Breaking News

YAU DA GOBE 17-18

 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

  🌹YAU DA GOBE 🌹

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & writing by mmn faree

🅿️17&18

......Wani irin mummun fad'uwar gaba taji"had'e da muguwar katsawa da cikinta ya Mata lokaci guda!fatanta Allah yasa ace mafarki takeyi ba gaske ba....HASBINALLAHU WANI'IMAL WAKIL....kalmar data fad'a azuciyar ta kanta duke"tana dafe da k'irjinta sbd bugun dayake Mata tamkar zai fito.... Sumayya!kinyi shiru kobaki amince da Wanda nazab'a miki bane??"

     da sauri ta girgiza Kai had'e da cewa nagode Abba Allah yak'ara girma..baki washe abba yace Masha Allah naji dad'i sosai sumayya Allah yyimiki albarka"insha Allah wata rana zaki alfahari da auren Aliyu"munyi mgn dashi d'azun gobe zaizo kugaisa kinji?"sumayya da zufa keta keto mata cikin dakiya had'e da b'oye tashin halin datake ciki "tace to Abba"Abba yace haka nakeson ji"jikinta asanyaye tafice.... straight dak'in ta ta wuce ta fad'a kan katifarta tasaki kuka me cin Rai"me yake Shirin faruwa dani ni sumayya?"tafad'a afili tana shashshekar kuka...da gudu ta wuce toilet sbd cikinta daya juya..ta kusan Kai 10 minit ,tukum ta fito tanata ajiyar zuciya"tayi tagumi"afili tace tabbas wannan auren bbu alkhairi acikinsa!yaushe Zan huta naji dad'i?"natabbata fansa yakeson d'auka akaina"sbd abinda namasa nasan baya sona nima bana sonsa...wlh natsanesa dama ace Yaya Sadiq ne Zan aura "Koda ummansa bataso, ai ba gd d'aya zamu zaunaba... sak'a da warwara kawai takeyi ita d'aya ad'aki...

    "Ahankali mamar ke tafiya sbd tsohon cikin dake jikinta"tanata sallama sumayya batajiba"zamatayi gefen Sumayyar had'e da cewa ke lfy?"ajiyar zuciya sumayya tasaki had'e da fashewa da kuka"bazakiyi mgn sai kuka "lafiyarki?mama dan girman Allah kitaimake ni Abba yajanye auren nan akaina .wlh bana sonshi na tsaneshi sbd besan d...ke dakata!Ashe ke butulu ce bansani ba?"dan uwarki nasake jin wa an nan maganganun abakinki ranki zai b'aci"ke yanzun ko mahaukaci alh yazab'a miki bakin karb'a kodan sbd halarcin daya Mana arayuwar mu...kokuwa sokike ki auri muttala d'in?"kigodewa Allah da yabaki miji amatsayin Aliyu"aishima basonkin yakeyi ba"inkin shiga gidansa ,a aikace zakiyi abinda zakija hankalin sa yasoki...matar gdn bata son ganin wannan aure sbd tanason ya auri y'arta jidda"kodan sbd mak'iyan mu bakin nuna kina soba!to wlh kima sake shiri kinji nagaya Miki shashasha kawai...

Mama kiyi hakuri dan Allah"yunk'u rawa mama tayi ta shi.tana dubar sumayya tace inhar kikabi umarninmu to bbu damuwa"akasin hakan kuwa nidake ne...bata jira cewar taba tafice...



   Sumayya tasaki kuka had'e da kwanciya tana tunanin Wai ita wannan me girman kan zai aura"gefe guda na zuciyar ta najin haushin meyasa sadda yamata wulak'anci a asibiti bata fad'aba?"da yanzun bashi zata aura...yah Allah gani gareka nasan su mama bazasu tab'a fahimtata ba"tafad'a afili tana ajiyar zuciya...


***************


Zarah ce kwance ad'akinta tana chats da friends d'inta a what's app.. saidai rabi hankalinta nakan musty datagani a online....tana shiga status taga ya aza wani pic...da sauri ta bud'e...wani fad'uwa taji gabanta yyi ,sbd ganinsa atsakkiyar wasu coppers sanye da kayansu na bautar k'asa"d'aya acikinsu ta dafashi"kasancewar ta ba musulma ba...da sauri tamasa reply da...meye haka broth?"zaka tsaya acikin mata har wata na tab'aka !me hakan ke nufi?"kokuwa kanaso kanuna musu cewa baka damu da addi nin kaba da al'adarka...


    Koda musty yagani "murmushi yyi dama sbd ita ya aza yaga zataji haushi..sai yamata reply da cewa"miye aciki baby? "yanayin  mu'a mulane Muna tare Koda yaushe Dan anyi pic ba laifi ba ne ko kinga nakama wata acikinsu?"

Koda ta suba saitaja tsaki had'e da cewa ohk hakan yyi kyau dg yanzun nima Zan fara pics da coppers d'in damuke tare tunda abune me kyau ko?"

     Yana duba beyi reply ba sai kawai yamata vedio call! tab'e baki tayi had'e da rejecting d'in kiran...can Kuma sai yakira voice call"Saida takusa tsainkewa tukum ta d'aga...ajiyar zuciya yasaki"zarah naji tak'i mgn"ahankali yace baby me yasa kinfi son b'acin Raina ne kullum?"dakata mlm !kanacan ina nan"shine Kuma har namaka laifi"kaida dama kullum cikin maka laifi ake"ina ita Yasmeen d'in taka take ?"wacce ka shareni sbd ita...shine zaka wani hauni da fad'a...ta Ida fad'a cikin masifa... murmushi yasaki"sbd yasan kishine yasata Masa masifa "asalima ada girmamashi takeyi"wato yanzun bakisan mekikayiba ko?"eh sai kafada ai "bacewa kikayiba zakiyi pic da coppers maza bacin kinsan banaso....kaga jira"Ina ruwanka dani? damuwa kayi danine"Kai meyasa kayi da wa'acan k'azaman saini ka hanani ko?"to Kama d"auka namayi pics dasu ,Kuma nacika status d'ina d pics d'in....uhummm baby pls karkiyi ?"sbd me ?sbd inasonki "hmmm Allah ko?"ai wannan tsohuwar mgn ce "inhar kana sona ai bazaka ambaci kuje tare d Yasmeen ba"sbd haka bana sonka kana yaro dakai kace nikakeso..Kuma wlh inhar baka goge pic din ba" gobe sai nayi pics dasu kaji na rantse....dit ta kashe wayar tana Jan tsaki..musty kuwa ba k'amin haushi yajiba "saidai ya kud'urta aransa bazai gogeba sbd bata isa tabashi umarniba saidai shi yabata...Kuma pics bata isa ta d'auka da kowane k'azamin copper ba...sauka online din yyi yafara had'a kayansa sbd gobe moyar 6 zai hau yasan zuwa 10 ya isa kano ,tunda gobe Friday yyi week end dinsa acan..Koda yagama kimtsawa bekira kowaba ,sbd yanason musu bazata....


*Washe gari*


Zarah bata cikin walwalarta sbd jiya musty yabata haushi"musammun sbd taduba status nasa yafi a k'irga amma be goge pic din ba..haka tasami ummi a dining area sukayi break fast tamata sallama ta wuce skul d'in datake d'auka...

  


    Musty kuwa tun 6 ya wuce Tasha...Gurin 10 da wasu mintina Mai acaba ya ajiyeshi bakin get na gidansu... k'ofar yyi knocking"baba Mai gadi yafito sbd son ganin wanene"murmushi yyi yace uban gidana Kaine haka?"musty na murmushi yace eh baba Ina kwana?" Yace lfy qlau alhmdllh....baba zarah ta fita yau?eh ta fita Gurin karfe8 ai...musty yace ohk ga trolley d'ina baba ka kaiwa ummi Dan ALLAH" bara na dawo..to baba Mai gadi yace Yana karb'a..da sauri musty ya wuce bakin titi yatari acaba sbd dama yasan skul d'in...Yana isa skul d'in..kaitsaye office d'in Principle ya wufe yamasa bayani akan yyi meeting da duka y'an bautar k'asar suka yasanar musu zarah matar aurece...beyi wani musu ba "sukayi sallama...ya wuce section d'in junios...hangota yyi ta fito dg wani class...sanye take da kayan bautar k'asar sai farar hijab iya gwiwar hannu..tayi kyau sosai Masha Allah yafad'a Yana sakin murmushi yanufeta...da farko batayi zaton shi bane Saida yakusa isowa kusa da ita tukum"cak ta tsaya sbd mugun mamaki tace broth!my baby! yafad'a Yana dage gira had'e da sakin murmushi"hararar sa tayi had'e da cewa me ruwanka dani dazazo nan?"babu gaisuwa ko ya hanya sai k'orafi to kiyi hakuri ki maida wuk'ar...amma ba yau kazo garin nan bako?"yau nazo Mana!kina mamakine?"tab'e baki tayi had'e da cewa ko d'aya mamakin me zanyi?" tunda bbu runka Dani nima haka"idanunsa k'yam akanta yace nikuwa keda ruwa dake baby"yanzun kizo muje gd" bata fuska tayi tace ni bbu inda Zan tafi sai 12 tayi... Allah ko?"tace eh"yace to bbu damuwa in nagwada d'aukarki ta k'arfi da yaji aidole ki biniko?"had'e rai tayi tana hararar sa"cikin jin haushi tace aisaika saka niya wlh dana mareka kuwa...Dan ALLAH zoki kwatanta.. yafad'a Yana matsowa gab da ita.da sauri tayi baya"fuska ya daure cikin kakkasar murya yace wlh ko kizo muje kokuwa na jaki!ganin bbu wasa afuskarsa yasa tafara bashi hakuri...sake had'a rai yyi had'e da cewa anjima zasuyi meeting duka y'an bautar k'asar su San kematar aurece"nayi mgn da pc sbd haka inkimma karyata bazasu yardaba "aikince zakiyi pics d coppers ko?"to wlh Bismillah!duk shegen da yyi pic dake kashinsa yabushe sbd nasanar da pc ko mgn inba doleba banaso kiyi d maza... sannan inkin k'aryata nasiyeshi da kud'i bazai yardaba...tamkar wata doluwa haka zarah ke kallon musty cike dajin haushinsa "saikawai taja tsaki tayi wucewarta staff room abinta.

d'age kafad'arsa yyi ,irin ko ajikinsa d'in nan yyi tafiyarsa zuwa gd...



🍁🍁🍁🍁🍁🍁


Tun d'azun yashigo office d'in Dr Nasir kasancewar yanzun yafito dg tearter"yyi zaune yak'i mgn"tun Dr Nasir na tunanin gajiyace har dai yagaji  yace Wai safana lfy ne?"

     gajeran tsaki yaja had'e da cewa wlh ni ana mugun takurani wlh...yanzun Wai Abba dole yau bayan juma'a naje gurin wannan k'azamar yarinyar...hhhhhhhhh yo ai abokina ni hakan yamun dad'i wlh !cewar Dr nasir..tsaki Dr safana yaja had'e da cewa kaga mlm banisan iskanci miye abin dariya anan?

kafi kowa sanin halina kada muje gunta kanamun haka kaja yarinya ta rainani..wlh na tattakata bbu ruwana da naje gidansu...Dr Nasir yace me yyi zafi abokina" abin bana tada jijiyar wuya bane"Allah yakaimu anjiman "sannan Dan Allah karage zuciyar nan taka"d'azun ma haka "ka mari wani saurayi sbd yarako budursa ganin likita harka fitar Masa da jini"tab'e baki Dr safana yyi had'e da naga mahaukaci ne shiyasa nakoya Masa hankali"inbacin hauka ko aure bbu atsakanin sa da ita miye abun Ina dubata yashigomun office"nace yafita sbd shi bagidaje ne yak'iya"meye laifina dan nakoya Masa hankali...kayi daidai my man"hararar sa Dr safana yyi had'e da ficewa...



***************

Musty ne parlour Yana lunch had'e da kallon wani amerikan firm a MBC (2)"bayan yadawo dg masjeed"Dr safana da Dr Nasir suka shigo"ko wane da manyan Kaya ajikinsa.

Cikin girmamawa musty yagaidasu"Dr safana yace autan ummi saukar yaushe?"wlh d'azun da safe Yaya...kaganka Masha Allah kamar wani ango...dr nasir yakarbe zancen da cewa ai yakusa angwancewar...akule Dr ke kallonsu Yana k'ok'arin yin mgn yaji ance ah ah Nasiru Kaine agdn?"cewar ummi dake shigowa parlourn..cikin girmamawa Dr Nasir yagaida ita"kafin ummi tace suje suyi lunch "Dr safana yace ak'oshe suke"musty yace Yaya naji batun saka rana'gsky naji dad'i sosai d....kaga mlm kacigaba da cin abincinka Kar ka k'ware gurin yin mgn... murmushi kawai musty yyi bece komai ba"sukayiwa ummi sallama suka fito"parking space suka nufa "Dr Nasir yabude motar yazauna driver sit"yyinda uban gayyar yazauna gun me zamn banza suka nufi gdn Abba...



Bangaren sumayya kuwa"akan tursasawar ummi ta gyara parlourn bak'i tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta maroon lace...amma fuskarta bbu kwalliya"kallo d'aya zaka Mata kasan tana cikin damuwa"tayi tagumi ,zunbule liyar  hijab d'in ta nakusa da ita "tana jiran ace tazo tasaka"sbd ta k'udurta aranta bazata tab'a saka gyale ko yin make up ba sbd shi....ke inkin gadama kije gasu can aparlourn bak'i!saura kiyi wani abinda bedace ba kiga yadda zanyi dake...cewar mama cikin kakkausar murya...wani mugun fad'uwa gaban sumayya yyi .haka tayita furta addua aranta "ta Mike tasaka hijab ta fice...mama ta girgiza kanta cike da tausayin  y'ar tata..harga Allah tana tausayawa sumayya akan auren musammun datasan mazan wannan zamanin sai addua kawai dukda tasan Aliyu mutum ne nagari beda makusa"to amma tasan shima bashi yace Yana soba ,bashi akayi"saidai kawai tayita Mata addua kawai..da wannan tunanin mama Takoma d'akin ta sbd dama abba yakirata yace ta turo sumayya gasu Aliyu sunzo...