Breaking News

KWARATA 23

🅿 ------ 23

          Har gari ya waye ban sake komawa bacci ba , da safe bayan na gama duk abinda nakeyi na fara kiran lamba 4 , lamba 3 wato d c o kuma na haÉ—ashi da Amisty bana iya wata mu'amula dashi saboda gaskiya baida tsabtataccen baki danni Allah yayi min Æ™yanÆ™yami idan na raina maka tsaftar baki tou na raina maka kuma bazan yadda inyi wata mu'amula dakai ba gaskiya.


       Lamba 2 wato Bello shi yana nan kuma muna tare har yanzu babu wani abu daya shiga tsakani na dashi saidai ina fereshi yadda ya kamata ina kwalkwalar kuÉ—inshi babu dare babu rana, daya bani haÆ™uri ma cewa nayi saiya nemo min Babana sannan zan Æ™yaleshi !


      Lamba 1 Alhaji ne kuma ya rigamu gidan gaskiya , na goge komai nashi a wayana daga number har vidio babu abinda na bari,

    Lamba 4 shine mijin Zalifa kuma yanzu shine abun hari na, É—an wasa na, domin shine zan jijjiga zanyi wasan kura dashi kuma saina lashe kaf tattalin arziÆ™ishi saina cinye komai zan maidashi matsiyacin Æ™arfi da yaji, idan kuma yana da rabo akaina tou in sameshi mai tsafta idan dai É—an gayu ne kamar Dikko zan riÆ™e mishi wuya ya zama abokin tafiyana...

     Kiranshi nayi amma har ya tsinke bai É—auka ba , haka tsarina yake kira É—aya nakeyi idan ba'a É—auka ba bana sake kira , idan kuma ya biyo kiran ina maraba dashi ,

      Daga tsakar gida naji Amisty ta luÆ™aÆ™a wata irin ashariya irin na shararrin "yan tasha , saida gabana ya faÉ—i , ban gama saita kaina ba naji taci gaba da cewa na rantse da girman Allah wannan karon bazan bar Sultana tayi haÆ™uri ba , saita wulaÆ™anta shi ko waye ubanshi ...

Da sauri na miƙe na fito tsakar gida jikina sai kyarma yakeyi saboda ni hayani da zage zage ɗimautani sukeyi , ina fitowa na kalli Amisty nace wai mene ne ? Kusa dani Amisty ta matso tace ke wai mu Hafsa zata tonawa asiri , kallon inda Hafsa take tsaye nayi sannan nace wai miye ?

       Wayar Hafsa, Amisty ta miÆ™o min tare da cewa shiga kiga cht insu da Dikko , bayan ta tura mishi saÆ™o ta whatsapp ya kirata tsakanin minti 10 bayan tura saÆ™o, kiji zagin da yayi miki Mother Æ™arshen hukuncin da yayi yasa an rushe shagonmu kuma yace idan dai yana lumfashi kika fito karuwanci yace sai yayi miki wulaÆ™ancin da ko ance ki faÉ—i kalmar iskancinci da bakinki sai kince kin tuba , 

       Yace zai baki azaba mai azaba É—aya daga cikin irin azabobin daya tanadar miki shekaru biyu masu zuwa , kuma idan kinyi taurin kai yace zai tafi dake ya É“atar dake inda babu wanda zai sake jin labarinki daÆ™iÆ™iyar banza dake....

        Zuciyata ta kawo maÆ™oshi amma ban nuna É“acin rai ba nace ma Amisty wai duk inji shi Dikkon yace haka ? Amisty tace imana kinsan dai bana miki Æ™arya idan baki yadda dani ba ki samo wani ya karanta miki duk duniya Sultana babu wanda nake ma soyayya irin wacce nake miki , nabar uwa da uba na zaÉ“e ke , rayuwata da komai nawa sadaukarwa ne a gareki idan ba duk abinda na faÉ—a miki Dikko ya rubuto ya turo ba Allah ya tsine min albarka !

        Murmushi nayi sannan na kalli Hafsa nace to ke Hafsa mi ya kawo har kukayi magana na da Dikko ? Latse banzan bakinta tayi sannan tace niba magana nayi mishi ba shine yayi min maganarki , Amisty tace ke jira kiji zan ubanki Æ™arya zan miki ko me kike nufi ne ? Kallona Amisty tayi sannan tace vidionmu ta tura mishi da hotuna kuma itace ta faÉ—awa Dikko muna da shago inba haka ba ya akayi yasan wurin harya zo ?

      Hafsa tace tou naje na faÉ—a Amisty kiyi magani na , ai tun kafin ta gama rufe bakinta Amisty ta rufe ta da duka tana cewa amanar Æ™ungiya zaki ci dan ubanki , an yadda dake zaki ci mana amana , ko an faÉ—a miki muma bamu iya karatun da rubutawa ba ? Tana magana tana dukan Hafsa , kokowa har Æ™ofar gida saboda cikin gida mata sun kasa ansar Hafsa dama su "yan gayu basu iya faÉ—a ba sai sakata suka iya...

         A Æ™ofar gida dakel masu aikin rusa tsohon gidanmu suka raba faÉ—a , kuma sukayi sasanci cewa da Allah mu daina faÉ—a ayi haÆ™uri , candai ake basu haÆ™uri niko wuri na samu na zauna wai nice daÆ™iÆ™iya , kamar ni abokin hamayya zai faÉ—a cewa ni daÆ™iÆ™iya ce , wallahi wannan kalmar tafi komai muni a rayuwata , itace kalmar da aka taÉ“a faÉ—amin ta É“atamin rai kuma tamin ciwo ta kartar min zuciya har sai da naji masassara ta saukomin , wai ni Dikko yace ma daÆ™iÆ™iya , gumi naji yana bimin kumatu ina kai hannuna na shafo kunci na naji lema , ganin ruwa a hannuna ya tabbatarmin da kuka nakeyi....

Bayan an raba su Amisty shine suka zo kusa dani suka zauna hada Hafsa dan kunsan su "yan duniya basu fushi duk yadda aka cakusa dole sai an koma an jone , kowa tambayata yakeyi abinda yasa nake kuka amma banyi magana da kowa ba , Hafsa ce ta fara bani haƙuri akan abinda tamin murmushi nayi amma ban mata magana ba ,

        Muna na zaune Æ™ofar gida a saman dandamali har su Nana mun jera layi babu mai mayafi a cikinmu mundai fito karuwan na zahiri da zahiri, saboda wancan hannu duk Dikko ya cinyesu babu gida ko É—aya filin wurin ne kawai saboda duka wurin ya sayeshi harya tsallako gefen gidanmu yaci gaba da siyewa.

        Muna nan zaune muna jiran tsammani Umar yazo , yaron Dikko wanda ya yakaini gidan Alhaji , yana fitowa daga mota ni ya fara gani , shegiyaaaaa , ashe da kina nan ina kuÉ—i na da kika cinye "yar damfara ?

       Murmushi nayi da gefen bakina sannan nace zaki ya shiga gaban É“auna , idan dai wanda ya mutu zai dawo tou ka kwantar da hankalin ka kuÉ—inka zai dawo aljihunka babu É“ata lokaci ,

       Aiko kuÉ—ina baza su ciwo wurinki ba sai kin bani abuna , dariya nayi tare da cewa wallahi basu ansuwa wurinka bakai ba kayan banza ko Dikko naci gabanshi naci uwarshi naci ubanshi a iskanci ai shine dai kake taÆ™ama dashi ko ?

      Kusa dani Umar yazo yana Æ™oÆ™ari wanka min mari na riÆ™e hannunshi tare dayin wani irin lafiyayen fito , babu É“ata lokaci "yan dabana suka bayyana , kallonsu nayi tare da cewa ku shiga dashi ciki ku bashi ruwa yasha , É—aukarshi sukayi sama sukai cikin gida dashi , saida suka bashi kashin bala'e sukai mishi lullusar fitar hayyaci , saida suka tabbatar jikinshi yayi tsami sannan suka tillo banza Æ™ofar gida...

      A lokacin ni kuma ina saman mota ta nayi kwanciyata , yayin da Amisty ke gefe na tana shan sigari A ` i da Saude kuma suna zaune kan dakali suna lido, Nana da Karima kuma nace su koma cikin gida saboda su matan aure ne ,

     Dakel Umar ya miÆ™e ya shiga motarshi yaja ko masu aikin da yazo dubawa bai duba ba ya tafi , bai zame ko ina ba sai wurin "yan sanda , muna Æ™ofar gida zaune muka ga motar "yan sanda , wai anzo kamani , 

      Bayan mun gama magana dasu nace su jirani ina zuwa , cikin gida na koma na shirya cikin shiga ta alfarma, wata riga na É—auka na saka a leda bayan nasa anyi mata kitar wulaÆ™anci ga kuma jikina da yasha sahun akaifun Hafsa nasa ta yayyakushe ni dan na shirya Æ™ullawa Umar sharri na gaske.

       Dani da Hafsa da Amisty da A ` i da Saude muka tafi domin ni sune sheduna , mu biyu a gaba ukku a baya , cikin mota ta muka tafi saboda itace motar kece raini Hafsa ta tuÆ™a har muka isa police station, Umar na zaune a waje jini sai bin jikinshi yakeyi tuni ya kira Dikko ya faÉ—a mishi, Dikko yace da an kamoni a rufeni duk abinda yake zai shigo katsina gobe idan Allah ya kaimu , dan hankalinshi ya tashi da yaga dukan da nasa akayi wa Umar.

        Office É—in d c o aka kai case inmu , ga gaske ni kuma gani nazo da kwarata masu biyawa mutum buÆ™atarshi , dan suma sunyo shiga mai É—aukar hankali duk namiji mai lafiya ya gansu sai yaji hankalinshi ya tashi ,

        Kujera Amisty ta jawo min na zauna sannan suka koma bayana suka tsaya , shigo da Umar akayi a daidai lokacin da ni kuma na fara gaishe da mai girma d c o , kafin ya ansa gaisuwar tawa Umar ya miÆ™a mishi waya Dikko ya sake kira domin ya faÉ—awa Dikko munzo station in ,

      FaÉ—a Dikko yakeyi tare da cewa bai ce a jira aji abinda ya haÉ—amu ba kawai rufeni yace ayi , D C O yace ranka ya daÉ—e ai sai anyi binceke Dikko yace ba abinda za'a bincika umarni yaba d c o a rufeni kawai , d c o zai sake magana Dikko ya daka masa tsawa dole d c o ya dauke wuta , jikina fa yayi sanyi amma ta maza nayi tare da miÆ™ewa na anshi wayar daga hannun d c o nace Dikko faÉ—a a cikin waya bashine ke nuna jarumta ba , kuma rufeni na kwana a ofishin "yan sanda bashi ne zai nunamin kai cikakken jarumi bane ba , 

        Kaine kaÉ—ai maganin fitsarata idan ka isa kazo kayi magani na basai kasa an kulleni ba , kuma kake cewa kar ayi bincike kasan abinda shi yaron naka yayi min ne ? Cikin É—aga murya nace tou mutunci na fa zai buÉ—e kaga yadda ya yayyage min jiki ? Kuma da aka mishi magana cewa yayi kai ka tsaya mishi ya hau duk macen da yaji tayi mishi, kuma D C O ya faÉ—a maka idan bai yayyageni ba , da sauri Dikko ya rufe idanuwanshi tare da matse gwangwanin maltinar da aka kawo mishi baisha ba , azabar matsa yasa gwangwanin ya fashe maltinar ta watse...

       Har a zuciyarshi ya yadda da abinda na faÉ—a mishi dan yasan Umar manemin mata ne na Æ™arshe yayin da Umar ke cewa wallahi mai gida Æ™arya takeyi kawai naje duba masu aiki tasa "yan daba sukai ta dukana ! Cikin wata irin hayagaga Dikko yace rufemin baki É—an iska mutumin banza idan na sake jin maganar ka saina ci mutunci ka wallahi ,

       Tausasa murya yayi tare da cewa ba d c o wayar , miÆ™a mishi nayi Dikko yace da gaske ya yayyakushe ta ? D   C O yace Eh ranka ya daÉ—e , to dole zaice Eh tunda ga sahun akaifa a jikina ya fito sosai, nidai bansan yadda suka Æ™are ba  D  C O yace muje kawai ,

       Muna shiga mota na sauke ajiyar zuciya , kai Dikko É—an bala'e ne na Æ™arshe baida mutunci gaskiya Allah ya rufamin asiri yau da sauro da zarnin fitsari ya hanani bacci , kallon Amisty nayi sannan nace kinji É—an bala'e da saboda ni zaizo lallai dana yabawa aya zaÆ™inta , dariya nayi tare da cewa aidai mun daki banza....

        Bayan wata É—aya...

          A halin yanzu suna na ya fara zagawa a cikin gari, domin dai harkar iskanci ta buÉ—e mana sosai muna ganin maza daga shiyyoyi da dama , a cikin gidana nan maza ke zuwa su zaÉ“i macen da suke so a tafi hotel acan ake raÆ™ashewa, yanzu bamu da shago domin Dikko ya saye wurin kuma yasa an rushe shi , tou ina gidana anan nake baje kolin iskanci na dani da yarana...

Cikin wannan wata bakin gwargwado kowa ya samu ci gaba na rayuwa Nana namiji yake zuwa wurinta ta kora mishi sharfi akan kayan mata da maza , itama a hankali idonta ya fara buÉ—ewa ta iya gogayya da maza , dan daga ita har Karima yanzu bata mazansu suke ba,

       A fanni na kuwa ni har yanzu ban samu tsaftataccen namiji kamar Dikko ba , amma idan aka zo tafiya da mace ni nakeyin ciniki namiji ya bani kuÉ—i kuma itama macen idan ta dawo zata bani kasafi na , tunda kafin a tafi nasan ko nawa za'a baki , na zama kawaliya kenan..

     Idan namiji yazo ya duba a cikin matanmu bai samu wacce tayi masa ba ya faÉ—amin irin mace da yake so ni zan nemo mishi ita walau budurwa walau zawara har matar aure ma ,

        Mijin Zalifa munyi waya dashi amma har yanzu bamu samu haÉ—uwa ba , yadai bada an kawo min kuÉ—i masu yawan gaske ta dalilin waya da mukeyi ta É“atsa dashi , na siyar da motar da Alhaji ya bani nayi ciko na siyi mota ta gani ta faÉ—a , kuma ni nake tuÆ™a abuna domin yanzu na iya mota , jikina yaÉ—an Æ™ara ginuwa ya kuma goge hutu ya zauna dan dole dan idan baka san gidan da nake rayuwa ba zakace daga G. R. A  na fito, na Æ™ara waye kuma idanuwana sunyi fashewar da duk mutum yayi mamakinshi,

       Shirye muke cikin shiga mai nuni da mutanen gari ga naku , ma'ana maza ga matan bariki, biki akeyi a gidan Æ™anin Babana yana aurar da É—iyarshi, dan haka nace kowa ya shirya muje , mota ukku mukayi hada Zalifa, mota ta , ta Hafsa sai ta Zalifa sai napep É—aya ta "yan daba...

       Tunda mukayi parking idanuwan jama'a ya dawo kanmu, fitowa nayi tare dayin magana Æ™asa Æ™asa nace gafa "yar gado nayi gado amma kuma har na zarce... 

Ina gaba tawagar karuwai suna bin bayana , duk wanda ya ganni sai ya kauda kai tare yin gulma ta , a cikin gidan biki kuwa hankalin jama'a ya tashi ganin iskanci dana taro bamai riƙuwa bane , ƙanin Babana yana tsakar gida shima da mutane ana ta mishi Allah sa alkairi dan ba'a daɗe da ɗaura auren ba , mazauni su Amisty suka nemomin na zauna na ɗauki ƙafa ɗaya saman ɗaya na ɗora...

       Kallona yayi tare da cewa Sultana haka kika zama karuwa ? Saboda shi irin mutanen nan ne masu sakin magana babu tsafta , murmushi nayi tare da gyara zaman É—aurin kallabi na sannan nace Eh wallahi ai shine nazo na nuna muku tunda nasan duk wani É—an uwa da abokin arziÆ™i yazo shine nazo wanda basu gani ba suma su gani....

Dariya Amisty tayi tare da buɗe jakarta ta jawo shigarinta ta banka mata wuta , saida taja ta bada hayaƙi sannan tace wannan gaskiya ne Mother , ƙanin Babana yace nan zaki zo ki kawo mana iskanci ? Tou ki tashi ki koma inda kika fito tunda ke kin lalace karki zo nan ki gurɓata mana tarbiyyar "ya "ya kije can ki ƙari iskancin ke ɗaya....

         Kallon Baba nayi tare da cewa gaskiya ne dan naga idan guguwa ta taso wuri É—aya takeyin borinta amma tsawar hadari tana gaurayi kaf faÉ—in sararin samani , ruwan sama ko na sarari yake jeÆ™ewa bai taÉ“a baa na cikin É—aki kashi duk wanda kaga yasha kashin ruwa cikin É—aki tabbas kwanon É—akinsa ya huje , idan yayi dibara saiya doÉ—e wannan haryar da zai bawa ruwa damar shigo mishi É—aki. Gyara zamana nayi tare da ci gaba da cewa duk na kirki baya san na banza amma ni mutanen kirki sune abokan rayuwa.....


       MiÆ™ewa nayi tare da cewa ka bada tarbiyya a gida zamanin Sultana yana warware tuggun kowa , duk wanda ya kalleni a taron nan yace tir da halina ya saurari zuwan zamani na akan "ya "yanshi, har na fara tafiya na tsaya tare da juyowa nace yawwa idan kaga É—an uwan naka Babana , ka faÉ—a masa cewa ina matuÆ™ar kewarsa a kusa dani...

        Sallama nayi da duk wanda ya kamata tare da buÉ—e bakin jakata nayi alkairi , banga "yan gidanmu ba ko É—aya amma nace idan sunzo ace musu ina nan tsohuwar anguwarmu , gidan karuwai kawai zasu tambaya za'a kawosu har É—akin magaji Sultana , na Æ™arasa maganar tare dayin murmushi sannan nayi gaba masu sauran imani suka bini da addu'ar shiriya yayin da wasu ke cewa ubana yajamin...

      Muna fitowa daga gidan kowa ya shiga mota muka ibi sararin hanya.....