikin kwanciyar hankali saidai fatan samun
lafiya ga khadijah
Tafiya suke cikin mota, Mujaheed ne ke driving sai Rafeeq
dake kallon gefen titi
A hankali yace "Nafara kewarshi" Mujaheed ya
kalleshi yace "Allah sarki Captain J, Allah yaba khadijahrshi lafiy..........."
baik'arasaba wayarshi
ta d'auki k'ara alamar shigowar kira, d'auka yayi tare da cewa "Hello
little yakike?" shuru yayi kafin yace "Haba my love bamuma shiga
Abujar ba amma idan mun isa zanyi maki text, don Damun isa streight office zamu
wuce, so take care of your self" shuru yayi kafin yace "Ok bye
bye"
Juyowa yayi ya kalli Rafeeq da ya zuba mashi na mage yace
"kodai maganin mayu kafara sha wannan irin kallo haka?"
Harararshi Rafeeq
yayi yace "takanka zanfara" Bayan su d'an d'auki lokacin ba wanda
yace komai, Rafeeq ne yakawar da shurun ta hanya furta "Ihsannnn"
"ka kasa fad'i mata ko?"
"eh, naso ace su Abu da Ammi sunzo d'aurin auren nan ko
don in gwada masu wacce nakeso kafin ingaya mata, saidai wannan uban
azarb'ab'in Jiddan yasa anyi komai a gaggauce"
Kallonshi Mujaheed yayi yace "haba Abokina be strong
mana kada mace tasaka jin tsoro, kagaya mata kawai, saboda ko su Abu sunzo basu
zasu gaya mata kana sonta ba"
"eh nasani, kedai katayani da addu'a Allah yasa rabona
ce"
"insha Allah rabonkace ma, yaushe ne tafiyarka
eygpt?"
"sai munsamu wani hutun, don nayi missing d'in su Ammi,
ga Rafeeqa tadame ni yaushe zanje"
Da haka suka cigaba da firarrakinsu har suka isa Abuja
***
Wani irin kululun bak'in ciki takeji da takasa had'eshi wai
yazatayi ne? Ta biyoshi har katsina, amma abin haushi yayi aure harda wani
tafiya india honeymoon shida makauniyar matarshi, ita yama zatayi yanzu haka
zatayi ta jiranshi har sai ranar da yadawo?
Lallashinta Ashanty keyi saboda yadda Laila ke kuka saika
d'auka mutuwa akayi mata
Murya irin wadda tasha kuka tagaji ta kalli Ashanty da
jajayen idonta, tamkar Jiddan ne a gaban tah tace "zan jira dawowarka
Jiddan da yarda Allah saina dagargaza Rayuwar shegiyar data aureka (anya zaki
samu nasara akan haka🤔) sannan in mallake ka ko baka aureni ba saina
cika burina akanka"
Nace uhmmm abinda Laila bata sani ba Jiddan ko wine ya daina
sha tunda ya mallaki ruhin ranshi yayi ma mahaifinshi alk'awarin hakan bare
wani guntun Romancing d'inki😜
Da haka sukaja motarsu suka wuce Abuja zaman jiran dawowar
Captain J
***
Ko a cikin jirgin wuri ne na musamman inda bakowa ke zama ba
suke zaune
Rungume take a jikinshi ayayin da take baccinta cikin
kwanciyar hankali, shikuwa sai Kallonta yake kamar ya had'iyeta don so
Hannunta ya kamo tare da murza zoben dake hannunta yana
mamakin yadda akayi har yanzu bata cire shiba, wata kwalla yaji yataru a cikin
idonshi, wanda nakasa gane ko tami cece,
Kiss yayi mata a kumatu yaci gaba da shafa fuskarta, tare
dayi mata fatan samun lafiya
Shigar dare sukayi ma k'asar, shatar taxi ya d'aukar
masu zuwa wani babban hotel, bayan
yakama masu d'aki mai hawa na bakwai, ma'aikatan hotel d'in ne suka taimaka
mashi wurin shigar da kayansu cikin lipter
So yake ya tashi yaje yayi wanka yai alwala don sauke farali
dake kanshi kafin yayi masu order abinci, amma khadijah ta hanashi, ita'ala
dole bazai barta ita kad'ai ba, saima wani k'ara mak'aleshi take, wanda ya
haddasa ma jikinshi mutuwa tare da tada mashi wani mik'i, dakyar yasamu ya
lallasheta yashiga, bayan ya fito ne ya taimaka mata itama ta shirya
Room service ne yayi nocking, tashi yayi ya amso masu abinci
da sukayi order, bayan ya bud'e abincin ne khadijah tace "yayana naji
k'anshi abinci"
"Open your mouth" batayi jinkiri wurin bud'e
bakinta ba yasa mata abinci, lumshe idonuwanta tayi saboda d'and'anon girkin
dataji cikin bakinta wadda ke ratsa sassan jikinta
Tsura mata ido yayi kasancewar sleeeping dress ne jikinta wanda ke nuna surar jikinta, shagalta
yayi da Kallonta wanda take yaji wani abu na mashi yawo cikin kai natsuwarshi
na neman barin jikinshi wata irin sha'awa ce ke fizgarshi, bayan yayi ma kanshi
al'k'awrin bazai tab'a kusantar ta harsa radda ta dawo cikin hayyacin ta, ganin
ya neman tadama kanshi hankali wanda batasan yanayi ba tunda baganin shi take
ba yasa yayi saurin kawar da idonshi akanta, da haka suka gama cin abincin su
suka bi lafiyar gado
***
*NIGERIA*
Mujaheed yayi waya da Islam yakai sau biyar tsakanin
isowarsu Abuja zuwa yanzu, wanda yasa da sunfara wayar Rafeeq zaifara tsoki
saboda bak'aramin takura mashi suke ba, ga damuwarshi inya kira Ihsan bata
d'auka
Yanzu ma tsokin yayi tare da d'aukar wayarshi ya k'ara gwada
sa'arshi ko wannan lokacin zata d'auka
Zaune suke ita da Mama suna cin tuwo, tuwon takeci amma
zuciyarta na ga 'yar uwarta ko wane hali take ciki, saida ta had'e lomar tuwon
dake bakinta sannan tace "Mama kun koyi waya da yaya khadijah?"
"a'a basu kira ba tukun, dan kinsa akwai banbanci
lokaci tsakanin mu dasu, may be sai zuwa anjima kiga sunkira ko kuma wayewar
gari"
Kallon agogo tayi tace "Mama har yanzu Abba shuru
baishigo ba", "eh yace zaije wani wuri, kila sai zuwa anjima kiga
yashigo"
Wayar Ihsan ce tayi ringing, kallon allon wayar tayi ta
kauda kai, Mama ta kalleta tace "meye haka, bakiranki akeba kinaji"
"wallahi bansan ko waye ba, ya kusa wata biyar yana
kira na daga yakira wrong number shikenan yanace, shiyasa ko ya kira bana
d'agawa"
"Ihsan kenan,ai bakisan inda rana zata fad'i ba, ki d'aure
ki d'auka kiji abinda zaice maki inkinga da shashanci yazo saiki rabo dashi,
idan.............wayar ce ta k'ara d'aukar Ringing akaro na biyu
Kallon Mama tayi sannan ta d'auki wayar tare da shigewa
d'aki
Baiyi tunanin za'a d'auka ba kamar yadda zuciyarshi ke raya
mashi, saiji yayi an d'aga kiran, tsabar mamaki baisan sadda yasaki wata
sanyayyar ajiyar zuciya ba
Sallamarta ce ta doki dodon kunnenshi, batare da bata lokaci
ba ya mayar mata da aminci ya tabbata garesu
"don Allah bawan Allah kayi hak'uri kadaina
kirana".... "zandaina kiranki, amma sai kingaya mani dalili, don
nasan ke bamatar aure bace............."taya kasan ni ba matar wani bace?
"sanin hakanne yasa nace ke ba matar wani bace, kuma in
kin misalta hakan kiyi mani rantsuwa da cewa kina da aure, toh nikuma nayi maki
alk'awarin daina kiranki"
"naji ni ba'ita bace, to miyasa kake
bibiyata?............"saboda ina sonki kuma naji ajikina ke matata
ce............."to kayi hak'uri an tsaida mani miji"
Dammmm yaji gabanshi ya fad'i dakewa kawai yayi ya cigaba da
cewa "banyadda antsaida maki miji ba" ya k'arasa maganar cike da nuna
kishi
K'arya ba halinta bane yasa tace mashi "kayi hak'uri ni
kawai karatuna ne agabana don haka banajin zai'iya had'a soyayya da
karatu"
"shikenan pretty kibani damar ko gaisawa
murink'ayi".............."toh naji, saida safe" tare da yanke
kiran batare data saurari mai zaice ba
Ganin alamun ta katse kiran ne yasa ya kalli Mujaheed yana
dariya, shikuwa ganin kallon dake mashi yasan yau andace Ihsan ta amsa wayarshi
A b'angaren Ihsan kuwa tunani take anya wannan mutumin
baisanta ba? Saboda taji ya kirata da pretty, sannan tanajin muryarshi kamar ta
tab'a jinta shiyasa ta yanke hukuncin bazatayi mashi k'arya ba don kar wata
rana taji kunya
Washe gari Jiddan yakira su Mama ya shaida masu sun'isa
lafiya gashi zasu tafi asibiti ma yanzu, bayan sun gama wayar da su Mama yakira
su Daddy da Rafeeq suma ya shaida masu sun'isa lafiya.
Mrs Abdul
Sule
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITED BY HALIMA Mk*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
*page116~129*
*INDIA*
*y*ana gama waya dasu Rafeeq ya juyo ya kalli khadijah dake
zaune bakin gado tana jiranshi su tafi, tsayawa yayi yana k'are mata kallo
saboda tayi mashi kyau dukda ba kwalliya tayi ba, hot pink d'in gown ce jikinta
sai tayane kanta da Black veil sai takalminta ma Black mai karamin dunduniya
Matsowa yayi kusa da'ita ya zauna tare da rik'o mata hannu
"khadijah mutafi ko?" zunburo baki tayi tace "yayana baka shafa
mani lipstick d'ina ba"
"keda zamu Asibiti menene na shafa lipstick"
yitayi kamar zatayi kuka yai saurin tashi yana cewa "sorry bari na shafa
maki, haka yashafa mata pink d'in lipstick wanda yayi dai-dai da colour d'in
gown d'inta
Abinka da farar mace sai tayi wani irin kyau
Tsurama D'an k'aramin bakin nata ido yayi yana
Kallonta, wani irin kishi yakeji ace
wani yaganta a haka
Itakuwa jin shurun
yasa tace "yayana muje, ko kana wani abu ne?"
Kamo hannunta yayi "mutafi" har sunkai bakin k'ofa
yaji bazai iya d'aurewa ba yabarta tafita da lipstick d'in, yasa yajawota da
k'arfi ta fad'a bisa fad'add'en k'irjinshi, tallafo kanta yayi yana kissing
d'inta sosai saida yagaji dan kanshi sannan yalashe lipstick d'in bakin nata
Kwat-kwata batayi yunk'urin hanashi ba don sak'on nashi
nashigarta ta kowane sassa na jikinta
Jin Tsayuwar na neman gagararsu, gashi yana neman fita
hayyacin shi yasa ya kyaleta, ajiyar zuciya suka saki a lokaci d'aya
K'ara gyara mata rolling kanta yayi yaja hannunta suka wuce
Ko a cikin motar tacika da tsoron shi, dan tasan ga dukkan
alama Jiddan yana da buk'atar kusantarta, duk yana lura da yanayin ta amma
baimata magana har saida suka isa Asibitin "khadijatu na ki kwantar da
hankalinki nasan abinda kike tunani, bazan tab'a yimaki wani abuba har sai kin
samu lafiya kinji ko don haka cool your mine" d'aga kanta tayi alamar ta
gamsu da zancenshi
Ba'a wani b'ata lokaci ba aka k'arb'eta saboda duk wani
shirye-shirye anyisu kafin su zo
D'aki ne na mussaman aka bata, bayan Jiddan yak'ara gaya
masu yadda accident d'in yafaru da kuma bayanin da doctor d'in nigeria yayi
mashi, duk suna maganar ne acikin harshen nasara
Take suka fara binciken musabbabin abinda yahana mata gani
Kwana d'aya rak suka d'auka suna bincike kasancewar suna da
wadatatun kayan aiki, Alhamdulillah don ko sunyi nasarar ganin matsalar inda
suka yimashi bayani
"Buguwar da tayi ne yasa ta manta wasu abubuwa sannan
akwai wata jijiyar dake aiki tsakanin idanuwanta da brain d'inta itace tasamu
matsala shiyasa ta daina gani, amma wannan ba wata babbar matsala bace akwai
aikin dazamu yimata insha Allah ganinta zai dawo, sai abubuwan data manta
sukuma a sannu zata tuna mussaman ma in an shawo matsalar ganin nata"
Ya kirasu Abban khadijah yayi mashi bayanin halin da ake
ciki, yakuma shaida ma daddynshi komai kamar yadda su Rafeeq suka kirashi suma
yagaya masu yadda ake ciki
Haka yayi ta jinyar khadijah don hatta wanka shike mata tun
tanajin kunya harta hak'ura ta kyaleshi tun ranan da taga tafad'i a toilet bata
k'ara yadda tashiga ita d'ayaba saidai yayi mata da kanshi
Shiko shikadai yasan a zabar da yakesha duk randa yayi mata
wanka don wani irin sha'awa ce ke damunsa jiyake kamar yayi ta suburbud'arta
amma bazai iya ba harsai radda ya alk'awanta ma kanshi
*NIGERIA*
waya take amsawa saiga Ihsan tayi sallama, a hankali tace
"ya Muhsin sai anjima munyi waya ga Ihsan nan tazo" daga can
b'angaren Muhsin yace "Ok badamuwa kigaida ta" daga haka yayi hanging
up d'in call d'in
Murmushi Ihsan tayi "lalle Samrah baki karatu kin
biyema ya Muhsin ko?"
"Ihsan bazaki gane ba wallahi idan kayi dace da masoyi
mai sonka tsakani da Allah kadace, inma takai tamaki zance su Daddy ma sun
sani"
Kad'a kai Ihsan tayi "keni rabani da wani zance soyayya
ina sweety na take?"
"tana kitchen ita da Ummi wai fankasu take son ci"
"nima kuwa zanci dadina da seemah bata da k'iwa keko
kina nan kin zama uwar soyayya"
Dariya Samrah keyi tana cewa "itama duk jirgi d'aya yakwasomu"
Ita dai Ihsan ko Kallonta batayi ba ta wuce kitchen d'in
Tana zuwa ta tarrada da seemah na aiki lokacin Ummi ta fita
hakan yasa ta cigaba da tayata suna fira, cikin firar tasu ce seemah ke gaya
mata A.j yazo gurin Daddy yana son ya bashi iznin nemanta, kuma Daddy ya amince
mashi
Itadai Ihsan tana jinta amma tunani take yadda mutum zaice
ya had'a soyayya da karatu
Haka suka gama girkin suna fira daga baya Ihsan itama take
shaida masu wanda yakirata, Seemah ce take gaya mata koma waye kila yasanta
Lokacin data koma gida take gayama Mama ashe Muhsin Samrah
yake so shikuma Aj Seemah yakeso, kasancewar bata da abokiyar sirri kamar
mahaifiyarta, itama Mama tajawo 'yayanta jikinta kamar k'awayenta shiyasa duk
wani abu da suke ciki suna sanar mata
Sai a lokacin Mama ta gwada mata cewa aita dad'e da sani
saboda ita suka fara gayamawa kafin su sanar da su Seemah
Haka kwanaki sukai ta tafiya, saidai Rafeeq baik'ara kiran
Ihsan ba tun ranan da yakirata,
Ita kanta tarasa dalilin dayasa take tunanin mai yasa bai
k'ara kiranta ba, alhali bawani sonshi take ba balle har tadamu da rashin
nemanta da bayyi ba
Shikuwa Rafeeq wani aiki aka turasu kullum yana busy shiyasa
baikirata ba ga dalilin nabaison ya takura mata tunda ta nuna batason soyayyar,
amma harga Allah yana son yakirata ko muryar ta yaji
*INDIA*
kwanan ta biyu da dayin aikin idon saidai har yau basu bud'e
mata shiba, wanda yak'ara jefa Jiddan cikin wani hali na tararrabi, bai gushe
da tunanin saba wani d'an tsamurmuren likitan idon yashigo tare da sauran
nurses dake rufa mashi baya
Tunda aka fara k'ok'arin warwarewa bandeji da suka rufamata
a ido, Jiddan ke addu'ar Allah yasa a dace don har kyarma jikinshi keyi
Saidai aka gama warwarewa bandejin gaba d'aya doctor d'in
yace ta bud'e idonta a hankali karta bari Haske yashiga gaba d'aya
A hankali takeson bud'ewa saitaga wani irin haske sai
tarufe, d'aurewa tayi harta samu ta bud'e su duka saidai biji-biji take ganin
mutanan dake wurin shiyasa ta shiga kyafta idanuwanta sai kuma ta koma tana
gani lafiya lau
Jiddan dake rik'e da hannunta duk yabi ya diririce godiya
kawai yakema Allah (S. W.A)
Akanshi tafara sauke idanuwanta, saida kuma takasa kauda
kwayar idanta daga cikin tashi, shima ita yake kallo saida suka d'auki kusan
five minutes a haka, don haka doctor yayi ma kowa alamar da akyalesu a hakan
Itakuwa khadijah gani take kamar ta shekara goma bata ganshi
ba, ga kamanninshi da suka canza mata daga yadda ta sanshi, saidai tasan shine
ba wani ba
Shima yana tuna rabonda ya ganta yau shekara bakwai kenan
Wani irin sak'on soyayya idanuwansu suka shiga aikawa juna
wanda bamai iya fahimtar mai suke isarwa saisu
A hankali tad'aga hannunta ta shafi sajen dake fuskarshi don
ya birgeta kuma ita bata masan dashi ba, tana kai hannunta saman sajen taji
wani irin shock da sauri tajanye ta cigaba da kallonshi, Jitayi kamar tana son
tuno wani abu, saurin kawar da idonta tayi daga gareshi sakamakon wani irin a
zababben ciwon kai da taji lokaci guda ga idonta dasuka yimata nauyi