Breaking News

NOOR AL HAYAT 51-60






 
Khaleel ya fara ajiye jawahir a kofar gidansu, yana lura ranta bai so ba ta bude motar ta fita da kyar ma ta dau ledan siyayyar da tayi kamar baxa ta dauka ba, ko sallama bata yi masa ba ta dai daga ma su sudais dake kallonta hannu ta wuce ciki abun ta, ya lumshe ido ya bude sannan yyi reverse ya bar layin, yana isa kofar gidansu khadijah ya bude motar ya fito sannan ya bude back seat yana kallonsu sudais da suka yi jigum kamar xa su shige jikin uwarsu, yyi murmushi yace "Toh ku fito" da taimakonsa suka sauko kasa ya basu ledojin yace su shiga ciki, Khadijah xata fito khaleel ya dakatar da ita, sudais dake lekanta yace "Uncle Anty bata sakko ba" khaleel ya shafa kansa yace "Xata sakko yanxu ku shiga ku kai ma Umma chocolates din ku ta ajiye maku" yaran suka wuce ciki suna yi suna waiwayowa, khaleel ya shiga motar yana kallonta da damuwa yace "Ki gaya min plss me ya sa ki kuka khadijah, is it me?" Girgixa masa kai tayi a sanyaye wasu hawayen na gangarowa idonta, ya kasa daurewa ya rungumeta yace "No plss I don't want to see you cry, it hurt me, don Allah ki gaya min meye matsalar ki, me ya sa ki kuka a supermarket?" Tayi lamo jikinsa taji ta kasa kukan kuma, duk kamshin sa ya cika ta, murya can kasa yace "Khadijah" a hankali tace "Uhn" yace "Kukan me kike yi?" Ta lumshe ido cikin sanyin murya tace "Sudais" still khaleel yyi na kusan 10 seconds kafin ya dake cike da karfin hali yace "What about him?" Har lkcn idonta a lumshe tace "I saw him" dagota khaleel yyi da sauri yana kallonta at first a bit shock, sai kuma ya hade rai yace "Where?" Ta ki kallon kwayar idonsa tace "A inda muka je shopping" da kyar ta ci gaba wasu hawaye na taruwa idonta tace "He shunned me, he pretend he don't knw me...." Kasa ci gaba tayi ta fara kuka a hankali, khaleel ya lumshe ido, jin ta a jikinsa kuma yasa tayi shiru, a hankali yace "Khadijah..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" dai dai kunnenta yace "forget about sudais plss, forget him...." Sai kuma yyi shiru, Khadijah taji kamar an xare mata radadin da take ji a xuciya, taji ta samu relieve, hankalinta ya kwanta fiye da xaton ta, murya can kasa tace "Toh, nagode" ji yayi kamar yyi kissing dinta but yyi controlling kansa bai yi hakan ba, har lkcn idonsa a lumshe yace "I... I know I love you from day 3 of our encounter....." Duk da yanda gaban Khadijah yyi mugun faduwa don bbu Wanda ya taba fadi mata wannan Kalmar duk tsawon rayuwarta hakan bai hanata fara tunanin me ya faru a rana ta uku da suka fara haduwa da khaleel a UK ba.


Khaleel ya dago kanta yana kallonta, tayi saurin rufe idonta, murmushi yyi murya can kasa yace "Kin tuna ko in tuna maki" dauke kanta tayi xata bude motar yace "Wait" still tayi a wajen bata yi motsi ba, yace  "promise me baxa ki sake kuka a kan hanya ba, sannan you wil forget your past and face the future" shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Khadijah" ta gyada masa kai kawai, yace "Noo, say it out" bata san lkcn da tayi murmushi ba a hankali tace "Ohk" yace "Ohk kadai" kamar bata son ya ji ta tace "I promise" yyi murmushi yace "Yauwa baby" ta turo baki tace "Tana can kayi dropping dinta a gida" wara idanuwansa yyi yace "Wai jawahir?" Khadijah ta ki dago kanta, murya can kasa yace "Ita daban ke daban..." Daga haka ya bude side dinsa ya fita ita ma ta fito yana kallonta, a hankali tana fidgeting fingers dinta tace "Thanks" bata jira cewar sa ba ta wuce cikin gida da sauri, ya bi ta da ido. Aliyu na jin alamar Farouq xai shigo parlorn ya jefar da wayarsa dake hannunsa kan kujera kusa da wanda yake, yyi concentrating kan nasa wayar dake hannunsa, Farouq yace "Toh baka taba abincin ba har ynxu Dr" Aliyu yace "I told you I am not hungry fa, ni xuwa ma xan yi in tafi yanxu" Farouq yace "So soon" mikewa Aliyu yayi yace "Sure, tun da baka da kirki" Farouq yyi murmushi yace "Ko da kai da khaleel baku fada min komai ba na dai san akwai yar tsama tsakaninku, domin kuwa kamar yanda ka min xancensa haka shi ma yyi min naka, amma bai yi requesting karban digit dinka ba ko sanin inda kake, shi yasa kai ma baxan baka na sa ba" ko Kallonsa Aliyu bai yi ba ya nufi kofa Farouq ya bi bayansa yana murmushi, Aliyu na isa gida direct sama ya tafi, har xai shiga dakinsa ya dawo ya bude kofar dakin baby, tana linke kaya ya same ta, ganinsa ta hade rai ya karasa cikin dakin, da farko rasa abun cewa yyi can kuma yyi karfin halin cewa "Ina yan gidan?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Suna asibiti" yana kallonta yace "Who is sick?" Tace "Iklima" sai a lkcn ya tuna yana kokarin fita mumy ta kira saleem yayi driving dinsu xuwa asibiti, yace "Anyi hospitalizing dinta ne?" Baby ta gyada masa kai, yace "Su waye a asibitin?" Tace "Su mumy, mun dawo daukan abu ne da Anty Khadijah" yace "Tana ina?" Tace "Tana dakinta ina ji" fitowa yyi daga dakin har xai wuce nasa sai kuma ya bude na anty Khadijah, babu kowa a dakin ya gani, ya dinga kallon jakarta dake kan gado an xaxxage komai na ciki, karasawa yyi ya ga duk tarkacen takardu da kayan kwalliya ne sai wani kulli a fallen zani, dauka yyi yana jujjuyawa yana kallo, murya ya ji kasa kasa a bathroom, yyi still ya kasa kunne don saurare, "Wllh ban sani ba, sai bayan da aka daura auren alamomin cikin ya fara bayyana...." Aliyu yyi tiptoeing xuwa bakin kofar bayin ya jingina da bango yana jin muryar Anty Khadijah radau amma fa a hankali take maganar "Ko kafin bikin sai da na fita tsakar dare na duba ajiyar yana nan yanda yake na kan dutse" shiru ta d'an yi sai kuma tace "Aa gaskiya ta gun angon kadai ne da matsala, shi ma da bai gano cikin ba nasan da idan ya sha wannan garin da ka bada a ruwan shayi shkkn sai kuma yanda muka yi da shi to bai sha ba, to bai sha ba" da damuwa tace "Haba na kan dutse tuni fa aka cire cikin ban san meye matsalar ba tana dai can a kwance har yanxu cikinta ciwo kamar baxa tayi ba, kilan rashin sabo ne, kasan da karafuna ake cire cikin, ni dai yanxu abinda nake so shine ka taimaka ka karkato mana da hankalin shi yaron, wllh shi ke ba mu matsala" tace "Ehh Aliyu sunansa, wlh taurin kansa ya fi karfinsa, ka ladabta min shi... ka tuna wani hadi da ka taba min da dadewa shekaru masu d'an yawa na xuba masa a ruwan tea....?" Da sauri tace "Yauwa to ka kara min irinsa ta haka ne kadai xa mu samu abinda muke so, sai ya tattara ta ya tafi da ita, ita kuma 'ya ta ka tada min kafadunta" runtse ido Aliyu yyi jin furucinta na karshe ya dinga nanata innalillahi wa inna ilai hi raji'un a xuciyarsa, Anty Khadijah tayi wani ihu tace "Dubu Dari da hamsin kuma na kan dutse??? Haba haba a dube ni domin Allah mana, yanxu kudaden wuya suke wllh, ina xan samo har dubu dari da hamsin ni ba Sana'a ba, sai fa yayata ta bani.... Da ma atm dinta na guna ne ban ki in sa ta ba, Duk fa yan kudadena sun kare ta dalilin xuwa gun ka da nake na kan dutse" ta kwantar da murya bayan wani lkci tace "Amma ka fa san nace ni baxan sake wannan harkar da kai ba kake ambatosa yanxu, sai in ce ma yayata xan je ina? Kawai duk ka bi ka wahal da mutum haba na kan dutse, wajen fa da nisa" da sauri tace "To to na ji, ko xuwa jibi xan taho, sai kuma batun yan gidan don Allah ka kara gume min bakinsu wannan karan har da wata kakarsu ta gun uba ana ce mata yaya naga xata bani ciwon kai ita ma, da yake ta fi shekara 10 a gun yar ta dake aure kasar waje to dai yanxu ta dawo duk da ba gida daya muke ba amma dai ance prevention is better den cure, ita ma a kulle min bakinta plss, sannan abu na karshe, ina yarinyar nan da na sa kayi ma Aliyu hadin nan saboda ita, wata warce nace yayata ta dauketa shekarun baya......" Da sauri tace "Yauwaaaa na kan dutse, to ina son yau dai a bincika min ita, a wani garin take yanxu, kuma ya rayuwa ta kaya da ita, ta haife cikin ne ko ta xubar? A bincika min na kan dutse" cike da confusion Aliyu ke kallon kofar bayin don bai gane komai ba a xancen ta na karshe ba, wani hadin take nufi aka yi masa, wani cikin? kuma wacece?? daga haka tayi sallama tace "Toh sai ka ji ni na wajena" Aliyu dake ta xufa yyi saurin barin bakin kofar sai dai tun bai bude kofar dakin ya fita ba ta shigo dakin, wayancewa yyi kamar shigowarsa kenan, tayi tsuru tsuru tana kallonsa, ya sunkuyar da kai yace "Ina yini" kasa amsawa tayi, just to make her comfortable yace "Yanxu na shigo baby ke ce min an kwantar da iklima ban sani ba" ta hadiye abu da kyar tace "Toh ya aka yi?" Ya isa gefen gado ya xauna a hankali yace "Anty ina son mu yi magana dake plss" tana kifta ido tace "Ina ji" yyi kasa da murya yace "Anty ki taimaka ki taya ni ba mumy hakuri, nasan tana fushi da ni, Anty abinda yasa ku ka ga na damu hada ni aure da aka yi da iklima naga ba jituwa muke ba, kuma fa kuna ganin bata jin maganar kowa gidan nan, idan ta fita sai lkcn da ta ga dama take dawowa to ta ina xan fara bata umarni ta bi a matsayina na mijinta yanxu?" Tuni hankalin Anty Khadijah ya kwanta ta kara tabbatar da shigowar sa dakin kenan bai ji wayarta ba, tace "Toh Aliyu hannunka na rubewa ka cire ka yar ne! Sannan ikliman da ka sani da ba ita ba ce yanxu, wllh wllh ta canxa fitan nan xuwa gidan kawaye da take duk ta bari, wllh ta nutsu saboda rokon Allahn da ake mata" a hankali Aliyu yace "Toh shi kenan Allah sa hakan ne mafi alkhairi" Anty Khadijah tayi mugun jin dadi ta na murmushi tace "Toh Amin, amma ka dade baka sanya ni farin ciki irin yau ba my son, Allah ya maka albarka, kuma duk abinda ya faru a da can mu yafi juna Sharrin shaidan ne" yace "Haka ne Anty, yanxu asibitin xa ku koma?" Ta girgixa kai tace "Yanxu daga nan ma kasuwa xa mu da baby kayan ciki xan siyo in farfesa mata shi ke ran ta...." Aliyu yace "Toh mu je sai in ajiye ku a kasuwan daga can in karasa asibitin dubata" Anty Khadijah ta dade bata shiga farin ciki irin na ranan ba, ta kasa yarda Aliyu ne ke mata wannan jawabin, ta dau jakarta ta bi bayan sa tana shi masa albarka. Tare da baby suka tafi kasuwar, Aliyu ya tsaya cikin mota ya jira su gama siyayyarsu ya ajiye su gida sai ya wuce asibiti kamar yanda ya ce, har lkcn he was very shock, ya kasa gaskata abubuwan da ya ji, duk jikinsa ya yi mugun sanyi, Anty Khadijah ta dinga sa ana yanka kayan ciki har na dubu shidda duk na Iklima kadai, Baby dai na tsaye kusa da ita tana kallon ikon Allah, kamar ance baby ta juya ta wara ido tana kallon wasu twins dake tafiya tare da wata dattijuwa duk tana rike da hannunsu, da sauri tace "Innalillahi Anty kalli yaran can" da sauri Anty Khadijah ta juya ita ma idonta ya sauka kan yaran ko kiftawa bata yi, Baby tace "Anty don Allah da wa suka maki kama?" Anty Khadijah ta share wani xufa tana ci gaba da kallon yaran tunani kala kala a ranta, kamar daga sama suka ji ance baxawara??? Duk suka juya da sauri, kyauta suka gani tsaye cikin shiga ta alfarma gun mai kayan miya tana rike da haba baki bude tana kallon Anty Khadijah, Baby tayi wani kara xata tafi ta rungumeta da gudu Anty Khadijah ta fixgota, kyauta na rike da haba har sannan tace "Ikon Allah su baxawara ashe rai kan ga rai? Ana nan ana xawarcin gidan mutane ko anyi aure?" Anty Khadijah da kamannin ta suka canxa tayi kan kyauta kamar xaki kan kace me ta cakumota tana kunduma mata xagi tace "Ni kike kira baxawara don kaza kazan ki, a ina kika taba sani na" dambe ta fara yi da Kyauta da ta xage ita ma lkci daya sai gashi ta na na Anty Khadijah ta da kasa ta dinga duka tana tula mata kasa a fuska mutane suka taru kansu amma kyauta taki saketa dukarta take kamar an aikota tana tula mata kasa a fuska da baki, Baby da ta rude ta tafi da gudu ta kira Aliyu dake mota, Cikin masu kallon fadan har da Nanny da ta ja yan biyun hannunta suka tafi wani rumfa suka tsaya kallon ikon Allah, da kyar aka janye kyauta kan Anty Khadijah da jini ke ta dalala a hancinta da baki, Kyauta ta kunduma mata wani mugun xagi tace "In kin cika yar halak cikin uwar ki da uban ki mu hadu a ba wani shege gobe mu da sa daga inda aka rabamu, axxaluma yar uwar shaidan kawai" daga haka kyauta ta bar wajen tana cewa "Alhmdllh na san inda na dosa a rayuwa yanxu, ke kam a cin arxiki xa ki kare kina rabe gidan mutane" Aliyu ya bi ta da kallo baki bude, Da kyar aka daga Anty Khadijah dake kunduma ma kyauta xagi bayan ta ga ta tafi, Baby ta kama hannunta suka nufi gun mota da sauri ganin yanda ake kallonsu, naman da basu amsa ba kenan duk da ta bada kudi, Aliyu dai ya kasa motsi inda yake, a hankali ya juya xai bar wajen ya ji ance "Uncleee" ya juya da sauri idonsa ya sauka kan twins dake wani gefe a tsaye Nanny kuma na siyan abu a shago bayan taga karshen damben, ya wara ido ya buda hannunsa shureim ya taho da gudu ya daga sa sama ya rungumesa yace "What are you doing here sweetheart?" Shureim ya washe fararen kananun hakoransa yace "We came with nanny and Anty to get something, Ga Nanny a cikin shop Anty kuma tana cikin mota tana jiran mu" kallon sudais Aliyu yyi ya ga yana tsaye ne yana kallonsu, a hankali ya ajiye shureim yana rike da hannunsa ya isa gun sudais haka nan yaji gabansa na faduwa ya duka dai dai height dinsa yace "How are you angel?" Sudais ya sauke idonsa yace "Am good" daga haka ya shiga shagon da Nanny take ciki, Aliyu ya bi sa da kallo, shureim yace "Uncle what are you doing here?" Aliyu yace "I came to get something also, why is ur twin behaving strangely, and he looks sick..." Fitowa sudais yyi don ba can cikin shagon ya shiga ba yana kallon Aliyu yace "Because I don't like you, stay away from me and my brother" Kallonsa Aliyu yake ko kiftawa babu, Shureim ya tura sudais yace "You are mean...."


Sai da sudais ya gama kallon d'an uwan nasa sosai kafin ya kai masa mari yana huci yace "How dare you call me that" Aliyu na ganin shureim yayi kan sudais ya daga sa sama ya rungume sa a hankali yace "Yi hakuri ka kyalesa sweetheart" kuka shureim ya fara yi hana sa dukan sudais da Aliyu yyi, Sudais na huci yace "I don't like you both" dai dai fitowar Nanny daga shago, da sauri ta karaso tana tambayar me ya faru ganin shureim na kuka hannun Aliyu, sudais ya fashe da kuka shi ma yace "Nanny shureim started 1st, he insulted me" Nanny ta hade rai tace "Ohh har cikin market din ma sai kayi fada sudais, kai dai baka ji kuma nasan kai ka fara tsokanarsa ba ruwan shureim, silly boy kawai from henceforth bana sake xuwa ko ina da kai, ko kace xaka bi ni sai na ma duka" juyawa sudais yyi ya fashe da matsanancin kuka da gudu ya bar wajen xai je gun uwarsa, bin bayansa Nanny tayi tana kwala masa kira don ta can tsallake khadijah take kuma titin is very busy, amma sudais yaki tsayawa kuka kawai yake yana gudu yana kiran Anty, Aliyu na ganin haka shi ma ya bi su da sauri shureim na hannun sa, khadijah dake cikin mota tana xaune maxaunin driver don ita ta kawo su kasuwar haka nan kawai taji gabanta ya yanke ya fadi dai dai lkcn da taji ihun da mutane ke yi, tana juyawa kawai ganin Sudais dinta tayi a tsakiyar titi shi ma duk ya rikice ihun da mutane ke yi, ga mota har biyu sun taho da gudu ko wanne na son kauce masa, tunda take bata taba irin ihun da tayi ba a lkcn, lkci daya ko ina na kasuwan yyi tsit don duk yanda motar ta so avoiding sudais hakan bai yiwu ba, sai kuma a ka dau salati Khadijah ta fito a rikice jikinta na rawa ganin sudais kwance cikin jini ta fasa wani ihu kanta na juya mata, suman da ya kamata tayi nanny ce tayi sa a lkcn, ita kanta bata san me ya hanata sumewan ba, Aliyu da yyi still shi ma ya kasa motsi na few seconds ganin abinda ya faru lkci daya yaji strength ya dawo masa, ya ajiye shureim dake ihu yana kiran dan uwansa ya nufi gun sudais dake a kwance kan titi cikin jini mutane sun taru kansa mata na kuka maxa na salati, har da kyauta cikin mutanen, babu rabon Anty khadijah xata ga abinda ya faru don tsabar kunya bata jira Aliyu ya fito ba ta hau adaidaita da baby suka koma gida, cikin tashin hankali Aliyu ya karbi yaron hannun wani mutumi dake jijjigasa yana salati, a nan Aliyu yaji kamar bai taba xama likita ba duk rayuwarsa gaba daya basira ta dauke masa ya rasa ya xai yi da sumammen yaron dake hannunsa fuskarsa duk jini, cikin matsanancin kuka khadijah ta isa gun ta wani fasa ihu a gigice ta durkusa jikinta na rawa take cewa "Na shiga uku, don Allah ku taimakeni kar ya mutu ku rufa min asiri, kar ku bari ya mutu" daga kai Aliyu yyi a karo na farko yana kallonta jin muryarta, lkci daya signal dinsa ya sake daukewa yana mata wani irin kallo ita kuwa sai jijjiga sudais take ba tare da ta kula a hannun wa yake ba tana kuka tana cewa ya tashi kar ya tafi ya bar ta, kyauta ta saki salati baki bude tana kallon khadijah tace "Kamar khadijah nake gani ni kyautar Allah" khadijah ta kalleta ita ma da sauri, da gudu ta nufe ta rikota tana kuka cikin rauni tace "Anty ku taimake ni kar ya mutu don Allah, kar ya tafi ya bar ni" Kyauta ta kwalalo ido tace "Yaron ki ne Khadijah?" Khadijah ta dinga gyada mata kai tana kuka sosai, kyauta ta fashe da kuka tace "In sha Allahu baxai mutu ba xa mu tafi asibiti yanxu khadijah, baxai mutu ba..." wata mata ta fixge yaron a hannun Aliyu a mugun fusace ganin khadijah kawai yake kallo tace "Dubi mutum kamar an dasa sa a gun ya sa yaron da ba mu san ko ya mutu ba ko yana raye a gaba yana kallo, wannan wani irin uba ne kai, ni na xata taimkon gaggawa xai bada...." Khadijah ta tsayar da kukan da take ta sake kyauta ta nufi matar ta rikota cikin rudewa tace "yaro na bai mutu ba kar ki kara cewa ya mutu don Allah kar ki kara, wllh bai mutu ba, Allah baxai sa ya mutu ba" sosai ta ba mutanen gun tausayi wani mutumi ya sa sudais tare da matar a motarsa domin xuwa asibiti, mutumin ya kamo hannun Aliyu dake tsaye yana kallon khadijah da har sannan bata lura da shi ba yace "kar ka damu he will be alright in sha Allah shiga mu je asibitin tare" bayan motar Aliyu ya shiga suka dau hanyar asibiti, sai a sannan basirar sa ta likita ya dawo masa ya karbi sudais a rude ganin numfashinsa na sama ya dinga basa numfashi, banda kuka babu abinda matar dake kusa da shi take tana addu'ar Allah ya raya sa, jin mutumin dake ta sharara gudu a mota yyi parking Aliyu ya dago kai tare da bude motar ya ga asibitin da yake aiki ma mutumin ya kawo su, Aliyu ya fita rike da sudais yyi cikin asibitin da sauri nan aka shiga emergency da yaron, sai bayan kusan minti talatin Aliyu ya fito tare da wani likita daga emergency ward da aka shiga da sudais suka bar likita daya a kan sa da nurse, Dr Saif ya nufi gun su khadijah dake xaune reception da kyauta da wasu mutane har sun gaji da lallashinta don ko tayi kuka har ta gode Allah, tsabar tashin hankali ko gane asibitin bata yi ba, shureim dake jikinta ma kukan yake yana tambayarta me ya samu sudais, Nanny da ta suma an kwantar da ita asibitin ita ma, mikewa khadijah tayi da sauri ganin likitan, Aliyu ya tsaya daga inda yake har lkcn mask na bakinsa da hanci, Dr Saif yace "Ina mahaifiyar yaron?" Khadijah dake kallonsa gabanta na faduwa tace "Ni ce" Aliyu ya cire mask din dake fuskarsa yana kallon khadijah da wani irin mamaki, at the same time confusion, likitan ya tsaya kare mata kallo kamar bai yarda ba, can dai yace "Toh mahaifinsa fa?" Tana share hawayen dake xubo mata cikin rawar murya tace "Baya nan" likitan na kallon Shureim ya xaro ido yace "Subhanallah yan biyu ne?" Cikin kuka khadijah ta gyada masa kai, jikin likitan yyi sanyi sosai, ya shafa kan shureim dake kuka yana rike da mayafin Khadijah a hankali yace "Don't worry my boy ur twin will be okay in sha Allah, madam xa ki iya shiga ki gansa amma plss kar ki wani damu ciwo ne kawai yaji a kai sai bruises, so don't cry while inside, shi kuma wannan ki bar sa a nan ba sai kin shiga ba" daga haka ya juya yana kallon Aliyu dake nesa da su kafafuwarsa sun kasa daukarsa saboda shock yace "Dr plss see her inside, amma kar ta dade a ciki" daga haka ya kama hannun shureim yace "Big boy xo mu je office ka jira mumy" shureim xai masa taurin kai sai ya bi mamarsa ya daga sa sama kawai ya wuce office dinsa da shi don bai son ya ga dan uwansa a halin da yake ciki yanxu, Tuni Aliyu ya mayar da mask din fuskarsa yayi gaba kamar me counting step dinsa Khadijah na biye da shi a baya, tsabar tashin hankalin da ke tare da ita bata ko kalli wanda take bi ba balle ta san waye. Suna shiga ward din Aliyu ya tsaya bakin kofa ita ta shiga ciki gabanta na faduwa, ko gama ganin sudais bata yi ba ta fasa wani ihu, Nurse din ta karaso da sauri ta fitar da ita dakin tace "Haba madam, sai kace ba musulma ba wannan ihu haka" khadijah ta fashe da matsanancin kuka tana jijjiga nurse din tace "Don Allah Anty kar ku bari wani abu ya samu yarona, they all I have, plss ku taimake ni" rungumeta nurse din tayi tace "It's ohk madam jikin ai da sauki, you just pray Allah ya tashi kafadarsa kuma kada Allah ya sa ya tashi da wata matsala" Khadijah ta xame kasa tana kuka tace "Na shiga uku wllh kilan mutuwa xai yi ya bar ni, don Allah ku taimaka min" juyawa nurse din tayi ta koma ciki ta rufe kofar, Aliyu ya kasa ci gaba da kallon khadijah lkci daya idonsa ya kada, yaranta? To waye ubansu? Abinda ya dinga masa yawo a rai kenan, kawai ya ga ta mike ta nufo sa, kana gani kasan ta gaji da kukan ta riko sa cikin rauni tace "Plss Dr kar ku bar min yarona ya mutu don Allah ina rokan ku, they are all I've got in this world bayan ummata, plss ka taimaka Dr ku cire masa abinda ku ka sa masa a hanci ina son yarona" Aliyu ya kasa ce mata komai lkci daya hawaye ya kawo idonsa, da ba don a rude Khadijah take ba bbu abinda xai hana ta gane Aliyu ne gabanta saboda kwayar idanuwansa amma saboda tashin hankali bata gane ba ganin, hawayen idonsa ta tsayar da kukan da take xuciyarta na bugawa tana kallonsa ko kiftawa babu, bayan few seconds cikin sanyin murya tace "Dr ya mutu koh?" Aliyu bai iya yace komai ba ya ji ya kasa controlling kansa hawaye suka shiga sakko masa, he don't want to believe Khadijah conceived with him, he don't want to believe she conceived that deadly moment, if so then he is not worth to be forgiven, bai cancanci ta yafe masa ba, don ya mata xaluncin da dole baxata iya yafe masa ba, sai a sannan maganganun da Anty khadijah take a waya daxu ya fara dawo masa, ya juya ya hade kansa da bango yana hawaye sosai duk ya ji ya tsani kansa, yanxu yaran nan nasa ne kenan?? He is there illegal father, the cute boys... Are his and Khadijah's, they got them out of wedlock.... Lkci daya ya juya ta dalilin sound da ya ji bayansa, nan ya ga khadijah sume a kasa.


A hankali khadijah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi ta dinga bin inda take kwance da kallo, Umma ce xaune dakin da Nanny da ta ci kuka har ta gode Allah, sai kyauta da tayi tagumi, Umma ta mike da sauri ganin khadijah ta bude ido ta karasa kusa da ita da damuwa tace "Sannu daughter, how are you feeling now?" Mikewa xaune Khadijah ke son yi amma kanta yyi mata nauyi ga kirjinta dake mata xugi, Umma ta riketa tace "Koma ki kwanta" Kyauta ta iso kusa da ita ita ma da damuwa tace "Sannu khadijah" Shiru khadijah tayi kamar me son tuno abu, Umma ta hade rai tace "Don't stress ur self thinking of anything, just relax...." Hawaye ya kawo idonta ta kamo hannun kyauta cikin rawar murya tace "Anty mai girki ina sudais dina, ya mutu koh? Don Allah ku gaya min, kar ku" Umma ta dakatar da ita a mugun fusace tace "Ke kika kashe sa halan? Ji wani xance da kike ma mutane khadijah" Girgixa kai khadijah tayi da sauri hawaye na sakko mata, Kyauta tace "Toh yana nan lafiya khadijah, har ya tashi shi ma, suna can tare da d'an uwansa da wani likita" Khadijah na goge idonta tace "Toh xan iya ganinsa don Allah?" Harara Umma ta watsa mata tace "Da drip din xa ki je ki gansa, kuma ki rufe min maki haka, ance maki yana lafiya" Khadijah bata sake cewa komai ba sai dai ban da faduwa babu abinda gabanta yake, Umma ta mike ta shiga hada mata shayi, Nanny ta xauna kusa da ita cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Khadijah, Sudais yana nan lafiya har ya tashi, suna tare da Shureim yanxu haka" Sai a sannan khadijah ta ji hankalinta ya kwanta sosai, Nanny ta mika mata wayarta tace "An kira ki har sau biyu, but I picked..." Khadijah ta karbi wayar tana kallon wanda ya kirata ta ga Khaleel ne, ta kalli nanny a hankali tace "Me ya ce?" Nanny tace "Na gaya masa abinda ya faru, yace xai xo clinic din" Khadijah bata ce komai ba ta ajiye wayar, ta ji tana ma son ganinsa, jin xai xo hankalinta ya kara kwanciya. All this while Aliyu na ward din da sudais yake tare da Shureim, kwata kwata bai son ya bar su ko na minti daya, da ya fita ba a jimawa xai dawo kuma har lkcn ya ki cire mask din bakinsa da hanci, damuwa ce sosai tare da shi, da ya kalli yaran ya tuna nasa ne sai yaji hawaye a idonsa, shi kuma irin tasa kaddarar kenan?? Har yan biyu ba ta hanyar aure ba, har ransa yake jin tausayin kyawawan yaran, he wished ba ta haka suka xo ba, Shureim bai ganesa ba sai dai ya lura da irin yanda sudais dake kwance ke kallonsa, A hankali ya isa kusa da yaron ya duka a sanyaye yace "You want something??" Sudais ya girgixa masa kai, Shureim ya kallesa da sauri na few seconds kafin yace "The voice.... sounds familiar" murmushin karfin hali Aliyu yyi ya sauke mask din fuskarsa a hankali yana kallon yaron, Shureim yyi shiru yana kallonsa can ya juya ya rungume hannunsa ya hade rai yace "You caused my brother's accident" Jikin Aliyu yyi sanyi sosai, ya mayar da dubansa kan sudais ya ga ya ki kallonsa shi ma ya hade rai, bude kofa aka yi xai mayar da mask dinsa da sauri yaji muryar colleague dinsa, Dr Muktar ya karaso yana kallon yan biyun yace "Maa sha Allah, he is recovering fast" ya kamo hannun Sudais yace "How are you feeling now handsome?" A hankali Sudais yace "Alhmdllh" Dr mukhtar yyi murmushi yace "Good" kallon Aliyu yyi yace "Kasan kuna yanayi da boys din nan sosai, da ba don na san baka taba aure ba bbu abinda xai hanani cewa yaranka ne Dr" Aliyu ya kirkiri murmushin karfin hali yace "Gaskiya ne" Dr mukhtar yace "Naga kamar sun ma shiga ranka kai ma tunda gashi ka ki barin ward din tun daxu" Aliyu yace "Sure they are cute" Dr mukhtar yace "Just came to check on them dama" daga haka ya juya ya fita, Aliyu ya kamo hannun yaran murya can kasa yace "Am sorry for all that happened sweethearts forgive me plss" a hankali Shureim yace "Ohk..." Kallon sudais da yyi shiru yyi yace "And you sweetheart?" Sudais ya sauke kansa yace "Me too" jawo yaran jikinsa ya yi cikin sanyin murya yace "I love you boys" lkci daya idanuwansa suka kada, how he wish Khadijah xata yafe masa ba tare da ta sa masa heart attack ba, ta ajiye komai su xauna tare da yaransu, bai taba saba maganar mahaifiyarsa ba amma da kamar wuya wannan karan, it will be different.... he will marry Khadijah and have his boys in sha Allah, and he will neva be ashame showing them as his children, wani mugun son yaran ne ke fixgarsa yana rungume da su, bude kofar dakin aka yi Umma ta shigo tare da wani likita, khaleel na biye da su a baya, A hankli Aliyu ya daga mask dinsa sannan ya juya suka yi ido hudu da khaleel, Dr Abdul yace "Dr their grandma and a Dr also, my frnd Dr Ayman" Aliyu sai kallon khaleel yake kamar yanda shi ma khaleel ke kallonsa duk da fuskarsa a rufe yake, Umma ta kalli Dr Abdul sanin ance baxa a bar su su shiga gun yaran ba tace "Mun gode Dr" Dr Abdul yace "Ba komai Mama" Dr Abdul yace "Ayman bari in koma bakin aiki na" khaleel yace "Tnxx Abdul" daga haka Abdul ya fita, Shureim ya sauko saman gadon ya rungume khaleel, khaleel ya daga sa sama yace "How are you" kamar xai yi kuka yace "I am fine but my brother isn't" Khaleel ya ajiye sa ya karasa yana kallon Sudais cike da tausayinsa, Shureim kuma ya nufi gun Umma dake kallon Sudais ita ma a sanyaye, plaster ne gaba daya kansa, khaleel ya kamo hannunsa yace "You will get well soon in sha Allah my boy" Sudais xai fara kuka ya rungume sa yace "Noo don't cry be a strong boy" Sudais yace "Uncle ina Antyna" khaleel yace "Xata xo yanxu" sudais yace "Ka kai ni wajenta I want to see her" Khaleel yace "Noo she will be coming soon" Aliyu dai na tsaye yana ya na kallonsu, Can ya kalli Umma yace "Plss Maa it shouldn't take long xa ku iya tafiya yanxu the boy need rest" Umma tace "To xa mu fita yanxu Dr" khaleel ya juya yana kallon Aliyu, mikewa yyi ya isa gabansa yana kallon cikin idonsa yace "Then discharge him now, xa mu je gida in ci gaba da treating dinsa or I take him to another hospital" Aliyu yyi murmushi daga cikin mask din fuskarsa yace "And who are you to say that? His father? Or?" Umma tace "Aa bai kai haka ba Dr xa mu fita yanxu ai" wani kallo khaleel ya dinga ma Aliyu, Umma tace "mu je khaleel tunda a bakin aikinsu suke" kallonta khaleel yyi, duk da bai yi niyyar fita ba amma ya ji kunyanta yace "Toh umma" daga haka ya nufi kofa Shureim ya bata fuska kamar xai yi kuka yace "Uncle are you leaving us?" Sudais ma ya dinga kallonsa Kamar xai yi kukan, Khaleel ya juyo yace "Noo sweetheart I am around" Daga haka ya fita, Umma ta bi bayansa tana kara ba Aliyu hakuri tana fita ta rufe kofar, wata cleaner ce ta shigo dakin da abinci da ruwa da Aliyu ya sa ta siyo, ya mika ma Shureim nasa ya karba, Ya shiga ba sudais nasa da kansa. Khadijah duk ta damu tana son ta ga yaranta ganin har da Shureim ma tun da ta bude ido bata gansa ba, amma tsoron Umma yasa ta kasa cewa komai don tana iya balbaleta yanxu tunda ta ce mata they are all fyn, Khaleel dake tsaye dakin yana kallonta ya lura da yanayinta, ita ma ta tsaya kallonsa amma ta kasa ce masa komai ya san she Wants to say something, ya kalli Umma dake magana da wasu neighbours dinsu biyu da suka xo duba sudais, Nanny kuma ta koma gida tayi girki, Kyauta ma ta koma tace xata dawo ko da daddare da mai gidan ta, Khaleel ya karaso kusa da ita a hankali ya d'an duka yace "What?" Murya can kasa kamar xata yi kuka tace "I want to see my kids plss" wani kallo ya mata, sai kuma ya d'an yi murmushi yace "To sannu mai kids" ta bata fuska tana kallonsa alamar please, yace "Ohk wait bari Umma ta raka bakin nan sai in kai ki" lkci daya hankalinta ya kwanta tace "Toh ngdd" Umma na fita don yin rakiya ya cire mata drip din hannunta da ya kusa karewa, duk da jirin da take ji ta mika masa hannunta ya rike ta sauko daga kan gadon ta sa takalminta sannan suka fita ward din da sauri tana jin kamar xata fadi ba don ya rike hannunta ba, direct ward din da yan biyun suke ya nufa da ita, a hankali ya murda kofar ya bude, khadijah tayi ido hudu da Aliyu dake ba sudais abinci, still tayi a gun taji komai nata ya tsaya, xuciyarta ya dinga bugawa da sauri da sauri, Shureim ya sakko ya taho da gudu ya rungume ta, sudais yyi murmushi cike da jin dadi ganin uwar tasa yace "Anty...." Mikewa Aliyu yyi ya rufe abincin yana kallonta da khaleel yace "You can come over... But just few minutes" Khadijah ta warce hannunta a na Khaleel ta janye Shureim a jikinta ta juya ta bar wajen kamar xata tashi sama, direct reception ta nufa, tana kallon nurses din cike da masifa tace "Who is the Dr in charge of this hospital..." Kallonta nurses din suka tsaya yi, can wata ta mike tace "Me ya faru madam" tana huci tace "ohk, I want my kid discharge immediately, ku bani bill din in biya in bar nan yanxun nan plss" cikin tsawa ta kare maganar nurse din ta koma ta xauna tace "Easy madam, this a hospital, they are patients all over, ki je gun likitan da ya karbe su, shi xai yi discharging dinsu ba mu ba madam" khadijah na mata wani kallo tace "Wani likita kenan ina office dinsa kuma?" Nurse din tace "Dr Aliyu, kina haurawa sama office dinsa is by ur right, xa ma ki ga sunansa a jiki" kallonsu Khadijah ke yi xuciyarta na bugawa jin sunan da suka kira, can ta juya kamar xata tashi sama ta wuce upstairs din, Har lkcn khaleel dai na tsaye bakin kofa yana kallon Aliyu, Aliyu ya isa dab da shi yana masa wani kallo yace "Da matsala ne malam, naga kallon yyi yawa?" Wani murmushi khaleel yyi yace "You watch and see" Dawowa khadijah tayi dakin cikin tashin hankali ta nufi gun yaranta ta cire dip din hannun Sudais ta sauko da shi kan gado ta kama hannun Shureim ta nufi kofa, tsayawa gabanta Aliyu yyi yana kallonta da kyau yace "Ba inda xa ki je da su Iman" xaro ido tayi jin abinda ya fada ta tura sa da karfi amma go gezau, xuciyarta na heaving da mugun mamaki tace "Ba inda xan je da su kamar yaya??? ka taba sanin su ne, ko kuma ni ka san ni ne? Where did you knw us from" yyi wani murmushi yace "Khadijah, am giving you my words, you are not moving a step forward with my kids, ki fadi duk amount da kika ga yyi suite din ki, tun daga daukar cikinsu, rainon cikin, haihuwarsu har xuwa girman su yanxu and I will pay you, kilan hakan kadai xai sa ki yafe min idan na amshi wahalata da na hada ki da at a very tender age, ni kuma baxan ji kunyan daukansu in kai su gida gun iyayena a matsayin yaran da na haifa out of wedlock ba, shikenan kema na raba ki da wahala na raba ki da rikon 'ya yan da kika samu ta hanyar fyade da aka maki, sai ki tafi kiyi auren ki hankali kwance ba tare da kin kara tunanin kina da yaran da kika haifa ba ta hanyar aure ba, I am collecting my boys today for ur own good"

Kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bakin ciki da takaici ne fal idanuwanta, xuciyarta ya dinga mugun bugawa, ta hadiye abu da kyar, lkci daya idanuwanta suka yi jajir cikin muryar da ba ta ta ba tace "Come again Aliyu... I didn't get you" Cire mask din bakinsa yyi gaba daya yana kallonta da kyau cikin husky voice dinsa yace "You are not daft Iman, you heard me right, or you ask ur bodyguard xai maki bayani da kyau" bai rufe baki ba ta sauke masa mari tana huci, wani murmushi khaleel yyi yana shafa sajensa yace "Seems you both need privacy" daga haka ya juya ya bar wajen har sannan yana murmushi, Aliyu ya kauda kansa na few seconds kafin ya juyo a hankali yana kallonta da wani irin mamaki, hawaye na sauka idonta tana girgixa kai tace "Allah ya isa tsakanina da kai Aliyu, shari'ar mu da kai dama na fada maka sai a lahira, kuma yarana ba naka bane, ba kai ka haifar min su ba, you don't have any right over them, idan duk duniyar nan xa su hade nan wlh wllh baxan baka su ba, ni na sha wahalan kayana ni na haife su, baka isa ka raba ni da su" ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi, hakan yasa su shureim ma suka fara kuka suna rike da ita, kallonta kawai Aliyu yake da idanuwansa da suka yi jajir, ganin khaleel ya bar wajen khadijah ta kama hannun yan biyun ta da sauri ta juya xata bi bayansa Aliyu ya fixgota yayi jamming kofar yana mata wani mugun kallo, lkci daya ta cakumosa tana kuka mai taba xuciya tace "Ka bude mana mu fita Aliyu, ka bude kofar in fita da yarana kar in tara maka jama'a" yanda ta rikice haka yaranta ma suka rikice suna kuka, daukar ta Aliyu yyi ya nufi bathroom dake ward din ya tura ta ciki yace "I will teach you sense Khadijah...." daga haka ya rufe kofar da makulli ta dinga bubbuga kofar a rude tana kuka tana kiran sunansa, Sudais ya kara fashewa da matsanancin kuka yace "Why are you doing this to our Anty, plss let her out" Shureim ya dinga bubbuga kofar shi ma yana kuka yana kiran ta, Aliyu ya hade kansa da bango ya runtse ido xuciyarsa na bugawa, lkci daya ya juyo ya kama hannun yaran gaba daya suna turturjewa ya watsa masu wani mugun kallo da idanuwansa da suka yi ja, ba shiru suka yi tsit ko wanne a tsorace, ya bude kofar ward din ya fita da su, ward na intensive care ya shigar da yaran tunawa da yayi bai taho da motar clinic din ba, banda kuka babu abinda suke yi suna kallonsa a tsorace, fuskarsa daure yace "I don't want to hear any of you cry again" shiru suka yi sudais ya riko hannunsa yace "plss bring out our Anty from the toilet" sauke idonsa kasa yyi a hankali yace "Ohk i will do that now" daga haka ya fita ya rufe kofar yanda baxa su bude ba, sama ya wuce da sauri ya shiga office din Muktar ya dau makullin motarsa sannan ya sauko, yana bude kofa su sudais suka yi tsit daga kukan da suke, Shureim yace "Uncle where is she plss" hannunsu ya kama ya fita da su, ya bi ta bayan asibitin xuwa parking space, back seat ya saka yaran gaba daya sannan ya shiga driver seat ya tada motar ya bar asibitin. K'asa kuka twins din suka yi a motar saboda Aliyu da ya hade rai, kana ganinsu kasan a tsorace suke barin Shureim, driving kawai yake har ya iso gida bayan yyi parking ya fito ya bude masa motar yace "Come down" da farko kin sakko suka yi, ganin kallon da yake masu duk suka fito, Shureim na goge idonsa cikin rawar murya yace "I thought you where a good friend, plss don't kidnap us away from our Anty, she will be sad" Duk da hawayen da ya taru idon Aliyu hakan bai hanasa durkusawa gabansu ba ya rungume su gaba daya yace "I didn't kidnap my kids, I brought you two to ur Granny" Sudais ya xaro ido yace "We left her at d hospital and this is not our home" Aliyu na kallonsu cikin sanyin murya yace "This is your father's home" A tare suka hada baki gun ce masa "Where is he?" Shiru Aliyu yyi yana kallon handsome boys din, sudais yace yace "Anty told us our father... Is a Barrister, she said he travelled immediately we where born and that... he will come to us one day" Jikin Aliyu yyi mugun sanyi yana kallonsu, Shureim yace "We will love to see our dad" mikewa Aliyu yyi ya kama hannunsu ya wuce cikin gida da su. Sudais ya bata fuska kamar xai yi kuka yace "I thought you are taking us back to our Anty" gaba daya yan gidan na parlor xaune ana jajanta abinda Kyauta ta ma Anty khadijah, saleem sai cewa yake da ma da shi aka je ya lallasata ya cire mata hakora ya ga wanda ya tsaya mata,  mumy dai bata ce komai ba sai kallon Anty khadijah dake kwance kasa take duk jiki yyi tsami don ma ta gasa jikin da ruwan xafi, baki a kumbure har da ido, iklima ma an sallamota tana sama a kwance, gaba daya occupant din parlorn suka dinga kallon Aliyu da twins din hannunsa, Anty khadijah ta mike xaune da sauri ita ma tana kallonsu, Baby ta mike da mugun mamaki tana kallon yaran tace "Laah yaran da muka gani a kasuwa daxu, yaya where did u knw dem from, mai ya samu kan wannan" Aliyu ya isa har gaban Mumy dake kallon yaran ya sake hannunsa, a sanyaye yake kallonta, yyi gathering courage da kyar yace "Yaran da Iman ta haifa kenan, she got pregnant after the incident" Ba Anty khadijah kadai ba har Mumy sai da ta girgixa ta mike tana kallon yaran dake ta kallonta sannan ta mayar da dubanta kan Aliyu cikin wani yanayi tace "How did you knw Abuturrab, where did you get dem from???" hawaye suka shiga sakko masa yana kallon mahaifiyar tasa a sanyaye yace "I met them today mum, I don't knw if Khadijah will ever forgive me... I ruin her at a very tender age, this boys are my blood, Mumy na kawo su gida ne don nima in yi facing ko da kadan ne daga cikin abinda tayi facing a rayuwarta duk da ni na fita ga ta...." Kasa ci gaba yyi ya bar parlorn ya wuce sama hawaye na sakko masa, Anty khadijah dake ta xufa ga cikinta da ya tsure tace "Mun shiga uku, Anty fati kin ga wani sharri koh, kin ga wani hauka irin na Aliyu ko? yaushe Aliyu ya isa haifan wa ennan yaran? ta je an mata ciki a wani waje ta makala masa kuma ya yarda saboda wawa ne shi... a ina ma ya ganta???" Kai kana gani kasan kame kame kawai take duk ta rude, Su Shureim sai bin kowa na parlorn suke da kallo a tsorace, baby ta fashe da kuka cike da tausayin yayanta, Salim ma sai kallon yaran yake a duk jikinsa yyi sanyi ganin kamannin Aliyu sak tare da su, Mumy ta fashe da kuka sosai ita ma tana kallon yaran, hakan yasa su ma suka fashe da kuka, babu abinda take gani tare da yan biyun sai Aliyunta lkcn da yake kamar su, Anty khadijah ta haura sama kusan a guje tana cewa "Yau na ga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, ina yake ya xo ya fitar mana da shegun nan da ake shirin kakaba masa, ya xo ya mayar da su inda aka basa su, amma Allah ya isa tsakaninmu da yarinyar nan, ta rasa wanda xata ma sharri sai Aliyu saboda tsautsayi ya gifta tsakaninsu? Ni dai nasan da hankalin Aliyu baxai mata fyade ba, sharrin shaidan kawai da kuma sharrin ta don ita ke shisshige masa, wlh baxa mu amshi shegu gidan nan ba, kaf xuri'ar mu ba a taba haka ba baxa a fara a kan d'an yayata ba" tana wucewa sama mumy na share hawayenta ta kama hannun yan biyun ta wuce sama xuwa dakinta da su. Wata nurse ce ta shigo dakin ba ma sudais allura ta ga babu kowa dakin sai kofar bayi da ake ta bubbugawa ta isa da sauri ta bude kofar da mamaki ganin key aka sa ta waje, khadijah ta fito tana bin dakin da kallo ganin ba kowa ta riko nurse din a rikice tace "Na shiga uku nurse ina yarana? Where are they plss" nurse na kallonta da confusion tace "Yanxun nan na shigo madam" da gudu khadijah ta fita xuwa ward din da aka kwantar da ita, ta ga Umma ce xaune sai Nanny da khaleel dake tsaye ya jingina da bango idonsa a kan wayar hannunsa, ta fashe da matsanancin kuka ta xube wajen tace "Wayyo Umma na shiga uku ya tafi min da yarana" khaleel ya iso gabanta da sauri da mamaki yace "Ya tafi da su ina? Kina kallonsa ya tafi da su" ficewa yyi ward din da sauri, Umma da ta gigice tace "Wa ye ya tafi da su Khadijah, waye shi" Khadijah ta riko Umma tana kuka sosai tace "Umma Aliyu, ya tafi da yaran, ya wuce min da yarana" a sanyaye Umma ke kallonta, Nanny ta bi bayan khaleel da sauri tana cewa "Me ya kawo sa asibitin, mun shiga uku" umma ta dago Khadbijah ta rungumeta, cikin rawar murya take cewa "Umma kar ku bari ya raba ni da su, baxan iya rabuwa da su ba, don Allah a taimake ni a karbo min yarana ni na yafe masa duniya da lahira ya bar min yaran, wllh na yafe masa har cikin xuciyata amma yayi hakuri ya ba ni yarana" tana kai wa nan ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kiran Umma, hawaye ya shiga sakko ma umma ta rasa abinda xata ce ma 'yar tata.


Direct office din Dr Abdul khaleel ya wuce, ya samesa xaune yana aiki, ganin khaleel ya bar abinda yake yi yace "He is improving ko Dr" khaleel bai tanka sa ba isa gabansa ya dafa table yana kallonsa bbu yabo bbu fallasa yace "Dr Aliyu.... Where is his home?" Dr Abdul yace "Aliyu? Ba yana office ba?" Khaleel yace "Baya nan" da mamaki Abdul yace "Hope babu matsala dai?" A takaice Khaleel yace "Babu, ina gidansu yake" Abdul yace "Toh, he is not the type that mingle gaskiya I dont knw his home" juyawa Khaleel yyi ya fice office din, direct parking space ya nufa ya hau motarsa ya wuce gidan Farouq. Umma ta dinga kwantar ma khadijah hankali duk da taki saurarenta, daga karshe Umma ta fita ta biya bill dinsu don bata ga amfanin xaman asibitin ba, na khadijah kadai suka karba ban da na sudais kamar yanda Aliyu yyi instructing din su, da kafa suka fita asibitin don Umma bata xo da mota ba, suna isa bakin titi ta tsayar masu da abun hawa suka wuce gida. Girgixa kai Farouq yyi yana kallon Khaleel yace "Ni fa ba ruwana, kamar yanda na ki ba sa address din ka, to kai ma baxan baka address din sa ba gaskiya, ku kuka san abinda ya hada ku can.." Wani kallo khaleel ke masa kafin ya mike ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya wuce, yana driving ya dau wayarsa ya fara kiran Khadijah, har ya katse bata dauka ba, nan ko tana zaune ita kadai daki tayi kukan har ta ji ba dadi, Umma kuma na parlor da Nanny sun yi jigum, Umma ta rasa ta ina xata fara yanxu ta ina xa su fara xuwa neman yara, Jin wayar ya sake ring Khadijah ta daga da kyar ta kai kunne, jin muryar ta jikin khaleel yyi sanyi, a hankali yace "Plss ki kwantar da hankalin ki Khadijah, xa a amsar maki kids din ki, he have no right over them, in sha Allah we will get back ur kids" kasa cewa komai tayi tana share hawayen da ke xubo mata, yace "Kin san address din can gidansu?" Shiru tayi kafin ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "Na manta" yace "Amma xa ki gane gidan?" Nan ma ta d'an yi shiru, anya xata gane gidan yanxu kuwa, murya can kasa yace "Khadijah?" Tace "Kilan in gane" yace "Good, kuna clinic din har yanxu?" Ta girgixa kai tace "Mun dawo gida" yace "Toh xan taho yanxu, but promise me baxa ki sake kuka ba plss" a hankali tace "Toh baxan yi ba" yace "Good, ina tahowa yanxu" daga haka ya katse wayar, Sosai Khadijah ta ji hankalinta ya kwanta, ta ji ta samu natsuwa. Tun da Aliyu ya shiga dakinsa bai sake fitowa ba, Mumy da maganganun Anty khadijah suka fara sa mata ciwon kai ta daga kai tana kallonta a karo na farko tun shigowarta dakin, ban da kumfar baki kamar wata xararriya babu abinda take tana nuna yan biyun dake xaune kan gadon Mumy, suma yaran kallonta kawai suke a tsorace, Baby ma na tsaye sai hararan Anty khadijah take tana tabe baki, Mumy ta dakatar da ita a tsawace tace "Khadijah ki fita ki ban waje don Allah ki bar ni in ji da guda daya, ciwon kai kike kara min ki fita don Allah, ko makaho ya shafa yaran nan yasan na waye, Baxa ayi DNA din ba...." Anty khadijah da idanuwanta suka kankance da mugun mamaki tace "Anty fati ni kike cewa in fita in baki waje don ina nuna damuwa ta kan shegun da aka makala ma Aliyu aka ce nasa ne, Ni Anty fati??" Mumy tace "Ehh ki fita nace" tayi wani murmushi tace "Xan fita yanxu kuwa" daga haka ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, Mumy ta kalli yan biyun dake bata tausayi har ranta, a hankali tace "Me xa ku ci?" Sudais dai bai ce komai ba, Shureim  ya girgixa mata kai shi ma bai ce komai ba, karasowa tayi ta xauna gun yaran tana kallonsu, wani sonsu take ji a xuciyarta, ta d'an yi murmushi tace "Ayi maku noodles and egg?" komawa Sudais yyi ya kwanta ta kai hannu jikinsa taji xafi sosai, kallon baby tayi tace "Xaxxabi ne jikinsa fa sosai..." Baby ta karaso ita ma ta taba yaron taji xafin jikin ta kalli Mumy tace "Mumy ko in kira yaya?" Mumy tace "Kira sa" juyawa tayi ta fita, ita ta fara dawowa dakin sannan Aliyu ma ya shigo, kallon yaron yake har ya isa kan gadon ya taba jikinsa, dago sa yyi ya xaunar da shi, yana kallonsa yace "Are you feeling pain anywhere?" Sudais ya nuna masa kan sa, kamar xai yi kuka yace "I want to go to my Anty plss" Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Ohk I will take you there"  Mumy dake kallon Aliyu tace "Ina ita khadijahr take?" Kamar Aliyu baxae ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa murya can kasa yace "Bayan ta bani su tayi tafiyarta" wani kallo Mumy ke masa ganin yanda yyi maganar, can ta girgixa kai tace "Karya kake..." Da sauri ya kalleta, sai kuma ya marairaice yace "Mumy bata sani ba na taho da su, idan ta sani baxa ta bani su ba" Bude baki Mumy tayi tana kallonsa, da damuwa tace "Me yasa xaka yi haka Aliyu, me yasa xaka raba su da uwar su...." Kasa cewa komai yayi, Mumy da duk jikinta ya kara yin sanyi tace "Aliyu tell me how everything happened, garin yaya kayi ma yar mutane haka, where was I that day? kar ka boye min komai plss, tell me the truth...." kallon Mumy Kawai yake ko kiftawa babu, can ya xauna gefen gado ya rike kansa yana jin kamar ya fara mata hawaye, bai son tuna mummunar ranan nan a rayuwarsa, Mumy na kallon Baby tace "Baby xo ki tafi da su ki dafa masu indomie ki basu, shi wannan ki kai sa dakin ki ya kwanta" Baby ta karaso ta sakko da boys din daga kan gado ta wuce da su dakinta, Mumy na kallonsa tace "Ina ji Aliyu" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali ya fara magana, "Mumy ni dai nasan I woke up fine that very day...." Ya d'an yi shiru, nan ya fara ba ma Mumy labarin abinda ya faru ranan bai boye mata komai ba har yanda bayan kwana biyu ya ba ma khadijah kudi me yawa yace ta wuce gun ummarta, hawaye kawai Mumy ke yi tana kallonsa a sanyaye, bai iya ya dago kai ba shi ma hawayen na sakko masa cike da karfin hali yace "Mumy nayi abinda nayi ne out of confusion, I was confused, ban taba xaton xan aikata ma khadijah haka ba, bayan tafiyar ta ku shaida ne, nayi bankwana da kwanciyar hankali da farin ciki na, I never had rest of mind again kuma na kasa gaya maki abinda ya faru ban san ya xa ki dau xancen ba, shi yasa a ko da yaushe nake ce maki ki taya ni da addu'a, wani lkcn idan na kwanta bacci ita kawai nake gani, kuma it's not as if nasan da cikin bane, kawai ni dai nasan ban kyauta mata ba saboda marainiya ce bata da kowa, ban san ta Inda xan fara nemanta ba don ban san kowa nata ba, da babu abinda xai hanani nemanta Mumy, idan baki manta ba akwai wani lkci da na taba tambayar ki ko kina da number warce ta kawo ta kika ce baki da shi, ni ban sa ko Khadijah xata yafe min ba and it looks as if I don't deserve that.... Amma abinda ke bani mamaki har yanxu shine yanda aka yi Anty khadijah ta san abinda ya faru bayan bata gidan kuma ita ta fita tare da su baby a ranan, gidan ya rage daga ni sai Khadijah, sai kuma jiya tana waya a bathroom din dakinta, I overheard all what she was saying on the phone.... Nan ya gaya ma Mumy duk abinda ya ji Anty khadijah ke fada a waya jiya, yana girgixa kai yace "We shud keep on pretending mum, she was so shock da ta gan ni a dakin, but i pretend ban ji komai ba, hakan kuma ya sa hankalinta ya kwanta, a sannu abinda take yi xai bayyana a fili tun da ba mu da hakkinta, kuma ina mai tabbatar maki soon komai xai bayyana, ke dai kawai ki ci gaba da sa mata ido, xan dai sa su Sanusi su tone bayan gidan to check what she was talking about on phone" Mumy ta dinga kallonsa ko kiftawa babu cike da shock, ya goge idonsa har lkcn bai kalleta ba yace "And... Mumy kilan idan ke kika yi ma khadijah magana xata iya yafe min, ni ta ki saurarata har yanxu, kuma mumy plss kar ki ce min baxan iya aurenta ba, hakan kadai ne xan iya mata in wanke kaina, I knw I can't pay her all what she passed through, kar ki hana ni aurenta mumy..." Mumy ta sauke ajiyar xuciya har lkcn tana mamakin abinda Aliyu ya fadi mata kan Anty khadijah, she is still finding it hard to believe that, infact bata ma yarda bane tasan Anty khadijah baxata yi abinda Aliyu ke fadi ba, Aliyu yace "Mumy kinyi shiru" Mumy ta kallesa ta kara sauke ajiyar xuciya sannan tace "Idan kuma ita bata son ka fa?" Ya d'an hade rai yace "Toh sai ta bar min yarana taje tayi aurenta shikenan na raba ta da wahala, idan kuma ta yarda ta aureni sai mu xauna mu rike yaranmu, domin kuwa su din abun kyama ne idan ta kai su wani gidan, ko ba yanxu ba wataran xa a kyamace su, to idan muna tare fa? We can never do that to them" Mumy bata kuma cewa komai ba tayi nisa tunanin da take na Anty khadijah, Bude kofar dakin Anty khadijah tayi ta shigo tana kallon Mumy da kumburarrun idonta da ta sha kukan takaici, kallo daya Mumy ta mata ta dauke kai xuciyarta na kara karyata Aliyu, Aliyu kam bai ma kalli inda take ba, tana kallon Mumy tace "Ina son sanin matsayin auren iklima a gidan nan Anty fati, na hada kayana idan Ita ma in hada nata ne toh..." Sai a sannan Aliyu ya kalleta yace "Anty aure ya taba mutuwa ba ayi saki ba?" Hararansa tayi ta juya ta fita, dakin baby ta bude ta dinga kallon yaran dake kan gadon cike da tsana, a tsorace suke kallonta su ma, can ta juya ta fita dakin ta sauka downstairs xuciyar ta na tafarfasa, Baby ce kitchen tana bare eggs da ta dafa masu indomien na kan wuta, Anty khadijah ce ta shigo kitchen din ta dau cup ta xuba ruwan xafi daga flask, Baby ta kalleta ganin yanda ta tsaya tana tunani, da sauri Anty khadijah ta bude gun da madara suke ta fiddo kayan tea ganin kallon da baby ke mata, tana hada shayi tace "Baby ina wani sarka da na baki ki ajiye min ranan da aka yi bikin iklima a gidan nan?" Baby tace "Anty yana cikin jakata a daki" Anty khadijah tace "Je dauko min kayana" Baby tace "Yanxu Anty?" Anty khadijah ta balla mata harara tace "Aa anjima" a sanyaye baby ta juya ta fita kitchen din bayan ta rage gas kar indomien ya kone, Anty khadijah ta fara kalle kallen kitchen din da sauri, lkci daya ta fita waje ta kofar kitchen din ta tafi gun da ake  ajiye snipper, Baby har ta fara haura stairs ta d'an tsaya, da sauri ta koma ta rabe jikin bango tana lekan kitchen din ta ga Anty Khadijah bata ciki, har xata juya ta bar wajen sai ga Anty Khadijah da gudu ta dawo kitchen din ta bude abun hannunta ta xuba cikin indomie da ke kan wuta, Xaro ido baby tayi taji kafafuwarta sun kasa daukar ta, lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya da sauri ta haura sama, dakin Mumy ta shiga ta fashe da kuka, Aliyu ya mike yana kallonta yace "Me ya faru?"


Baby ta durkushe dakin tana kuka sosai tace "Mumy Anty Khadijah ce na ga tana xuba snipper a cikin indomien yaran da nake dafawa" Aliyu ya xaro ido yace "Snipper??" Da sauri ya nufi kofa mumy tayi maxa ta dakatar da shi, ya juyo hankali tashe yana kallonta, Mumy na kallon Baby tace "Ta gan ki?" Girgixa kai baby tayi tana hawaye, Mumy ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tace "Je ki dauko yaran ki kawo su nan, kar ki ce mata komai" Aliyu sai kallon mumy yake xuciyarsa na bugawa, Mumy ta kallesa tana kkrin goge hawayen idonta tace "Kar ka ce mata komai, let pretend we don't knw... Don't say anything Aliyu" Baby ta dawo dakin da su sudais mumy ta daura su kan gadon tana kallonsu a sanyaye, ta dubi Baby tace "Tafi ki xubar da indomie din, kar ki ce mata komai kin ji, ae basu da hakkinta don hka bbu abinda ta isa tayi masu wanda Allah bai masu ba" Baby ta fita dakin a sanyaye hawaye ya ko tsaya mata, ganin abun take kamar a movie, ynxu da bata dawo ba haka xata dau indomien ta ba yaran su ci su mutu?? Anya Anty khadijah na da conscience kuwa, me yan yaran suka mata, Aliyu kam ya kasa cewa komai, Mumy ta dinga share hawayen dake ta xubo mata, me tayi ma khadijah ta mayar mata da family dinta haka, dama laifi ne idan ka jawo naka ya xauna tare da kai?? Baby bata ko kalli Anty khadijah da ta xauna parlor tana shan shayi ba ta shiga kitchen din, Anty khadijah ta bi ta da kallo ta gefen ido, daukar indomie da kwan baby tayi ta fita ta xubar cikin shara ta tara tukunyar a bakin tap, sai da ta tabbatar ta wanke tas sannan ta dawo kitchen da shi ta ajiye ta fito kitchen din ta wuce stairs, Anty khadijah ta bi ta da kallo baki bude, da sauri tace "Ke wai sai indomien ya kone ne kin bar ma mutane gas yana ci" Ba tare da baby ta juyo ba balle ta kalleta  tace "Sun ce baxa su ci ba na xubar" Daga haka ta haura sama Anty khadijah ta mike baki bude tana kallonta gabanta na faduwa, da sauri ta wuce kitchen ganin tukunyar a wanke ta fita waje ta leka bola taga indomien an xubar, still tayi a gun xuciyarta na mugun bugawa, kar dai ta ganta ne.... Jiki a sanyaye ta dawo cikin gidan tana adduar Allah yasa dai ko ta ganta kar ta gaya ma Mumy, Mumy da kanta ta sakko ta shiga kitchen din da ruwan gora biyu a hannunta, ta dumama ruwan sannan ta wuce sama da shi a cup don tana da kayan shayi a dakinta, Anty khadijah ta bi ta da kallo a sanyaye, shikenan kila baby ta gaya mata kenan, da sauri ta fita da wayar ta tafi can baya xata yi kira, nan daki mumy ta hada ma yan biyun tea ta basu Aliyu dai na xaune dakin yana kallon innocent kids din, baby da har sannan jikinta yake a sanyaye tana tsaye dakin ita ma. Duk da yanda Umma ta so bin Khadijah da khaleel xuwa gidan Aliyu kamar yanda khaleel yace kasa furta hakan tayi saboda kunya, Nanny ta dai raka Khadijah har bakin motar khaleel ta koma ciki, khaleel ya din ga kallon khadijah ganin yanda ta fada saboda kuka ta bude front seat a hankali ta shiga kanta a kasa, tausayinta ya ji har ransa ya tada motar ja suka bar layin, sai da suka hau saman titi a hankali yace "But you promised not to cry again Khadijah" da sauri ta kallesa da idanuwanta da suka rine tace "I didn't cry again, ai na riga na maka alkawari, wllh ban kara ba" a hankli yace "Toh naji dadi, kin dai san sunan anguwar su Aliyun koh?" Kai ta gyada masa, yace "Ina ne?" Tace "GRA" yace "Ai biyu ne Gra din, new or old?" Ta buda hannu a sanyaye alamar bata sani ba, wayarsa ce ya fara ring ganin me kiransa ya gangara gefen titi ya daga kiran tare da yin sallama, bayan sun gaisa da mai kiran nasa yace "Salman dama plss am asking... Can you connect me to a lawyer that you knw is just perfect, ni ba xaman Nigeria nake ba so I don't really knw, there is this case that I need one for... I don't want to talk about it to my family shi yasa I decided to contact you" Sai kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bayan wani lkci ya shafa lallausan gashin kansa yace "Sure... Ina jira, thanks much" daga haka ya katse wayar, ya juya ya kalleta ta dauke kai da sauri, d'an shiru yyi kafin yyi murmushi yace "Frnd dina ne, xae hada ni da lawyer yanxu, I think it's better we sue him, kulasa ayi hayaniya ba yi da fa'ida, and xai iya kai yaran wani gun, so ynxu two cases xa ayi da shi, 1st na rape... Sai kuma na biyu ya dawo rana daya yana claiming yaran da bai ma san kin dau cikinsu ba saboda rashin kunya...." Ita dai Khadijah ba ta ce komai ba, yace "So bari in jira xae turo min number Wani barrister da xanyi contacting yanxu" a hankali khadijah tace "Toh nagode, Allah...." Fingers dinsa ya daura bakinsa a hankali yana kallon kwayar idonta, ba shiri ta sauke idonta tayi shiru ta samu kanta da yin murmushi, text ne ya shigo wayarsa ya dauka yana kallon number da sunan barristern da Salman ya turo masa, dialing number yyi yana ganin ya shiga ya kai kunne, Sai da aka daga sannan Khaleel yyi sallama cikin cool voice dinsa, jin an amsa yace "Barrister barka da yamma" daga daya bangaren aka amsa masa da barka dai... Khaleel yace "You are speaking with Dr Ayman, plss ina son assigning din ka ne kan wani case, hope i won't inconvenience you..." Barristern ya amsa masa da "Sure, but na baro office yanxu" Khaleel yace "Waow.. So yanxu ya xa mu yi, and we need to talk today barrister" Barristern yace "Okay mu hadu eatry yanxu don ban shiga gida ba" Khaleel yace "Maa sha Allah ina godiya for ur time barrister" sunan eatry din Barristern ya gaya masa daga haka suka yi sallama, Khaleel ya katse wayar yana kallon khadijah yace "So mu je mu samesa eatry din yanxu koh" kai kawai ta gyada masa ya tada motar ya nufi eatry din, khadijah tayi nisa tunanin da take, gaba daya ji take kamar tayi shekara da shekaru rabonta da lovely twins dinta, bata taba tunanin tana son su har haka ba sai ynxu, ta ji ta kara tsanar Aliyu fiye da komai na rayuwar ta, she hate him with passion... kallonta kawai khaleel yake bayan ya gama parking cikin babban eatry din, a hankali ya kai hannunsa kan nata, lkci daya ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, yyi kasa da murya yace "Thinking about ur twins?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta tana kallonsa a sanyaye, ya girgixa mata kai yace "You've broke the promise" da sauri ta goge idonta tayi murmushi cikin sanyin murya tace "Don Allah kayi hakuri" murmushin yyi shima ya fiddo handkerchief dinsa ya mika mata, ta karba a sanyaye tana goge idonta, kamshin handkerchief din ya kara kwantar mata da hankali, ganin bata maido masa ba ya bude motar ya fita ita ma ta fito ya rufe motar, yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin eatry din.


Khaleel ya dinga bin few mutanen da ke xaune eatry din da kallo yana tafiya a hankali, ganin he can't tell who is barrister a cikinsu ya wayarsa ya shiga kiran contact dinsa, at one end of the eatry ya ga wani mutumi da ke backing din su ya dau wayarsa dake gabansa ya kai kunne, nan khaleel ya gane shi ne, yace "Alryt na gan ka barrister" daga haka ya katse wayar ya kalli khadijah yace "Mu je" tana biye da shi har suka isa gun da barristern ke a xaune, Khaleel ya ba sa hannu suka yi musabaha, sannan ya ja kujerar da ke side din barrister ya kalli khadijah yace "Come over" ta karaso a hankali ta xauna shi kuma ya xauna yana  facing barristern dake operating wayarsa, Khadijah ta dago kai a karo na farko tana kallon barristern da har lkcn idanuwansa ke kan waya yana kkrin silencing wayar, ji tayi komai nata ya tsaya ta dinga kallonsa ko kiftawa babu xuciyarta na bugawa, dai dai lkcn da shi ma ya dago manyan idanuwansa don kallon bak'in nasa yana cewa "Alryt... Barkan...." Makalewa sauran maganan nasa yayi ya dinga kallon khadijah ko kiftawa babu, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta mike ta bar wajen da sauri tana hade hanya, Mikewa yyi shi ma da sauri ya bi bayanta yana cewa "Amiraa..." Khaleel ya bi su da kallo da catlike eyes dinsa yana shafa beard dinsa, lkci daya sudais ya tsaya cak kamar wanda ya tuno wani abu, a hankali ya juyo yana kallon khaleel dake kallonsa shi ma, dawowa yyi da sauri yana girgixa kai yace "Am.. am really sorry plss, don't knw if she is ur wife, kayi hakuri.... I.." Sai kuma yyi shiru very confused, khaleel dai bai ce komai ba ya mike kamar bai son tafiya ya nufi kofar fita, Sudais ya xauna ya dafe kansa xuciyarsa na ci gaba da bugawa, Khaleel na fita can gun motarsa ya ga khadijah tana hawaye, ya iso gabanta ya tsaya yana kallonta yace "Who is he?" Tana share idonta a sanyaye tace "Sudais" shiru yyi na few seconds yana juya wristwatch din hannunsa, can ya dago kansa yana kallonta yace "So what next?" Ganin Sudais ya fito eatry din ya tsaya nesa da su yasa bata ce ma khaleel komai ba wasu hawayen suka dinga sakko mata a sanyaye tana kallon sudais, har ya iso inda suke shi ma duk a sanyaye yake, yana kallon khaleel a hankali yace "Am sorry Dr Ayman, idan matar ka ce kayi hakuri ka bani just 2mins in mata magana plss" da damuwa ya kare maganar, Khaleel ya d'an yi murmushin karfin hali sai dai bai ce komai ba, durkushewa Khadijah tayi gaban Sudais cikin rawar murya tace "Me yasa baka son ganina a rayuwar ka kuma barrister, I won't be a burden to you again, amma ko xumunci ne sai kayi da ni don Allah, me yasa ka gan ni kayi pretending you've never known me all ur life, did I deserve that? Ni nasan har karshen rayuwata baxan mance ka ba Sudais, kai din wani haske ne a rayuwata har kullum, baxan iya biyan ka abinda ka min ba but plss allow me to show appreciation always, I have missed you for many years.... I thought baxan sake ganin ka a duniya ba, sai gashi na ganka kayi shunning...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Sudais da idanuwansa suka kada lkci daya ya isa gun khaleel yace "Plss is she... Married??" A hankali khaleel ya girgixa masa kai, Sudais ya runtse ido ya bude yana kallonsa yace "Sorry I have to do this" yana fadin haka ya dawo ya durkusa gabanta ya rike hannunta gam cike da karfin hali yace "I know I have soo missed you Amira, I missed you... Nayi kewar ki da yawa, nayi kewar ki fiye da wanda kika min, nayi kewar twins dina, ba da son rai na na tafi na bar ku ba Amira... I have no option, kullum dake nake kwana nake tashi a rai na, but ya xan yi?? Mami na..." Kasa karasawa yyi, idonsa ya kada sosai, ita ma kuka take a hankali tana kallonsa, lkci daya yace "Where are my boys??" Tsayar da kukan da take tayi tana kallonsa a sanyaye, ganin kallon yasa gaban Sudais ya fadi sosai shi ma ya dinga kallonta, Khaleel dake rungume da hannayensa yana ta kallon dramar su yace "That's exactly what brought us here barrister" mikewa Sudais yyi da wani expression ya isa kusa da khaleel yace "What happened to them?" Khadijah ta mike tana goge idonta cikin rawar murya tace "Aliyu..." Kasa karasawa tayi, Sudais da idanuwansa suka sauya launi ya juya a hankali yana kallonta cikin husky voice yace "Aliyu did what?" Khaleel yace "Took them away from her" Sudais ya tsaya kallon khaleel mouth agape... Lkci daya yanayinsa gaba daya ya canxa, ya kalli khadijah dake hawaye yace "I will teach him the lessons of his life" khaleel ya daga kafada bai dai ce komai ba, Sudais ya kalli khadijah yace "Har yanxu gidan nan da muka je suke?" Tace "Nima ban sani ba" kallon khaleel yyi yace "We have to go to the house now..." Khaleel yace "Ohk then" har Sudais xai ce khadijah ta taho su tafi a motarsa sai kuma yyi saurin barin hakan a ransa, muryar Khaleel ya ji yana cewa "Or ko xaki je da barrister a car dinsa, xan bi bayan ku ni" shiru khadijah tayi tana wasa da fingers dinta, can ta saci kallon Sudais ta ga kallonta yake, tayi saurin dauke kanta, bata san lkcn da tace "Ohk, xan hau tricycle ku tafi kawai, xan gane gidan kila" ta gefen ido khaleel ya kalleta bai dai ce komai ba ya nufi motarsa, shi kansa Sudais bai ce komai ba, can ya shafa kansa a hankali yace "You don't worry tun da tare ku ka xo da shi, ki tafi ki hau tasa motar Amira" shiru ta yi tana kallonsa, murya can kasa yace "There are a lot of things to talk about Amira, but let settle Aliyu's case first" kai kawai ta gyada masa yace "Toh tafi kar ya tada motar" A hankali ta juya ta nufi motar Sudais ya bi ta da kallo ko kiftawa babu, tana isa xata bude motar khaleel yace "No, no you don't worry Khadijah ki tafi ku je tare da shi, we will meet there" daga haka ya fara reverse ta koma baya hankali tana kallonsa har ya fita, Jiki a sanyaye ta dawo gun sudais dake ta kallonsu, yana ganin haka ya xaga ya bude mata front seat, kanta a kasa ta shiga motar bata son ya ga hawayen idonta ya rufe motar, kafin ya xaga ya shiga maxaunin driver ta goge idonta da sauri, yana  rufe side dinsa ya tada motar yyi reverse ya fita shi ma, ta madubi yake ta kallon motar khaleel dake jiran nasa yana hawa kan titi ya dau hanyar gidansu Aliyu khaleel ya bi bayansa, lkci lkci sudais ke kallon khadijah da tayi nisa tunanin da take, murya can kasa ta ji yace "Amira" da sauri ta kallesa yace "Waye Dr Ayman?" Kallonsa ta tsaya yi ta kasa cewa komai, a hankali yace "Kin yi shiru" Ta dauke idonta daga kallonsa bata ce komai ba still, hakan yasa bai sake ce mata komai ba, sai da suka yi nisa taji sanyayyan muryarsa yace "Saurayin ki ne koh?" Khadijah ta saci kallonsa still ta ki cewa komai ba, a sanyaye yace "Ki min magana pls Amira" Ajiyar xuciya ta sauke a boye, murya can kasa tace "Just as u tried ur best not to make me feel lonely in this world, shi ma abinda yake min kenan... He is also playing same role in my life." Ta gefen ido Sudais ya kalleta na few seconds kafin ya lumshe ido ya bude yace "you didn't answer my question Amira" Khadijah ta juya tana kallonsa tace "Lkcn da kake tsaka da taimako na, where you my boy friend?" Kasa ce mata komai yyi na few seconds, murya can kasa yace "Ohk.. But I am now, I want to be noe" juyawa tayi tana kallonsa da sauri, ba tare da ya kalleta ba ya gyada mata kai yace "Yea...."



Sorry it's short..., but breakfast ae dama ba dayawa ake cin sa ba, very light.... 😁


Har suka isa gidansu Aliyu babu wanda yace komai cikinsu, khadijah tayi nisa tunanin da take bata ma san sun iso ba, Sudais ya fito daga motar ya xaga side dinta ya bude mata ganin bata fito ba, sai a sannan ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, tayi saurin sauke kanta ta fito daga motar ya rufe, kallon motar khaleel sudais yyi, dai dai sannan shi ma ya fito daga motarsa, Sudais ya karasa gun sa yace "I pray we meet him at home" Khaleel ya daga kafada yace "Allah ya sa" Sudais ya kalli Khadijah dake tsaye jikin motarsa sai kallon gidan take a sanyaye, gate din gidan ya nufa khaleel ya bi bayansa, bai tsaya sauraran mai gadi Usman dake tambayar sa daga ina ba ya kutsa kai ya shiga gate din ya juya yana kallonsa yace "Six years isn't that far, bai ci ka mance ni da wuri haka ba malam" khaleel ma ya shiga gidan yana kallon mai gadin murmushi dauke fuskarsa ganin yanda yyi kasake yana bin Sudais da kallo, A sanyaye Khadijah ta gaida Usman da ya xaro ido yana kallonta da mamaki yace "wannan kamar Khadijah??" Murmushi ta kirkira ta shiga cikin gidan ta bi bayan su sudais da suka nufi entrance din shiga gidan, haka kawai gabanta ya dinga faduwa tayi slowing pace dinta, Sudais ya danna bell ya ja gefe ya tsaya, bayan wani lkci aka bude kofar, Baby ce tsaye bakin kofar ta dinga kallonsa na wasu seconds kafin ta gaishesa, yana kallonta ya amsa da murmushi yace "Can we come in?" Barin bakin kofar tayi ta rasa abinda xata ce masa, ya kula she is lost don haka ya shiga parlon khaleel ya bi bayansa, tuni khadijah ta labe jikin bango jin baby ce ta bude kofar, hawaye suka shiga sakko mata ta kasa shiga parlorn, Anty khadijah dake xaune parlorn ta dinga kallon Sudais kamar me son tuno inda ta san sa, sarai ya dau fuskarta ya gane ta, a hankali yace "Hello?" Ta mike tana yamutsa fuska tace "Daga ina? Wa ku ma kuke nema?" Yana kallonta yace "Bak'i ne.... Amma nayi mamakin da baki gane ni ba Hajiya" Ta hade rai tace "Do I have any business with you da xan gane ka, malam nan gidan masu aure ne, ka fadi wa ka ke nema, ba haka nan ake shiga gidan mutane ba, from all indications ma batar hanya ku ka yi " Ya taka har gabanta ya tsaya yana mata kallon cikin ido ya fiddo ID card dinsa yace "Barrister Aliyu.... May be this will make you remember me fast" mikewa tayi da sauri tana masa wani kallo, sai kuma ta shiga kalle kalle don ta tabbatar babu kowa parlorn, ta hadiye abu da kyar tace "Wa kake nema malam, me ka sake dawowa yi gidan nan?" Jin bai ce mata komai ba sai murmushin da yake ta juya da sauri ta kalli khaleel da ya nemi kujera ya xauna yyi relaxing a kai, Murya suka ji a stairs duk suka juya, Mumy ta sakko tana kallonsu da mamaki tace "Sannun ku da xuwa" Sudais ya amsa ta karaso parlorn tace "Are you looking for Someone?" Sudais yace "Sure" juyawa yyi ya kalli bakin kofa ya ga khadijah bata shigo ba, ya juya ya koma bakin kofar, yana fita yace "Come in khadijah" Khadijah ta girgixa masa kai cikin rawar murya tace "Baxan iya ba, kuma kila ba nan ya kawo su ba" sudais yace "Trust me, kawai ki biyo ni" daga haka ya shiga parlorn ta bi sa a d'an tsorace don jin muryar Anty khadijah ya kara daga mata hankali, baby ce ta fara xaro ido ganinta lkci daya ta nufe ta da gudu tace "Imann" kasa amsa mata Khadijah tayi, Baby ta rungumeta, hakan yasa khadijah ta fashe da kuka kamar yanda baby ma ta fara kuka, tuni Anty khadijah ta rikice bakin ta na rawa tace "Me ya kawo yarinyar nan gidan nan, me ta xo yi...." Ba tare da Sudais ya kalleta ba yace "Ta xo amsan yaranta" Anty khadijah ta yo waje da ido tace "Tayi aure cikin gidan nan ne da ta xo amsan yara??" Khadijah da ke hawaye a sanyaye ta daga kai ta kalli inda mumy take ta ga kallonta take ko fiftawa babu, sunkuyar da kai tayi kamar me counting steps dinta ta isa gaban mumy hawaye na sakko mata, Mumy da idanuwanta suka kawo ruwa ta rungumeta murya can kasa tace "Khadijah.." duk wannan abun Aliyu na sama tsaye yana kallonsu, cikin rawar murya Khadijah tace "Mumy ki ce ya bani yarana na yafe masa wllh.... Intervene plss mumy" Mumy ta kasa cewa komai sai kuka, Anty khadijah sai wuri wuri ta ke da ido a parlorn ta kasa cewa komai, A hankali Aliyu ya dinga sakkowa stairs din har ya iso parlorn, Khadijah ta dinga kallonsa tana jin tsanar sa, Sudais ya taka har gabansa yana kallonsa da kyau yace "Aliyu?" Aliyu yace "Sure, any problem?" Sudais ya gyada kai yace "Fito mata da boys dinta" Aliyu ya rungume hannunsa yana kallonsa with interest yace "Bodyguards din nata har biyu ne kenan" Khaleel yyi calm smile pretending Aliyu doesn't even exist in the parlorn balle har ya ji abinda yace, shi dai yana xauna kan kujera har sannan, Sudais da idanuwansa suka sauya launi yace "You are stupid... I mean very stupid" Murmushi Aliyu yyi yace "Ku dai da ku ke biyota ne xa a kira da haka, look... ba ku da right din da xa ku dinga interfering a case dina da ita, it's almost a family issue so stay out of it....." Khadijah bata san lkcn da ta isa gabansa ba idanuwanta suka kankance don bala'i tace "Wannan da kake gani ya fi Ka right, when I say right ina nufin right, wllh ya fi ka 100% right over those children, he is almost their father, and will always remain their father, na tsane ka Aliyu, na tsane ka.... I hate you" Tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai, Mumy ta rasa abinda xata ce ban da kuka bbu abinda take, Aliyu yace "Dama ban ce kar ki tsane ni ba Khadijah, you have all right to do so, but Iman am sorry baxan ba ki yaran nan ba, you've past through a lot, ki bar ni da su yanxu let me also play my role, ki tafi ki je ki ci gaba da rayuwar ki da bodyguards din ki, thank God you said he is almost their father not their father, ni kuma I am their biological father..." Tapping dinsa Sudais yyi xuciyarsa na tafarfasa, strictly yace "Malam kasan wanene ni kuwa? Did you knw why I am taking it gently with you, baka sani ba sure.. Then knw this, it's because of ur mother, na ga alamar she deserves some respect, don haka cikin salama ka fito da yaranta yanxu ka bata idan ba haka ba...." Aliyu ya tabe baki yana d'an murmushi yace "You do ur worst....Barrister" Bude baki Sudais yyi yana kallonsa, Khadijah ta durkushe wajen ta kara rushewa da kukan takaici, mikewa khaleel yyi yana ma Aliyu wani kallo yace "Amma kai jahili ne na ga alama, islamically baka da right over yaran nan, kai har yaran da ka samu ta hanyar zina kake alfahari da kake bragging baxa ka bada ba?? Is this how senseless you are" Yar dariya Aliyu yyi yace "U watch ur tongue gidanmu ka xo ka same ni, so you have no place to tell me nonsense, baxan bada yara ba nace" Sudais ya sake tapping dinsa yace "Good, ka saurare sammaci gobe, nasan dai baxa kayi denying kayi raping din yar mutane a court ba koh, sannan kuma don rashin kunya ka dawo kana claiming yaran da baka san da su ba, baka san da yanda aka yi Allah ya raba ta da su ba... You are wicked Aliyu" Aliyu yace "Ka kai ni gaba da kotu.... If there is any" Daga haka ya juya ya haura sama ya bar su wajen, Juyawa Sudais yyi yana wani murmushi yace "Alryt xa mu hadu a can din" daga haka ya nufi kofa yana kallon khaleel yace "Can we?" Mumy ta dakatar da shi da sauri, ya juyo yana kallonta, karasowa gabansa tayi tana goge hawayen idonta tace "I am really short of words, sai dai baxa ayi haka ba my son don Allah ku yi hakuri, xancen baxai kai kotu ba in sha Allah, sure islamically ba shi da right a kan yaran, ina mai tabbatar maku xai bata yaranta in sha Allah, and plss idan baxan bata maku lokaci ba ku bani just few out of ur time ina son mu yi magana da ku" Sudais bai ce komai ba, sai dai shi kansa yasan tun shigowarsa parlorn ya ga darajar matar shi yasa ma bai ma Aliyu haukan da yayi niyya ba, kuma albarkacin irin rikon da tayi ma khadijah truly she deserve some respect, sauke kansa yyi kawai ya koma ya xauna yace "To ina ji Ma" Mumy ta xauna ita ma tana ci gaba da share idonta ta bi parlon da kallo taga babu Anty khadijah, Baby ce kadai jingine da bango tana hawaye, a sanyaye Mumy ta fara cewa "Amma ya ku ke da Iman?" Khaleel ya kalli Sudais da ya kallo sa shi ma, ya ci gaba da operating wayarsa, Sudais ya d'an shafa beard dinsa yace "Yan uwanta ne mu" Mumy ta gyada kai, ta fara magana cikin sanyi tace "It's not as if ina supporting Aliyu don d'a na ne, plss dont quote me wrong, amma ina son ku sani it's a mistake he made kuma ba da gangan haka ya faru ba, tsautsayi ne ya gifta tsakaninsu, ni na haifesa na kuma san halinsa, ita kanta Iman xata shaide sa.... It's not ordinary hakan ya faru da shi" Sudais yace "But kinsan bayan ya sa ta tafi da aka gano tana da ciki na maido ta nan gidan?" Kallonsa mumy take da d'an mamaki, can tace "Gidan nan?" Yace "Sure?" Jikinta yyi mugun sanyi tace "Wa ku ka samu gidan?" Sudais yace "Matar da muka fara samu a parlor xuwan mu yanxu, she humiliated us and sent us away then" Kasa cewa komai mumy tayi lkci daya hawaye ya kara cika idonta da kyar tace "Kana nufin khadijah ce ta Kore ku, kuma kun gaya mata abinda ke tafe da ku?" Sudais na gyada kai yace "Kwarai, I was even thinking she is his mum then, the way she reacted...." Mumy tace "Amma kun samu Aliyun?" Girgixa mata kai yyi yace "Ce mana tayi baya kasar gaba daya" Mumy ta fashe da kuka tace "Amma Allah ya isa tsakanina da khadijah, she just ruin my family, yar uwata ce amma ko bare baxai min haka ba, yanxu tana sane da abun nan amma bata gaya min ba, she never told me anything about it da babu abinda xai hana ni nemo Iman duk inda take, greatest mistake din Aliyu shine ce mata da yayi ta tafi, kuma wllh ni shaida ce tun daga ranan Aliyu bai sake samun kwanciyar hankali ba, kuma bai taba gaya min abinda ya faru ba sai dai yace in taya sa da addu'a, gashi nan dai har yanxu ya ki yin aure" Ko kadan khadijah bata damu da abinda mumy take fada ba ku ma bai shigeta ba, Briefly Sudais ya ba ma Mumy labarin yanda rayuwa ya kasance ma khadijah bayan Aliyu yace ta tafi... Ban da kuka babu abinda Mumy take duk jikinta yyi mugun sanyi tausayin Khadijah ya cika ta, ita dai tasan da tasan abinda ya faru kenan da ta sa Aliyu ya nemo ta Duk inda take amma yyi wautan rashin gaya mata, Mumy ta mike ta isa gun khadijah ta duka gabanta tana kuka tace "Khadijah ina neman alfarmar ki yafe ma Aliyu, ko don albarkaci na forgive him plss, kadararrku ce a haka, don haka ki ta godiya ma Allah, amma kiyi hakuri kar ki bar sa a xuciyar ki" Khadijah da xuciyarta ya mata rauni ita ma tana kukan tace "Mumy ni fa na yafe masa amma yayi hakuri ya bani yaran don Allah" mikewa Mumy tayi tace "Xai baki Khadijah, ina gidan ku yake yanxu?" Khadijah ta fada mata address din, Mumy tace "Toh kiyi hakuri ku je na maki alkawarin xa mu biyo ku da yaran yanxu" shiru khadijah tayi tana kallonta xuciyarta na bugawa sai take ga kamar kawai labari mumy take mata don ta tafi, baxa su bata yaran ba, Sudais ya mike yace "Toh shkkn, Ma... Muna xuba ido sai kun xo" Mumy ta kalli khaleel a sanyaye tace "Ku yi hakuri balarabe, Allah ya ba ku lada, amma don Allah ku bar jin haushin Aliyu ba yin kansa bane, nasan xa ku yi ta mamakin jin ina cewa ba yin kansa bane kamar na shiga xuciyarsa, but plss just do consider him" Murmushi khaleel yyi ya mike yace "Bakomai Ummu, Allah ya kara girma" tace "Amin nagode" daga haka ya nufi kofa, sudais ya kara mata sallama ya bi bayan khaleel, Khadijah na biye da su a baya tana goge idonta, ta kasa kallon baby dake bakin kofa har lkcn, A hankali baby tace "Iman plss forgive me brother, ki yafe masa don Allah" hawaye na sakkowa idonta take maganar, Khadijah tayi murmushin karfin hali tace "Na yafe masa" daga haka ta fita parlorn. Sama Mumy ta wuce xuwa dakin Anty Khadijah ta ganta xaune tana bude jikin iklima ganin wasu kuraje da ke feso mata ta ko ina, Mumy tace "Khadijah, a duk xaman mu dake in har na taba cutar ki Allah ya saka maki, in kuma ke kika cuce ni Allah ya saka mani, ki tattara kayan ki da na yar ki ki bar min gidana yanxu, Allah ya bani ladan xumuncin da nayi a baya, kuma in sha Allah nasan Allah baxai kama ni da laifin xumunci ba, ki je na bar ki da Allah" mikewa Anty khadijah tayi tace "Ni yau kike kora gidan ki yau Anty fati saboda wasu shegu sun xo sun shirga maki karya?" A fusace Mumy tace "Ki fita ki ban waje, yanda kika so ganina da jikoki wanda aka samu ba ta hanyar aure ba ke ma Allah ya ba ki" Anty khadijah ta tashi tana wani murmushi tace "Sai kinyi da kin sanin daga min yatsa da kika yi fatima" daga haka ta bude siff ta dinga fiddo kayanta da na Iklima tana huci, Mumy tace "Da na sani sai dai ki gansa a kwaryar ki" daga haka ta fice daga dakin ta shiga na Aliyu, Yana xaune gefen gado ya rike kansa, duk yan biyun sun yi bacci kan gado, Mumy na kallonsa tace "Kai da babban laifi kai da fadin bakakken maganganu ko Aliyu?" Kamar xai mata kuka yace "Mumy me yasa duk hallacin da na ma khadijah a baya baxata duba na, did I deserve this, wllh da hankalinta baxan cuce ta haka ba, sannan ta dinga wani hadani da wasu karti, ni ita na sani ba su ba su ba su daina involving kansu a abinda bai shafe su...." Katse sa mumy tayi tace "Don't tell me nonsense, dole duk mai conscience idan ya ji labarinta ya so ya kwatar mata hakinta, kasan irin cutar da ka mata kuwa ka raba ta da kowa nata?" Aliyu ya rike kansa bai ce komai ba, Mumy tace "Sai ka tashi mu tafi can gidan nasu yanxu" Aliyu ya dago ya kalleta da kyar don wani Sara masa kansa ke masa yace "Mumy wllh ni baxan iya rabuwa da Iman ba, baxan iya rayuwa ba ita ba, my life has being miserable tun da na sa ta bar gidan nan, Don Allah ki rokar min ita ta amince mu yi aure, I don't think xan iya auren wata ya mace a duniya idan ba ita ba, plsss even for the sake of this innocent children ta amince mu yi aure" Mumy tace "yanxu kuma??" Tashi yyi Yace "Wllh Mumy idan tace baxata aure ni ba, I promise to go away with this kids baxa ta sake ganinsu ba har karshen rayuwarta, ai da can ba da su take rayuwa ba" Mumy na masa wani kallo tace "Na ga alamar ka fara xarewa, da yaran xaka mata baraxanar ta aure ka kenan, a hakan xata amince ta aure kake tunani, kasan ko kotu aka je yaran nan ba naka bane Aliyu, ba ta hanyar aure ku ka same su ba don haka ka janye wannan baxan maganar da kake yi, kuma kar ka bata min rai" Wani murmushi yyi bai dai ce komai ba, Jikin mumy yyi sanyi ta bi sa da kallo, tsoronta kar ya tafi da su kamar yanda yace, da kyar tace "Ka tashi mu je gidan na su, nasan even for my sake ma xata amince maka" daga haka ta fita dakin. Sai kusan magrib suka isa address da khadijah ta ba mumy, Aliyu ke driving din, Sai baby a gaba, mumy kuma na xaune back seat da yan biyun, tana rungume da little Sudais da jikinsa yyi xafi sosai duk da allurorin da Aliyu yyi masa, kai kana ganin yaran kasan hankalinsu ya kwanta da mumy, Shureim na kallonta yace "Are we going to visit you again mama?" Tana murmushi ta shafa kansa tace "Sure sweetheart" parking Aliyu yyi kusa da gidan ya juya yana kallon Mumy, Mumy tace "Ina jin nan ne" Shureim yace "Ehh mama nan ne gidanmu" Mumy tace "baby sauka ki kwankwasa gate din" Baby ta sauka tayi yanda Mumy tace, Mumy ta sauko tare da boys din, Aliyu ya fito shi ma ya dau sudais, bayan wani lkci Nanny ta bude gate din, da gudu Shureim ya tafi ya rungumeta, Nanny ta ji dadin ganin su sosai ta dinga yi ma su Mumy sannu da xuwa, Kallo daya tayi ma Aliyu ta gane shi ne uban yan biyun, ta yi masu iso har parlor, Sannan ta shiga daki don Umma na ciki tana sallah, Khadijah ma tasan sallan take yi, Umma ta sa Hijab ta fito bayan Nanny ta sanar mata bakin da suka yi, Har lkcn Sudais na jikin Aliyu, Shureim dake jikin Mumy ya tafi da gudu ya rungume Umma yace "I miss you Mumy na" Umma ta xauna tana murmushi ta ja sa jiki sannan suka shiga gaisawa da su Mumy, jikin mumy yyi sanyi sosai don bata taba xaton xata tarbesu da kyau haka ba, shi dai Aliyu ya kasa daga kai ya kalleta, shi ma bai yi xaton haka ba, Khadijah dake xaune kan darduma lkci daya taji ranta yyi mugun bacci jin yanda Umma ta sake masu, jin muryar yaranta yasa ta lumshe idonta, amma ta ki fitowa parlor ta same su don bata ma son ganin Aliyu, Mumy na kallon Umma tace "Ina Khadijar Hajiya?" Umma ta kalli Nanny dake tsaye tace "kira Khadijah" sosai Khadijah ta dake xuciyarta ta mike ta bi bayan Nanny kan ta a kasa, har ta shigo parlorn bata yarda ta dago kanta ba ta gaida Mumy, Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa babu, Shureim ya nufeta ya xauna jikinta yace "Anty mun dawo, I like the house so much..." Khadijah ta ki kallon yaron amma har ranta bata ji dadin abinda yace ba, ita fa in dan ta ita ne yaranta basu da uba, ita dai tasan Allah ne ya bata su, kuma tana gode masa, fuskarta daure ta dago tana satan kallon Aliyu dake ta kallonta suka hada ido ta masa wani harara ta dauke kai, lkci daya ta mike ta ja hannun Shureim suka bar parlorn, tana xaunawa kan gado ta jawo yaron gabanta tana kallonsa da kyau tace "Did that stranger tell you anything?" Shiru yyi da farko kafin yace "But he is not a stranger Anty, this is the 4th time we are meeting with him" ta xaro ido xuciyarta na bugawa tace "Where and where" yace "Anty ranan nan da muka kusa yin accident, that i told you he made sure we where fine...." Gabanta yayi mugun faduwa tace "And where?" Yace "We met again at the airport da xa mu je holiday a UK, shi ma xai je can..." Ta runtse ido xuciyarta na tafarfasa tace "And where????" Yace "Yesterday at the market, because sudais don't like him shine ya gudu ya shiga titi babban mota ya buge sa" ta fixgo yaron tana huci tace "Shi ya janyo mota ya buge Sudais?" Kai ya gyada mata ta jefa masa wani kallo tace "And you are telling me he is kind yana neman kashe maka brother, daga yau ka sake yarda ko kallon ka yayi sai ya xuke maka jinin jikin ka gaba daya, baka san shi vampire bane" buda baki yyi yana kallonta da surprise, can yace "Me yasa bai shanye mana ba a gidansu?? Anty he is kind fa, ni dai I like him, he was with us....." Tsawa tayi masa ta turasa har sai da ya kusa faduwa hawaye cike idonta tace "Xan fasa maka kai... Nace stay away from him, you have no business with that wicked man" Shiru yyi a tsorace yana kallonta, a hankali yace "But he even told us he is our father not barrister as you told us...." Mikewa tayi hankali tashe xuciyarta na mugun bugawa tace "He is a liar... Karya yake maka barrister ne babanka, ba abinda ya hada mu da shi" cikin rawar murya tace "Tafi ka kamo hannun sudais ku xo nan yanxun nan" da sauri ya fita, yana isa kusa da Aliyu yace "Uncle, Anty tace I shud call my brother now" shiru yyi yana kallon yaran, haka ma Mumy da Umma, Aliyu yayi kasa da kai a hankali yace "Umma ki d'an mata magana ta bari in je da shi, he is sick dole xa mu koma asibiti" a fusace Khadijah dake jin sa ta fito tace "Ina ruwanka da rashin lafiyarsa? Ka bani yarona ai nasan hanyar asibiti, give me my son" tsawa Umma tayi mata ta mike tace "Tafi ki bar parlorn nan kar in bata maki rai, shashasha" ta fashe da kuka ta juya da sauri ta bar wajen, Umma dake kallonsa a sanyaye tace "Ka je da shi, Amma ko xuwa gobe sai ka kawo shi" a sanyaye yace "Na gode Umma" su mumy basu bar gidan ba sai kusan karfe taran dare bayan mumy ta mata bayanin duk abinda ya faru, Umma ta raka su har bakin mota jikinta a sanyaye.


Umma na dawowa cikin gidan ta tafi daki gun Khadijah a daki, xaune ta sameta kasa ta hade kai da gwiwa tana kukan takaici, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Amma Khadijah ban taba xaton haka daga gare ki ba, da ilimin ki bai kamata kiyi abinda kika yi ba, ina ce ko ba komai xai ci albarkacin mahaifiyarsa, ke da kanki kin bani labarin irin abubuwan da tayi maki while with them, me yasa xa ki mance hakan da wuri,  don me laifin d'an ta xai shafeta, me yasa ko don ita baxa ki raga masa ba, ni ban ce lallai sai kin kulasa ba, Amma for the sake of his mum...." Cikin kuka tace "Umma kiyi hakuri, but I have nothing to do with Aliyu and his family again, I will pretend ban taba rayuwa tare da su ba, don Allah su rabu da ni su bar min yarana su je na yafe masu, ina jin kunyar mahaifiyar sa shi yasa nake raga masa, only me knew wat I passed through in life, ni kadai nasan abubuwan da na fuskanta a rayuwa shekarun baya, Umma na sha wahala, na ji na tsani rayuwar, ban taba sanin xan yi surviving ba ummata, da ba don sudais ba da ban san me xai sameni ba, me yasa rana tsaka Aliyu xai dawo rayuwata yana min gadara a kan yaran da bai ma san da su ba, why Umma??" Umma ta xauna duk jikinta yyi sanyi tace "Ni ba nace ki yarda da Aliyu bane Khadijah, amma kiyi hakuri ko domin mahaifiyarsa ki yafe masa, ki mance past din ki" tana kallon umma da jajayen idanuwanta tace "Na yafe masa amma kar ya sake cewa shi ne uban yarana, kuma da kai na xan shirya in tafi in dauko yarona gidansu gobe, it's better Barrister sudais ya raba ni da su then ace Aliyu, saboda shi ne ya sha wahalar su kuma shi ya koya min sonsu ba don shi ba kilan da sun mutu yanxu" shiru Umma tayi ta kasa cewa komai tana kallonta, mikewa khadijah tayi ta hau saman gado ta kwanta, Umma ta mike a sanyaye ta kama hannun Shureim dake ta kallon uwar tasa ta fita da shi. Mikewa xaune khadijah tayi jin wayarta na ring ta dau wayar, ganin khaleel ne ta daga ta kai kunne tayi masa sallama cikin sanyin murya, Daga daya bangaren ya amsa a hankali yace "Sun kawo maki yaran Khadijah?" Ta fashe da kukan takaici tace "they brought just one, Shureim kawai suka kawo, ya tafi da sudais" Khaleel yace "Saboda me?" Cikin kuka tace "Wai xai kai sa asibiti, I don't knw ko meye damuwarsa da ciwonsa, ni dai ya rabu da yarana, ya kyale min su" Khaleel yyi shiru na wani lkci kafin yace "Kar ki damu xa su dawo maki shi, bana son ki kara sa ma kanki damuwa Khadijah, and plss because of his mother let take everything easy, kar ma ki sake kulasa, sure baxata bari ya dauke maki kids ba, kin san ana barin halak ko don kunya, am sure soon xa a dawo maki da little Sudais kin ji" kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta, yace "Sleep without worries plss Khadijah" a hankali tace "Toh nagode" daga haka ya katse wayar, ta koma ta kwanta ta lumshe ido, cikin dare misalin karfe biyu Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da slh taga wayarta yyi haske alamar shigowar text, ta mike a hankali ta isa gun wayar, message din barrister Sudais ta gani ta dauka ta bude tana kallon content din, "Dear am sorry I didn't call, na shiga gida ne da wuri jiya, but mun yi communicating da Dr Ayman, he told me everything, you don't worry xa a dawo maki da little sudais soon, gobe da safe xan xo in sha Allah, sleep without thought plss" tabe baki tayi ta ajiye wayar ta koma kan darduma ta xauna, har kusan asuba Khadijah bata runtsa ba, damuwa yayi mata yawa sosai ga yawan faduwar gaba da take ta ji, karfe hudu saura umma ta shigo dakin da Shureim ganin khadijah kan darduma ta isa kusa da ita da yaron tace "Gashi ya ki bacci, his temperature is high but na basa paracetamol, wai xai xo wajen ki" xaunawa Shureim yyi kusa da ita yana kallonta yace "Anty yaushe sudais xai dawo, I want to see him" Umma tace "Au abinda ke damun ka kenan" murmushii tayi ta juya ta fita tace "ka gamu da aiki kam" Khadijah ta jawo sa jikinta a hankali, taji jikin nasa ya dau xafi sosai, dago kansa tayi tace "Are you feeling pain anywhere?" Ya girgixa mata kai yace "I want to go to my brother" ta rungume sa sosai tace "Gobe xai dawo ka ji" ba a dau lkci ba yaron yayi bacci a jikinta ta mike ta daukesa ta kwantar kan gado, ta koma ta xauna tana jiran lkcn sllhn asuba. Washegari da safe Mumy na xaune kusa da Sudais da Aliyu ke sa ma drip da damuwa tace "Abuturrab ko xa ku je asibiti dai a kara duba sa, he is suffering slowly..." Aliyu ya kalleta yace "He will be okay mum, na dubasa babu wani matsala, a hankali xai dinga recovering, and it looks as if he is missing his twin, tun jiya yake ta tambayar sa" Tace "Toh ko xa a mayar da shi gidan ne?" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Mumy bari ya kara samun lafiya" Baby ce ta shigo da wayar Mumy dake ring ta mika mata ta fita, Mumy ta karba ta daga kiran, shiru ta d'an fara yi kafin tace "Ehh ni ce, who is on the line" ganin Mumy bata sake cewa komai ba sai shock da ya bayyana a fusakarta, a hankali afterward ta sauke wayar daga kunnenta tana kallon screen din, Aliyu dake kallonta yace "Waye mumy? Me ya faru?" Kallonsa tayi a sanyaye tace "Ka sake kiransu kilan ban ji da kyau ba ne" Aliyu ya amshi wayar ya kira number, bayan wani lkci aka dauka, abinda aka fadi ma Mumy aka sake maimaita masa, ya d'an bude ido shi ma lkci daya yace "Subhanallah, to ga mu nan xuwa, mun gode" daga haka ya katse wayar yace "Mumy wai Anty khadijah na asibiti..." A hankali mumy tace "Toh sai ku je, ni kam baxan je ba" ya bata fuska yace "No plss mumy kar ki ce haka, tunda har aka kira ki mu je kawai, baxa a biye ta halinta ba, kuma ai ba a canxa ma tuwo suna she still remain ur sister" da kyar Aliyu yyi convincing Mumy ta yarda xa ta je. Umma tayi pecking din goshin Shureim har sannan jikinsa da dumi tana shafa kansa tace "You behave your self kaji my boy, kuma ban da fada a gidan" Kai ya gyada mata, Khadijah ta kama hannunsa suka fita parlorn, khaleel na jingine jikin motarsa har suka iso inda yake, ya duka yana kallon kyakkyawan yaran a hankali yace "How are you Darling" murmushi Shureim yyi yace "Am fine uncle" mikewa khaleel yyi ya kama hannunsa yana kallon khadijah yace "Toh sai mun yi waya..." murmushi tayi tana bin sa da kallo tace "Nagode, byee" daga haka ya bude front seat ya saka Shureim ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya bar layin, Khadijah ta juya to koma ciki feeling relieved. Shureim na wasa da wayar khaleel yace "Uncle baxan sake ganin Sudais ba?" Khaleel ya d'an buda ido ya kalllesa yace "In ji wa ya gaya maka haka?" Ya langwabar da kai bai ce komai ba, duk sai ya basa tausayi, a hankali Khaleel ya shafa kansa yace "Xai dawo soon ka ji my boy" har khaleel ya isa gida Shureim bai sake cewa komai ba, gida ne mai girman gaske, Shureim ya wara ido yana bin makeken compound din da kallo yace "Uncle is this ur home" khaleel yyi murmushi ya gyada masa kai bai dai ce komai ba, yaron yace "It's big" parking khaleel yyi a parking space ya fito ya xaga ya sakko da yaron sannan ya nufi entrance na babban parlorn gidan yana rike da hannunsa, yara ne da baxa su wuce Shureim din ba su uku duk maxa kusan duk kamanninsu na larabawa suna wasa parlorn da puzzles, suna ganin khaleel suka yo kansa da gudu suka rungume sa suna gaishesa da larabci, ko wannensu cike da murnan ganinsa, Dukawa yyi duk ya shafa kansa yana murmushi yace "I brought you a new friend, Shureim by name" Murmushi Shureim yyi yana kallonsu yace "Hey"  sallama suka yi masa gaba daya, khaleel yyi dariya sosai, ya mike ya kama hannun Shureim suka wuce sama yana waigo yaran, bedroom din Ummun sa ya tafi da shi, Wata balarabiya ce da baxata haura sittin ba xaune dakin tana waya da halshan larabci, ya xauna gefen makeken gadon ta, ya dau Shureim ma ya ajiye sa gefensa, tana gama wayar ta juya tana kallon khaleel tace "Sai yanxu" gaisheta yayi ta amsa da murmushi ta na kallon shureim tace "Ina ka samo mana yaro" Ya shafa kai a hankali yace "Ummu... Khadijah da nake baki labari, he is her son Shureim" Umma tace "Maa sha Allah, xo in ganka sweetheart" Shureim ya sauka kan gadon ya tafi gunta ta jawo sa ta rungume sa tace "Ya ummun ka fa?" Yace "She is fyn" Khaleel yace "Twin dinsa baya tare da shi ne duk ya daga hankali shine nace bari in kawo sa nan sai su dinga wasa da su fadeel tunda suna hutu su ma" Ummu tace "That's nyc, Ina twin din nasa ya tafi" khaleel yace "Ya tafi familyn Dad dinsa ne" Umma tace "Ayya, toh Allah ya sa wannan din ya saki jiki a nan" Khaleel yace "Ameen" Mikewa yayi ya fita dakin ya bar ta da Shureim tana masa tambayoyi tana murmushi. Baby ce ta tsaya tare da Sudais dake bacci dakin Abbansa, Mumy da Aliyu da saleem suka tafi asibitin da aka kira Mumy a zaria, Har suka isa ward din da aka gaya masu Anty Khadijah take mumy gabanta bai bar faduwa ba lkci daya kuma ta dinga tunanin wa gare Khadijah a cikin garin Zaria da ta taho, Aliyu ya murda kofar ward din ya shiga Mumy na biye da shi, kwance suka ga Anty Khadijah kafafuwanta duk biyu an mata dauri, ga wani katon plaster an mata rawani da shi a kai, hannunta daya ma daurin ne, mumy ta kasa karasawa cikin dakin sai hawaye duk jikinta yyi mugun sanyi, saleem ma ya makale jikin kofa ya kasa shiga yana kallonta baki bude, Aliyu ne yyi karfin halin karasawa cikin dakin yace "Subhanallah.... Innalillahi wa inna ilai hi raji'un" Anty khadijah ta juyo wuyanta da kyar tana ganinsu ta fashe da kuka muryarta can kasa tana magana da kyar tace "Aliyu duk na kakkarye, Wayyo Allah na ku taimake ni" Kasa cewa komai Aliyu yayi ya xauna kujera dake wajen duk jikinsa yyi sanyi yana kallonta, Wata nurse ce ta shigo dakin tace "Likita na magana da mutum daya cikin ku" Aliyu ya kalli Mumy tayi karfin halin cewa "Ka je" mikewa yyi cikin sanyin jiki ya bi bayan nurse din, Ba a dau lkci ba wata nurse ta sake shigowa da wasu allurai ta xuba su cikin ledan ruwan dake jikin Anty khadijah, yunkurin amai ta fara yi daga kwancen, nurse din tayi saurin sa hand gloves ta dagota ta dauko wani tasa ta sa mata dai dai bakinta tana mata sannu, amai ta dinga kwarara kamar xata amaye hanjinta, Mumy tayi karfin halin karasowa a karo na farko cikin muryar kuka tace "Sannu Khadijah" Nurse din ta mayar da ita ta kwantar tana ihu alamar ta fama daurinta ta ajiye tasan aman ta fita, wata cleaner ta shigo ta dau tasan ta shiga toilet. Har likitan ya kai aya Aliyu kallonsa yake da shock, cike da karfin hali yace "Ciki kuma Dr?" Likitan ya mika masa result din yace "In sha Allah, gashi nan har wata uku" kasa cewa komai yyi ya mike ya bar office din rike da sakamakon, tun bayan da suka yi hatsarin jiya da daddare da aka taho da ita asibiti ga karaya ta ko ina, ga amai da take ta kwarara ya sa likitan ya sa a mata gwajin ciki don a san irin treatment din da xa a mata, ai ko result na fitowa ya ga cikin ne da ita har wata uku, Aliyu ya share xufar dake keto masa ya shigo ward din yana kallon mumy dake ta goge hawaye tana kallon yar uwar tata, mika mata result din hannunsa yyi ya jingina da bango duk jikinsa a sanyaye.


Mikewa Mumy tayi tana kallon Anty khadijah a mugun tsorace tace "Ciki kuma khadijah? Ciki fa??" Da kyar Anty khadijah ta juyo kai tana kallon Mumy, Aliyu ya juya ya fice daga ward din, mumy ta fashe da kuka tana kallonta tace "Ciki fa Khadijah, innalillahi wa inna ilai hi raji'un, turr da halin ki Khadijah, tsofe tsofe dake khadijah" Mumy ta xauna kan kujera ta dafe kai tana kukan abun kunyan da Anty khadijah ta dauko masu, Aliyu ko minti biyar bai kara a cikin asibitin ba ya bar ma saleem makullin motarsa ya hau motar haya xuwa Kaduna, don gaba daya hankalinsa na sudais, har ya isa gida kuma yana mamakin Anty khadijah, wai ciki... jiki a sanyaye ya wuce sama xuwa bedroom dinsa, har sannan baby na xaune dakin kusa da sudais dake bacci, tana ganinsa ta mike tace "Yayanmu ya jikin Anty khadijahn?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Da sauki" daga haka ya kai hannu goshin sudais ya ji babu xafi kamar daxu da safe, ya kalli baby yace "Bai tashi ba tun daxu?" Ta girgixa kai tace "Bai tashi ba, amma yana ta kiran Anty cikin baccin" shiru yyi na d'an lkci sannan yace "Make him a cup of tea" juyawa tayi ta fita dakin, Aliyu ya xauna gefen gado, shi dai ya kasa cire mamakin da yake yi a ransa na Anty khadijah wai ciki.... Sosai Shureim ya sake jiki gidansu Khaleel cikin lkci kankani suka saba da yaran kanin khaleel mata da ke hutu a gidan, duk da kusan sun fi yin larabci, Ummun khaleel ma ta dinga jan sa jiki don yaron ya kwanta mata sosai.  Yana tsaye ya jingina da mota idonsa a kan gate din gidan har ta fito, Hijab ne har kasa jikinta, ba tare da ta yarda sun hada ido ba ta karaso ta tsaya nesa da kusa da shi ta rungume hannayenta tace "Ina kwana" yana kallonta murya can kasa yace "Lafiya lau Amira, ya gidan?" Tace "Lafiya lau" yana shafa kai yace "Sorry ban xo ba jiya kuma ban kira ba, but we communicated with Dr Ayman ya gaya min komai, you don't worry idan bai dawo da shi ba ko xuwa gobe I will personally meet his mum, kiyi hakuri kin ji, let just take everything easy because of the mother Amira, consider her generosity to you, kar ta ga baki mata kara ba" Ita dai Khadijah bata ce komai ba tana wasa da xoben hannunta, Ya d'an yi shiru kafin a hankali yace "ina shureim?" tace "Yana gidansu Dr Ayman" kallonta ya dinga yi yace "Me yake can?" Tace "Ya dai tafi da shi ne kawai" yace "Ohk that's nyc" shiru ne ya biyo, "We need to talk Amira" abinda ya fadi kenan yana dubanta da kyau, a karo na farko tayi masa kallon cikin ido tace "About what?" Jikinta ne yyi sanyi tuna baya da tayi, their moment together lkcn tana laulayi, lkcn da ta fara samun sauki, lkcn da cikinta ya fito har xuwa lkcn da ta haihu, shi ma kallonta yake ko kiftawa babu, taji kamar ta fara hawaye a wajen, murmushi yyi ya dauke kai a hankali yace "Yanxu kin girma sosai, kilan kin fi karfina ko Amira, may be I am not ur class...." Sauke idonta tayi daga kallonsa cikin sanyin murya tace "Ban gane ba" openly yace "Xa ki iya auren mai mata?" Bata kallesa ba bata kuma ce komai ba amma sai da gabanta ya fad, wani murmushin ya kuma yi yace "That says it all, you are not interested" sai a sannan ta daga kai ta kallesa tayi murmushin karfin hali ita ma tace "I know marrying u is not even enough in biyaka abinda ka min a rayuwa barrister, but..." Ya katse ta da sauri yace "But what?" A hankali kuma a sanyaye tace "It looks as if you are afraid of ur wife, ba lallai ta bari ka kara aure ba..." lkci daya mood dinsa ya canxa yace "Says who Amira?" Ta sauke idonta kasa tace "Gashi nan saboda ita mun hadu after six years a super market amma kayi kamr baka taba sani na ba, kuma saboda ita ka kasa kirana jiya kana gida ka min common tambaya...." Ya dakatar da ita yace "Sai hakan ke nufin ina tsoronta kuma Amira, ba tsoro bane ina gudun fitina ne kawai, kema kin san it will look somehow in maki magana a mall ranan muna tare da ita kin san halin ku mata da kishi, a gida kuma it's not proper in yi waya dake...." Khadijah tayi murmushi tace "Upon ur profession? Ta mance wa ta aura ne?" Shiru yyi yana kallonta, a hankali yace "Kawai dai ki ce baki ra'ayina Khadijah" Tana wasa da xobenta cikin sanyin murya tace "I didn't say that Barrister, just that bayan duk wahalan da na sha a rayuwa bana son inyi aure kuma in kasa samun kwanciyar hankali, kasan lalurata, ina da ciwon xuciya, ni yanxu ko kadan bana son hayaniya.... Ban san me yasa ba" tana magana ne hawaye cike idonta, "Ban da haka bani da abinda xan iya biyanka da shi a duniya barrister da ya wuce in amince da auren ka a yanxu, but am afraid..." hawaye na sakko mata ta kai karshe, Lumshe ido yyi na few seconds kafin ya bude ya ga kallonsa take, da sauri ta sunkuyar da kanta yace "Kar ki damu da matata Amira, beside ba gida daya xa ku xauna ba" ita dai bata ce komai ba amma gaba daya hankalinta a lkcn ya tafi kan khaleel..., lkci daya jikinta yyi mugun sanyi, A hankali ta ji yace "Plss Amira..." Ta daga kai a sanyaye tana kallonsa. Mumy ce xaune tayi tagumi nesa da Anty khadijah dake ta ihu tana cewa xata mutu axaba ya isheta a cire mata kafafuwan ta huta  damuwa ce sosai tare da Mumy tayi kukan takaici har ta gaji wannan wani irin bala'i ne, da ta tuna wai ciki gare Anty khadijah sai ta fashe da kuka sosai, da kyar ta tashi jin ring din wayarta dake ajiye cikin jaka ta bude ta fiddo wayar ta daga ta kai kunne hade da sallama, "Don Allah ina magana da Hajiya Fatima ne?" Mumy tace "Ni ce" matar tace "Alhmdlh, Hajiya Laure ce, dalilin kiranki yanxu shine tun jiya nake neman Hajiya Khadijah a waya bana samu, ga yar ta da ta bari nan kuraje sai ruwa suke suna fashewa, don Allah a turo a dauketa gaskiya, ni ban san wani irin ciwo take ba ni mai yara a gida, don Allah a xo a dauke ta gidana don ko tashi bata iya wa" Mumy ta kasa cewa komai jikinta ya kara mutuwa, cike da karfin hali tace "Toh xa a xo a dauketa, hatsari khadijahr tayi jiya" Hajiya Laure tace "Hatsari kuma? Toh Allah ya kiyaye, ni dai a xo a dauke yar nan gidana babu ruwana" daga haka ta katse wayarta, Mumy ta dinga goge hawayen idonta, bayan wani lkci ta kira Aliyu ta ji ko xai je dauko ikliman, yana dagawa cikin sanyin murya tace "Abuturrab," yace "Na'am Mumy, ina yini" tace "Alhmdlh, ya jikin yaron?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Muna Asibiti fa Mumy" tace "Asibiti kuma, jikin ya ki ne?" A hankali yace "Toh da sauki, but xa a duba kansa ynxu to check if everything is okay" Tace "Ikon Allah, to Allah ya basa lafiya" yace "Amin mum" daga haka ta katse wayar ba tare da tayi masa maganar ikliman ba ma, Aliyu ya ajiye wayarsa yana kallon Sudais da aka cire ma oxygen a lkcn, Baby na share idonta a hankali tace "Yaya ko xaka kira mum dinsa, kaga ita yake ta kira fah" ya kalli kanwar tasa yace "I don't have her contact" tace "Toh barristern nan da suka xo tare fa?" Shiru Aliyu yyi tunawa da yayi ya dau number khaleel a wayar Farouq ranan, daukar wayarsa yyi ya fiddo number yana kallo, da kamar xai yi dialing sai kuma ya fasa ya mike yace "I will go get her now" Da makullin motarsa ya fita xuwa parking lot, yana shiga motarsa ya nufi gidansu Khadijah, yana isa yyi parking ya fito ya nufi gate, a hankali ya tura ya ji ma a bude yake ya shiga, kamar bai son tafiyar yake yi har ya isa entrance din cikin parlorn, ya kai hannu ya danna bell, Khadijah dake kitchen tana girkin lunch ta fito kitchen din da sauri, bata damu da ta sa Hijab kan kananun kayan jikinta ba don a tunaninta Nanny ce ta dawo daga kasuwa, bude kofar tayi suka yi ido hudu da Aliyu, tayi still a wajen na yan sakwanni kamar an dasa ta, da sauri ta bar bakin kofar tayi hanyar daki ya bi ta da kallo, can ya sa kafa ya shiga parlon ya xauna kan kujera, kan gado Khadijah ta fada tana maida numfashi ga gabanta dake ta faduwa, Kar umma ta fito parlorn babu Hijab ya sa ta mike da sauri ta shiga dakin Umma, xaunawa tayi har ta gama waya kamar xata yi kuka tace "Umma kun ga abinda nake gudu kenan koh? Meye ya kawo Aliyu gidan nan yanxu, why will he come to this house kuma ba tare da yarona ba" Umma na kallonta da mamaki  tace "Yana ina?" Fuska daure tace "Yana parlor mana" Umma tayi shiru, sai kuma tace "Toh ai sai ki tsaya ki ji me ya kawo sa koh" Khadijah ta kara hade rai sosai tace "Umma ni idan xan koma UK da yan biyun xan tafi gaba..." Shiru tayi a sanyaye tunawa da tayi ai a can ma ta fara jam da Aliyu, Umma tace "Ki tashi kije ki ji abinda ke tafe da shi, ni kar ki min fitsara" rai ba dadi Khadijah ta mike ta fita, labewa tayi da bango a corridor tana kallonsa, the mouth, the nose, the eyes, worst of all the face... Sosai jikinta yyi mugun sanyi, wayarsa kawai yake dannawa idonsa a kai, kamar ance  ya waiga suka hada ido gabanta yayi mugun faduwa, tayi saurin dauke kai, shi ma hakan yayi, ta hade rai bbu yabo babu fallasa tace "Me ka xo yi gidan nan malam?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ur son, yana son ganin ki" Bata san lkcn da ta fito parlorn ba ta taho gabansa tace "Yana ina?" Ya mike bai kalleta ba yace "At the hospital" lkci daya hankalinta ya tashi tana kallonsa tace "Har yanxu jikin nasa?" Aliyu ya girgixa kai ba tare da ya kalleta ba still yace "Da sauki" daga haka ya nufi kofa yace "Ina jiran ki a waje" juyawa tayi da sauri ta koma dakin umma cike da damuwa tace "Umma wai asibiti xa mu je wajen Sudais" Umma tace "Asibiti kuma, an maida shi asibitin ne?" Gyada kai tayi kamar xata yi kuka tace "Ehh" Umma tayi shiru na d'an lokaci sannan tace "Toh ki je, Allah ya kiyaye, idan ba a sallamesa ba xuwa anjima sai in taho nima, ki tafi da wayar ki xa mu dinga magana" Khadijah tace "To" sannan ta koma dakinta ta dau waya ta fita, Aliyu na mota yana jiranta har ta fito, ta hade rai ta bude front seat din ta shiga ta rufe, shi dai bai ce komai ba ya tada motar yyi reverse suka bar anguwar, danne danne kawai take a wayarta, lkci daya tayi dialing number Khaleel ta kai wayar kunne, yana dagawa yace "Ya aka yi Ummu twins?" Ta sauke idonta kasa tace "Xan je clinic gun sudais ne yanxu" yace "Clinic, did they call you?" Ta gyada kai a hankali tace "Ehh" yace "Ohk toh Allah ya tsare, ke da waye?" A takaice tace "Driver!" yace "Ohk, text me the hospital name yanxu" tace "Toh" daga haka ta katse wayar, shi dai Aliyu driving dinsa kawai yake, bayan wani lkci fuska daure kamar ana tilastata tace "Wani asibitin ne?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban sani ba" wani kallo ta dinga masa ganin ko waigo wa bai yi ba tayi tsaki, har suka isa asibitin babu wanda yace komai cikinsu, bayan yyi parking ya bude motar ya fita ya nufi entrance din clinic din, sosai ta ji ranta ya baci ta fito motar ta rufe tana hararansa, ba tare da ya juyo ba yyi locking motar da makullin hannunsa, sai da ta karanta sunan clinic din sannan ta bi bayansa tana turo baki, tuni ya shige ward kafin ta shigo reception, ta dinga kalle kalle ta rasa inda ya shiga, gaishe da nurses dake wajen tayi, wata nurse tace "Tare ku ke da Dr Aliyu?" Khadijah ta gyada mata kai, nurse din tace "Ohk ki je daki na biyar nan ya shiga" Khadijah ta mata godiya ta bi hanyar da ta nuna mata tana kirga wards din har ta xo na biyar, Aliyu na tsaye jikin window yana kallon result din scan da aka ma Sudais Khadijah ta shigo dakin, tsaye tayi bakin kofa tana kallon sudais dake kwance, Baby na ganin ta ta mike, a sanyaye Khadijah ta karaso ciki, baby na murmushi tace "Sannu da xuwa Iman" Khadijah ta mayar mata da murmushin tace "Ya su mumy?" Baby tace "Suna lafiya" tsayawa Khadijah tayi tana kallon Sudais dake bacci restlessly, har ya rame daga jiya xuwa yau, Baby tace "Jikin da sauki ma" Khadijah bata iya ta ce komai ba tana kokarin ganin hawaye bai zubo mata ba, Baby ta ja mata kujera tace "Ki xauna" kamar ta san da kyar take tsaye dama, Khadijah ta xauna tana ta kallon yaron nata, Aliyu ya juya ya fita daga dakin, text din sunan asibitin ta tura ma khaleel. Ba a dau lkci ba wani Dr ya shigo ward din Khadijah ta dinga kallonsa, allura biyu yyi ma Sudais, Khadijah ta mike da sauri jin ko bude ido bai yi ba, tana kallon likitan hankali tashe tace "Dr ban ji yyi kuka ba kuma yana kukan allura" yar dariya likitan yyi yace "Toh ai ba dole yyi kuka ba madam" daga haka ya juya ya fita, ta dinga kallon sudais xuciyarta na bugawa, ita kanta Baby mikewa tayi tana kallonsa, Khadijah ta kai hannu tana tashinsa, sai da ta jijjiga sa sosai ya bude idonsa a hankali, yana ganinta ya rike hannunta murya can kasa yace "Anty don't leave me plss, where is shureim" Sosai ta ji hankalinta ya kwanta ta taba jikinsa ta ji bbu xafi, ta xauna kusa da shi cikin sanyin murya tace "Get well soon plss son" hawaye cike idonta ta kare maganar yace "Ohk, Anty shureim" ta kwantar da murya tace "Xai xo anjima ka ji" ya gyada mata kai, Aliyu ne ya shigo dakin, yana kallonsu yace "why did you wake him?" Ba tare da ta kallesa ba ta hade rai a takaice tace "Because he is my son" tsayawa yyi yana kallonta, Baby jikinta yyi sanyi ita ma, ta mike kawai ta fita daga ward din, Aliyu ya dau wayarsa ya fita shi ma, Mumy ya kira bayan ya gaisheta yace "Mumy ina jin fa dole xa a fita da yaron nan waje" cikin tashin hankali Mumy tace "A fita da shi kuma? Jikin ya ki ne har yanxu Abuturrab" yace "Akwai matsala ne scan da aka yi masa, just pray for him mumy" Mumy ta kasa cewa komai Aliyu ya katse wayar, Khadijah sai kallon sudais take da ya kara rufe ido kamar mai bacci, ta dau waya ta kira khaleel, bugu biyu ya dauka, tace "Plss ka d'an xo da Shureim" yace "Ohk, let me go back to pick him" Cikin minti sha biyar khaleel ya kirata yana asibiti, Khadijah ta mike ta fita don shigowa da shi, da gudu Shureim ya taho ganinta da yayi tun daga nisa ta bude hannunta ta rungume sa, "Anty plss I want to see sudais now" ta shafa kansa tace "You wil see him sweetheart" daga haka ta mike tana rike da hannunsa ta kalli Khaleel dake kallonsu, ta d'an yi murmushi ta sauke kanta kasa tace "Ina yini" yace "Lafiya lau ya mai jikin?" Tace "Da sauki, ya ma koma bacci yanxu" daga haka ta fara tafiya rike da shureim ya bi bayan su har suka isa ward din, tun da Khaleel ya shiga yake kallon sudais har ya karasa kusa da shi, ya juya yana kallon Khadijah yace "Yaushe aka kawo sa asibiti?" Ta bude hannu alamar bata sani ba, yace "Wa ya kawo sa?" Ta turo baki tace "Shi ya kawo sa" khaleel yace "Ina yake?" Tace "Kilan yana office" juyawa yayi ya fita ta bi sa da ido, can ta mayar da dubanta kan sudais, shureim na kusa da shi kan gadon da damuwa yake cewa "Sudais are you still sick? Plss get well soon so that we can play together, I am missing you" Kallon sa kawai Sudais yake bai ce komai ba, hawaye ya cika idon Khadijah ta karasa kusa da shi ta kamo hannunsa tace "Sudais talk to ur brother he is missing you" Sudais ya gyada mata kai amma bai ce komai ba, ta xauna kujera hawaye na sakko mata tace "Plss get well son, I want to see u hale and hearty once more" Aliyu na rubuce rubuce yana duke gaban table dinsa khaleel ya shigo, kallon kallo suka tsaya yi, can khaleel ya karasa cikin office din yace "What exactly is the little boys problem now?" Ba tare da Aliyu ya sake kallonsa ba ya dau takardan scan da aka yi ya mika masa, Khaleel ya karba yana dubawa, shiru yyi na yan dakiku kafin ya kalli Aliyu yace "So what next?" Mikewa Aliyu yyi yace "We will be going to India tomorrow" kallon khaleel yyi yana kwasan takardun da ya gama rubutu a kai yace "Don't tell her anything about it...." Kallonsa kawai khaleel yake bai ce komai ba, can ya juya ya fita daga ward din ya koma reception ya xauna, kai kana ganinsa kasan he is disturbed, Khadijah tayi ta jiran dawowan khaleel amma shiru, taji duk hankalinta ya tashi, kallon Shureim dake ta damun sudais din da magana ta yi xata ce ya daina damunsa taji muryar sudais a hankali yace "Anty tell him to let me I want to rest" idonsa a rufe yake maganar, Ta kalli shureim da damuwa tace "Leave him plss shureim ka ga ba shi da lafiya" Shureim ya bata fuska yace "Then I will rest with him too" ita dai bata ce komai ba, wasu likita biyu da nurse daya suka shigo ward din, daya ya sauke Shureim kasa daga kan gadon, wasu alluran likitan ya kara masa guda biyu, daya likitan yace "Xa a canxa masa daki yanxu madam...." Juyawa Khadijah tayi ta fice daga dakin xuciyarta na bugawa, Khaleel na xaune har sannan a reception, bai jira ta karaso ba ya mike ya fita kamar bai ganta ba, sama ta wuce ta bude office din Aliyu, tsaye ta gansa jikin window ya juyo suka hada ido, ta isa kusa da shi hawaye cike idonta tace "Tell me what's wrong with my son Aliyu, ka gaya min plss" ta fashe da matsanancin kuka tana kallonsa, ya dauke kai yace "He will get better soon, it's just a minor illness" ta tsayar da kukan da take cikin sanyin murya tace "Are you assuring me??" Yana kallon kwayar idonta yace "Sure, Allah xai basa lafiya" juyawa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo. Karfe Biyar na yamma Umma ta xo clinic din, hankalinta ya tashi sosai ganin Sudais ita ma, Khadijah dake xaune cikin sanyin murya tace "Umma kawai xaxxabi ne, Allah xai basa lafiya" ita dai umma bata ce komai ba, abincin da ta kawo ma bai ci ba, khaleel yace ta bar sa anjima xai ci ana basa abinci a drip, Da ladabi Aliyu ya shigo ward din ya gaida umma ya fita, har aka yi isha suna clinic din, Aliyu ya samu khaleel dake xaune waje yace "You tell her to go home it's getting late" Khaleel bai kallesa ba yace "Allow her to be with her son, kuma it's better ka gaya mata matsalar yaran sai ta bi ku xuwa India gobe" Aliyu bai ce komai ba na kusan minti daya, can ya juya ya bar wajen, tara saura umma ta wuce, babu yanda Khadijah bata yi da shureim ya bi ta ba amma ya ki, haka umma ta tafi ta bar sa. Khadijah na xaune ta jingina da gadon da sudais yake misalin goma saura wayarta ya fara ring, dagowa tayi tana kallon wayar, ta dauka a hankali ganin sudais ke kiranta ta daga ta kai kunne cikin sanyin muryarta tayi sallama, muryar mace taji tace "Amira koh?" Khadijah tayi shiru tana saurarenta, tace "Toh jiddah ce, matar Barrister Aliyu, ina son sanin meye hadin ki da mijina tun da girma da arxiki" mamaki ya cika Khadijah, jiddah tace "Ohh shiru xa ki min kina ji na?" Khadijah tace "Toh uwata ce ke da baxan yi shiru ba, why not ki tambayi shi mijin naki meye tsakaninmu xa ki kirani, ko kin mance profession din mijin naki" wani tsawa jiddah tayi tace "Kee maxa kalmashe kalamanki, kinsan wacece ni, na fi ki sanin aikin mijina malama, sannan mijina baya kiran client dinsa baya kuma saving numbers dinsu sai dai su kira sa suyi introducing kansu ke ko gashi duk shi ke kiran ki kuma ku dau mintuna masu yawa kuna magana, halan baki san yana da aure bane, baki san mijin aure bane?" Tsaki Khadijah ta ja tace "Kan ki ake ji, wannan kuma sai ki je ki samu mijin naki ki tambayesa" daga haka ta kashe wayarta, jiddah ta kirata ya fi sau hudu bata daga ba  lkci daya taji xuciyarta ya fara mata xafi duk da ba wai hayaniya tayi da ita ba, taji ranta yyi mugun baci. Wata nurse ce ta shigo ta nuna mata wani spare gado dake ward din tace ta kwanta, khadijah ta mike tana kallon Sudais duk da bata son barin sa, ta kai hannu goshinsa still taji ba xafi temperature dinsa is normal, ya bude idonsa a hankali, har ranta ta ji dadin hakan don har umma ta xo ta tafi bai bude idonsa ba, xata yi magana ya riga ta yace "Anty ina Shureim?" Tace "Yana waje tare da uncle" ya bata fuska yace "Me yasa ya tafi?" Ta kwantar da murya tace "You said he shud allow you to rest, shine ya tafi da uncle" a hankali yace "Anty kice ya xo plss, I want to tell him am sorry" jikinta yayi sanyi tace "Toh xan kira sa yanxu" daga haka ta nufi kofa tana waigo yaran da ya bi ta da ido,


Khaleel na xaune waje idonsa a kan wayar hannunsa Khadijah ta nufosa, ya daga kai yana kallonta har ta iso inda yake, yace "Is he awake?" Tace "Yace yana son ya ga shureim wai" Khaleel yace "Yana sama" ta d'an bude ido tace "Wajen wa?" Bai ce komai ba, hakan yasa ta hade rai tace "But me yasa ka bar sa ya je can? Why did u allow him go to him?" Khaleel ya ci gaba da danna wayarsa yace "He followed him, sae in hanasa..." Juyawa tayi a fusace ta wuce office din Aliyu, Khaleel ya d'an yi murmushi ya tashi ya shiga clinic din shi ma, Aliyu na tare da Dr Mukhtar Khadijah ta shigo office din, duk suka juya suna kallonta, ta dinga kallon office din tana neman shureim can ta hango sa kwance kan gadon masu ciki a office din yana bacci, karasawa tayi xata tashe sa, taji Aliyu yace "Don't wake him" ko kallonsa bata yi ba xata daga yaron taji jikinsa yyi xafi sosai, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, a firgice ya farka ta rikesa sosai tana kallonsa da damuwa tace "Shureim me ya faru, ur temperature is high" rungumeta yayi yyi lamo jikinta, ta sauke sa kan gadon ta nufi kofa, Aliyu ya bi ta da kallo, ba su kai ga kai wa kofar ba yaron ya shiga kwarara amai, ta dukar da shi da sauri ita ma ta duka hankalinta tashe tace "What's wrong shureim, me ka ci?" Dr Mukhtar ya taho gun su ya dagosa  yana masa sannu, dai dai nan wata nurse ta shigo tana kallon Aliyu tace "Dr, ur attention" daga haka ta fita, Khadijah ta bi nurse din da kallo, Aliyu ya fita office din Dr Mukhtar ya cire ma Shureim rigar jikinsa yana rike da hannunsa ya isa table din Aliyu, duba sa yyi, bayan wani lkci ya ajiye stethoscope din hannunsa ya nuna ma Khadijah bathroom yace "Ki gyara masa jiki sai ki kwantar da shi kan gado, let me get him drug? Ya ci abinci?" Ta girgixa masa kai yace "Ohk" daga haka ya fita xuwa gun nurses, Ganin duk basa wajen yayi tunanin ko an kawo emergency ne, ya kalli direction din Emergency ward, yaga Aliyu tsaye ya jingina da bango, Karasawa Mukhtar yyi gun sa, ganin yanayinsa yace "Me ya faru Dr?" Kallonsa kawai Aliyu yake ya kasa cewa komai, Dr Mukhtar ya shiga cikin emergency ward din, khaleel ne kusa da gadon da sudais yake ya hade kansa da karfen gadon, Dr Mukhtar ya dinga bin Doctors din da kallo, ganin yanda suke tsaye hopelessly, can ya kalli Sudais lkci daya jikinsa yyi mugun sanyi, gaba daya he became lost of words ya kasa karasawa cikin ward din, juyawa yyi da kyar ya fita office din yana kallon Aliyu dake jingine da bango har lkcn, ya dafa shoulder dinsa cikin sanyin murya yace "Hardluck Doctor, Allah ya masa rahama" Aliyu bai iya yace komai tunaninsa daya a lkcn Khadijah, Khaleel ma ya fito ward din yana kallon Aliyu amma ya rasa abinda xai ce, Aliyu yyi karfin halin ce masa "Plss take her home"  Khaleel ya bar wajen a sanyaye ya fiddo wayarsa yyi dialing number sudais, yana dagawa a hankali yace "Barrister the boy is late" daga haka ya katse wayar, kujera Aliyu ya nema ya xauna jin ya kasa ci gaba da tsayuwa, sai a sannan ya ji hawaye na sakko masa ya rike kan sa, how will Iman take this?? Who is to break the news to her, Khaleel ma na tsaye ya jingina da bango yana tunanin yanda xai yaudareta ya mayar da ita gida, can ya nufi sama xuwa office din Aliyu ya ganta ta fito office din rike da shureim, khaleel na ganinta sai da gabansa yyi mugun faduwa ya nufeta da sauri sai dai bai bari taga idonsa ba trying hard to be okay yace "Where did u see him?" Da damuwa tace "Amai yake ta yi Dr, kuma jikinsa da xafi" Khaleel ya duka yana kallonsa yace "What happen shureim" yace "I want go to Sudais" Khaleel ya hadiye abu da kyar yace "Okay xan kai ka my boy" daga haka ya mike yace "Bani wayar pls ina son inyi call mine is out of airtime" mika masa wayar hannunta khadijah tayi ya kama hannun Shureim yace "Mu koma ciki in duba sa" tace "Ai wani Dr ya duba sa yanxu" yace "Ehh let me check him again sai a basa magani" tace "Toh ku tafi, let me go to sudais..." da sauri ya juyo yace "Noo ki xo mu je sai ku tafi tare da shureim he won't be happy idan bai ga shureim ba" a hankali ta bi bayan Khaleel dake rike da shureim, office din Dr Aliyu ya shiga, ya xaunar da Shureim kan gadon office din, ya kalli khadijah yace "You stay with him ina xuwa" daga haka ya juya ya fita, Number Umma ya shiga dubawa a call logs dinta, Ummata... yaga tayi saving number da, nan ya gane number umma ce, yayi saurin kwashe number a tasa wayar, ya sauka kasa bayan yyi dialing, ba a dau lkci ba Umma ta dauka, ya gaisheta cikin sanyin murya yace "Umma khaleel ne, I called to inform you that Sudais is late umma, yanxu ya rasu" mikewa umma dake xaune tayi cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilai raji'un ya rasu?" Jikin Khaleel yyi sanyi jin yanayin da umma ta shiga, a hankali yace "Ku yi hakuri Umma, but har yanxu Khadijah bata sani ba kuma ba a son ta sani a nan so plss, ban san ya xa ayi ko xaki kirata ki dai fada mata wani abu da xai sa ta wuce gida yanxu, cos we can never convince her taje gida ynxu" Kuka kawai Umma take ta kasa cewa komai ta katse wayar ta dinga salati wanda hakan ya ja hankalin Nanny ta shigo, cikin tashin hankali tace "Umma me ya faru?" Da kyar Umma ta iya ce mata "Sudais" tun umma bata fada ba Nanny ta san kwanan xancen ta fashe da kuka ta xube wajen tana salati ita ma, tausayin khadijah ya sa Umma ta kasa controlling kanta, kuka take kamar ranta xai fita, babu mai lallashin wani ita da Nanny, Khaleel ya kasa komawa sama gun khadijah duk iya kokarin sa na ganin ya dake ya ji ya kasa kuma, kujera ya nema shi ma ya xauna yana ganin abun kamar a mafarki yanxu shikenan yaron nan ya tafi, Nurses din ma gaba daya duk jikinsu a sanyaye yake, Aliyu yyi karfin halin fiddo wayarsa ya shiga kiran Mumy, bayan ta daga cikin sanyin murya yace "Mumy ya rasu yanxu" Yanda mumy ta rikice a lokacin sai ayi tunanin sun yi shekara shidda tare da yaron ne, ta dinga kuka kawai ya katse wayar sa,Sudais ne ya shigo reception din duk hankalinsa a tashe ya nufi khaleel cike da karfin hali yace "Dr plss kar ku ce min yaron nan ya rasu, tell me he is still alive" Khaleel ya kasa ce masa komai, Sudais ya tafi gun wata nurse yace "Take me to him plss" nurse din ta nuna masa emergency, da sauri ya shiga wajen, kallon gawar yaron ya dinga yi ganin kamar mai bacci da murmushin sa a fuska, sudais ya karasa gadon ya hade kai da karfe hawaye na sakko masa ya dinga nanata "Innalillahi wa inna ilai hi raji'un" Bai taba ba yaron mutuwa yanxu ba, ranan da aka haifesa tare da d'an uwansa ya tuno, da irin wahalar da khadijah ta sha kamar baxa ta yi ba, ya ji ya kasa controlling hawayen sa, memory din ya dinga dawo masa freah, tun daga san da yaran suka fara wayo, suka yi mugun sabawa da ahi har xuwa ranan da ya barsu suna kukan xa su bi sa amma har ya fita bai waiwayo su ba, cikin raunin murya sudais yace "Allahummaghfir li-fulanin Aliyu warfa' darajatahu fil-mahdiyyina, wakhlufhu fi'aqibihi fil-ghaabirina, waghfir-lanaa wa lahu yaa Rabbal-'aalamina, wafsah lahu fee qabrihi wa nawwir lahu feehi" daga haka ya karasa rufe masa idanuwansa amma ya kasa barin dakin hawaye na xuba idonsa, ya jima bai ji mutuwar da ta taba sa haka ba tun bayan rasuwar maminsa 3 years back, hakan yasa ya kasa daina hawaye, ya ki fita ward din don gani yake kamar yaron xai tashi. Da kyar Umma ta iya dialing number Khadijah, khaleel dake xaune ya jingina da kujera jin wayar na vibrate ya kalla da sauri ganin Umma ke kiranta ya mike ya ba wata nurse yace "Plss ma ki dan taimaka ki kai ma warce ke office din Dr Aliyu wayar nan" ta amsa ta wuce ta kai ma khadijah, a stairs suka kusa cin karo xata sakko, nurse din ta mika mata khadijah ta karba ganin umma ke kiranta ta daga wayar, Umma tayi gathering courage bayan ta saita muryarta tace "Khadijah ki dawo gida yanxu ina son ganin ki" hankalin khadijah ya tashi sosai jin yanayin muryar umma a tsorace tace "Umma baki da lafiya ne?" Hawaye na sakko ma Umma cikin sanyin tace "Ehh bana jin dadi ki dawo yanxu kin ji daughter" tashin hankali ne sosai tare da Khadijah ta dinga kallon wayar sannan ta sauka kasa da sauri, khaleel na ganinta ya mike da sauri, ta nufe sa da damuwa tace "Dr Umma ce ta kira wai bata da lafiya yanxu" ya dake yace "Subhanallah, bata da lafiya kuma?" Ta gyada masa kai hawaye cike idonta, yace "Toh bari inyi dropping din ki gidan yanxu..." Tace "Toh, Shureim din yana ta aman har yanxu amma wani Dr na gun sa" Khaleel yace "Toh shkkn mu je" juyawa tayi ta nufi ward da little sudais yake kafin a kai sa emergency tace "Let me check sudais kafin in tafi pls" Khaleel bai san lkcn da ya fixgota ba ta kusa fadawa kansa  da mamaki take kallonsa, ya wara ido yace "Mu je, idan mun dawo sai ki duba sa, bacci yake daga can na fito yanxu" kasa cewa komai tayi Khaleel na rike da hannunta ya nufi kofar fita ta dinga bin sa, Aliyu dake xaune one side of the clinic duk yana kallonsu ya lumshe ido to prevent more tears, he still can't believe that cute boy, his blood is gone forever, kiran Abbansa ne ya shigo wayarsa, ya san mumy ta kira sa ta fada masa kenan, don tun bayan da Mumy ta gaya masa abinda ya shiga tsakaninsa da khadijah da batun yan biyun ya dauke masa wuta duk da a ranan ma ya bar kasar, a hankali ya mike ya daga kiran Abban nasa. Har suka isa gida khaleel bai ce ma khadijah komai ba, sai dai ya lura duk a sanyaye take, yaji wani mugun tausayinta na dawainiya da shi, jiki ba kwari ta fita daga motar bayan yyi parking ta wuce ciki tana tsoron yanda xata je ta samu Umma, Xaune umma take har lokacin a daki tayi kukan har taji ba dadi, nanny ma duk ta fita hayyacinta da ta tuna sudais ya mutu sai ya rushe da kuka don tun suna jarirai take tare da su. suna ganin khadijah duk suka shanye kukan Khadijah ta karasa da sauri ta xube gaban umma gabanta na mugun faduwa tace "Ummata mai ya faru, why are you crying plss" rungume ta umma tayi ta sake fashewa da wani kukan, Khadijah duk ta rikice ita ma ta fashe da kuka tace "Umma don Allah ki gaya min me ya faru, waye ya mutu?" Nanny ta mike ta bar dakin wani sabon kukan ya xo mata. A sanyaye khaleel yyi reverse ya koma clinic din, dai dai lkcn da Sudais ya fito daga emergency ward, Dr Mukhtar kuma ya sakko kasa rike da shureim, shureim na ganin Khaleel ya nufe sa da sauri, Aliyu ya bi yaron da kallo a sanyaye, khaleel ya duka yana kallonsa murmushin karfin hali dauke fuskarsa yace "How are you feeling now?" A hankali yaron yace "Uncle I want to see my brother plss" Khaleel ya dinga kallonsa ko kiftawa babu, can ya kirkiri wani murmushin yace "He is sleeping now" ya fashe da kuka yace "Nooo, I want to sleep with him too" daga haka ya juya xai tafi inda dan uwansa yake, khaleel ya jawo sa da sauri yace "He is sick, baka son ya samu lafiya, idan kana damunsa baxai samu lafiya ba ai" cikin rawar murya yaron yace "Toh uncle kar ya tafi ya bar ni" Khaleel dake kallonsa ko kiftawa babu a hankali yace "Ina xai je?" Shureim yace "Gida" tashi Khaleel yyi ya kama hannunsa ya fita duk jikinsa a sanyaye. Aliyu dake xaune ya dinga kallon colleagues dinsa dake tambayarsa inda xa a kai gawar sudais ko a nan xai kwana, mikewa yyi da kyar yace "Xan tafi da gawar gida yanxu" a kunnen Barrister sudais da sai lkcn ya fito daga dakin da gawar sudais yake, ya karaso inda Aliyu yake fuska daure yana masa wani kallo yace "Gidan mahaifiyar sa xa a kai gawar yanxu...." kallonsa kawai Aliyu ke yi, Sudais yace "You will be the one to go break the news to her" Aliyu ya d'an bude ido yace "Why me?" Sudais bai sake saurarensa ba ya koma ya dauko gawar ya fita xuwa gun motarsa Aliyu ya bi sa da wani irin kallo. Kusan a tare duk su ukun suka isa gidan, khaleel ya fara fitowa sannan ya sakko da Shureim yana kallon Sudais da ya fito shi ma amma gawar na motarsa, dauke kai khaleel yyi ya shiga ciki yana rike da shureim, Aliyu ya fito daga tasa motar da Doctors biyu suka bi bayan Khaleel, Sudais ya kasa shiga ciki ya jingina da motarsa yana tunanin yanda Khadijah xata dau xan cen rasuwar d'an ta, lumshe ido yyi wasu hawayen na sakko masa, Nanny ce ta bude masu kofa khaleel yasa ta shimfida tabarma a nan balcony, duk gabansa faduwa yake damuwar sa daya khadijah, xuwa yanxu dai umma ta daina kuka bayan ta ce ma khadijah rasuwa aka mata, Khadijah sai kallonta take a sanyaye bayan ta gama kukan ita ma don bata san waye ya rasu ba kuma umma bata gaya mata ba, Umma ta sa Hijab ta fito a sanyaye ba tare da tace ma khadijah komai ba, khaleel ya dinga kallon umma da wasu hawayen ke xubo mata ganin su, Aliyu ya kasa kallonta a sanyaye yace "Allah ya yi masa rahama, ya sa mai ceto ne" Khadijah ta fito daga daki da sauri jin muryar Aliyu, kallonsu ta dinga yi daga inda take tsaye can ta karaso da sauri tana kallon khaleel gabanta na faduwa tace "Dr ina sudais din?" Khaleel ya kasa kallonta kuma ya rasa abinda xai ce, dai dai nan Barrister sudais ya shigo parlorn shi ma bayan ya ajiye gawar sudais kan tabarmar da ya gani balcony baya son ya shiga ciki da shi tukun, suna hada ido da khadijah yyi saurin sunkuyar da kansa, A hankali khadijah ta juya tana kallon umma dake share sabbin hawayen dake xubo mata, ta juya ya kalli Nanny da ta jingina da bango tana hawayen ita ma, a rikice ta nufi Aliyu ta durkusa gabansa cikin rudewa tace "Aliyu ka gaya min wani abu ya sami sudais dina ne, don girman Allah ka gaya min" kasa ce mata komai yayi ya kasa kallonta, lkci daya hawaye ya cika idonsa, mikewa khaleel yyi ya nufi kofa xai fita cos he can't stand it any more, ta mike kamar mahaukaciya ta bi bayansa da sauri, tsaye khaleel yyi balcony ganin gawar yaron a wajen don bai san Barrister ya shigo da shi ba, ya juya a hankali yana kallon khadijah dake kallon gawar kan tabarma an rufe, lkci daya jikinta ya dau rawa ta kamo hannun khaleel cikin rawar murya tace "Dr meye wannan, what is it...." Jawota khaleel yayi jikinsa ya rungume ta gam, cikin sanyin murya hawaye na taruwa idonsa yace "Don't forget Khadijah, Allahn da ya baki shi ya fi ki son sa.... Ba wayon ki ba ba dubarar ki ba ya sa ya baki, to yanxu ya amshe kayan sa, sudais addu'arki kawai yake bukata gare sa yanxu, pray to meet with ur son once again in

Jannah...." Jin Khadijah tayi shiru ya dago kanta a hankali yana kallonta, a hankali yaji tana neman sulalewa hannunsa yaki saketa, a haka ta suma yana rike da ita. A hankali khadijah ta bude idanuwanta bayan lokaci me tsawo, kwance take kan gado ta dinga bin mutanen dake xaune dakin da kallo, Wata kawar Umma ta taso ta dawo kusa da ita ganin tashi take son yi ta taimaka mata ta xauna, da kyar tace "Anty me ya ke faruwa?" Umma tayi karfin halin xuwa kusa da ita ta xauna tace "Ya jikin khadijah" shiru khadijah tayi tana ta kallon umma, lkci daya ta fasa ihu ta mike ta fice daga dakin da gudu suka bi ta, Aliyu ne ya fara mikewa a compound din ganin ta fito, ga maxa ko ina, Khaleel dake rungume da Shureim dake bacci jikinsa ya dinga kallonta amma ya kasa tashi, haka barrister sudais, tana ganin Aliyu ta taho gun sa ta rike hannunsa cikin matsanancin kuka sosai tace "Aliyu don Allah kar ka ce min sudais ya mutu, you assured me he will be fyn, kar ka ce min ya mutu don girman Allah" kasa cewa komai Aliyu yyi yana kallonta, ta rungume sa tana kuka kamar ranta xai fita tace "Ka ce min bai mutu ba Aliyu, wllh ina son sa, kar ya tafi ya bar ni" Aliyu ya ja ta suka bar wajen xuwa inda babu mutane ya xaunar xa ita ya durkusa yana kallonta, a hankali yace "Iman kin san Allah xai baki shi?" Ta girgixa masa kai hawaye na xuba idonta tace "A'a"


*Sorry if I disappoint anybody*