KWARATA 47
Aminci Allah yaddar Allah wadatar zuci farin ciki da kwanciyar hankali ya tabbata a gareku masoyana a duk inda kuke...
A gaskiya banajin daɗi kuma banyi tunanin haka daga gareku ba , domin kullum burun marubuci himma dan karya taɓo illar makaranci , shifa rubutu bawai kare zube akeyinshi ba , yana buƙatar natsuwa tunani sannan kuma kai mai rubutun wane saƙo ne kake san isar wa ? Tun farko na kira littafin nan da KWARATA... Sannan kuma nayi masa inkiya da Ƙalu bale gareku matan aure , wane ƙalu bale ne matan auren zasu kiyaye ? Ban faɗa ba ? Nayi duba da irin zamani da muke ciki wanda aka mayar da zina ba'a bakin komai ba , kuma wannan labari dana rubuta duk maibin labarin idan ya lura ina dunƙule hausata ne saboda gudun warwarewar tarbiya , nayi amfani da wata hausa ta