YAU DA GOBE 19-20
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌹YAU DA GOBE 🌹
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & writing by mmn fareesa
🅿️19&20
,,,,,,Tsaye tayi bakin k'ofa sbd yadda gabanta ke mugun fad'uwa" addua kawai takeyi azuciyar ta"kafin tayi shahada ta murd'a k'ofar tashige...Dr safana kuwa yacika yyi famda shanya sun da sumayya tayi"kallon agogon dake daure atsintsiyar hannunsa yayi...kafin yaja tsaki akaro na bbu adadi"cikin b'acin rai yadubi Dr Nasir had'e da cewa kaga malam katashi muje kawai"ba'ayi macen data isa nayi Mata irin wannan jiranba"inbacin tsohon wulak'anci tun yaushe muke nan? dazata
shanyamu"saikace wata classic lady"yoko classic lady bata isa b...look abokina!be a man mana"tunda mukeso aidole muhak'ura ko?" Dr nasir yafad'a Yana kurban juice da aka ajiye musu...wani banzan kallo Dr safana yamasa had'e da cewa kana sab'o wlh ,inbacin sbd Abba ko hanyar da wannan k'azamar tabi ,bazan bi ba!kafin Dr Nasir yace wani abu sanyayyar muryar sumayya ta karad'e parlourn tana musu sallama"kasancewar suna mgn basuji k'arar shigowartaba....gogan kuwa inda take be kallaba"sai Dr Nasir yasaki murmushi had'e da amsawa "yadubeta fuska asake yace ranki yadad'e irin wannan shanyawa haka?"murmushi sumayya tayi had'e da cewa"Yaya Nasir Ina wuni?"satar kallon Dr safana Dr Nasir yyi yaga Yana latsa wayarsa. hankali kwance tamkar bbushi ackin parlourn"Mik'ewa tsaye yyi Yana cewa lfy qlau amaryarmu"Kinga sweet heart d'inki yyi fushi saiki matso ki rarrashi kayanki"ni bara na wuce"yafad'a Yana dariya sbd yasan ya k'ular da Dr safana"sumayya kuwa tab'e baki tayi had'e da d'ukar da kanta kawai.... k'arar rufe k'ofar yasakata jin zuciyar ta na bugawa "wato dg ita saishi a parlourn?"ta tambaki kanta...sunkusan Kai 7 minit bbu Wanda yyi mgn"sumayya kuwa tunani tayi aranta gara ko gaidashi tayi kawai...shikuwa gogan yad'auki alk'awarin muddin bata gaisheshiba to saidai su dauwama ahaka...INAA WUNI?"tafad'a batare data kalleshi ba "yatsina fuska yyi"bayan yad'auki kusan second 10"kafin yace LAFIYA!
inaso nabaki shawara! yafad'a Yana hararar ta"yyinda itakuma bata yadda ta kallesa ba"cikin d'aure fuska tace..banida wata damuwa bare abani shawara"sannan ko Ina neman shawara bazan iya nema agunkaba ko d'aukar shawarar taka sbd haka karik'e abarka"damuwa ta guda"shine aurenka... murmushin rainin hankali yasaki Mai sauti kafin yace "akansa nakeso nabaki shawarar ai"inba akansaba kin Isa kisanni balle har nabaki shawara!hmmmm hakane gsky"saidai inaso kasani akan aurenka bana neman shawara nabarwa Allah komai"Amma inzaka iya bijirewa Kai yashafa Kuma hakan zaimun dad'i wlh...ke k'aramar marar kunya...muddin kika yadda kika shigo gidana saikin gwamce Zama gidan yari akan Zama agidana"yafad'a Yana mik'ewa tsaye Yana huci had'e da nunata da yatsa"yace wawiya kazama !kinyi kwantai shiyasa aka lik'amun...nasan aranki kinaso ayi auren...gulma tasaka ki nuna bakyaso to wlh muddin kikasaka sakaryar zuciyar ki tasoni zakisha wahala..sbd ni bazan tab'a sonkiba...shiru kawai sumayya tayi sbd zuciyar ta ta kare datayi mgn kuka zatayi..dama abinda tayiwa gudu a auren nan kenan yarik'a wulak'anta...wayoyinsa yad'auka"cikin izzah da gadara yabuga k'ofar da k'arfi yafice....Dr Nasir kallo d'aya yamasa yagano azuciye yake,hakan yasa yasharesa har suka shiga mota"yabarshi sayi mgn da safe bayan ya huce...
Sumayya kuwa Saida ta share hawayenta"kafin ta d'auki ruwa aroba ta fice "bakin parlourn tatsaya ta wanke fuskarta"tukum ta koma part nasu "ta hau online anan taga sameera sai sannan take sanar Mata auren daza'a Mata"Samira kuwa taji dad'in hakan sosai"sbd Sumayyar ta tab'a sanarmata abinda Dr safana yamata time d'in dataje asibitinsa...har tana zolayar sumayya da cewa dama abin yakoma soyayya k'awata!sbd jin haushin maganar Saida sumayya tayi kwana2 bata Mata mgn.... mama kuwa batabi takan Sumayyar ba...
"Kwance yake abed room d'in sa "gaba d'aya bacci yak'auracewa idanuwansa sbd irin maganganun da sumayya ta fad'a Masa..yyi murmushi had'e da gyara kwanciyar sa sbd irin abinda yashirya Mata inta shigo hannunsa"gaba d'aya sai yaji bayada wata damuwa yyi kwanciyar sa har bacci yyi awon gaba dashi..
****************
Hakafa rayuwar tayita tafiya"ayanzun haka musty yakoma bayan yagama week end d'insa"haryanxun Kuma zarah taki amincewa dashi"shikuma yak'i Dena nuna Mata soyayyarsa dukda har yanzun Yana shareta...ummi kuwa tasaka musu ido"ta maida hankalin ta ga Yaya Aliyu akan hidimar aurensa"ayanzun haka aikin part d'in dazasu zauna akeyi... hajjah da anty zainab sunyi farin ciki sosai da wannan aure"ayanzun haka anty zainab ummi ta wakilta had'a lefe... dukda Yaya Aliyu besan yanuna bayason auren "Amma lokacin da ummi tamasa mgn yaciro kud'i a bank afara siyayyar lefe tub'urewa yyi"Saida tamasa Jan ido...
*6 weeks ago*
Abbane da anty zainab sai ummi tsaye "bakin k'ofar labour room"kallo d'aya zaka musu kagane cewa suna cikin damuwa... k'arar bud'e k'ofar da akayi yasaka dukansu dubar k'ofar... nurses ne 2 suka fito fuskarsu awashe"hakan yasa Abba sakin ajiyar zuciya had'e cewa yayadai ta sauka??"
D'aya tace eh Masha ALLAH !tasamu twins duka maza... Alhmdllh Abba yafad'a shidasu ummi ,bakinsu awashe....
Zaune sumayya take a porlorn su ,gaba d'aya hankalinta atashe yake sbd ganin su mama na asibiti tun d'azun baa Kira ance ta haihu ba"wayarta ta kallah had'e da dauka ta binciko number in mama ta Kira...wata nurse ta d'aga tana cewa me wayar tayi bacci tana d'akin hutu... sumayya tace ta saukane?"nurse d'in tace eh...wani ihun murna tasaki.hakan yasaka nurse d'in kashe wayar tana dariya... sumayya na k'ok'arin tashi aka hank'ado labule aka shigo...jidda da safeenah ce" bbu ko sallama"kallo d'aya sumayya ta musu ta d'auke kanta"aikin banza agola kafi d'an masu gd inji masu iya mgn...to bari kiji tunda uwarki ta shiga ta fita kunyiwa Abba asiri sbd ki auri Yaya Aliyu dashine mijin da Zan aura ko?"cewar jidda tana watsawa sumayya mugun kallo.. Wani irin b'acin Rai sumayya taji"ana ci Mata mutunci akan wanda baya gabanta ,shima baya sonta"banza y'ar k'auye kawai" tunda anzo anacin jar Miya da cinyar kaza aidole kiyi shiru"Kuma muguwar uwarki acan asibitin zata mutu bazata iya....dakata !kinzo inda bazan iya jurewa ba wlh"ince dai akan Ina zaune gidanku kukemun haka ko?"to bazan d'auki irin wannan cin kashinba..inhar keba marar kunyar k'arya bace kibari gaban Abba da jama'a saikiyi wannan rashin mituncin...ke y'ar iska dakata wlh karki nemi kimana rashin kunya"muyi miki mugun duka wlh...cewa safeenah tana hararar sumayya... murmushi sumayya tayi had'e da cewa inhar zaku iya hakan to Bismillah!duk sakarcin dakuke yi bana kulaku"sai yanzun dakuka saka mahaifiyata... sannan maganar Yaya Aliyu dakike yi"nacewa da shine Zaki aura...a wasik'ar jakinki ko kike tunanin hakan ?uwar data haifeki ke wasik'ar jaki...hmmm bbu komai taki kika zaga "cewar sumayya tana mik'ewa tsaye fuska a'daure"ta dubi jidda ido cikin ido"tace inaso Dan ALLAH bayan na auri Yaya Aliyu kiyi k'ok'ari kishigo ata 2"nikuwa namiki alk'awarin barmiki shi"amma kisani Yaya Aliyu keba choice d'insa bace Kuma agabanki Zan nuna Miki shi NAWANE....cewar sumayya !saidai maganar ba har ranta takeba ,tafadi hakan sbd tabawa jidda haushi...jidda kuwa sbd tsabar bak'inci batasan sadda tayi kukan kuraba takaiwa sumayya cafka...karki kuskura ki tab'ata!cewar anty zainab (kanwarsu Abba) .dg sumayya har jiddan juyawa sukayi suka kalli bak'in k'ofar"wani mugun kallo anty zainab tamusu had'e da cewa ba shakka inbakuyiba da ance ba jamilah ta haifekuba"yanzun har part nasu kuke zuwa kuyi rashin mutunci?"
Tun d'azun Ina jinku abakin k'ofa"inda banzoba dukanta zakuyi kenan?"
Kicin kicin da fuska jidda tayi tana gunguni k'asa k'asa...anty zainab tace kiyi yadda zanji Mana marar kunyar banza da wofi..ai wlh Koda Aliyu yace ke yakeso bazan bada goyan bayan ki aureshiba! sbd baki dace dashiba"kaf halin mahaifiyarku bbu abinda kika bari... Sadiq ne na k'warai a y'ayan hjy jamilah.gsky adena zagar Mana uwa!cewar safeenah tana turo Baki...anty zainab tace zaku fice kubawa mutane guri ko kuwa?"amma kusani dg yau ko ance kusake zuwa part d'in nan kuyi rashin kunya baza kujeba"kaf saina zayyane wa Yaya abinda yafaru...jidda da safeenah suka zaro ido sbd sun San halin abbansu..ji sukayi tamkar subata hakuri "amma girman kai yahana , musammun tunda agaban sumayya ne.. k'ofar suka nufa zasu fice"anty zainab tace sai kuyiwa uwarku albishir "Maryam d'in dabakwaso tahaifi y'an 2 duka maza...duka maza??"jidda da safeenah suka furta atare"suna ficewa..tsaki anty zainab tayi had'e da kallon sumayya dake tsaye tana sauraronsu ,tace muje ciki sumayya dg asibiti nike. nazo daukarwa mamanki kayane dazata canza... murmushi sumayya tayi had'e da cewa to anty Ina wuni?"lfy lau sumayya kiyi hakuri kinji"insha Allah kece da riba ki barsu da halinsu"YAU DA GOBE zatayi aiki akansu indai rayuwace.... y'ar dariya sumayya tayi had'e da cewa lahh bbu komai anty!kafin su shige bed room d'in mama...
Zaune suke a parlourn gdn"mama ce sai anty zainab (kasancewar ana zata zauna har ayi suna sbd tarabu da mijinta sbd bata haihuwa)sai sumayya dake zaune kan carpet tana rik'e da baby guda"yyinda gudan ke hannun anty zainab....hjy jamilah bbu ko sallama ta shigo afusace"sai huci take. tana cewa zainab ! zainab!!Ina kike juya? murmushi anty zainab tayi.sbd dama tasan muddin sai hjy jamilah tazo sbd tasanar wa Abba abinda su jidda sukayi...yakuma hukuntasu .kallon ta tayi had'e da cewa gani ! Mai abun haihuwa 'to dukda Ina juyar na godewa Allah daya bani ilimi da hankali....ke dakata !rashin kunya zakimun sbd kema anbaki kinsha ?akan agola zakiyiwa y'ayan d'an uwanki sharri "ki had'a d'a da ubah ko?" Sbd ke bakisan zafin haihuwa bako?" To Bari kiji ni warkice daidai k'ugun kowa"bacin kungama kilbibinku na rakata labour room"shine saikin debo jiki kinzo sbd kima yarana sharri"yo Allah natuba saime?"ai bakan wannan alh yafara haihuwa ba"ke Kuma algunguma keda y'arki dani kuke zance" inhar tacika y'ar halak dg yau tadena Zama agdn nanzakusan kunshiga gonata...hjy jamilah ta fad'a tana yiwa k mama mugun kallo! murmushi mama tayi had'e da cewa ni bana fad'a! fad'a sai jahili sbd haka damuwarkice "Ina cikin farin cikin kyautar da Allah yamun...mitss taja tsaki had'e da cewa oh nikike cewa jahila kenan?"shiru sukayi suka k'yaleta harta Gama tujarar ta ta fice...anty zainab tace Allah yakyauta...
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
Ahakafa akayita karban barka har ranar suna yazagayo"yara sukaci suna UMAR da DA USMAN (wato sunan mahaifin Dr safana da sunan Abba)ana kiransu da muzaffar da mu'annas...hjy jamilah kuwa zahiri take nuna b'akin cikinta afili"duk wata hidama da akayi bbu ita bbu y'ayanta basu shiga.anty zainab kuwa washe garin suna Takoma gdn hajjah"ummi kuwa tsakaninta da hjy jamilah sai harara"musammun sbd taga harda ummi aka Kai mama asibiti ta haihu..ummi kuwa Bata damuba ,sbd halin hjy jamilah ba bak'onta bane..
Gefe guda Kuma bikin Dr safana da musayya sai k'ara matsowa yakeyi"ayanzun haka saura 3 week bikin...har angama Gina inda zasu zauna... sannan tun zuwan farko da Dr safana yyi besake zuwa Gurin sumayya ba"Dr Nasir yaso suzo sbd suji ko akwai event d'in da za'ayi"amma Dr safana yace baza'ayi bidi ar komai ba.sai inzai auri rukky"wato auren SO...amma dukda haka Dr Nasir yace shizaije yaga Sumayyar da k'awayen ta...itama sumayyar anata b'angaren bata buk'atar ayi wani event"saidai Koda anty zainab taji"cewa tayi dole ayi....
WA'AZI , MOTHER'S EVENT DA KAMU...Kuma dole Dr safana yaje kamu da kanta zata sakashi yazo...itadai sumayya jin anty zainab kawai takeyi batace komaiba"sbd aganinta ai saiyazo sannan yaji dame dame za'a yi"tasan kuwa ba zuwa zeyi gunta"shiyasa Koda Samira tayi Mata magana akan ina Invitation card?"biki saura3 weeks"yaushe har zasuyi inviting din friends d'insu?ai yanzun yakamata biki saura 3 weeks sufara gayya..itadai sumayya shiru kawai tayi"sbd ada ganin abun takeyi kamar wasa"Amma ganin anfara shirye shiryen biki yasakata gasgata abun,dakuma kayan Mata da aketa bata dana gyaran jiki...dukda batason Sha saidai bbu yadda ta iya..
********
Ayau yakama lahadi"biki yarage saura 20 days akuma yau ake kawo lafen sumayya...gaba d'aya shirye shiryen tarban bak'i akeyi"anty zainab da Inna mariya (matar baba Iliya)sai hjy bintu(k'awar mamace anan makwab tansu take) sune keta hidimar abinda za'a tarbi bak'i dashi...yyinda mama ke gefe da twin's dinta sbd tana Kara da alkunya na d'an fari"saidai kallonsu take tana zaune...hjy jamilah kuwa tunda taji yau ake kawo "tasaka ido tana jiran 4pm tayi suga kayan lefen...dukda zuciyar ta acunkushe take akan abinda Abba yamata na cewa sai ana gobe daurin auren sumayya Sadiq zaizo...bacin tunda yatafi kusan 2 month kenan. saidai suyi waya amma be zo gidaba..sai Abba yanuna mata cewe sbd Aliyu zaizo badan Sumayyar datake k'i ba....
Ummice zaune da zarah da wasu k'awayen ummi sunata duba kayan lefen...wayar ummi tayi ringing... d'agawa tayi tana murmushi had'e da cewa autana kayi wuyar gani!sai yaushe zakazo bikin?"wlh bansaniba ko d'azun zarah tamasa mgn da safe akan me da me za'a yi?"yamata banza..to shikenan...ta fad'a tana yanke wayar"zarah ta tabe baki had'e tashi sbd tayi wanka tunda da ita za'a tafi..ummi ta dubeta had'e da cewa auta yace sai saura kwana3 biki zaizo"Allah yakaimu kawai zarah tace tayi tafiyarta..
Da misalin karfe4:30 pm"bakajin komai sai tashin bud'a a part d'in mama sbd kayan lefen sumayya tuni sun iso"Yan uwansu na Kano da mak'ota da abokan arziki had'e da dangin Abba sunata ganin lefen sumayya akwatina12 da sark'an gold da zobenta....Masha ALLAH! abin sai Wanda yagani komai yaji akwai manyan suturu na alfarma...hjy jamilah tagama gani da k'yar ta daure wa zuciyarta ta nufi part d'in ta...tana shiga tasami yayarta saratu...byn sun gaisa ta dubeta had'e da cewa Ashe y'ar kishiyarki alh zaiyiwa aure?"tab'e baki hjy jamilah tayi had'e da cewa aikuwa abinda yasa bana murna d bikin shiyasa wani nawa be saniba...Yaya saratu tace Wai jamilah har yanzun bakisan annabi yayi wafati yabar duniya?"kiyita abubuwa"yanzun ace ga jidda nan ta kammala NCE d'in ta Amma batayi aureba"badon komaiba sbd duk Wanda zaice Yan sonta saikin kawo wata makusa akansa "kin nuna akwai wani nakasu atare dashi...kwanaki har gdnsu yarinyar nan khadija (first love d'in Sadiq)kika ci Mata mutunci itada iyayen ta akan tarabu da sadi...sbd ke yanzun abin jindadine agunki ace ga y'ayanki ba'a aurar dasuba sai agola?"Kinga Yaya saratu Dan ALLAH kirabu dani naji da abinda ke damuna Dan ALLAH...tashi tsaye Yaya saratu tayi had'e da cewa bbu komai"inkinada rabo kya gane wata Rana"nizan wuce gd"amma sainaje naga lefen na musu Allah yasa alkhairi...tabe Baki hjy jamilah tayi... yyinda Yaya saratu ta fice...
Zaune yake a compound d'in gdnsu sbd marece yyi Yana Shan iska"sanye yake da Fara k'ar d'in t shart da dark blue din jeans..kansa da sajensa yasha gyara sai shek'i yakeyi"idonsa alumshe Yana tuna irin rigimar da rukky tagama masa d'azun akan wannan k'addarar bikin nasu..Horn yaji"hakan yasa yakalli bakin get yaga motar Dr Nasir ce...tsaki yaja Yana shafa k'atuwar sallayarsa dake tsakkiyar goshinsa take k'ara Masa kyau...da ido kawai yaketa kallon Dr Nasir dake waya Yana cewa eh anty ganinan nazo ,yanama nan..ok yafad'a Yana kashe wayar had'e da yiwa dr sallama Yana Zama kusa dashi...ango ango!! irin wannan kyau haka?"inaga sumynka ta shigo hannunka ai....pls inkasan maganarta zaka cigaba damun pls katafi kawai...uhummm aikuwa saidai kayi hakuri sbd wlh akantane"yacigaba da cewa anty tasameni d'azun a office byn katafi"akan me da me za'a yi event na biki?"tsaki Dr safana yyi had'e da saikace Mata me?"tab'e baki Dr Nasir yyi had'e da cewa nafad'a Mata ra'ayinka"tace in nazo innasameka na kirata"naku ma kiratan...kaga saitazo tunda ita ta Isa dakai saika bi umarninta...Dr safana yace kaga mlm baza kuzo ku had'amun zafi biyuba...shiru yyi sbd hango anty zainab da yyi....byn ta iso taja kujera ta zauna suka gaida ita...kafin fuska bbu wasa tace"Aliyu nasan Nasir yasanar maka dalilin zuwana"shin meyaza zaciyarka bata tank'waruwa ne?"to bari kaji"Koda ba'a yi bidi'a ba ,dole kayi invitation card kabata tarabawa k'awayenta...ni Ina neman alfarma kabari ayi WA'AZI MOTHER'S EVENT DA KAMU....shiru yyi kafin yace za'a yi anty! amma banda kamu...inhar bandashi duka afasa"cewar anty zainab cikin fushi... yyinda Dr Nasir yyi shiru ga dariya nacinsa... ahankali yace to shikenan za'a yi duka anty"yauwa my son ko kaifa"insha ALLAH YAU DA GOBE saikayi alfahari da auren sumayya.kallon Dr Nasir tayi had'e da cewa Dan ALLAH kuyi mgn da Wanda zai buga katin. ko zuwa gobe agama sai kokaine ka kaimata"tunda yau saura19 days...sunfara gayya d wuri....Dr Nasir yace insha Allah dama zanje naga k'awayenta muji abinda za'a Basu"hakan nada kyau Nasir "bana shiga ciki"tafad'a tana barin wurin...Dr safana ya harari Dr Nasir had'e da cewa inzakaje karma kasanarmun sbd bazan jeba"cikin tsokana Dr nasir yace bbu komai saika jira aka maka ita"ranar nasan saikayi 1month baka fitaba"wani punch Dr safana yakaimasa yyi saurin kaucewa Yana dariya...
€€€€€€€€€€€
Kamar yadda Dr Nasir ya tsara hakan takasance"byn yabata invitation card"yabukaci ganin k'awayen"hakan yasa ta hadashi da Samira..duk abinda yadace yabasu...
Hidima akeyi bbu Kama hannun yaro"yyinda sumayya ke cikin damuwa da tashin hankali daurewa kawai takeyi sbd bbu yadda zatayi...batun Kaya kuwa Abba yacewa mama baya buk'atar komai tayi...Amma dukda hakan kudin da dangin uban sumayya suka kawo 100K da abinda ke gareta Dana gudun muwar y'an uwa da abokan arziki ,tayiwa sumayya kayan kicin nagani na fad'a...
Masha Allah anyi wa'azi jiya"yau Kuma akeyin kamu gobe daurin aure akuma ranar ake mother's event...
Ajiya musty yasauka garin"yyinda Sadiq yau Yana hanya...
Da misalin karfe 4:25pm....
Share
By mmn fareesa 🖊️