Breaking News

NOOR AL HAYAT 91-100 END


 NOOR-AL-HAYAT*✨


 Mikewa Sudais yyi yana murmushi ganin su, Aliyu ya karasa gun sa shi ma murmushin dauke fuskarsa ya basa hannu suka gaisa, Sudais ya duka yana kallon 


Shureim yace "How are you son?" Shureim ya washe masa hakora yace "Fine Uncle" Khadijah dai har sannan bata dago kanta ba gabanta sai faduwa yake, Sudais ya 


dago yana kallonta yace "Good morning Amira" sai a sannan ta kallesa tayi murmushi a sanyaye tace "Ina kwana Barrister" yace "Lafiya lau, ya gida" a hankali 


tace "Alhmdllh" a karo na farko ta kalli direction din da Anty khadijah ke kwance, ita ma kallonsu kawai take, duk tayi baki ga ciki 6aro 6aro ya fito, 


khadijah bata ganeta da farko ba ta dinga kallonta babu kiftawa, gaba daya Anty khadijah ta canxa kamar ba Anty khadijahr da ta sani yar gayu fara ba, Aliyu 


ya karasa har kusa da ita yana kallonta a hankali yace "Sannu Anty, ya jikin?" Maimakon ta basa amsa sai ta fashe da matsanancin kuka ta dafe kanta, ya duka 


kusa da ita cikin sanyin murya yace "Haba Anty, kuka kuma? There is no need for that, in sha Allah xa ki samu lafiya soon, kiyi hakuri...." Shi dai Sudais 


kallonta kawai yake daga inda yake a tsaye, a xuciyarsa kuwa tunani yake anya ma da gaske kanwar mahaifiyar Aliyu ce ba kawai kara ake yi ba, shi bai ma 


wani ga resemblance ba, Khadijah ta sunkuyar da kanta hawayen da ya taru idonta ganin condition din Anty khadijah suka xubo mata, Anty khadijah na girgixa 


kai cikin kuka tace "Kaico na... kaico... don Allah ku rufa min asiri ku yafe min Aliyu, ku yafe min ko xan samu saukin abinda nake ji kullum, ku yafe min 


kar in....." Katse ta yayi da sauri yace "Anty ni baki min komai ba na sha gaya maki, idan ma kinyi wllh na yafe maki duniya da lahira Allah ya yafe mana 


baki daya, don Allah ki daina cewa haka, Allah xai baki lafiya albarkacin annabi Muhammad S.A.W" kuka take yi sosai tace "Aliyu nasan idan ka san gafarar da 


nake nema gun ka baxa ka yafe min ba, ba lallai ka yafe min ba coz i don't deserve it, ni din muguwa ce, na cuce ku, na ci amanar yayata, wllh sharrin 


shaidan ne ba yin kai na bane, ga sakayya tun a duniya Allah ya maku, ashe dama mugunta na komawa mai shi....." mikewa Aliyu yyi bai sake ce mata komai ba 


don ji yayi har xuciyarsa ya karaya, Ashe tana sane mugunta take yi dama, cikin magiya da kuka tace "Aliyu don girman Allah, don xumuncin dake tsakanina da 


mahaifiyar ka ka yafe min abinda nayi maku da khadijah...." Aliyu na kallonta ya dake duk da yasan sauran xancen yace "Me kika yi mana ni da ita Anty?" Tana 


shessheka, fuskarta caba caba da hawaye tace "Wllh ni ce nayi asiri na xuba lipton din da baiwar Allahn nan ta kai maka ranan ka sha, Kuma na kwashi yaran 


duk muka bar gidan, na bar ku daga kai sai ita, ni ce silar abinda ya faru tsakanin ku, ni ce sillar lalata ta da kayi" shi dai Aliyu bai ce komai ba, sai 


dai har wani tafarfasa xuciyarsa yake duk da ya riga ya gama jin ranan da take waya, khadijah da Sudais dai ta bari cikin shock din xancenta, Baby ta mike 


ta kama hannun Shureim dake ta kallon Anty khadijah ta fice daga ward din, Anty khadijah ta kara rushewa da kuka tace "Wllh sharrin shaidan ne la'ananne, 


shi ya sa min tsanar ta khadijah, shi ya asasa min k'in ta a xuciya, don duk xamanta gidan bata taba min komai da ya wuce biyayya da girmamawa, abinda yasa 


na aikata abinda nayi ina tsoron kar wataran ka ce kana sonta da aure don naga yanda kake tausayinta kuma kake damuwa kan lamarinta, gashi naga yanda Mumy 


ma ke sonta, shi yasa nayi duk haka... ban mance ranan da suka dawo bayan ta bar gidan da wancan bawan Allahn ba wai tana dauke da cikin ka na ki saurarensu 


nace su tafi kuma suka tafi, toh yanxu wa gari ya waya, ka lalata mata rayuwa ta tafi ta fuskaci kalubale iri iri wanda da alama hakan alkhairi ya xame 


mata, sai gashi dai bayan shekaru da dama kai din dai ka aureta, Ni kuma ga yanda nawa rayuwar ta kasance, ga 'ya ta can rai a hannun Allah, yanxu ina ji 


ina gani nima xan girbe abinda na shuka" ko kadan Sudais bai ji tausayinta ba sai ma kawai ji da yayi ya tsaneta, dama akwai mutane irin haka a rayuwa, the 


wickedness is just too harsh, khadijah dai na tsaye tamkar wanda aka dasa a gun, gaba daya jin xancen Anty khadijah ta dinga yi kamar a mafarki, lkci daya 


ranan da ta je kai ma Aliyu Lipton a daki ya fado mata, irin yanda ya dinga cewa ta tafi da yanayinsa a lokacin ya dawo mata fresh a memory dinta, bata 


manta ba har saloon yace ta tafi sanusi ya kai ta amma saboda tausayin halin da ta gansa ta ki tafiya, ashe duk asiri ne dama, sai a sannan ta fashe da kuka 


sosai ta juya ta fice daga ward din, Anty khadijah ta dinga kuka tace "Aliyu nasan ita ba lallai ta yafe min ba idan kai ka yafe min... Nasan da wuya don na 


xalunce ta da yawa" Aliyu bai iya yace komai ba, Sudais ya fita ward din, bin bayan khadijah yayi ya sameta can waje tana aikin rusa kuka, Baby ma na nesa 


da ita amma bata samu courage din xuwa inda take ba, Sudais na kallonta a hankali yace "Amira" juyowa tayi tana kallonsa hawaye wasu na bin wasu, yace "Kiyi 


hakuri, duk abubuwan da take fada anyi su an wuce ya kuma xama passed tense, this is ur new life... Don't allow ur past to spoil ur happiness, kin dai ji da 


kunnen ki kuma kin tabbatar ba yin kan Aliyu bane, ba laifinsa bane, ba halinsa bane, babu wanda ya tambayeta kuma babu wanda ya matsi bakinta amma sanin 


cewar hakkin ku ke bibiyar ta shi yasa ta fallasa kanta, don haka just forgive her and life moves on, gashi ita ma ai tana reaping shukar da tayi, yanda 


kika haifi yara out of wedlock ita ma gashi haka xata haifa, gwara ke naki yaran masu gata ne, ita fa, kilan ba lallai tasan uban cikin ba, sannan ga karaya 


har kafa biyu, da wuya kuma kafufuwanta su dawo dai dai ba fatan hakan na mata ba, shi yasa idan mutum xai gina ramin mugunta yasan size din da xai gina, 


let bygone be bygone Amira, ki koma yanxu kice ke kin yafe mata, sai ki ga ta dalilin hakan kila ta samu wani saukin... " Kai kawai khadijah ke gyada masa 


hawaye na sakko mata duk jikinta yyi sanyi, yace "Mu je" ba musu ta bi bayansa har suka koma ward din, amma ta kasa karasawa gadon tana daga inda take a 


tsaye cikin rawar murya tace "Anty ni na yafe maki, 

Allah ya baki lafiya ya kuma yafe mana gaba daya" kallonta kawai Anty khadijah take hawaye na sakko mata, sai a sannan wani tausayinta ya rufe khadijah, ita 


ma hawayen ya dinga sakko mata, ta isa har bakin gadon ta kamo hannunta cikin rawar murya tace "Na yafe maki, kema ki yafe min for making you go the wrong 


way, don nasan da ban je gidan ba baxa ki jefa kanki a halaka ba, Allah ya baki lafiya ya tashi kafadun ki Anty" cikin rawar murya Anty khadijah tace "Amin 


Nagode, Allah ya baku xaman lafiya da xuri'a dayyaba, ya kauda duk wata fitina tsakaninku, I wish Allah xai bar min rai na inyi witnessing din haka, amma 


ina jin kamar mutuwa xan yi, Alhmdllh naji dadi da na sauke wannan nauyin a kai na don kullum da shi nake kwana nake tashi, ban san ta ina xan fara ba, 


Allah ya yafe mana baki daya kuma ya shiryi masu xuciya irin tawa" Khadijah ta kasa amsa mata sai kuka kawai take, Aliyu yace "Ameen, baxa ki mutu ba sai 


lokacin ki yayi Anty" Ita dai bata ce komai ba sai kukan takaici da danasani da take yi, ganin kukan da khadijah take, Anty khadijah tace "Ku tafi Aliyu kar 


in bata maku mood, Allah maku albarka, ya kuma kaddara saduwar mu" Yace "Ameen mun gode, xan dawo nan da kwana biyu" tace "Allah ya kai mu nagode" Gun 


Barrister ya nufa yana kallonsa yace "xa mu koma Barrister, Allah ya bada lada" Barrister yyi murmushi yace "Ameen, Allah kai ku gida lafiya" Dawowa yyi ya 


kama hannun khadijah da kamar daman jiran hanyar kuka take suka fita dakin bayan ta daga ma Barrister dake murmushi hannu. Baby bata iya tace masu komai ba 


duk jikinta yyi sanyi, Aliyu ya kama hannun Shureim dake ta kallon uwarsa da damuwa ganin kuka take yi, ya bude back seat ya sa shi a ciki, ya bude mata 


front seat, shiga tayi tana goge hawayen dake xubo mata, ya rufe motar yana kallon baby, a sanyaye tace "Allah ya tsare hanya yayanmu" yace "Ameen, tare ku 


ka xo da Barrister?" D'an murmushi tayi bata ce komai ba, yayi dariya yace "Nasan rakiya kawai yayi koh?" Dariya tayi bata ce komai ba, yana murmushi ya 


xaga ya shiga driver seat ya ja motar suka fita asibitin, Shureim na kallonsa kamar xai yi kuka yace "Uncle why is Anty crying?" Aliyu ya kalleta yayi 


murmushi yace "Allura aka mata" Shureim ya fashe da kuka yace "Me yasa uncle" parking Aliyu yyi ganin kukan da yaron yake, yana kallon khadijah yace "Kinga 


dama idan ba neman hanyar kuka kike ba toh ya ishe ki haka Iman" ta balla masa wani Harara tace "Toh ina ruwanka, hanyan nake nema dama" murmushi yayi, ya 


kwantar da murya yace....


✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨


 Ya kwantar da murya a hankali yace "Haba my Ummu Shureim..." turo baki tayi ta dauke kai tana goge idonta, ya juya yana kallon shureim, murmushi yayi yace 


"Toh kaga tayi shiru kai ma kayi shiru" Kai ya gyada masa yana kallon mum dinsa, ya dawo kusa da ita a hankali yace "Anty kiyi hakuri" kallonsa tayi, tayi 


d'an murmushi tace "Toh na yi" komawa yayi ya xauna, Aliyu ya tada motar ya ci gaba da driving, murya can kasa yace "Mu bari next time sai mu je duba 


iklima, coz i really don't have the energy to start consoling you again" tace "Ni ka kai ni yanxu, ba wani next time, I will be going back to schl soon" 


murmushi yayi yace "Ohk then" hanyar family house din su iklima Aliyu ya dauka, bayan minti kusan sha biyar suka isa babban gidan, yayi parking a waje suka 


shiga, yan gidan basu wani tarbe su ba, hakan bai wani dame Aliyu ba, ita dai khadijah jikinta yayi sanyi, autar su mahaifin Iklima ta nuna masu wani kofa 


tace "Tana can" Aliyu ya mike yana kallon khadijah ita ma ta mike, Shureim xai tashi ya duka ya dafa shoulder dinsa a hankali yace "You wait for us here 


sweetheart ka ji?" Kai Shureim ya gyada masa ya koma ya xauna, Aliyu ya nufi kofar dakin khadijah ta bi bayansa gabanta na faduwa, ita kadai ce kwance dakin 


mai dauke da yar katifa ko leda babu, katifar ma babu xanin gado, da ganin dakin babu me shiga ciki, Ga cup da plate da spoon dinta nan gefen gadon, da 


kadan iklima ta fi skeleton kwance a kan gadon, khadijah ta kasa karasawa cikin dakin tana iya kokarin ganin bata fashe da kuka ba ta toshe bakinta, Aliyu 


ya karasa ciki yana kallonta shi ma a sanyaye, Durkusawa yayi kusa da ita a hankali yace "Sannu iklima" maimakon ta amsa masa sai hawaye, duk jikinsa yayi 


sanyi ya kasa cewa komai lkci daya shi ma idonsa ya kada, khadijah ta fashe da kuka sosai ta juya ta fice daga dakin, Da kyar Iklima ta iya bude baki tace 


"Kace ta yafe min don Allah" Ya sauke idanuwansa kasa a hankali yace "Kina shan magani iklima?" Girgixa masa kai tayi hawaye na xuba idonta, ya fi minti 


biyu durkushe gabanta bai iya yace komai ba, can ya dago da kyar yace "Wa ke kula da ke?" Nan ma ta girgixa masa kai, cikin sanyi yace "Yaushe rabon ku je 


asibiti?" Kallonsa kawai take alamar maganar ma baxata iya ba, mikewa yayi a hankali ya fita dakin, ya kalli khadijah da ta hade kai da kujera tana kuka 


Shureim na kusa da ita shi ma yana kukan yana kallonta, Babu wanda yace masu komai, kowa na harkan gabansa a babban gidan, gun yayar mahaifin iklima da ya 


sani ya nufa a waje, tana xaune su kusan uku suna hira, ya d'an duka ya gaishe ta, ta amsa tana tambayarsa yaushe ya xo, yace "Ba mu jima ba, mama nace 


iklima na xuwa asibiti kuwa?" Matar tace "An kwan biyu ba aje ba tunda uban nata bai turo kudi ba kilan ya gaji shi ma, mu kuma ya bar mu da wahala" Shiru 


Aliyu yayi yana kallonta, can ya mike yace "Toh bari mu je yanxu" tace "Kar ma ka bata lokacin ka ko tashi bata iya yi, idan ba likitan xaka je ka gayyato a 


asibiti ba" Bai ce komai ba ya koma parlorn sannan ya shiga dakin da iklima take, Kallonta kawai yake yana kokarin gano stage din da cutar nata yake, bayan 


wani lokaci ya juya ya fita, gun khadijah ya nufa yace "Tashi mu je" Ta mike da kyar har lokacin kuka kawai take, Aliyu ya dau shureim ya rungumesa suka 


fita, bank ya fara tsayawa, ya kalli khadijah kafin ya bude motar ya fita xuwa gun automated teller machine, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar, wani 


babban pharmacy dake area din ya tafi, yana kallon khadijah da taki daina kuka yayi kasa da murya yace "Am begging you ki daina kukan nan Iman, baki kyauta 


ma yaron nan, even for his sake kiyi hakuri ki daina kukan" Juyawa tayi tana kallon Shureim da ke kuka bakin rai shi ma, hadiye kukanta tayi xuciyarta na 


mata xafi, Aliyu ya bude motar ya fita, bayan kusan minti goma ya dawo rike da ledan magani masu yawa da tsada, murmushi yayi ganin yanda Shureim yayi shiru 


yana kallon khadijah dake ta kukan xuci, Bata taba tunanin ganin Iklima a yanda ta ganta ba, ta ji duniyar ba bakin komai yake ba, wani store Aliyu yayi 


parking ya fita ya siya cartons of malts da Madara masu yawa, sai locozade boost, a booth aka xuba abubuwan da ya siya, ya shiga motar ya kalli khadijah da 


ta jinginar da kanta jikin kujera ta fada duniyar tunani, kamo hannunta yayi ta juya a hankali tana kallonsa, murmushi ya sakar mata yace "Kowa da irin 


kaddararsa, su irin tasu kenan, so you just have to pray for them, Allah ya sa mu cika da imani" wasu sabbin hawayen suka sakko idonta, ya tada motar suka 


bar wajen, shi kadai ya shiga dakin iklima ya ajiye magungunan gefenta yaran gidan suka dinga shigowa da abubuwan da ya siyo, Yana kallon iklima ya fiddo 


magungunan gaba daya ya shiga nuna mata yanda xata sha, kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan ya nuna mata yace "Idan kin ji kina jin yunwa sai ki 


daure ki tashi ki sha malt ko madara, idan lokacin shan maganin ki yayi ba a baki abinci ba sai ki sha malt ki sha drugs din kin ji?" a hankali ta gyada 


masa kai, ya fiddo dubu talatin a aljihunsa ya daga gefen katifar ya ajiye mata yace "Ki dinga aika yaran gidan su siyo maki fruits sai ki basu ko dari biyu 


don su dinga xuwa kin ji?" Nan ma ta gyada masa kai, ya d'an yi murmushi yace "Allah ya sauwake lil sis, idan kina son ki samu lafiya sai kin yi ta shan 


drugs din ki" Nan ma dai ta gyada masa kai, yace "Xan dinga xuwa duba ki always, idan kika fara samun sauki xan kai ki gun Mumy dama Abbanki ne yace a kawo 


ki nan" kallonsa kawai take, jikinsa yayi sanyi ganin hawayen dake sauka idonta, da kyar yace "I will be back soon" daga haka ya mike ya fita dakin ta bi sa 


da ido, Har suka shigo kaduna, Daga khadijah har Aliyu duk jikinsu a sanyaye yake, tuni Shureim yayi bacci bayan motar, Aliyu na gama parking ya juya yana 


kallon khadijah da ta bude motar ta fita, fitowa yayi shi ma ya bude back seat ya fiddo Shureim, ya rufe motar ya bi bayanta, bedroom dinsa ya shigar da 


Shureim ya kwantar da shi, ya fita ya shiga dakin khadijah, kwance ya sameta tayi lamo jikin pillow, ya xauna gefenta yana kallonta, ita dai bata yarda ta 


kallesa ba, kamo fingers dinta yayi yace "You need not to worry this much Iman, kin san condition din ki fa" Bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ya dagota 


ya rungume ta, ta kwantar da kanta kirjinsa tana shesshekar kuka, murya can kasa yace "Kiyi addu'ar Allah ya basu lafiya Iman" Sun fi minti biyar a haka, Ya 


dago kanta a hankali yana kallonta, rufe idonta tayi, yyi murmushi yana kallon cute lips dinta, kamar tasan me yake yi ta kwace kanta ta mike ta koma can 


karshen gado ta kwanta, shafa kansa yyi yace "Ki tashi kiyi sllh" daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita, throughout ranan haka khadijah 


ta kasa samun natsuwa, Aliyu yayi lallashin har ya gaji, duk ta 6ata mood din little Shureim ma, Bayan magrib ya dawo masallaci ya shiga bedroom dinsa dai 


dai lkcn da wayarsa ya katse, karasawa yayi ya dauka yaga Mumy ce ta kirasa, ya xauna gefen gado ya shiga kiranta, tana dagawa yayi mata sallama, jin 


yanayin muryarta a hankali yace "Mumy baki da lafiya ne?" Mikewa yayi yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" lkci daya ya ajiye wayar ya koma ya xauna ya 


rike kansa, bai san lkcn da hawaye ya dinga xuba idonsa ba, ya fi minti biyar a haka kafin ya mike da kyar ya share idonsa ya dau makullin motarsa ya fita 


daki, yana ta tsaye corridor kafin ya bude dakin khadijah xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta da gado, Shureim na xaune kusa da ita, kasa 


karasawa cikin dakin yayi yana daga bakin kofar yace "Iman xa mu je can gida yanxu" ta kallesa kafin tace komai har ya juya ya wuce, a tunaninta gaida Mumyn 


xa su je su yi, ta mike ta linke pray mat din ta ajiye, ta kama hannun Shureim suka fita bayan ta kashe wutan dakin, ganin yanayin Aliyu ta kallesa da 


damuwa tace "Ko dai wani abu ya faru ne?" Yana driving idonsa kan titi yace "Nothing" har suka isa gida bata sake cewa komai ba, yayi parking ya fito ita ma 


ta fito tana rike da shureim suka bi bayansa, sosai gabanta ya fadi ganin mutane a parlorn, Aliyu ya isa gun Mumy ya durkusa gabanta, khadijah ta kasa 


karasawa xuciyarta na bugawa, upstairs ta wuce xuwa dakin baby da sauri, baby na ganinta ta fashe da kuka sosai, cike da karfin hali khadijah ta durkusa 


gabanta tace "Me ya faru baby" Baby tace "Iklima..." Hawaye ya shiga sakko ma khadijah ta hade kanta da gado tana salati a ranta. Daren ranan a gidan suka 


kwana gaba daya, mutuwar Iklima ya girgixa kowa barin khadijah da Baby, da ta tuna yanayin da suka sameta daxu da rana sai taji hawaye ya ki tsaya mata ashe 


mutuwa xata yi, gashi ko magana bata samu ta mata ba saboda tashin hankali, babu wanda ya wani rintsa a gidan har asuba. Washegari da safe Umma suka xo 


gidan da Nanny don yi ma Mumy gaisuwa, da Umma ta tashi tafiya Shureim yace xai bi ta, haka Umma ta wuce da shi don har da kukan sa, sai bayan da aka yi 


sadakan uku Khadijah da Aliyu suka koma gida da daddare, har sannan shock din bai bar ta ba, har ranta taji ta yafe ma Iklima don ita a iya tunanin ta ma 


bata mata komai, ajiye abincin da Mumy ta basu su tafi da shi tayi a nan tsakiyar parlor ta wuce sama Aliyu da ya bi ta da kallo yace "Iman" juyowa tayi 


tana kallonsa, yace "Baxa ki ci abincin ba" ta girgixa masa kai, yace "Ba fa ki ci komai tun daxu ba" Bata ce komai ba ta haura sama, kitchen ya shiga ya 


dau plate ya wanke sannan ya dawo parlorn ya bude abincin ya dibar mata ya rufe sauran ya wuce sama, kayanta ya sameta tana cirewa, tana ganinsa ta durkushe 


kasa da sauri kamar xata yi kuka tace "Baka iya sallama ba ne" d'an murmushi yayi ya sauke idonsa daga kallonta yace "Yi hakuri" ta turo baki tace "Ka ajiye 


ka tafi" Ajiye mata abincin yayi ba tare da ya kalleta ba ya juya ya fita, zani ta dauka ta daura ta xauna kusa da shinkafa da miyar da ya ajiye mata ta dau 


spoon din ta fara ci a hankali, Bata wani ci da yawa ba don har sannan bata da appetite ta mike ta shiga bathroom, sai da ta wanke bakinta sannan tayi wanka 


ta fito, Hijab ta sa ta dau sauran abincin da ta rage ta fita da shi ta dawo dakin, ta dau lkci xaune gaban madubi tana shafe shafenta ya bude kofar, xaro 


ido tayi ta duka, ya koma da sauri yace "Ohh sorry, Assalamu alaikum..." Tayi saurin daukan hijab dinta ta sa ganin har ya sake shigowa ta hade rai tace 


"Bana son haka Aliyu, ba sai an amsa ake shigowa ba" dariya ta basa sai dai bai yi ba, ya mika mata wayar hannunsa yana kallonta yace "Gashi Dr Ayman xai 


maki gaisuwa" ta hararesa ta karba wayar tace "Toh ni ka fita" juyawa yayi ya fita dakin, ta kai wayar kunne, muryar Khaleel taji yace "Uhm lallai, ya fita 


koh?" Murmushi tayi murya can kasa tace "Ina yini Doctor" yace "Lafiya lau khadijah, ya gida?" Tace "Alhmdllh, ya jawahir" yace "She's fyn, ya karin 


hakuri?" A sanyaye tace "Mun gode Allah" yace "Allah ya mata rahama" tace "Ameen mun gode" yace "Maa sha Allah, good nyt" tace "Alryt, my regards to 


jawahir" yace "In sha Allah" daga haka ya katse wayar, ta ajiye gaban madubin ta mike ta cire hijab dinta ta dau kayan baccin da ta fiddo ta saka, ta linke 


Hijab dinta ta ajiye sannan ta kashe wutan dakin ta kwanta, har bacci ya fara daukanta taji an bude kofar dakin ta bude ido da sauri, tana ji ya rufe kofar, 


Bai kunna wutan ba yana tsaye daga inda yake a hankali yace "Iman, wayana fa?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya fi minti daya tsaye kafin ya juya ya fita a 


hankali ya rufo mata kofar, sai a sannan ta mike xaune, tana ta xaune kan gadon kafin ta sauko ta tafi gun mirror ta dau wayarsa ta saka hijab ta fita, a 


hankali ta bude kofar dakinsa ta shiga.


Ta fi 10 seconds a tsaye ganin babu haske a dakin, bata kunna wutan ba saboda akwai d'an hasken na corridor kuma a bude ta bar door din, ta nufi gaban 


mirror a hankali don ajiye wayar hannunta, lkci daya ta juya jin an rufe kofar dakin duhu ya gauraye ko ina, saurin ajiye wayar tayi ta nufi kofar tana cewa 


"Why is that...." Xaro ido tayi ganin kamar nufota yake yi ta dinga komawa baya kamar xata yi kuka tace "Meye haka Aliyu, ka bude min kofa in fita, I only 


brought you ur mobile phone" murya can kasa yace "Why did you pretend you were sleeping" jingina tayi da banga xuciyarta na bugawa ta marairaice tace "Laifi 


ne don na kawo maka wayarka? to ka bani in mayar I thought you need it ne dama" Yana d'an murmushi yace "Better... dauka ki mayar" tace "Toh ka matsa" a 


hankali ya koma gefe idonsa a kanta, ta taho xata wuce gabanta na faduwa kawai ta ji ya fixgota xuwa jikinsa ya rungumeta gam, jikinta ya dau bari tace 


"Wayyo na shiga uku, meye..." Bai bata damar karashe abinda xata ce ba ta xaro ido tana kallon kwayar idonsa, passionately yake kissing dinta, tun tana 


kokarin kwace kanta har tayi give up, lkci daya jikinta ya mutu gaba daya ta ji ta kasa tsayuwa, bata ankara ba bayan lokaci me tsawo sai ganin su ta tayi 


saman gado, jikinta ya dau rawa a tsorace tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata tace "Noo Aliyu, I still haven't forget the experience, it's always 


fresh, don Allah kayi hakuri, and...." kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, Aliyu da lokaci daya ya bar abinda yake jikinsa yayi sanyi, ya kai bakinsa 


kunnenta cikin sanyin murya yace "And... what?" Cikin shessheka tace "You didn't follow the teachings of our prophet" komawa yayi a hankali ya kwanta ya 


lumshe ido yana maida numfashi, ta rufe kanta duvet har sannan hawaye ya ki tsaya mata gabanta na faduwa, a tunaninta yayi bacci don an dau lkci me tsawo 


bai motsa daga yanda yake kwance ba, a hankali ta mike ta maids wears dinta, xata fita ya mike ya jawota ya rungume cikin sanyin murya yace "I am... sorry 


Iman" ita dai bata ce komai ba, ita dai bata ce komai ba tayi lamo jikinsa, yana jin yanda xuciyarta ke bugawa, bayan wani lkci ganin ta nutsu ya kwantar da 


ita a hankali ya sauka daga kan gadon ya shiga bathroom, har bacci ya dauketa bai fito ba. Da asuba ta ji ana shafa fuskarta a hankali ta bude ido, murmushi 


ya sakar mata yana kallonta yace "It's time for prayer" Rufe ido tayi da sauri don ya kunna fitilan dakin, yana murmushi yace "In kashe wutan?" Cikin sanyin 


murya tace "Yes plss" mikewa yayi ya kashe, sai a sannan ta mike xaune a hankali, ya dinga kallonta cikin duhun, Bata yarda ta tashi kan gadon ba ta kallesa 


tace "Toh baxa ka je masallaci ba?" Yace "We just finished now" Turo baki tayi ta mike tace "Toh ni ba nan xan yi alwalan ba" yace "Saboda me?" Bata ce 


komai ba ta nufi kofa, ya mike da sauri ya rufe yace "Cinye ki xan yi a nan din?" Kamar xata yi kuka tace "Ka bude min plss" yace "Sai kin yi a nan" tace 


"Baxan yi ba" yace "Why?" Tace "I have my reasons, kuma ba dole bane ai" murmushi yayi yace "Baki son in ga kin yi wanka?" Xaro ido tayi tace "Kamar ya?" 


Yace "kamar yanda nayi jiya" ta hade rai tace "Ka bude min Aliyu" yace "Toh tafi bathroom kiyi wankan ki a can" ya fadi hakan yana nuna mata bayin sa, a 


fusace tace "Ce maka nayi wanka xan yi, a kan wani dalili xan yi wanka" Murmushi yayi ya koma kan gado ya kwanta yana kallo ta cikin duhun, ta fi minti goma 


tsaye tana masa magiya amma ya ki budewa, ta fashe da kuka daga karshe ta durkushe wajen, ya mike yana dariya ya bude kofar yace "Toh tafi kiyi wankan ki" 


sai da ta fita tace "Ba wanka xan yi ba sai dai swim" daga haka ta shige dakinta ta rufe tasa makulli, turo baki tayi ta shiga bathroom dinta tayi wanka ta 


dauro alwala ta fito. Tana ta xaune kan darduma har gari ya waye ta mike a hankali ta shiga gyara dakinta ta wanke har bathroom sannan ta fito parlor don 


gyaran gidan, sai kusan karfe takwas da rabi ta gama ta shiga kitchen, Irish ta deba tana fere wa, Jin kamshin da ya ziyarci kitchen din ta juya a hankali 


tana kallon bakin kofa, tsaye ta gansa ya jingina da kofar ya rungume hannunsa yana kallonta, sauke idonta tayi ta ci gaba da abinda take, ya karasa cikin 


kitchen din ya tsaya bayanta, murya can kasa yace "Good morning Iman" kasa cewa komai tayi, kuma bata juyo ba ta ci gaba da peeling din Irish da take, har 


ta gama yana tsaye bayanta, a hankali ta juyo suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, jawota jikinsa yayi yana kallonta cikin sanyi yace "Forgive me 


once more for what happened seven years back Iman, I made you a mother with kids out of wedlock at a very tender age, I know this will always remain in ur 


memory till the end,  nasan kuma da kin gan ni sai kin tuna da hakan, kamar yanda nima in dai na ganki I do felt guilt deep inside me, I want us to get rid 


of that Iman, I want to have peace with you as my wife, nasan baxan iya biyan ki irin wahalan da kika yi ta dalilina ba, but forget the past plss let build 


our new home Iman, i promise to love you till the end, I promise to be by ur side till the end, nayi alkawarin xame maki haske a rayuwar ki till the end, I 


never bargained for this Iman, Allah ya gani na so haskaka maki rayuwar ki xuwan ki gidanmu, na so maki duk abinda xan yi da baxa ki yi maraicin iyayen ki 


ba, sai dai muna namu Allah kuma na nasa, kaddara kuma ta riga fata, kuma a matsayin mu na musulmai we have to accept it either good or otherwise, all we 


have to say now is Alhamdulillah" Bata iya ta dago ba hawaye ya dinga xuba idonta, a hankali ta xame kanta daga jikinsa ta juya masa baya trying her best 


bata fashe da kuka ba, Juyawa yayi a sanyaye ya fita kitchen din, Bata da wani kuxari ta karasa duk abinda take ta juye ruwan shayi a flask sannan ta fita 


da breakfast din gaba daya dining ta ajiye, kwance ta gansa kan 3 seater idonsa lumshe, ta karasa cikin parlorn tana kallon sa, Bata taba yarda cewar yara 


na kama da mahaifinsu hundred percent sai a kan kids dinta, the resemblance is just too obvious, har ta isa kusa da shi bata sani ba, ta durkusa gefensa 


tana ci gaba da kallonsa a sanyaye ta kamo hannunsa, lkci daya ya bude manyan idanuwansa ya mike xaune yana kallonta shi ma, wasu sabbin hawayen suka cika 


idonta ta sauke kanta kasa a hankli tace "Toh ni me yasa basu yi kama da ni ba?" Da mamaki ya dinga kallonta, ta mike xata bar wajen ya jawota jikinsa yana 


murmushi murya can kasa yace "The kids?" Ta gyada masa kai hawayen idonta suka xubo, ya rungume ta sosai ya lumshe ido yana shakar kamshinta yace "Next 


one's xa su yi kama da ke in sha Allah" kwace kanta tayi ta hade rai tace "Next what?" Bude ido yayi, yyi dariya yace "Next kids mana" wani kallo tayi masa 


ta turo baki ta mike ta nufi dining ya bi ta da kallo yana dariya kasa kasa, sai da ta isa nan ta juyo tana kallonsa taga kallonta yake shi ma, a hankali 


tace "Breakfast..." ya mike yana murmushi ya iso dinning din, kanta a kasa tace "Do you still take coffee?" Yana kallonta yace "Sure..." kitchen ta wuce ya 


bi ta da ido ta dawo da coffee powder ta hada masa ta ajiye gabansa a hankali, sannan ta debar masa Irish da kwai ta ajiye masa tare da bread, ya wara ido 


yace "Duk ni kadai wife?" Bata ce komai ba ta hada nata shayin ta xauna tana sha, a hankali ta dago kai suka hada ido, kasa daina kallonsa tayi kamar yanda 


shi ma ya ke kallonta babu kiftawa, tasowa yayi ya dawo kusa da ita cikin sanyin murya yace "Billah Ina son ki Iman" ta sauke idonta bata ce komai ba. Karfe 


sha daya tana dakinta Aliyu ya shigo yace ta shirya xa su fita, lkci daya mood dinta ya canxa, dariya yayi don ya ma san dalilin hakan, ya karasa kusa da 


ita ya xauna gefenta yace "Baxan kai ki inda xa kiyi kuka yau ba, sai dai kiyi na farin ciki wife" ta turo baki kamar xata yi kuka tace "Ni ko daya bana so, 


am going no where..." ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "xa ki so wannan in sha Allah ummu Shureim, I am giving you 100% assurance"  a hankli tace 


"To xa mu dauko Shureim daga nan?" Kamar jiran tambayar yake ya girgixa kai da sauri yace "Nooo" da mamaki tace "Why?" Murmushi yayi yana kallon kwayar 


idonta yana shafa sajensa a hankali yace "Baxai bari in gwada maki yanda nake son ki ba anjima, he will be a barrier..." Wani kallo ta dinga masa tace "Ni 


dai yau yarona xai dawo, ba ruwana" Yar dariya yayi yace "Inaa sai na gama tabbatar maki da soyayyata anjima.." daga haka ya mike ya nufi kofa yace "Am 


waiting for you downstairs Iman, don nasan baxa ki shirya gabana ba" yana fadin haka ya juyo ya kalleta ya kashe mata ido ta bi sa da ido har ya fita, Aliyu 


yana ta xaune parlor yana jiran ta, message ya shigo wayarsa, dauka yayi ya bude yana duba address din da Dr Ayman ya turo masa, ajiye wayar yayi ya 


jinginar da kansa jikin kujera, shi kam har sannan ya kasa daina mamakin khadijah, he couldn't believe it, bai taba xaton xata hakura ta sauko da wuri ba 


haka har ta kulasa duk da maganganun Anty khadijah, he never expect that from her, murmushi kawai yyi tunawa da yayi kilan yana cin albarkacin yaransu ne 


that she is seeing in him, but he will surely teach her to love him not because of the kids, sakkowa tayi stairs sanye da hijab har kasa babu abinda ta 


shafa fuskarta banda powder sai chappete a lips dinta amma har wani glowing take, she is just the definition of true beauty, ya mike yana murmushi a hankali 


yace "Kin yi kyau wife" sauke idonta tayi har ta iso parlorn, ya isa har gabanta ya duka yayi pecking lips dinta a hankali, ta hade rai tana goge bakin tace 


"Bana so" yana murmushi yace "Toh yi hakuri na bari" daga haka ya kama hannunta suka fita, sai da suka bar gidan a motarsa suka hau saman titi tana kallonsa 


a hankali tace "Ina xa mu je plss Aliyu?" Kallonta yayi na few seconds sannan ya dauke kai, murya can kasa yace "Yanxu baki jin kunyan kiran sunana Iman?" 


Ta hade rai tace "Toh me xan kira ka?" Ya langwabar da kai yace "Sai ki sakaya even because of Shureim, though nasan I don't deserve that" jikinta ne yyi 


sanyi ta tuna yanda take kiransa seven years back, a hankali ta kallesa taga driving dinsa kawai yake ta sauke idonta tace "Toh xan ce maka Yayan Baby" 


murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba kuma bai kalleta ba, bayan wani lkci yace "Ohk then" sun fi 10 mins babu wanda yace komai tayi breaking silence 


din, ba don shirun dake motar ba da ba lallai ma yaji abinda tace ba coz it's very low, "Or Abu Shureim" abinda ta fada kenan sai kuma ta dauke kai kamar ba 


ita ta fada ba. 



Kinda very busy yesterday shi sa aka ji shiru, sorry for the short update, ltr xan yi wani in sha Allah. Tnx for understanding.🤗


Murmushi kawai Aliyu yayi bai ce komai ba, ya dau wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne tare da yin sallama yace "Muna hanya Dr, soon xa mu iso" ajiye 


wayar yayi, yana maida hankalinsa gaba daya kan driving da yake, bayan tafiya mai tsawo suka shigo wani anguwa, yayi parking dai dai wani gida, kalle kallen 


anguwar yake to make sure address din da aka turo masa daxu ne, ya dau wayarsa ya bude yana kallon number gidan, tada motar yayi yana driving a hankali har 


ya isa wani babban gida yayi parking, khadijah da ke ta kallonsa tace "Baka ma san inda xa mu ba kenan" ya kalleta ya wara manyan idonsa yana murmushi yace 


"Na sani mana, ba gashi mun xo ba" Dialing number Dr Ayman yayi yace "Ga mu a waje" Ba a dau lkci ba Khaleel ya fito daga babban gidan, duk a tunanin 


khadijah gidansa suka xo, Ya bude side din Aliyu ya basa hannu suka gaisa yana kallon khadijah yace "Good morning Madam" d'an murmushi tayi a hankali tace 


"Ina kwana Doctor" yace "Lafiya lau ya gida" tace "Alhmdllh" yana kallon Aliyu yace "Alryt, ku shiga ciki ni ana jirana xan wuce yanxu, sai na dawo anjima" 


Aliyu ya fito daga cikin motar yace "But..." Murmushi Khaleel yayi yace "You don't worry Umma ma na ciki with Shureim" Aliyu yace "Ohk then" Daga haka 


Khaleel ya nufi motarsa dake waje yayi parking, Aliyu ya kalli khadijah yace "Come down Iman" bude motar tayi ta fito tana mamakin me Umma kuma ta xo yi nan 


tare da Shureim, ta xagayo inda yake tace "Where is this please, and why are we here?" Yana shafa kansa yace "Xumunci muka xo..." gate ya nufa ta bi bayansa 


har suka shiga babban gidan, a tare suke tafiyar har suka iso entrance din babban gidan, haka kawai khadijah taji gabanta na faduwa, Aliyu ya juya yana 


kallonta ya sakar mata murmushi yace "Gidan ku ne nan Iman, gidan yayar mahaifiyar ki" Wani kallo ta dinga masa tace "Wace mahaifiyar tawa?" Ya sauke idonsa 


yace "Ur late Mum" daga haka ya shiga parlorn da sallama ta bi sa da kallon mamaki, juyawa yayi ganin bata shigo ba tana tsaye bakin kofar yayi kasa da 


murya yace "Come in plss Iman" yana fadin haka ya juya yana kallon mutanen dake xaune parlorn, very many of them, iyaye da yara, da kyar khadijah ta iya 


daga kafa ta shiga parlorn abinda ya fada na sinking kanta, Wai yayar mahaifiyar ta, how is that bayan ko Umma ma bata san dangin mum dinta ba? Kan jawahir 


dake xaune kasa kusa da Mahaifiyarta idonta ya fara sauka, Jawahir ta yi saurin sauke idonta kasa, Khadijah ta dinga bin mutanen dake xaune parlorn da kallo 


har idonta ya sauka kan Umma, Shureim dake jikin wani dattijon mutum ya taho da gudu ya rungume ta yana murmushi yace "Antyna" buda ido khadijah tayi ganin 


Safeenah da su Deejah, Safeenah ta mike da sauri ta iso inda khadijah take tana murmushi ta rungumeta hawaye cike idonta tace "Welcome sister" murmushi 


kawai khadijah ta iya yi bata ce mata komai ba xuciyarta na bugawa, Safeenah ta ja ta har xuwa cikin parlon, bin bayansu Aliyu yayi ya durkusa nan gefen 


wani guy da baxai wuce sa ba ya gaida mutanen dake parlorn, suka amsa duk a sanyaye, gaba daya occupant din parlorn kallon khadijah kawai suke, lkci daya 


Mahaifiyar Jawahir ta fara kuka, jikin khadijah yayi sanyi, ta isa gun Umma ta durkusa, Umma na murmushi a hankali ta kamo hannunta tace "Greet them 


khadijah, iyayen ki ne nan gaba daya xaune parlorn" Hawaye ya cika idon khadijah tana sake kallon mutanen parlorn, Umma tayi kasa da murya tace "Yes 


daughter, they are ur families" mahaifiyar Safeenah ta mike trying hard to control her tears tace "Come over daughter, come to me" mikewa khadijah tayi ta 


nufeta, matar ta rungumeta hawaye na sakko mata tace "Allah ya ji kan Maryam ya yafe mata kura kurenta, you are truly a carbon copy of her daughter... Allah 


ya albarkace ki, mun ji dadi da Allah ya sada mu da ke tun a duniya, it's really sad sai yanxu muke sanin 'yar kanwarmu, jinin kanwar mu, duk da ba laifinmu 


bane ba haka muka so ba, amma there is always a reason behind everything, it's great meeting you daughter" ita dai khadijah bata ce komai ba jikinta yayi 


sanyi sosai, Hajiya Rahmah ta xauna ta xaunar da ita kusa da ita tana share hawayen ta, jawahir dai ta kasa dago kanta ganin yanda mahaifiyar ta ke kuka 


yasa ita ma hawaye ya dinga xuba idonta, sai dai duk kukan mahaifiyar jawahir bai kai na mahaifiyar Maimoon ba immediate din Mum din khadijah, kuka take 


kamar a lokacin taji mutuwar kanwartata, komai ya dawo mata sabo, a karo na farko Alhaji Abbakar mahaifinsu Safeenah kuma babban yayansu late mahaifiyar 


khadijah gaba daya... yyi gyaran murya ya bude wajen da addu'a, yana murmushi yace "Alhamdulillah for the gift of life, Alhmdllh for a day like this, 


Alhmdllh for everything... Sure it's a privilege meeting with our daughter again after so many years..." kallon Khadijah yayi yace "Come over dear" Tashi 


tayi daga kusa da Umman su Safeenah ta dawo kusa da shi a sanyaye ta xauna kasa, da farko kasa cewa komai yayi kuma hakan na da nasaba da kamannin khadijah 


na mahaifiyar ta, bayan wani lkci yayi karfin halin yin murmushi yace "Khadijah kina yar shekara biyu rabon mu dake, sai yanxu bayan shekara ashirin Allah 


ya sake hada mu, kwarai kuwa babu wanda kika sani cikin mu kamar yanda mu ma bamu san ki ba, da xa mu hadu a hanya sai dai ki wuce mu wuce, which is a great 


shame" ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, nuna mata sauran maxan da ke parlorn su kusan uku xaune kusa da shi yayi da wanda yake kan one seater yace 


"Kin ga wa en nan gaba daya" ta daga kai a hankali tana kallonsu gaba daya, yace "Duk iyayen ki ne khadijah, they are all ur parent, and they are all here 


because of you, duk mun bar abubuwan da muke muka taho daga garruwa daban daban domin ki, gaba daya nan da kika ganmu yayyin marigayiya Maryam ne, 


mahaifiyar ki, ke din mai gata ce khadijah, kina da gatan ki" cikin rawar murya tace "Toh me yasa ni ban san ku ba, me yasa ba a nuna min ku ba, me yasa ba 


ku nemeni ba" tana fadin haka ta hade kai da kujera tana kuka sosai, Ya dafata cikin sanyi yace "Mahaifin ki Allah ya masa rahama shi ya raba mu da ke tun 


bayan rasuwar mahaifiyar ki khadijah, mun so rike ki ganin ba shi da yan uwa mata, amma sai yayi tunanin rabasa da ke muke son yi, Allah ya gafarta masa, 


mun samu matsala a kan hakan da shi, which contributed to his keeping u away from us for many years, a Abuja suka xauna da mahaifiyar ki, bayan rasuwar ta 


ne ya siyar da gidansa na Abuja ya dawo kano without even our knowledge, kin ji dalilin da yasa baki san mu ba khadijah, Kuma da mun san inda familyn 


mahaifin ki suke da babu abinda xai hana mu xuwa gare ki, sai dai yau ta dalilin mijin jawahir mun yi reuniting da ke...." Khadijah bata dago kanta ba 


hawaye na ta xuba idonta, Alhaji Usman yace "Wannan baiwar Allah da ta rike ki bisa amana tamkar yar da ta haifa cikinta Allah ya saka mata da gidan 


aljanna.... Mun ji duk kalubalen da kika fuskanta a rayuwa saboda maraici, bayin Allahn da suka tsaya maki through all the hardship Allah ya biya su da 


aljanna, it's really sad daughter, don kina da gatan ki, Amma ba komai haka Allah ya kaddara, Allah ya jin kan iyayen ki ya gafarta masa, ya kuma raya maki 


yaron ki, ya albarkace auren ki.... In sha Allah gatan da baki samu ba da yarintar ki xaki samu da girman ki, we will always be there for you daughter, uwar 


mu daya ubanmu daya da Mahaifiyar ki... Allah ya ji kanta" Khadijah ta dago tana share idonta a hankali tace "Ameen, nagode Abba" Gaba daya sai da aka mata 


introducing din cousins dinta da niece a parlorn, yawanci duk suna yanayi barin da matan, Safeenah da Maimoon kuwa kamanninsu ba a magana dama, har sannan 


Jawahir ta ki dago kanta daga karshe ma wucewa sama tayi, it was really a happy day for Khadijah jin ta cikin yan uwanta gaba daya, kuma a ranan ta fara 


ganin hoton mahaifiyar ta, bata taba sanin haka relatives ke da dadi ba sai ranan, da tun farko tasan da su tasan baxata wahala a rayuwa ba but that's her 


fate and she is happy with it, Aliyu bai jima gidan ba ya wuce ya bar ta, Umma kuma sai kusan azahar ta wuce ta bar Shureim ma gidan, Khadijah na daki tare 


da su Safeenah da deeja dake ta labari tayi tagumi tana kallonsu tana murmushi jawahir ta shigo dakin, suna hada ido ta sunkuyar da kai a hankali tace 


"Khadijah ki xo ku gaisa da Doctor xa mu wuce yanxu" Mikewa khadijah tayi tace "Toh" ta dau hijab tace ma su Safeenah tana xuwa sannan ta fita, Dr Ayman na 


xaune parlor tare da Shureim dake jikinsa ta shigo tana kallonsa murmushi dauke fuskarta tace "Ina yini Doctor" murmushin ya mayar mata yace "Alhmdllh 


khadijah" ta isa har gefensa ta xauna a kasa tana kallonsa cikin sanyi tace "I am very happy for ur effort in uniting me with my relatives doctor, Allah ya 


saka da alkhairi, I will never forget you in my life..." Kasa ci gaba tayi ta sunkuyar da kai hawaye na sakko mata, ya dinga kallonta a sanyaye, ta dago da 


kyar bayan ta goge idonta don bata son Shureim ya gani tana dubansa tace "This is among the greatest thing that have ever happened too me doctor, I really 


owe both you and Barrister, Kun haskaka min rayuwata kun taimakeni a lokacin da nake bukatan hakan, I don't know how to pay you both" ya d'an yi murmushi 


yace "May be that was why God brought you into my life, just to unite you with ur late mum's family, There is always a reason for everything you knw... Don 


haka kawai ki gode Allah ba ni ba" Kai ta gyada masa tana share hawayen da ya ki tsaya mata, ita dai jawahir na tsaye gefe a sanyaye bata ce komai ba, yace 


"Amma nan xaki kwana yau koh" A hankali tace "Ban sani ba tukun" yace "Alryt then, mu xa mu koma yanxu, and in sha Allah gobe xa mu koma Uk" ta kallesa a 


sanyaye tace "Toh Allah ya kai ku lafiya" mikewa yayi ya daga Shureim dake kallo yace "Sweetheart xa mu tafi yanxu je wajen Anty" ya bata fuska yace "Uncle 


ni xan bika plss" jawosa khadijah tayi tace "A'a xa su je da nisa" kuka ya fara yi ya koma gun Khaleel yace "Uncle plss" sai a sannan jawahir tace "Mu tafi 


da shi mana don Allah" Khaleel ya kalleta sannan ya kalli khadijah yace "Can we?" Shiru ta d'an yi sai Kuma a hankali tace "But his..." Sai kuma tayi shiru, 


Khaleel na murmushi yace "His dad bai sani ba koh?" kasa cewa komai tayi kuma bata dago ba, yace "Toh kira sa ki gaya masa nasan baxai hana ba" ba musu ta 


dau wayarta dake jikinta ta shiga kiran Aliyu, bayan wani lkci ya daga yace "Iman..." Tace "Wai Dr Ayman xa su tafi da shureim can they?" Murmushi Aliyu 


yayi yace "Sure" tace "Toh" daga haka ta katse wayar tana kallon Khaleel tace "Yace toh" Murmushi Khaleel yayi yace "Alryt then, sai mun hade a uk, sai ki 


gaya ma grandparents dinsa mun tafi da shi, I mean all his grannies cos he have a lot..." daga haka ya dau Shureim dake murmushi yana daga mata hannu suka 


fita da jawahir dake bin su a baya don ta sallami iyayenta, khadijah ta bi su da kallo har suka fita, kafin tayi murmushi ta mike a hankali ta wuce 


sama.....


Daren ranan a gidan khadijah ta kwana don Aliyu bai takura ta sai sun koma gida ba shi dai yayi wucewarsa, washegari yayyin mahaifiyar ta maxa duk suka wuce 


bayan sun cika ta da kyautan kudi mai yawa tunda basu samu sun mata komai na aure ba, Su Safeenah basu yarda sun bi iyayen nasu ba wai sai sun je gidan 


khadijah, Hajiya Rahamah tace "Gaskiya kam ya kamata ku je sai ku dawo anjima da yamma" Khadijah taji dadi sosai tace "Umma don Allah su kwana mana" Mum 


dinsu Jawahir tace "A'a su dai dawo da yamma" ta marairaice tace "Toh sai mu dawo tare" Hajiya Rahamah tace "Ki dawo kiyi me khadijah, ina kika taba jin 


amarya na yawo daga kai ta dakinta, wannan ma ai lalura yasa kika fito..." shiru khadijah tayi bata ce komai ba jikinta yayi sanyi, Driver aka sa ya maida 


su can gidan nata, Mum din Jawahir tace "Sai ki fara kiran mijin naki ki sanar da shi xuwan ku" a hankali khadijah tace "Toh..." Daga haka ta mike ta tafi 


daki ta dau wayarta, kiran Aliyu ta shiga yi, yana dagawa yayi sallama yace "Good morning wife" ta turo baki tace "Xa mu dawo gida yanxu da su Safeenah" 


yace "Ohk, in taho in dauke ku ne?" Tace "A'a driver xai maido mu" yace "Alryt then, Allah ya kawo ku lafiya, am already missing you dear" Bata ce komai ba 


ta katse wayar ta, Sha biyu saura suka dau hanyar gida tare da Safeenah, Deejah da Maimoon, a waje drivern yayi park duk suka sauka motar suka masa godiya, 


khadijah ta bude gate din tana gaida mai gadi dake gaisheta shi ma, sauran duk suka gaisa da shi sannan suka bi bayanta, a hankali ta murda kofar parlorn, 


Babu kowa ciki sai sanyin ac da tv dake a kunne, ta shiga su Safeenah na biye da ita har cikin parlon duk suka xaxxauna, tana murmushi tace "Bari in kawo 


maku ruwa" Bata jira cewarsu ba ta wuce Kitchen ta dauko tray da cups ta bude fridge ta daura lemo da ruwa a kan tray din ta dawo ta ajiye masu, Safeenah na 


murmushi tace "Thanks sis" murmushin tayi ita ma ta wuce sama, a hankali ta bude kofar bedroom din Aliyu, xaune ta samesa yana operating laptop, ta hade rai 


tace "Baxa ka taho ku gaisa da su ba" ajiye laptop din yayi yana murmushi yace "I was waiting for ur instruction ne dama kar in yi laifi" hararansa tayi ta 


juya ta wuce, yana murmushi ya mike ya bi bayanta, har ya shigo parlorn yana kallon su Safeenah yace "Sannun ku da xuwa" duk suka gaishesa da fara'a, ya 


xauna saman kujera yana murmushi yace "Lafiya lau, fatan kun baro mutan gida lafiya" duk suka ce "Alhmdllh" yace "Maa sha Allah" sannan ya mike yana kallon 


khadijah ya koma sama, mikewa tayi tace "Mu je sama ku yi alwala it's almost time for zuhr" tashi suka yi gaba daya suka wuce sama xuwa dakinta, sai bayan 


da suka idar ta cire hijab dinta tace "Let me cook something for us" mikewa suka yi gaba daya Safeenah tace "We will do that together" dariya kawai khadijah 


tayi, tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup suka hada gaba daya, aikin yayi sauri saboda yawansu, Safeenah na gama kwashe tuwon a leda tace "Toh ina xa a sa 


ma mijin ki" khadijah tace "It's not necessary, namu ne kadai, nasan eatry xai je shi" Deejah ta saki baki tana kallonta tace "Eatry kuma Namecy?" Murmushi 


kawai khadijah tayi, Maimoon tace "Uhmm lallai ma, tun yanxu xa ki fara sakaci haka Khadijah?? Har kina son mijin ki ya tafi wani waje ya ci abinci" 


Kallonta khadijah tayi bata ce komai ba, Safeenah ta dauko wani kwali mai dauke da cooler mai kyau ta fiddo babba da karami ta tafi sink ta wanke shi tas ta 


tsane sannan ta sa tuwo ta rufe, Deejah ta dau na miyan ta xuba miya da isasshen nama a ciki ta rufe duk suka daura a tray, ita dai khadijah na tsaye tana 


kallonsu kamar an dasa ta, Maimoon ta dauko plate mai kyau da spoon da cup ta dauraye ta daura kan tray din, Safeenah ce ta hada xobon dake ajiye tun daxu 


suna jiran ya huce, xobon ya ji kayan kamshi da abarba da cucumber, ta xuba kananun kankara kan thick xobon, sabon jug ta dauko ta kusa cika jug din ta 


rufe, tana kallon khadijah tace "Sai ki kai masa daki, ko shi ma waitress din eatry xa su maki??" Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba sai dai bata ce 


komai ba ta dau tray din abincin da drink ta fita kitchen din ta wuce sama, a hankali ta tura kofar dakinsa, yana xaune yana danna laptop har sannan, ya 


dago yana kallonta har ta iso inda yake ta durkusa ta ajiye tray din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, yayi 


murmushi sanin this might not be her thinking, infact it's not even her thinking... Khadijah ce xata kawo masa abinci haka kawai, shafa kai yyi yana 


murmushi. Kafin ta koma kitchen din duk sun wanke duk abubuwan da suka bata, Maimoon ta fito masu da abincin nan tsakiyar parlor, Xaunawa suka yi gaba daya 


suka ci a tare, Deejah ta gyara wajen ta tafi da komai kitchen, suna ta xaune parlor suna hira khadijah ta dinga jin kamar kar su ce xasu tafi, ta dinga 


addu'ar Allah sa su manta kawai su kwana, suna nan a haka har aka kira la'asar suka wuce sama xuwa dakinta duk suka yi sallah, sai a sannan suka fara shirin 


komawa gida, duk jikin khadijah yayi sanyi ta xauna can karshen gado tana kallonsu a sanyaye, Dariya Deejah ta dinga mata, Safeenah na gama gyara fuskarta 


ta dawo kusa da ita tace "Kar ki damu sis xa mu dinga haduwa frequently in sha Allah kin ji, Kuma ga waya xa mu dinga communicating" hawaye ne ya cika idon 


khadijah, Safeenah tayi dariya tace "Tabb, to mu fa gobe da safe xa mu koma Abuja, Deejah kadai ce a nan, kema nasan soon xa ki koma uk saboda karatun ki" 


Ita dai khadijah bata ce komai ba, bayan duk sun gama Safeenah tace "I notice something khadijah, it seems har yanxu baki kwantar da hankalin ki da mijin ki 


ba, are you still thinking of the past koh? I will advice you to just erase that of ur mind idan ba haka ba baxa ki taba samun kwanciyar hankali gidan ki 


ba, nobody is above mistake khadijah, barin ma irin wannan mistake din da aka yi ba da gangan ba, wllh idan baki maida hankali kin rungumi mijin ki ba kina 


ji kina gani wata a waje xata yi hakan ga mijin ki very handsome gentleman, Wallahi Kar ki kuskura wata ta hango maki shi a waje, don rashin samun kulawa 


gun ki xai sa ya ba ta waje dama, Haba sai kace ba wayayya ba Khadijah..." turo baki khadijah tayi, Safeenah ta dawo kusa da ita ta kamo hannunta tace 


"that's just it, kiyi hakuri ki xauna xuciya daya da mijin ki, forget the past, ni na tabbatar mijin ki yana son ki kema kuma kina son sa sosai" Khadijah ta 


sauke idonta a hankali, Maganganu sosai Safeenah ta yi mata da yasa duk jikinta yayi sanyi, daga karshe ta mike tace "Toh mu xa mu tafi khadijah sai mun yi 


waya" khadijah ta mike a hankali tace "Bari in gaya masa" daga haka ta fita ta shiga dakin Aliyu suka kusa cin karo don fitowa xai yi shi ma daga dakin, 


jawota yayi jikinsa ya rufe kofar yana kallon eye balls dinta, ta sauke idonta tace "Sake ni" ba musu ya saketa yana murmushi, tace "Xa su wuce" yace "I was 


thinking kwana xa su yi" ta girgixa kai tace "Gobe da safe xa su wuce Abuja" yace "Ohk ba nan suke ba dama?" Tace "Deejah ce kadai a nan" yace "Alryt am 


coming now" juyawa tayi ta fita, turarruka da kayan kwalliya na lefenta ta debar masu mai yawa suka sauka downstairs tana jin kewansu, ba a dau lkci ba 


Aliyu ya sauko, dubu talatin ya ba su gaba daya, suka ki amsa, khadijah ta hade rai ta karbi kudin hannunsa ta bude jakar Deejah tace "Ae ba ku kuka ce ya 


baku ba toh" Murmushi kawai Aliyu yake yana kallonta, suka masa godiya yace "No thanks sisters, or shud I drop you?" Safeenah tace "A'a mun gode xa mu tadda 


driver bakin titi" yace "Alryt then, Allah ya kiyaye hanya" duk suka amsa masa da Amin, har bakin gate khadijah ta rakasu, Maimoon tace "Kin ga ki koma haka 


mun gode sosai Khadijah, Allah bar xumunci" sai a sannan hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "I am going to miss you all" rungume juna suka yi 


gaba daya, tana ji tana gani suka wuce ta juyo ta koma ciki tana goge hawayen dake xuba mata, Aliyu dake parlor ya dinga kallonta har ta wuce sama. Ko minti 


talatin su Safeenah basu yi da barin gidan ba Barrister ya xo, Aliyu ya bude masa kofa suka gaisa, Barrister ya xauna kan kujera yace "Ya gidan" Aliyu na 


shafa kai ya xauna shi ma yace "Alhmdllh, ya aiki" Barrister yace "Mun gode Allah, ya mum shureim" Mikewa Aliyu yayi yace "She's upstairs" daga haka ya wuce 


sama, bude kofar dakinta yayi ya ganta kwance ta rufe fuskarta da pillow, ya isa kan gadon ya xauna kusa da ita ya dagota a hankali yace "Ummu Shureim" Bude 


ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi yace "Mu je ku gaisa da Barrister" tace "Ya xo?" Yace "Sure" shi ya taimaka mata ta sauko saman 


gadon bayan ta sauko ta kwace hannunta shi dai bai ce komai ba ta sa hijab dinta suka fita dakin, gaisawa suka yi da Sudais ya mika ma Aliyu takardan 


hannunsa yace "Bata ta gani, I don't want to do anything without her knowledge" Aliyu ya amsa ya mika mata, karban takardan tayi ta bude tana kallon content 


din, bayan wani lkci ta Dago a sanyaye tana kallonsa, murmushi yayi yace "Is that okay?" Girgixa masa kai tayi a hankali tace "Barrister ka kyalesa kawai, 


na yafe masa even for the sake of my dad" Karban takardan Aliyu yyi yana dubawa, Barrister na kallonta yace "Are sure Amira?" Kai ta gyada masa tana 


murmushi tace "Sure Barrister, na yafe ma kawu na, sai dai kuma tsakaninsa da mahaliccin sa" mikewa Barrister yayi yace "Toh Alhmdllh, Allah ya yafe mana 


gaba daya, but I don't think ur forgiveness will count, coz dukiyar marayu yyi tampering da" Aliyu na gyada Kai yace "Haka ne" Barrister yace "Alryt xan 


koma, abinda ya kawo ni kenan dama" tace "Toh nagode sosai Barrister, bari in kawo maka ruwa" yace "Noo Amira, am okay" Tare suka fita da Aliyu, a sanyaye 


ta wuce sama don ita da gaske take jin ta yafe ma kawun ta. Gyara bedroom dinta tayi ta share ta goge ko ina, ta fito dakin kenan taga Aliyu ma ya fito rike 


da tray din abincin da ta kai masa da rana, karasawa tayi ta amsa tray din hannunsa, yana kallonta yace "Thank you" bata ce komai ba ta sauka downstairs ta 


wuce Kitchen. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da magrib ya shigo dakin ya xauna gefen gado yace "Mu je ki raka ni" tace "Ina?" Yace "Gida, xan dauko 


wasu files a can" ta girgixa kai tace "A'a baxan fita ba, ni...." Ya katse ta yace "Ba fa shiga gidan xa ki yi ba" tace "Eh na sani" ya marairaice yace 


"Plss Ummu Shureim" turo baki tayi kamar xata yi kuka, yayi murmushi ya mike yace "Am waiting for you downstairs" A hankali ta mike ta linke pray mat din ta 


fita dakin, a kofar gidansu yayi parking yana kallonta yace "Baxan dade ba xan fito yanxu" kasa cewa komai tayi don sai take ga kamar bai dace ta ki shiga 


ba, can dai tace "Bari in gaida mumy" yace "Noo, ki bari ran Sunday sai mu xo gaisheta, it's already late yanxu" kallonsa ta tsaya yi, ya gyada kai yace 


"Yea dear" daga haka ya juya ya wuce ciki, kamar yanda ya fada bai dade ba ya fito ya ajiye takardun bayan mota sannan ya shiga maxaunin driver suka bar 


layin, yace "Me kike son ci in siya maki" ta girgixa kai tace "I am not hungry" yace "Nasan bakya Jin yunwa... abun dadi nake nufi" tace "Baxan ci komai ba" 


ya kamo hannunta yace "A'a, gwara dai a siya maki ko kaxa ce koh?" tace "Ni nace maka bana ci" parking yayi gun da ake siyar da kaji yace "Ai baki isa ba.." 


Daga haka ya fita ya siyo masu guda biyu, ya bude bayan mota ya ajiye, yana kallonta yace "Fresh milk kike so ko youghurt?" Tace "Daxu fa na ci abinci me 


xanyi da yoghurt ko fresh milk" Yar dariya yayi yace "Toh naji ni xan siya in sha" gun da ake siyarwa ya kara parking ya fita ya siyo chill fresh milk ya 


bude back seat ya ajiye sannan suka dau hanyar gida, da kyar khadijah ta yarda ta xauna parlor tana bata fuska, ta dinga kallon kajin da ya ajiye gabanta 


sai kamshi yake ga Madara a glass cup a gefe, so mouth watering, a hankali ta kai hannu ta dau cinyar kaxa daya tace "Ni wannan ya isheni" ya kalleta bai ce 


komai ba ya dau naman shi ma ya kai bakinsa, satan kallonsa tayi bayan ta cinye na hannunta don sosai naman yayi mata dadi, ta turo baki tace "Ashe ma da 


dadi" ya danne dariyar sa ko kallonta bai yi ba, ta dau wani kaxan ta fara ci, a haka sai da ta kusa cin rabin wanda ya ajiye mata, ta dau madaran glass cup 


din ta shanye gaba daya, sai a sannan ya dago yana dubanta yace "Amma da muka shigo ne kika fara jin yunwan koh?" Mikewa tayi da sauri ta wuce sama tace 


"Nima ban sani ba" Murmushi yayi ya bi ta da kallo kamar yanda ita ma take murmushin ta wuce sama, cire kayan jikinta tayi ta linke ta ajiye sannan ta shiga 


bathroom, wanke bakinta tayi, tayi wankan ta fito, Bata wani jima sosai gaban mirror ba, ta feshe jikinta da turarruka kala kala ta dau kayan baccinta ta 


sa, sannan ta sa net a dogon gashinta ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta kwanta ta ja duvet ta rufe jikinta ta lumshe ido. Har kusan karfe sha daya 


ta kasa bacci sabida thirst da take ta ji, ta tashi daga karshe ta sauka kan gadon, ta nufi kofa ta bude a hankali ta fito tana kallon kofar dakinsa dake a 


rufe, sauka downstairs tayi taga wutan parlorn gaba daya a kashe har kitchen, kunna wutan parlorn tayi ta nufi kitchen ta shiga tana kokarin kunna switch 


taji an cafkota, ihu ta fasa a mugun tsorace, ya kunna wutan da sauri ganin da gaske ta tsorata ya rungumeta yace "I am sorry iman, I didn't mean to scare 


the life out of you, wasa nake maki, kiyi hakuri plss" hawaye ya dinga xuba idonta jikinta na bari xuciyarta na bugawa, tausayinta yaji ganin da gaske ta 


tsorata, ya kasa karasa sauran coffeen da ya rage cup din hannunsa ya ajiye, yana rike da ita ya kashe wutan suka fito yace "I heard ur footsteps shi yasa 


na kashe wutan, am sorry for scaring you..." ita dai bata ce komai ba har lkcn xuciyarta bai dawo dai dai ba, suna isa stairs ya juyo da sauri yana kallonta 


yace "Me kika sakko yi" cikin sanyin murya tace "Ruwa xan sha" saketa yayi don xuwa ya dauko mata ruwan ta bi bayansa, yayi murmushi ya bude fridge ya fiddo 


ruwa ya xuba mata a cup ya mika mata ta amsa ta sha ya karbi cup din ya ajiye, yana rike da ita suka wuce sama bude dakinsa yayi xata kwace hannunta ta wuce 


nata dakin ya ki saketa ya jawota dakinsa ya rufe kofar, sanyi ne sosai a dakin saboda Ac da ya kure ga fitila kuma a kashe, xata bude kofa ta fita ya 


riketa murya can kasa yace "Kin san har yanxu ba muyi sallah mun nuna godiya ga Allah.. mu yi addu'ar xaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa ba Iman?" 


Da sauri tace "Ni dai nayi, Kai ne dai baka yi ba" yace "Noo kamata yayi muyi tare" tace "I am not clean...." Kallonta ya dinga yi cikin duhun yace 


"Really??" gabanta na faduwa tace "Ehh" yace "Ban yarda ba" ta hade rai tace "Saboda ni makaryaciya ce?" Yar dariya yayi taji ya dauketa cak sai saman gado, 


ya kwantar da ita yace "I have to check for my self..." Kara tayi a rikice tace "Nashiga uku, don..." Bai bari ta karasa ba ya rufe bakinta, tun tana turasa 


tana son kwace kanta har ta gaji, lkci daya kuma jikinta ya mutu, kwata kwata Aliyu bai bata breathing space ba, ya dinga exploring dinta as if his life 


depend on that... daga karshe ta sakar masa jiki gaba daya, sai dai bakinta bai daina cewa stop it plss idan ma ba kasa kunne kayi sosai ba baxa ka ji me 


take cewa ba, lkci daya ta rikice masa ganin ba da wasa yake ba, nan ta fara hawaye tana rokonsa, sai take ganin abun kamar na 7 years back, the only 


difference is that he is not fierce, just romantic and very careful, upon her plea bai iya ya kyaleta ba duk da yayi kokarin ganin yayi hakan amma ya 


kasa.... Bayan lokaci me tsawo ya dago a hankali ya ga bata gefensa kamar ynda ya bar ta, mikewa xaune yayi da sauri, shesshekar kukanta ya dinga ji can 


other side of the bed, ya tashi da kyar ya nufi wajen, takurewa tayi waje daya tana kuka a hankali, jikinsa yyi sanyi ya duka gabanta yace "I am very sorry 


Iman, I...." Rasa abinda xae ce mata yyi ya dagota ta fashe da matsanancin kuka, ya rungume ta xuciyarsa na bugawa yace "I didn't mean to hurt you again" 


gaba daya tayi laushi, kuka kawai take, ya dagota ya kwantar kan gadon yace "Kiyi hakuri plss Iman, forgive me...." cikin rawar murya tace "Kace min baxan 


ji xafi ba" Kallonta yake cikin duhun don bai ma san ya fadi hakan ba, ya kwantar da ita kirjinsa a hankali yace "But did you feeling any pain?" Kai ta 


dinga gyada masa hawaye na xubo mata, yayi shiru bayan wani lkci ya kai bakinsa kunnenta yace "Just like the 1st experience?" Girgixa masa kai tayi, Yana 


shafa bayanta yana murmushi sanin da ba dan shi yyi deflower dinta ba da bbu abinda xai hanasa cewa budurwa ce ita, kwantar da ita yayi ya mike ya shiga 


bathroom, ya hada mata ruwan wanka, ya dawo ya kai ta bathroom din, shi ya taimaka tayi wanka tana nonnokewa sannan ya fito tare da ita, babu bata lokaci 


kuma bacci ya dauketa, sai a sannan ya kunna wutan dakin yana kallon bedsheet din gadon, Bai ga abinda yake xato ba, yayi murmushi ya dawo kusa da ita yana 


kallonta yana Kara jin wani mugun sonta na fixgarsa, it's just great being with her, and it's the sweetest thing he have ever imagined, tashi yayi daga 


karshe ya shiga bathroom yayi wanka shi ma ya fito ya shirya sannan ya kashe wutan dakin ya kwanta kusa da ita ta shige jikinsa kamar jira take, ya 


kankameta hade da lumshe ido.



Da asuba khadijah na jin Aliyu ya fita masallaci ta mike xaune a hankali, gabanta ne ya dinga faduwa from experience, duk da dai wannan karan ko ciwon kai 


bata ji ba balle na jiki amma tsoro ne fal xuciyarta, ganin lkci na wucewa ta mike cike da karfin hali, the pain wasn't as much as she was expecting... Ta 


lallaba ta fita dakin ta koma nata ta sa makulli, wanka ta fara yi ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma tana azkar bayan ta idar taji an murda 


kofa, kallon kofar tayi sai dai bata motsa daga inda take ba, a hankali yayi knocking yace "Iman, are you alryt..." Shiru tayi bata ce komai ba, tana ji ya 


bude kofar dakinsa ya shiga, bayan wani lkci ya fito, hade kai tayi da gwiwa jin yana bude kofarta da makulli, bayan ya bude ya tsaya daga bakin kofa yana 


kallonta, a hankali ya karasa dakin ya duka kusa da ita xai dago kanta ta ki yarda, da damuwa yace "Look at me plss Iman, are you okay..." ganin ba yarda 


xata yi ta dago ba ya mike ya dagota, ihu ta fasa masa ta boye fuskarta jikinsa tace "Ni dai bana soo" Dariya ta basa yana rungume da ita yace "Meye baki so 


Ummu Shureim" a hankali tace "Ka fita" murya can kasa yace "Kunya ta kike ji?" Kai ta gyada masa a hankali, sosai ta basa dariya ya nufi gadonta da ita, ya 


kwantar da ita ta rufe fuskarta da pillow, Xaunawa yayi gefenta yana murmushi yace "Sai ma mun yi wanka tare anjima xaki san meye kunya" Bata san lokacin da 


ta dago ba ta xaro ido tana kallonsa tace "What???" Sai kuma ta maida kanta da sauri tana murmushi wai ita kunya.... Wani salon soyayya na daban Aliyu ya 


dinga gwada ma Iman kamar xai maida ta ciki, ko da yaushe suna manne da juna, Khadijah bata taba tunanin haka Aliyu yake ba shi da kunya ko na taro ba, idan 


aka ce mata xai iya abinda yake mata baxata yarda ba, coz he look so innocent in the face, tun tana kunya tana noke masa har daga karshe tayi give up ita ma 


a gidan ta sakar masa kanta, gida ya koma kamar na India, kunyan da take ma da daddare shi ma duk ta ajiye sa gefe amma fa cikin duhu, ita kanta bata taba 


sanin tana da soft spot ma Aliyu ba sai a yanxu, har ranta take jin sa, sannan ko na minti daya bata son ya bar ta duk inda xa su tare suke xuwa. Ranan da 


suka cika sati biyu gidan tana kwance jikinsa a parlor yana operating laptop, a hankali tace "Abban shureim..." Yana kallonta yayi pecking cheeks dinta yace 


"Ummu Shureim" ta turo baki tace "kaga mun koma makaranta fa" yace "I thought as much, dama in two days time xa mu koma can ai" Tace "Toh Allah ya kai mu" 


yana shafa fuskarta yace "Ameen baby" a ranan suka tafi yi ma Mumy sallama da yamma, Khadijah na xaune tare da Baby a dakinta taga Barrister ya kirata yayi 


sau uku, ita dai bata ce mata komai ba, amma sai suka bata dariya, karfe biyar saura suka shiga dakin Mumy xa su mata sallama don har gidan Umma da umman su 


jawahir xa su je, Mumy tace "Toh Allah ya kai ku lafiya, ya kiyaye hanya" Khadijah dake durkushe kusa da ita tace "Ameen Mumy" Mumy tace "Toh sai kun dawo 


biki nan da few months" Aliyu yace "Wani bikin Mumy" sai da Mumy ta fara dariya sannan tace "Na kanwar ka mana" Khadijah tace "Mumy baby?" Mumy tace "Ehh" 


xaro ido tayi tace "Lahh Mumy ba mu sani ba" Aliyu ya xauna yace "Mumy da Ahmad din?" Mumy tayi murmushi tace "Wannan bada ta kawai Abban ku yayi, ba Ahmad 


bane, an basa hakuri shi" Aliyu ya d'an hade rai yace "Bada ta kuma? To who?" Mumy tace "Barrister Aliyu" da khadijah ta fara dariya sai da Mumy da Aliyu 


suka tsaya kallonta, ta mike da sauri ta fita xuwa dakin baby tace "Wato abun har da munafurci koh Baby, ni din ne baxa ki gaya ma ba koh?" Baby tayi 


murmushi don tasan kwanan xancen, a hankali tace "Shi yace ba sai na gaya maki ba, xai je har gida as a mother ya same ki ya gaya maki" khadijah na murmushi 


tace "Am soo happy wllh, Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin lafiya" Har bakin mota baby ta raka su, suka wuce gidan Umma, bayan Umma sun gaisa da 


Aliyu ta bi bayan khadijah da ta wuce ciki, Ganin yanda tayi kyau ta cicciko Ummu tayi murmushi tace "Ko ke fa da kika kwantar da hankalin ki daughter" 


murmushi kawai khadijah tayi ta sunkuyar da kanta, Umma ta xauna kusa da ita tace "In ji dai ba matsala?" Khadijah tace "Babu Umma dama sallama muka xo maki 


xa mu tafi can Uk" Umma tace "Maa Sha Allah, ai hutun ya kare, Allah ya kai ku lafiya my daughter" Khadijah tace "Ameen Ummata" Umma tace "Amma ku je har 


Umman su jawahir ku yi mata sallama" khadijah tace "Eh dama xa mu je Umma" Umma tace "Toh hakan na da kyau, kin san kawun ki yana yawan kira mu gaisa" 


Khadijah ta kalleta da sauri tace "Abbansu Safeenah?" Umma tace "A'a ba shi ba, mai bi masa" xaro ido khadijah tayi sai kuma tayi dariya tace "Umma Abban su 


Maimoon ne, dama umman su ta rasu 3 years back suka gaya min" Umma tace "Toh ya aka yi don Umman su ta rasu, Allah ya ji kanta" Dariya kawai khadijah take, 


Umma dai sai kallonta take, can ta turo baki tace "Umma ni dai don Allah kar ki ce masa A'a" buda ido Umma tayi, sai tayi dariya tace "Amma baki da kunya 


yarinyar nan" Khadijah ta mike ta fita tana dariya, minti talatin suka yi a gidan, xa su wuce umma ta ja khadijah xuwa daki tace "Daughter, ya kamata ku je 


can katsina da Aliyu ki gaida yayan Mahaifin ki" shiru khadijah tayi da farko, sai kuma a hankali tace "Toh Umma xa mu je" Umma tace "Good, Allah ya kiyaye 


hanya, ki kula da mijin ki fiye da yanda xa ki iya, ki kuma rike tsaftar ki don nasan kina da ita, Allah ya maki albarka" khadijah na murmushi tace "Ameen 


Umma" da haka suka bar gidan suka dau hanyar gidansu jawahir, can ma basu dade ba bayan sun yi ma Umman jawahir sallama suka koma gida. Da daddare ganin 


Aliyu xai takurata ta dinga turo baki tana kwace kanta jikinsa, ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Baki son mu tafi da babynmu daga nan Iman" ta 


marairaice masa tace "Ni dai ka kyaleni bacci nake ji" yace "Plss" kukan shagwaba ta fara masa wanda hakan ya rikita sa, bai kyaleta ba sai da yaga ta fara 


bacci da gaske, ya fi awa daya kankame da ita, ko da yaushe jin abarsa yake intact, murmushi yayi ya manna mata kiss a lips daga karshe ya kwantar da ita ya 


shiga bathroom. Washegari suna breakfast tana kallonsa tace "Abban Shureim, Ina son mu je katsina mu gaida Uncle dina" ya kalleta yace "When, Kin san gobe 


da safe xa mu wuce" Tace "Toh idan mun dawo bikin su baby sai mu je?" Yace "A'a idan kin ce mu je yanxu ma sai mu je ai" ta langwabar da kai a hankali tace 


"Mu je plss" yace "Alryt then" karfe sha daya suka bar gidan, suka dau flight xuwa kano, daga can yayi masu charter na taxi da xai kai su har kt, tun da 


suka shigo kt misalin karfe daya da rabi na rana gaban khadijah ke ta faduwa, taxin ya ajiye su dai dai gidan kawunta, ita kanta tayi mamakin yanda ta gane 


gidan, Aliyu ya fito ita ma ta fito tana kallonsa tace "Mu shiga" Bin bayanta yayi suka shiga gidan, Babu kowa compound din da ya xama wani iri kamar gidan 


da yayi shekara hamsin, Har parlor ta isa da sallama Aliyu ya tsaya daga bayanta, kallon kawun nata dake xaune k'asa a one side of the parlor yana fama da 


ciwon kafa sosai tayi, ta kalli Hajiya maimuna da ta fito kitchen jin sallama ta gaisheta a sanyaye, daga ita har yaran dake parlorn kallonta suka dinga yi 


kamar basu santa ba, ita dai tasan basu gane ta bane, Ta isa har kusa da ita a hankali tace "Mama Khadijah ce" bude baki Hajiya Maimuna tayi tana kallonta 


da wani irin mamaki, Khadijah ta sauke idonta kasa, ba ita ba har kawu Jibril shi ma bude baki yyi lkci daya hanjin cikinsa ya kada don kullum da threat din 


Barrister Sudais yake kwana yake tashi, Aliyu ya xauna kusa da shi yace "Ina yini kawu?" Kawu ya kallesa yana maxurai yace "Lafiya lau daga ina, wa ku ke 


nema" Aliyu yayi kasa da murya yace "Ni ne mijin khadijah, mun xo gaishe ku ne kawai kawu" da sauri yace "Toh madalla... Gaisuwa ce kawai koh" Aliyu ya 


gyada masa kai yace "Eh kawu" khadijah ta karaso har gabansa ta durkusa kanta a kasa tace "Ina yini kawu?" Yace "Lafiya lau" Kai kana ganin yanda yake 


maxurai kasan duk a tsorace yake, Aliyu yayi murmushi yace "Ka kwantar da hankalin ka kawu, xumunci kawai ta sa ni in kawo ta tayi" Yana gyada Kai kamar 


kadangare yace "Madallah" Khadijah dai ta kasa cewa komai, bata taba xaton ganin Kawunta da iyalensa a halin da ta samesu ba, ganin gaba daya mutumin is 


uncomfortable Aliyu yace "Kawu xa mu koma yanxu, don gobe da safe xa mu wuce uk shine tace in kawo ta..." Kawu ya kasa kallon khadijah sai gyada kai yake 


yana cewa Madallah Kamar xararre, Dubu hamsin Aliyu ya ajiye gabansa, Kawu ya dauka yana kallonsa, lkci daya idanuwansa suka kada yace "Maa sha Allah, 


nagode nagode nagode Allah yayi albarka" Aliyu yace "Ameen" a sanyaye Khadijah tace "Allah ya baka lafiya kawu" hawaye ta gani idonsa amma yana ta boyewa 


bai son su gani yace "Toh Amin, sai a yayyafe...." murmushin karfin hali tayi tace "Nima ku yafe min kawu, Allah ya yafe mana baki daya" hatta Maimuna sai 


da tace da khadijah a yayyafe da xasu wuce, ganin bata ga kishiyarta ba tace "Mama Ina mamansu Usman?" Maimuna tace "Ta amshi takardar ta ta wuce kusan 


shekara kenan" khadijah bata ce komai ba duk jikinta yayi sanyi har suka bar gidan xuwa inda xa su samu mota xuwa kano. Sai bayan la'asar suka shigo kano, 


Khadijah sai bata fuska take irin ita ta gaji din nan, ya langwabar da kai yace "Toh ai we still have 3 more hours journey kike bata fuska madam" ta xaro 


ido tana kallonsa tace "Ni dai na gaji wllh" murmushi yayi yace "Just reserve this comment, xa su maki amfani anjima idan mun isa gida da daddare" Kallonsa 


kawai take kamar mai son gane ma'anar abinda yace, can tace "Kamar ya?" instructing din mai adai daitan da ya tsayar masu yyi yace "Airport xa ka kai mu" 


Khadijah ta turo baki ta shiga shima ya shiga yana matsa cinyarta a hankali, tayi kara tana kallonsa, dauke kai yayi da sauri yana murmushi, har suka isa 


airport idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, ya siyar masu tickets na kaduna, hudu da rabi jirgin ya tashi, cikin few minutes suka sauka kaduna. A gajiye 


ta shiga parlor ta wuce dakinta direct ta fada kan gado, bayan kusan minti biyar ya bude kofar dakin yana kallonta yace "Sallahn fa?" Kallonsa tayi a 


hankali tace "Xan yi" yace "Toh tashi kiyi" Sai da ya idar da sllhn shi ma sannan ya fita eatry siyo masu abinci, yana dawowa ya shigo dakinta, xaune ya 


sameta kan darduma yace "Come down mu ci abinci" Tace "Sai na fara wanka" yace "Toh jira ni in xo muyi" mikewa tayi da sauri ta shige bathroom din ta sa 


makulli, yana dariya ya juya ya fita dakin. Karfe goma na dare tana kwance parlor kan 3 seater har bacci ya dauketa taji an dauketa kamar baby, ta bude ido 


a hankali tana kallonsa, ya manna mata kiss a lips dinta ya shiga bedroom dinsa ya kwantar da ita saman gado, ya kwanta shi ma ya shige jikinta... Kamar 


xata yi kuka tace "Bacci fa nake ji" yayi kasa da murya yace "Wai baki son mu tafi da tsaraban baby mai kama da ke UK ne?" Hararansa tayi ta juya masa baya 


tana turo baki, ya marairaice mata yace "Plsss Ummu Shureim" kukan shagwaba ta fara masa as usual, nan ta kara rikitar da shi, ita ma dai kamar jira take ta 


bada kai bori ya hau, they couldn't just get enough of each other, ta kankamesa kamar xata koma jikinsa su xama daya, ya kai bakinsa kunnenta cikin sanyin 


murya yace "I love you Iman..." Shiru tayi idonta a lumshe, bayan wani lokaci ta kwanta kan kirjinsa a hankali tace "I love you more Abu Shureim" kissing 


dinta ya shiga yi, and that really turn her on. Da asuba tare suka yi wanka ya ja su sallah a dakin, a hankali ta dawo kusa da shi ta durkusa murya can kasa 


tace "Good morning Abu Shureim" ya jawota jikinsa yace "Morning Ummu Shureim...." Murmushi tayi tace "I am missing him" yace "You better don't, shi din me 


iyaye ne da yawa, so kar ma ki wani sa shi a rai" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ki hada abubuwan da kika san xa ki bukata, anjima xa mu wuce airport" 


tace "But I have everything back there, a can gidana..." Kallonta ya dinga yi kafin yyi murmushi yace "Kina tunanin xan je gidan ki in xauna wife?" Shiru 


tayi tana kallonsa, yyi yar dariya yace "Lallai, I rather rent a new flat, balle ma muna da apartment can din, kawai I prefer staying a gun aunt dina ne 


saboda kadaici" murmushi tayi bata dai ce komai ba, sai dai ita ma hakan ya mata, coz she don't think xata iya xama gida daya da su Khaleel, it's just not 


possible, lakutan hancinta yyi yace "Kin fi son can ne saboda yar uwar ki" da sauri tace "Not at all, ur wish is my command sir...." Rungume ta yayi yace 


"That's sweet of you baby"


A year and a half later....


Tun da khadijah ta tashi yau take ta girke girke iri iri duk da xaxxabin da ta dinga yi kwana biyu da suka wuce, kana ganinta ka ga mai karamin ciki, yanxun 


ma daurewa take girkin da take yi, don aroma din na hawa mata kai but she have no option, Aliyu ne ya shigo kitchen din yana rungume da little Fatima, 


yarinya da baxata wuce shekara daya da few months ba, she is just a duplicate of her mother, babu inda ta bar khadijah, kyakkyawa ce ta karshe yarinyar, 


Khadijah ta kallesu tace "Dear kasan yanxu xata ce sai na dauketa kuma ni ba taya ni aiki xaka yi ba" Yar dariya yayi yace "Tsoro nake kar in fita da ita 


tayi ta min ihu a mota, xan je airport dauko Umma, same flight kuma suka bi da su Baby" Khadijah tace "Lahh da gaske?" Yace "Sure, Aryan ma ba yarda xai yi 


ya bi ni ba da sai mu tafi tare da su..." Tace "Ae tun daxu na gane gida yake son wucewa ya gaji da mu" dariya Aliyu yyi yace "Aa miskilanci ne kawai, ya ki 


yarda in dauke sa ma" Ta dauraye hannunta ta amshi Noor ta mana masa kiss a lips dinsa tace "Toh Allah ya tsare babyna...." Yace "Uhn you are looking for 


trouble koh" yar dariya tayi ta kashe masa ido tace "Don ma ban maka french one ba" Ya wara ido yace "Toh mu je daki ki min" ta hararesa tace "Naki wayon" 


juyawa yayi ya fita yana murmushi, yau ranan farin ciki ne gareta don a ranan xata sama qualified pharmacist, a ranan xa ayi convocating din su, kafin Aliyu 


su shigo gidan ta gama komai tana jiran Ummarta da yanxu take auren yayan mahaifiyarta wato dad din su Maimoon, tare da Baby uwar gida ga Barrister Sudais, 


fitowa parlor tayi jin shirun Aryan yayi yawa, xaune ta ga little balaraben kan kujera kiris yake jira ya fara kuka, ta karasa gun sa tana murmushi ta ajiye 


Noor, ta daukesa ta rungumesa tace "Haba sweetheart, in dafa maka indomie xaka ci?" Kitchen ta koma tana rike da shi ta daura ruwan indomie sanin abinda 


yake ci kenan, tana tsaye har ya dahu ta juye a plate ta dawo parlor ta xaunar da shi ita ma ta xauna ta shiga basa, Babu inda ya bar ubansa tun daga kyau 


har gashin kansa, hatta idonsa irin na babansa ne, murmushi tayi tana ci gaba da ba sa indomien yana ci, tana gama basa ta wuce daki da shi ta sauya masa 


kayan jikinsa duk da ba su yi komai ba ta dauko masa favourite toy dinsa ta basa ya amsa ta kunna masa cartoon ta xaunar da shi kusa da Noor da ta kwanta 


kan kujera, sannan ta shiga daki don yin wanka, tana shiryawa bayan ta fito ta ji shigowar mota, ta gama saka kayan da sauri ta fito, Aryan na ganin xata 


fita ya sauka saman kujera xai fara kuka, ganin haka ta dawo ta daukesa, Noor ta fashe da kuka ita ma, dariya tayi ta dauketa ita ma, tana rike da su ta 


fita compound, tsaye tayi tana murmushi ganin motar Khaleel ne, jawahir ta fito daga motar, Aryan na ganinta ya fara murna, khadijah ta saukesa yaje da gudu 


ya rungume uwarsa ta daga sa tana dariya tace "Kai lallai khadijah, dubi yanda kika maida min yaro kato, wani irin abinci kike basa haka" dariya khadijah 


tayi tace "Bayan ma ya rame, duk kwanan nan a dole yake xaune gidan, naga alamar kewar ki yake" Khaleel ya fito daga mota yana murmushi ya nufo ta yace "Oum 


shureim good morning" tana murmushi ita ma tace "Morning doctor...." ya amshi Noor yana shafa dogon gashinta idonsa a kan khadijah yace "Congrat once more, 


Allah ya sanya alkhairi, our pharmacist..." Tace "Ameen Thumma Ameen, thanks much Abu Aryan" Bata rufe baki ba motar Aliyu ya shigo gidan, Baby ce ta fara 


fitowa daga motar tare da little Amira, khadijah ta wara ido tana kallonsu ta nufe su da sauri, Barrister Sudais ya fito daga gaban motar with Shureim, 


sannan Umma da ta fito ita ma rike da little Farouq yaron da baxai wuce wata bakwai ba da baby take goyo, khadijah ta rungume baby cike da murnan ganinta 


suka dinga babbaka dariya, lkci daya ta tafi gun Ummarta ta rungume ta ita ma, tsabar murna ta kasa cewa komai, ta rasa me xata ce, tana sake Umma ta daga 


handsome yaronta sama ta rungume sa ya dinga kissing fuskarta very happy seeing her..... Aliyu ya fito ya jingina da mota ya rungume hannunsa yana kallonsu, 


Kamar yanda Barrister Aliyu da Dr Ayman ke kallonsu suna murmushi su ma....




*ALHAMDULILLAH*



A nan na sauke littafina mai taken *Noor-Al-Hayat* kurakuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min....👏🏻 Darussukan dake ciki Allah yasa mu amfana da 


su Amin. Ina mika sakon gaisuwata xuwa ga mahaifiyata Hajiya Hajarah... She is my first love, my role model, my momma, my world, my everything... Allah bar 


min ke Hajjaju Yaya❤ My sweet Anty Didi ur daughter Jiddo is greeting with respect, tnx for being there for me during this book, Allah ya raya su 


Aneesah... And my second role model Anty Rukaiyya...😍 am so grateful for the encouragement from the beginning of this novel till the end, I always gat ur 


back small mum ur daughter Khaleesat Haiydar is saying a big thank you, Allah bar mu tare ya raya Little Khaleesat Haiydar, Baby and Jaheed... 

Na sadaukar da littafin *Noor-Al-Hayat* xuwa ga lovely sister na, my Blood... Khadijah M Bello (Amira/Baby) nd my sweet cousin like no other Khadijah Sadi 


Yusuf (Baby) Allah ya albarkace rayuwar ku ya raya mani ku bisa imani, ya baku ilimi mai albarka da amfani. Sakon gaisuwa ta na musamman xuwa ga wa enda for 


sure ba siyan littafin Noorul Hayat suka yi ba, ihisani kawai suka min, duk ina sane da ku kuma na so contacting din ku but I lost my contacts, ban san ya 


xan yi in same ku ba, Amma ku sani I will for ever be grateful, Allah ya biya maku bukatun ku na alkhairi duniya da lahira, nagode nagode.... And finally my 


fans, ban taba xaton yea da gaske I have fans ba sai a littafin nan, you guys really patronized me fiye da tunani na, you all made me feel loved😥 words 


alone can't express how happy I am, ku sani... Billah Khaleesat na ji da ku har ranta, Ina son ku, Ina alfahari da ku, Ina maku fatan alkahiri, Ina maku 


fatan rabuwa da iyayen ku lafiya, Ina maku fatan daukaka, Ina maku fatan gamawa da duniya lafiya, ina maku fatan samun aljanna, I wish you all the very very 


very best in life, nagode nagode nagode... Allah ya sa mu cika da imani ya yafe mana kura kuran mu...👏🏻


Taku har kullum Hauwa Bello Jiddah (Khaleesat Haiydar) 📚✍🏻


Thanks once more for patronizing my book fans... For those still wanting to buy the complete document it's just 300 Via transfer 👉🏻 3276052019 Hauwa Jiddah 


Bello, fcmb.


07087865788.