Breaking News

KWARATA 45

🅿 ------ 45

           Tsaye yayi yana kallona , ni kuma da gudu nayi cikin gida har na kusa faÉ—uwa , a mamakince Dikko yabi Sultana da kallo a ranshi yana cewa ko lafiya ?


     Mota ya koma ya gyara parking , yayi zamanshi ciki bai fito ba ranshi É—auke da tunani daban ² , ga zafin mutuwar matarshi ga ciwon auren da za'a É—aura mishi wanda rasuwar Sadiya yasa aka É—ageshi , ga iyayenshi sam² sun rufe idanuwansu akan aurenshi da Sultana...

     Ya É—an rame har yayi duhu saboda damuwa da tunani , a gajiye ya fito daga cikin motar ya nufi gidanshi , kafin ya ida shiga Baban Sultana ya faka tashi motar daga can gefe dan kar yayiwa Dikko laifi...

      Dikko yana ganinshi ya dawo suka gaisa , bayan gaisuwa yace am dama ina san ganin wannan yarinyar ne , cikin damuwa Baba yace ta sake janka ne ? Fuska dai a murtuke babu fara'a yace a , a zanyi magana da ita ne kawai !

    Baba yace tou Allah dai yasa lafiya , a É—an rashin jin daÉ—i Dikko yace ba komai fa , shi baya so yayi ta nanata magana kuma anajinsa amma a kasa fahimta ,

Cikin gida Baba ya nufo zuciyarshi cike da damuwa , tunda ya shigo gida yake kwalamin kira kamar ranshi zai fita daga jin yanayin maganarshi babu daÉ—i a zuciyarshi ,

      Da gudu na fito ina tambayar Baba lafiya , cikin faÉ—a yace me ya sake haÉ—aki shiga sabgar yaron can mara mutunci kuma ? ÆŠan iskan yaro da baya ganin kowa da mutunci , ya raina arziÆ™in duk wani mai farin gashi dake doron Æ™asar nan , fitinanne yaro dako bakin duniya baya tsoro ga rashin mutunci da masifa kamar kishiyar É“arauniya...

     A ruÉ—e nace ni babu komai , dakamin tsawa Baba yayi yana cewa babu komai inji waye ? Gashi can ya kafe mota Æ™ofar gida yana É“acin rai duk abinda nace bana so sai kinyi Mamana kina so dai ki samin É“acin rai idan na mutu kin huta ,

       Hannuwa na duka biyu na É—aga alamar bada haÆ™uri nace a , a Babana kayi haÆ™uri don Allah , dan bana so naga Baba yana fushi akan komai bare kuma ni daya É—auki soyayyar duniya ya É—oramin ,

     Sassauta murya yayi cikin tausayi yace tou kije ki bashi haÆ™uri nidai bana so kina jawoshi faÉ—a uwar masu gida , nace tou Baba , a tsorace na fita Æ™ofar gida gabana sai faÉ—uwa yakeyi ,

     Dikko yana tsaye ya jingina da mota , da gudu na isa inda yake na riÆ™e hannayen shi , na irin gani karka kasheni , kallona yayi cikin sigar so da Æ™auna yace tou kin kama min hannaye ai gara ki riÆ™eni gaba É—ayana tunda abin har yakai ga riÆ™e hannu ,

     Sakin hannuwan nashi nayi na É—aga kaina na kallo cikin kwayar idonshi , wani irin kallo yayi min kwayar idonshi tana motsawa a hankali wanda idan baka iya saka ido ba baka gane motsi takeyi ,

Hmmm me yasa kika gudu da kika ganni ? Ko na zama dodo ? Bansan abinda yasa bana iya ma Dikko ƙarya ba amma da nauhi wannan kalma mai muni ta fito daga bakina ,

      Tou tunda baki da abun faÉ—a ni zan faÉ—a nawa , shiru nayi ina saurarenshi , yace zanyi tafiya kuma bana tunanin idan na tafi zan dawo yanzu , bana so na shiga haƙƙinki da yawa dan ina baÆ™in ciki kiyi damuwa a rayuwa , ina so miki farin ciki bana so kiyi kuka haka kuma bana so ki kasance cikin damuwa ko Æ™unci ,

      Na baki daga yau zuwa jibi kwana biyu kenan ko ? Ya tambayeni , ina kallonshi banyi magana ba , yace tou kije ki natsu kiyi sharawa da zuciyarki shin kina so na ko bakya so na ?

     Cikin yarinta nace ni bama sai nayi shawara ba gaskiya bana sanka , kallona yayi sosai yace karkiyi Æ™arya An mata zakiyi nadamar hakan wata rana , nace wai ni ? Na Æ™arasa maganar ina masa kallon rainin wayau nace Allah ya sawaÆ™emin ai baka cikin tsarin mazan da nake so , cikin damuwa yace .

Kina da matsaloli fa daban ² An mata , saurara samar da farin ciki a domin É“atawa wani ba dai² bane , haka zafin murmushi a yayin da wani yake baÆ™in ciki da takaici hmm baya da amfani , karki damu kawai cewa zakiyi ina sanka , shi kenan fa babu wani wahala , uhum kana ba kanka wahala kaji , ince ina sanka ? Allah ya sawaÆ™emin ,

     Murmushi Dikko yayi maicin rai yace tou ni kuma na san a cikin kwanaki biyu da wannan taurarin idanuwan naki zaki zamo masoyiyata babu jayayya , zaki zo ki rumgumeni , numfashinki zai shiga kwalwata, zaki kalli idanuwana , ina sanka , idan har baki faÉ—a kina so na ba , shiru yayi yana kallon fuskata , zuwa wani lokaci yace sai kin faÉ—a , yana faÉ—in haka yayi tafiyarshi ya barni a wurin...

     Cike da damuwa na koma gida yayin da zuciyata ke shawarta ta ince ina san Dikko wata zuciyar tace karki sake ki faÉ—a ko zaki mutu ki barshi kawai kuje a haka , kina mace kice kina san namiji haba ai kinci Æ™asa ,

    Lokacin da kwana biyu ya cika zuciyata ta gama tabbatarmin da bata san Dikko , dan haka kuma na yanke shawarar sanar dashi bana sansa yayi haÆ™uri ,

     Da daddare bayan yazo ya aiko aka kirani dan har yanzu ban kunna wayar ba tunda na kashe ta ban sake buÉ—ewa ba , bayan na fita muka gaisa dashi , bayan gaisuwa yace ina saurarenki , nace gaskiya ansar dana baka tun farko itace har yanzu , 

     Shiru Dikko yayi , bayan wani lokaci yace , wannan rana ta kasance min ranar juyayi ne , bana fatan wannan ranar ta sake zomin , ranar Æ™arshe kenan banda wani Æ™warin guiwa , An mata ce kaÉ—ai abin alfaharina , umm abinda bana so ya kasance duk lokacin dana runtse idanuwana nakan iya ganin kyakkyawar fuskarki , bansan mace ba sai a kanki idan har na taÉ“a san wata mace a rayuwata to kece An mata ,

    Zan tafi idan har naci gaba da ganinki to zan É“ata miki , kiyi haÆ™uri bazan sake kiranki ba , haka ma zuwa ba zaki sake ganina ba An mata , kin daÉ—e kina Æ™onani inajin kamar na rasa wani abu , me zanyi ? Bazan iya koda dariyar Æ™arya ba , jawoni yayi ya rumgumeni duÆ™owa yayi ya kwantar da kanshi saman kafaÉ—a ta , cikin wata irin murya mai tsayawa a zuciya yace sai wata rana , ki yafemin don Allah karki riÆ™eni zan fita daga rayuwarki dan ina so kiyi farin ciki , zan tafi ki huta koda kuwa ni zan shiga halin damuwa ,

     Bayan wani lokaci ya É—ago ya kalleni , cikin kallonshi mai É—aukar hankali yaÉ—an É—auki lokaci yana kallona sannan yazo dai² bakina lumfashin shi yana fitowa saman fuskata , gashin gemunshi yana shafar dai² saitin bakina , lokaci guda jikina ya canja tsikar jikina ta tashi ban taÉ“a jin irin wannan yanayi ba , bafa haÉ—a bakinmu yayi ba , daga waje ya sunbace ni wani abu naji ya shiga jikina da gudu saida ya gama zagayawa ya dawo zuciyata ya shiga da Æ™arfi , ajiyar zuciya na sauke yanajin nayi ajiyar zuciya ya sakeni da sauri daga jikinshi yaÉ—an turani baya yace ki tsaya da kyau karki faÉ—i , zan bada saÆ™o Umar ya kawo miki kafin in wuce ,

       Kasa magana nayi nabi shi da kallo da sauri ya shiga mota ya bar Æ™ofar gidanmu da gudu , har ya fita daga anguwarmu  ina tsaye a wurin daya barni , yana É“acewa na kyalkyale da dariya , na zabgaga wani irin ihu , daga cikin gidanmu Zainab ta fito da gudu tana tambayata lafiya ?

      Sai dire² nakeyi kamar anyi ma doki allura Æ™arfi , Zainab tace wai miye yake faruwa haka ? Goge hawaye nayi nace har yanzu na kasa yadda da wannan , Zainab tace miye ne kika kasa yadda dashi ? Nace masoyina ya faÉ—amin dukkan na kasunsa , shi da yace zan rungumesa sannan na faÉ—a masa cewa ina sanka DK , 

    Zainab tace waye DK murmushi nayi nace baki sansa ba , Zainab tace tou ki faÉ—a masa kina sansa mana , nace ke jinan ya nunamin yatsansa yayin da yake Æ™alubalanta ta cewa a cikin wasu kwanaki zance ina sansa , murmushi nayi tare da rufe idona , nace kamar dai yadda yace naji ina sansa , Æ™ara É—aga murya nayi ina sanka mutumi na , ina sanka , Zainab tace to me yasa baki faÉ—a a gabansa ba ? A , a , a , a , idan na faÉ—a masa tou zaiyi ta jamin Æ™afane har abada , Zainab tace zakiyi duk abinda kike so amma kuma idan kika makara a soyayyarshi fa ? Nace sam ² ki rabu dashi kawai yayi kuka na wannan daren nasan bazaiyi zuciya ba da safe zai sake zuwa , ni kuma yana zuwa zance barka dai DK idan ba tare dakai ba ina ne zanje .....?

     Cike da farin ciki na shiga gida , Zainab ta rufomin baya , alwallah nayi na shige cikin É—akina ina farin ciki ,

      Dikko kuwa yana isa gidanshi wanka yayi , bayan ya shirya ya É—an faffaka abu mai mahimmanci ba kaya ya É—auka ba , wasu takaddu ne kawai ya tattara , layinshi ya cire ya ajiye , dube² yayi na irin banyi mantuwa ba kuwa ? Sannan ya fita daga cikin É—akin ,

     Wajen da aka tanada dan ajiye motoci ya samu Umar kamar yadda yace su haÉ—u , Ashiru a gefe sai Al ' Ameen , duk gaisheshi sukayi cikin girmamawa , bai ansa ba , makullin mota ya miÆ™ewa Umar tare da nuna mishi mota yace ka kaima yarinyar nan akwai kuÉ—i a but in tasha mai , Umar yace mai gida wace yarinya ? Yarinya nawa kasan ina tare da ita ? HaÆ™uri ya bashi tare da cewa tou ai naji bakace An mata ba , murmushin baÆ™in ciki Dikko yayi a zuciyarshi yace tace bata so na , kuma fa ba'a soyayya dole Allah ma yasa bansha wahalar shawo kan kowa ba dasai nasha wahala na shawo kan iyayena tace bata aurena , gara kawai na haÆ™ura nayi nesa da rayuwarta na barta ta huta  , Umar kallon motar yayi Al ' Ameen ma Æ™walalo idanuwa yayi cikin tashin hanki yace mai gida wannan motar zaka bata ?

     Cikin É“acin rai yace Ey ita zan bata , cike da hassada yace ko ka manta nawa ka siyota ne ? Dikko yace kila babanka ya nemomin kuÉ—in shi yasa na manta , dan wani irin haushin Dikko yakeji kuma Dady yace idan yayi masa wani abu bai yafe masa ba , Al ' Ameen ya kalli motar ya Æ™iyasta kuÉ—inta tou ai wallahi kaf garin katsina wannan motar ita É—aya ce tak , bazai manta ba lokacin da Dikko ya siyo motar wallahi ganinta ake zuwa yi ana mata hoto ko wata motar batayi ba kuma Dikko bai taÉ“a hawanta ba , shine zai É—auka ya bawa karuwa ? Kai amma yarinyar nan ta shanye mai gida da yawa , motar miliyoyin kuÉ—i haka ?

      Kaf ma'aikatan gidan nan suka haÉ—u suna ma Dikko addu'a Allah ya tsare , wallahi game da kyauta dai Dikko baisan darajar kuÉ—i ba , yana kyauta maisa mutum ya kasa gane bacci yake ko idonshi biyu ? Bayan ya gama sallamarsu ya shiga mota Ashiru yaja suka bar gidan ,

     Al ' Ameen kuwa sai Æ™ara kallon motar yake hada kukan baÆ™in ciki ina ma É—iyar "yar uwarshi ta samu wannan mota ? Mai gida baisan abunshi haka nan yake neman kuÉ—in baisan darajarsu ba wallahi , yo wannan mota ai daya sani siyar da ita yayi ya sayi gidaje masu kyau kawai ya É—auki mota ya ba shegiyar yarinyar da Z bata tantancewa , lallai zaima Yayarshi waya idan har Mai gida ya dawo nigeria Haneefa taje Abuja wurinshi...

      Daga gidanshi gidansu ya wuce kai tsaye , danyi musu sallama , momy tace idan an É—aura aure matarka zata isko ka , cike da biyayya yace tou , bedroom ta koma ta É—auko maganinshi tace gashi nan saura idan ka tafi ka yadda shi , ansa yayi ya saka a aljihun wandoshi , addu'a tayi mishi tare da mishi fatan alkairi harya fita , Dady kuma baya nan ,

     Cike da soyayya tabi bayanshi da kallo , haka nan taji dai bari ta mishi rakiya , bayanshi tabi har inda ya ajiye motarshi , saida zai shiga mota yaga Momy ta biyoshi , kallonta yayi yace inzo ? Murmushi tayi tace a , a , kusa dashi ta matsa tace karka zo rakiya nayi maka , taci gaba da mishi addu'a Allah ya tsare tana É—aga mishi harya shiga mota suka tafi ,

       Tun a mota ya goge hotunan Sultana , bayan yayi musu kallon Æ™arshe dayi mata addu'a Allah ya bata miji na gari , ya kuma sa ta yafe masa karta riÆ™eshi a zuciyarta , shi kuma Allah ya bashi haÆ™uri da dangana akan ta...

      Bayan ya gama goge ²nshi da addu'a shi ya anshi tuÆ™in motar dan gani yakeyi Ashiru ma baya sauri , tuÆ™in ganganci da wauta Dikko na fama da iskanci cike da kwalwarshi , ga raini ga rashin ganin mutuncin mutane amma yana da tausayi da taimakon wanda baya dashi , 

       10:09pm suka isa kano , anan aka canja abokan tafiya , saida jirginsu Dikko ya tashi Ashiru ya juyo katsina bai kwana ba , sauka lafiya mai gida Dikko Allah ya tsare....

      Cikin farin ciki na wayi gari kuma nayi alÆ™awari yau zan faÉ—awa Dikko nima ina sansa , duk wanda ya ganni yasan inajin daÉ—in wannan rana , saida hantsi ya É—aga na sheÆ™aÆ™a wanka na , naci gayuna dan nasan yau Dikko yayi kwanan haÆ™uri nasan ya Æ™agara gari ya waye zai fara zarya ganin dokuna ,

      Cike da farin ciki nayo Æ™ofar gida na zauna ina jiran isowar jarumina , har lokacin zuwanshi yazo ya wuce babu Dikko babu labarinshi , gida na koma na É—auko wayata na kunna , bayan ta gama kunnuwa na fara neman layinshi , amma dai inajin maganar É—aya ce kodai wayar tana kashe ko kuma babu kuÉ—i a wayata ,

   Gida na koma nasa aka dubamin ko banda kati , kowa sai yacemin akwai idan nace nawa ne sai su kasa lissafomin , Babana na bashi ya dubamin yace akwai kuÉ—i , nace nawa ne Baba ? Yace dubu É—ari biyu ne , nace tou kiramin wannan lambar na Æ™arasa maganar kamar zan faÉ—a masa ,

    Duba sunan da akayi saving in number yayi yai murmushi tare da cewa iye Mamana ta fara soyayya ya Æ™arasa maganar yana kallona kuma cikin zaulaya yayi maganar , cikin jin kunya na zauna kusa dashi ina dafa kafaÉ—arshi nace aini bana soyayya , yace ai ba wani ne ya bani labari ba nine na gani da idona , tou me yasa kace haka ? A dai² lokacin da yacemin wayar a kashe take ,

     Cikin rashin jin daÉ—i na anshi wayar kaina ya fara min ciwo haka nan naji É“acin rai ya lulluÉ“emin zuciya , cike da damuwa na fito tsakar gida , amma sai naga gidan kamar yana juyawa , Baba kuma yana min magana daga bayana wallahi kwata² banajin abinda yake faÉ—a ,

     Wai ance ana kiran Sultana , da sauri na fara kakkaÉ“a idona daya cika da hawaye inayin dariya cikin farin ciki , nayi Æ™ofar gida da gudu Babana ya fito da sauri ya biyo bayana yana lafiya ? Turus na tsaya ganin Umar , nayi tunanin zanga Dikko babu shi , sake cika da hawaye idona yayi nace ina yake ? MiÆ™omin makullun mota yayi a dai² lokacin da Baba ya fito yace gashi yace a kawo miki kuma akwai kuÉ—i a but wai kisha mai , sai ki bani tukuwici in wuce , nace tou ina shi Dikko yake ya aiko ka ? Umar yace yayi tafiya , 

      Kallona Baba yayi yace waye ya kawo wannan motar ? Hawayen da suka taru a idanuwa na suka samu damar gangarowa daga saman kumatu na , da sauri na juya na rumgume Babana ina kuka , É—agoni yayi daga jikinshi yace wai miye ? Waye ya baki wannan motar ? 

     Cikin kuka nace Dikko ne , kallon motar Babana yayi sannan ya kalli Umar yace wai wane Dikko ne ? Da hannunshi yayi mishi nuni da doki , kallona Baba ya sakeyi yace meke tsakaninki dashi ? Goge hawaye nayi na anshi makullin na buÉ—e but in motar , bandir in "yan dubu² ne guda goma , guda biyar na ba Umar nayi godiya , shima godiya yayi ya wuce abunshi...

     Umar yana tafiya Babana yace wai Mamana ke ya akayi ya baki wannan motar ne ? Nace shi yaga dama ya bani ita ba roÆ™arshi nayi ba , kallon motar Babana ya sakeyi yace aiko wannan motar bata hawuwa wurinki garin nan saidai a siyar da ita kuma duk ma garin nan bana tunanin akwai mai siyenta shima Æ™uruciya tasa ya siyeta , { ba rashin kuÉ—i baba yake magana ba da yace baya tunanin akwai mai siyenta } babu dai wanda zai ware wannnan kuÉ—aÉ—en ya siyi wannan motar kawai dan dai ya hau , murmushi nayi kaÉ—an nace baza'a siyar da ita ba gaskiya ,

     Baba yace ki hauta ace miki wa Mamana ? Nace idan na hauta kaji yadda za'a kirani , tou ina zaki ajiye wannan mota ? Nace gidan dokunanshi zata riÆ™a kwana ... Allah ya tsare Babana ya faÉ—a , na ansa da Amin ,

     Da kaina nakai ma masu gadin gidan ajiyar mota , suma kansu mamaki ya kamasu ya akayi motar mai gidansu tazo wurina ? Saboda kowa ya sani tashi ce shi É—aya yake da ita duk kaf cikar faÉ—in garin katsina , dan anyi surutun motar sosai a lokacin daya siyota kuma har yanzu ba'a gama ba , wannan ansa basu da mai basu ita....

     Na shiga cikin É—imuwar rayuwa nayi kukan rashin Dikko nayi harna gode Allah , na rasa ina zan saka kaina naji daÉ—i , "yar jakar daya bani a lokacin da muka kama shago dasu Amisty na É—auko na zazzage , cingom in daya bani nashi na É—auka nayi ta ci ina haÉ—iyewa , saida naji zan mutu na haÆ™ura na tattara sauran na mayar ,

     Na faÉ—awa iska ina san Dikko bansan adadin kalamai nawa suka fita daga sautin bakina ba , baida wani amfani dan Dikko dai baya nan kuma bazaiji ba , nayi kukan rashin Dikko har tsawon sati É—aya ina zubar da hawaye duk nabi na rame na susuce , na kira wayarshi kullum dai maganar É—aya a kashe , duk lokacin dana kira wayarshi naji kashe sai nayi kuka kuma bazan daina kukan rashin ka ba Dikko har abadan duniya....


    Bayan wata É—aya , 

       Abubuwa da dama sun faru , Babana ya warke tas kamar bai taÉ“a wani rashin lafiya ba , su Amisty kuma an Æ™aro iskanci domin dai suma a anguwarmu suka sayi gida  , 

      Ta siyi motar hawa ta baro iyayenta tana zaman kanta , Nana ma ta tashi daga gidanmu ta koma nasu Amisty , Saude A ` i Zalifa Karima ma duk sun tare a can , Hafsa ma nan take yini amma bata kwana , itama Asma'u anyi mata register kuma suna faÉ—a cewa yanzu zanga yanda ake shugabar duk wani É—an iska daya kwana a katsina suna da masaukinshi , idan inajin nima wata Æ™waro ce na kafa manya ²n karuwai kamar nasu...

      Lokacin da naji saÆ™on su Amisty dariya nayi , bana san komawa ruwa dan naji kwata bana sha'awar karuwanci dan zuciyata bata da lokacin sauraren kowa saboda Dikko yabi ya mamayeta da soyayyarshi , kafin inyi wani nazari na yanke hukunci naji gam × ³ a cikin kaina , kamar wacce aljannu yake shiga jikinta haka jikina ya fara fizge² idanuwana sunamin zafi sosai , kaina ya juye , nace tabbas zasu san nawa ba kalar nasu bane mu zuba mu gani dani dasu.

     A wannan halin Mamy ta sameni , bayan mun gaisa ta fara rattafomin bayani akan Baban budurwar Dikko , wacce mukayi faÉ—a da ita a mota.....