Breaking News

KWARATA 21

🅿 ------ 21

         Cikin farin ciki muka isa bakin shagonmu wanda yasha fenti kuma aka gwagwaÉ—a masa tambarin kwarata , tsayuwarmu da fitowarmu shine ya jawo hankalin al'umma masu wuce da wanda suke zaune saboda munzo da sabuwar shiga mai matuÆ™ar bada al'ajabi a karon farko da ta zama abin kallo ga jama'an gari...



          Takardun da aka gurzo wanda yake É—auke da tallar karuwancin mu nasa "yan daba suka raba titi biyu duk motar da zata wuce aka ci gaba da basu babu sauÆ™i babu sauÆ™aÆ™awa !


        Bakin shago mu mata muka koma muka jera layi amma babu wacce ta zauna tsaye muke , Nana da Karima suna daga gefe suna kallon ikon Allah ,

      Waya Hafsat ta fiddo ta fara latse latse daga baya kuma sai naga ta koma gefe guda tana waya , ta É—auki tsawon lokaci bata gama wayar ba haka nan kawai naji na tsargu da wayar , bayan ta gama sai ta goge number data kira...


      Ƙurawa Hafsa ido nayi harsai data kama kanta , tabbas akwai cuta a tare da rayuwar Hafsa akwai abinda take shiryawa ko kuma take so ta aikata idan kuwa na ganota da wani laifi na cin amana babu abinda zai hana na tona mata asiri,

        Yana gama waya da Hafsa ya buÉ—e saÆ™on da tace ta turo mishi , É—an soÉ“aro baki yayi irin na sakatattun "ya "ya sannan ya cire vidio ya É“oyeshi a gellery vault bayan ya gama gani...

       Saman kujera ya zauna ya saka takalmi har yanzu bakinshi a soÉ“are yake , saida ya gama sannan ya kalli Al ' Ameen yace mu fara zuwa ta wurin An manta sannan mu wuce don Allah , 

    Al ' Ameen yace mai gida da Allah ka fita hanyar yarinyar nan , murmushin Dikko yayi sannan yace wallahi sai anje idan baza kuje ba sai ku jirani ina dawowa , yana faÉ—in haka yayi gaba , Al ' Ameen biyo bayanshi yayi Æ™aramin yaron daya girma kawai zai riÆ™a juya su dandai suna Æ™asansu...

Da sauri ya wuce Dikko ya buÉ—e mota , É—an É“ata rai Dikko yayi sannan ya shiga ya zauna tare da kwantar da bayanshi saman lallausan kujeran motar ,  wayarshi ya ciro yayi mata kyakkyawan riÆ™o da duka hannayen shi biyu , sannan ya É—ora Æ™afa É—aya saman É—aya yake faÉ—awa Hafsat yana zuwa yanzu babu daÉ—e wa zaizo mata bankwana !

       Wata irin kururuwa Hafsa tayi ta farin ciki sannan ta koma motarta da gudu , Æ™ara barbaÉ—a powder tayi tare da Æ™ara shafa turare sosai , sannan ta gyara É—aurin kallabinta ta fito...

          Kallon mamaki nake ta bin Hafsa dashi anya yarinyar nan bazan zameta daga harkata ba ? Tafiyar nan kuwa zata tafi kodai in fita inyi harkata ni É—aya ? Ina wannan tunanin zuÆ™a zuÆ™an motocin Dikko sukayi parking a Æ™ofar shagon mu...

       Cikin rawar kai Hafsa ta tashi tayi wurin motar Dikko , Æ™afarshi ya É—ora saman murfin motar , kafin Hafsa ta isa wurin ya zura hannunshi aljihu ya ciro cingom , a daidai lokacin da Hafsat ta isa wurin motar , ko inda take bai kalla ba ya cire cingom inshi a cikin takaddar shi , 

         Tahowa ya farayi zuwa wurina tare da É—ora cingom in saman "yan yatsunshi na hannun haggu ya daki tafin  hannunshi na haggu da hannun shi na dama , buÉ—e bakishi yayi cingom in yayi tsalle ya shige ,

      ÆŠan tsuke bakinshi yayi kamar zaiyi kiss sannan ya lumshe idanuwanshi tare da nuna yanayin kamar abin harin sumbatar nashi yana kusa dashi , muah ya saki kiss a daidai lokacin daya tsaya gabana yaja kujerar rober ya zauna , sai yanzu ya fara tauna cingom É—in cikin izza da nuna shi wani isashshe ne , É—ago Æ™afarshi yayi ya biyo da ita ta saitin fuskata kamar zai takamin fuska naÉ—an ja baya , murmushi yayi tare da É—ora Æ™afa É—aya saman É—aya :•

      Robar ruwa Al ' Ameen ya miÆ™owa Dikko bayan ya zauna , É“alle murfin robar ruwan yayi yakai bakinshi yana kallona , shan ruwan yayi sannan ya cika bakinshi dashi ya miÆ™awa Al ' Ameen robar ruwan , murmushi yayi da gefen bakinshi sannan ya fara bultso ruwan daga bakinshi suna watsowa saman fuskata...

      ƘoÆ™arin tashi na farayi dan banda lokacin Dikko a yanzu sai bayan shekarun dana iba , ina Æ™oÆ™arin tashi ya maidar dani ya zaunar da Æ™afarshi nayi na tashi na kasa saida ya gama watsa min ruwan sannan na buÉ—e idona daya cika da hawaye na kalleshi , 

    Murmushi yayi sannan yayi magana cikin sigar lallashi haba ke ko an mata komai saurin kuka ke baki san wasa ba ? Karfa ki É—auki abin da zafi albarka na saka miki , kin zageni tass amma zagin yamin daÉ—i bayan shekaru biyu idan muka fara farautar juna a ranar zaki gane Dikko ba zakin roba bane , zakin gaske ne farin ciki mafarauta , maganar dana faÉ—a mishi jiya, cewa zakin roba dana sanin mafarauta, ci gaba yayi dacewa dani dake duk wanda ya fasa , ya jinjina kainshi tare da nunani da hannu , 

Tura kujerar da nake zaune yayi da ƙarfi da bango bai tareni ba babu abinda zai hanani faɗuwa , Al ' Ameen ya kira da sauri yazo tare da miƙo mishi wata "yar ƙaramar jaka tashi yayi ya duƙo kusa dani sosai lumfashin shi yana sauka saman jikina , saman jikina ya ɗora tare da cewa ga cingom nan zai isheki amfani daga nan har zuwa lokacin da zamu fara wasa , ɗan taɓe baki yayi tare da kallon wani wuri daban sannan ya juyo ya kalleni da magana zaiyi kawai sai fasa...

     MiÆ™ewa yayi ya juya ba tare daya sake cewa komai ba , bayanshi Hafsa tabi saida ya shiga mota ya zauna sannan yasa Al ' Ameen yayi rabon kuÉ—i wa duk wanda muke tare dashi har "yan dabana saida Dikko yasa aka basu kuÉ—i amma nidai bai bani ba kuma ban damu ba saboda dama ni basu nake jira ba !

        Al ' Ameen yana gama rabon kuÉ—i ya koma mota , har yanzu Dikko ni yake kallo gilashin saitin shi Al ' Ameen ya É—age zuwa sama sakamakon da yake Æ™asa , bai daina kallona ba har Al ' Ameen yaja motar suka tafi ,

Goge fuska ta nayi da hannu na , sannan na buɗe jakar da Dikko ya ajiye a gabana , irin cimgom in da yake amfani dashi ne sai farar takarda da akayi rubutu a samanta , suke nan a cikin "yar jakar , ban buƙatar dubawa sabona nasan gani kawai zanyi bazan iya karantawa ba, kuma babu wanda zan ba ya karanta min saƙon Dikko daga nan har lokacin da zan iya karantawa da rubutawa....

       Tunda Dikko yayi min wannan wulaÆ™ancin ban sake magana ba har aka gama raba takardunmu muka koma gida ban sake magana da kowa ba , kuma tunda nayi wanka na shiga É—aki ban sake fitowa ba saida gari ya waye '

        Bayan na gama duk abinda nakeyi na fito tsakar gida na zauna saboda ba yau zamu fara fita ba sai an fara kira a waya lokacin zamu tabbatar da cewa tallarmu ta samu karÉ“uwa a wurin jama'an gari,

       Nana na gani riÆ™e da kwalar rigar mijinta tana zazzaga jikinta irin abin nan da yara keyi idan suna faÉ—a , zama nayi ba tare dana kalli inda suke ba amma hankali na da kunnuwa na suna wurin su , wallahi sai ka sakeni kalmar da naji ta fito daga bakin Nana kenan kuma har yanzu bata saki rigar mijin ba.

      Audu yace ba Æ™in sakinki zanyi ba amma sai kin faÉ—amin abinda nayi miki wanda yasa kike so na sakeki ! Nana tace lallai bama ka da kunya da har kake tambayar abinda kayi , tou na gaji da zaman cida kaina zaman wahala zaman kunci kullin muna can barbaÉ—e kayanmu a saman kai bama Æ™erau bama sabuwar anguwa zama gidan haya , tou wannan aure dai a sahalewa juna uban kowa ya huta...

        Daga inda nake zaune nace Audu wai duk meya haÉ—aku ne wai ? Ku kullum faÉ—a ke Nana kamar kece kaÉ—ai matar aure a gidan nan ? Duk wadda kika gani da mijinta haÆ™uri takeyi ko suna wani saÉ“ani basa fitowa tsakar gida ke kullum dake da mijinki kamar abokan faÉ—a ? Gaskiya ki daina wannan rayuwar kece Æ™asan Audu dole sai kin kiyaye idan har kina san ganin daidai a rayuwarki.

      Sakar mishi riga kizo kiji wata magana, babu musu ta sake rigar mijinta ta taho wurina, shi kuma Audu fita yayi ba tare daya sake cewa komai ba,

      A Æ™ofar gida kuwa A ` i ce ta tare Audu bayan gaisuwa tace mishi naji shiru ya kamata kayi wani abu don Allah , zama Audu yayi a saman dakali sannan yace ki Æ™ara haÆ™uri , murmushi A ` i tayi tare da cewa ba komai Allah ya tsare ya dafa maka akan duk lamuranka , da amin ya amsa sannan ya wuce ita kuma ta shigo cikin gidanmu...

       A Æ™ofar É—akina A ` i ta samemu ina bawa Nana shawara , amma tana zuwa gaba É—aya ta jagula komai ta ida firgita Nana har na kasa gano gabanta bare bayanta,

       Ajiyar zuciya nayi tare da bin A ` i da kallo ban sake magana ba ina dai jinta tana ta É—ora Nana a hanyar banza ita kuma tana ta karÉ“ewa dan a ganinta shawarar A ` i itace mafita a gareta ,

         Æ˜awar Amisty da tayi ciki suka shigo da sallama ita da wata mata , inda nake zaune suka nufo gaisawa sukayi dasu Nana sannan sukace wurinki muka zo , miÆ™ewa nayi tare da cewa ku shigo na faÉ—i maganar tare dayin gaba suka biyo bayana !

            Wurin zama na basu sannan nima na zauna muka gaisa , bayan gaisuwa Æ™awar Amisty tace Sultana kin ganeni kuwa ? Murmushi nayi ban bata amsa ba , taci gaba da cewa idan da hali nima zan shiga Æ™ungiyarki , ga Æ™awata itama zata shiga, kallo nabi su dashi bayan wani lokaci nace ita Æ™awar taki tana da aure ne ?

     Dukanmu matan aure ne , Ni suna na Fadeela inji Æ™awar Amisty mai cikin shege , sai kuma ta nuna Æ™awar da suka zo tare tace ita kuma sunan ta Zalifa , saida na Æ™ara kallesu tsaf sannan nace miye dalilinku na shiga wannan Æ™ungiya ... ?

     Wacce aka kira da Zalifa tace wato ina da wata damuwa ce ta musamman wacce bazan iya biyanta ba ko cika burina ba dole saina shiga wannan Æ™ungiya mai albarka , ina so na samu goyon baya da taimakon tantiran dake cikin wannan Æ™ungiya ,

Murmushi nayi sannan nace wannan wace irin damuwa ce ? Gyara zama Zalifa tayi tare da cewa wato ina da wata maƙociya wacce na ɗauki amana da yadda na bata , bana ɓoye mata sirrina ko kaɗan .

Wata rana ta shigo gidana sai taji muna hayaniya da mijina , bayan mun gama mijina ya fita sai take tambayana abinda ya haÉ—amu , ban É“oye mata ba kamar yadda na saba na kwashe komai na faÉ—a mata , 

        Na Æ™ara da cewa bansan abinda nayi masa ba duk abinda bai taka kara ya Æ™arya ba sai yayi ta faÉ—a akanshi wani lokaci ma hada duka , sai tacemin yadda Allah ya halittani da kyakkyawar siga mai burgewa na kashe aurena zan samu wanda yafi mijina ,

     Nuna mata nayi cewa bana iya kashe aure na amma zan haÆ™ura gaskiya na zauna dashi a haka tunda ina sansa wata rana zai gaji ya daina , sai tacemin ai sai anbar zomo yake zama guza , mazan yanzu da asiri ake ladaftar dasu in bada kuÉ—i taje ta nemo min asiri inyi maganin mijina.

     Banji wani komai ba na bata kuÉ—i masu yawa dan tacemin itama mijinta da yake mata biyayya malamin yayi mata maganinshi , kuma naga yadda mijinta yake mata biyayya sosai kuma yanajin shakkunta dan haka na bata kuÉ—in nima a samomin asirin in riÆ™a dawwara mijina...

       Haka kuwa akayi tayi ta kawo magani ina barbaÉ—awa mijina a abinci ina zuba mishi a ruwan wanka da abin sha laya Æ™arÆ™ashin filo wasu layun a Æ™arÆ™ashin gadonshi , tunda safe kafin ya fita na kunna hayaÆ™i , shirka dai iri iri da Æ™azanta nayi ta barbaÉ—awa mijina yana lashe wa ,

        Haka tayi tamin wayau tana karÉ“emin kuÉ—aÉ—e , murmushi tayi tare da cewa kinsan me ya faru ? Nace mata A , a, tace kwasam sai ta tayar da fitina wa mijinta da yake aurenta , kuma yanayi mata wani irin azababben so yana Æ™aunarta fiye da duk yanda zan faÉ—a muku , amma saida ta kunno masifa ya saketa , har wannan lokaci bata daina kawomin asiri ba ,

        A daren ranar data kawomin magani na zubawa mijina a abinci yana gama ci babu laifin zaune babu na tsaye ya gwagwaÉ—amin saki 3 ita kuma ta aure min miji gani nan na fito bani ga tsintsu bani ga tarko kinji hukuncin da tayi min....

Murmushi nayi kaɗan sannan nace kin aihu da mijin ne ? Tacemin a , a , nace ita ubanta yana raye ne ? Tace min Eh nace ya yanayin samunshi yake ? Tace babu laifi gaskiya yana da rufin asiri , da kyau nace tare da cewa mijinki kina san ki koma gidanshi ko kuwa ya kike so ? Zalifa tace gaskiya bazan koma ba so nake kawai ku riƙe mishi wuya ku jawo shi a cikin ƙungiyarku ku ƙare duk wani tattalin arziƙinshi babu asiri Sultana ki fitar min ita daga gidan...

       Jinjina kai nayi tare da cewa ni bana asiri amma sharrina da kaidina yafi asiri bala'e a rayuwar É—an adam , waya na bata tare da cewa sakamin lambar mijinki ki ajiye min ita da lamba 4 , ansa tayi ta sakamin tayi saving kamar yanda nace , bayan ta dawomin da wayana nace babanta a wane anguwa yake ne ? Zalifa tacemin gaskiya bai cika zama ba , nace to karki damu zai zauna dan dole ki samo numbershi ni kuma nayi miki alÆ™awari su dukansu zamuyi musu aiki ...

       Zalifa tacemin ina da motar hawa idan zakuyi amfani da ita  , nace tou yayi kyau mun gode , jakarta ta buÉ—e ta fiddo kuÉ—i har naira dubu É—ari ukku tace gashi taba Æ™ungiya tata gudumawar , godiya nayi tare da Æ™walawa A ` i kira nace ta kawo musu form su cika , Zalifa tace karki damu zan cika anjima idan muka dawo akwai inda zanje yanzu , nace tou babu damuwa sai kun dawo...

       MiÆ™ewa sukayi zasu tafi nabi bayansu dan rakiya amma ban wuce Æ™ofar É—akina ba , anan na tsaya nayi musu addu'ar sauka lafiya , bayan sun fita na koma É—aki naci gaba da "yan hididdumu na , na tattara kaya saboda zamu tashi daga gidan yau zuwa sabon gidan da na siya , kuma duk nace matan gidan subini mu koma gidana da na siya , sauran É—akunan da suka rage zan nemo "yan gidanmu na tattara su wuri É—aya hadashi gogon wato Babana dan nafi so nayi karuwanci a gaban idonshi ya gane cewa ba'ayiwa iskanci haye....