Breaking News

SAMEEHA J


*_🧕SÂMÊÊHÂ🧕_*

              (J)

 A cikin Æ™asashen duniya daga ciki akwai chaina,dubai,da saran Æ™asashe masu harkar cinikaya da 9ja,yana da Æ™anne biyu mata da iyayensu suka rasu suka bari,shiya zama uwa da ubansu har suka sami mazajen aure a lokacin ya duÆ™ufa da sana'arsa iya cikin Najeria,Hajiya fatima ita ke bin Alhaji bukar sai Æ™anwarsu bilkisu wadda a yanzu take a abuja huse tana auran wani hamshaÆ™in É—an kasuwa dake harkar atamfofi,duk wata babbar atamfa Alhaji kasim shiyake safararsu daga dubai zuwa Najeria,si dai Allah bai azurtashi da yaro ko É—aya ba a tsakanin sa da hajiya bilkisu har yanzu,hajiya

fatima kuwa a nan kano kusa da Alhaji bukar take a wata unguwa da ake kira da gandun albasa,yaran ta huɗu,uku maza mace ɗaya,gidan kishiyoyi hajiya fatima ta faɗa amma duk da haka lafiya ƙalau take zaune da kowa,mace ce me haƙuri bata da faɗa ko kaɗan,idan kayi mata abu me daɗi da akasin haka murmushi ne kaɗai zai haɗaku,ya rabaku,hakan yasa ta baiwa ƴar uwarta hajiya bilkisu Hamida tun tana ƙarama,zumunci da ƙauna haɗe da shaƙuwa me ƙarfe yashiga tsakaninsu duk abinda hajiya bilkisu ta mallaka tofa hajiya fatima ma ta mallake shi,abin kowa na ɗan uwansa ne har yaran.

    A lokacin da Alhaji bukar yayi auran fari da matar sa Amina,suna mugun son junansu koya yayi magana É—aya to ta biyun fatima da bilkisu zai furta hakan yasa Amina ta riÆ™esu kamar Æ´an uwanta uwa É—aya uba É—aya zumunci me Æ™arfi ya shiga tsakanin su su kashe su bunne Alhaji bukar bai ma san ana yiba har cewa yake Amina ta Æ™wace masa Æ´an uwa ta wareshi shi kaÉ—ai dan sunga bashida É—an uwa namiji ana haka Allah cikin ikon sa ya baiwa Amina ciki ta sha wahalar laulayi kafin yayi Æ™wari yau idan fatima ta zauna a wajan ta,gobe bilkisu ce zata zauna haka suka dinga yi dan taimakawa matar yayannasu har cikin yayi Æ™wari ta fara ayukan ta na yau da kulum kamar ko yaushe har cikin ya kai watan haihuwar sa.

         """,karku so kuga yadda Alhaji bukar da Æ´an uwansa suka kwallafa rai akan Æ´a ko É—an da Amina zata haifa kaya tun tana murna har sai data fara fishi akan wanda Alhaji bukar yake siyowa musamman da aka ce É—a namiji zata haifa,Alhaji bukar ya dinga murna yana dariya shima ya kusa samun aboki kuma É—an uwa,É—a a wajansa, acewar sa duk saiya rama haÉ—e masa kan da akayi aka wareshi shi kaÉ—ai,dariya Amina da Æ™annansa suka saka,suka ce sunji sun ga ni shima layin su zai shigo idan Allah ya kawo shi duniyar,ba ayi kwana biyu da wannan muhawarar ba Amina ta tashi cikin dare da ciwon na Æ™uda kafin a kai ga asibiti jini ya É“ale hankalin kowa ya tashi akayi sauri akayi asibiti da ita,da gudu likitan daya ke kula da ita ya amshe ta yace Alhaji bukar yasa hannu da sauri ayi mata aiki sakamakon jinin data zubda bazata iya haihuwa da kanta ba saboda jikinta duk ya saki,nan da nan Alhaji bukar ya rattaba hannu aka shiga da Amina É—akin tiyata.





""Allahu akhubar,duk me rai mamaci ne,Amina rai yayi halinsa Allah ya karɓi abarsa bayan likita yayi nasarar ciro ƙaton jaririn ta me kama da ita sak,ko ganin yaron batayi ba ta cika,kar kuso kuga yanda Alhaji bukar ya fita hayyacin sa lokaci ɗaya ya sauya banda sumbatu babu abinda yakeyi,bilkisu na ƙanƙame da gawar tana,"Ƴar uwata ki tashi kiga abinda Allah ya baki,kar kiyi mun haka Amina dan Allah ki tashi,ga jaririn naki,innalillahi wa inna ilaihirraju'un Amina ki farka karki mutu Amina dan Allah ki tashi kiga kyautar da Allah yabaki.........fatima na kuka bilkisu nayi Alhaji bukar nayi,su kansu likitocin kwalla suke zubarwa abin akwai tausayi musamman da jaririn ya fara kuka yana ƙoƙarin saka hannunsa ɗaya abaki,Alhaji bukar ya amshe shi yana kuka ya ɗorashi kan Amina dake kwance kamar ka taɓata ta tashi,daga nan aka garzayo gida aka suturta Amina da ƴan uwanta aka miƙata gidan ta na gaskiya a ranar daga Alhaji bukar har ƴan uwansa basu rintsa ba,ko bacci ɓarowa bai saka su koda dai da gyangyaɗi ne ba banda kuka babu abinda suke yi barin ma da jaririn ya soma kuka.

"madara aka shiga bawa baby,ganin tana sa cikinsa na kumbura aka zauna shawarar yanda za'ayi,da fari dangin Amina sun so karɓar jaririn Alhaji bukar yace sam shi babu wanda zai rabashi da ɗansa ba zai bawa kowa ba,shi zai raini abinsa bilkisu ta ce ita abata shi ko me akesha nono yazo zatasha ta shayar da yaron fatima tace,Aa tunda ita bata jima da yayen Muhammad ba,abata shi zata shayar dashi insha Allah ba za'asamu wata matsala ba ko daga ɓangaran mijina ne,ita ko bilkisu duba da yanda bata taɓa haihuwa ba,ga kuma mijinta ba lallai ya amince da hakan ba haka kuwa akayi,fatima ta soma shan duk wani abu da zai dawo mata da ruwan nono,nan da nan abu yazo ta karɓi,Muhammad wanda ake kiransa da Sameer ta fara shayar da shi cikin ikon Allah yaro ya amshi nono bai wata biyu ba ya koma ƙato dashi nono ya amshe shi ga ƙarfi da yawaitar lafiya,ko ɗan zazzaɓin nan da yara kanyi shi babu abinda yayi har ya soma wayo Alhaji bukar na zuwa ganinsa duk sati wani zubin ma satin baya kaiwa har ya fara ƙetare Nageria yana barin ƙasar.




   ...........Kwanci tashi ga mai yawan rai har Amina ta cika shekara biyar da rasuwa lokacin Sameer ya girma masha Allah dashi musamman daya samu kulawa daga wajan Æ™anwar mahaifinsa yayi kyau dashi kamar a hannun mahaifiyarsa,a tafiya tafiyan ne Allah ya haÉ—a Alhaji bukar da momy lokacin tana goyon wata yarinya da bata fi wata takwas ba ta sanadin wani dayake bashi labarin mijin tane ya yarasu ya barta da ciki gashi an rasa inda Æ´an uwansa suke ga ita kanta nata Æ´an uwan ba Æ™arfi garesu ba duk sun guje ta kullum sai taje tayi wanki da wanke wanke a gidajen masu kuÉ—i take samun na lasawa idan ko Æ´ar ba lafiya sai abin ya baka tausayi,Alhaji bukar yaji tausayin ta sosai ya amince zai aureta ya taimaketa har yarinyar ta ta,shima yana da marayan yaro yana hannun Æ´ar uwarsa ba aÉ—auki dogon lokaci ba aka gama shirin haÉ—a komai aka É—aura aure momy ta tare da Æ´arta a gidan da Alhaji bukar ya gina sabo Aljannar duniya.


      Shigar momy gidan Alhaji bukar gaba É—aya hankalin ta ya tashi ta É—irsawa zuciyarta sai ta mallakeshi da dukiyarsa gaba É—aya data lura yana É—ora sunan É—ansa akan komai nasa ta fara kishi da baÆ™in ciki nan da nan ta bazama neman haihuwa,haihuwa taÆ™i zuwa,ba Æ™aramin kashe kuÉ—i momy tayi dan ta haihu da Alhaji bukar ba maganin hausa dana asibitin ba wanda bata shaba,data sha zakaga kamar bata shaba har ta yaye Æ´arta Zainabu abu wadda ake kira da Zee Zee.


""Kishi Momy tashiga yi dasu Hajiya fatima da bilkisu ba dama taji ɗan uwansu ya kira suna gaisawa ko anbawa Sameer yana ta gwalangwalansa dake sa Alhaji bukar ɗin dariya harda ƙyaƙyacewa ran momy ya cika ɓam ta kasa zaune ta kasa tsaye dolle sai da tashiga tsakanin Alhaji bukar da ƴan uwansa lokaci ɗaya yaje har gida ya ƙwato ɗansa da sharaɗin kar su kuskura su ƙara zuwa inda yake su saka aransu basuda wani ɗan uwa a duniya shi ya daɗe da ciresu a ransa har abada.


Wannnan magana ita take saka hajiya fatima kuka wiwi da rashin abin ƙaunarta Sameer bacci ne kaɗai ke rabasu ko baccin ma sai tajira yafarayi, yayi nisa tukuna take tashi taje ta kwanta ganin sameer take kamar mahaifiyarsa gashi mahaifinsa ya ƙwaceshi ya kuma saka takun kumin hana zuwa ganinsa har asibiti sai da hajiya fatima ta kwanta akan rabata da Sameer yaran ta suka dinga kuka zata mutu,daga baya ta fawalawa Allah komai,,hajiya bilkisu ba haƙuri ta daki ƙafa taje gidan yayan nasu,da kuka ta dawo da alƙawarin ita da gidan har abada saboda kafin ya sauko ma yazo ya sameta yafi awa guda a sama bai sakko ba,daya sako ɗin ma yaganta sheƙeƙe ya dubeta yayi mata korar kare daga ƙarshe matarsa ta zageta tas,ta hana Sameer zuwa gunta har tafita daga gidan tana jiyo ihu da kukansa yana kiran AUNTY NA,AUNTY NA NI ZAN BITA....


        Da wannan damar Momy ta Æ™ara maimaye kan Alhaji bukar baya ganin kowa da gashi sai ita da Æ´arta,ko mutane sun tsegunta masa halin momy,zagi da masifa ce tsakaninsu dashi sun sakawa iyalin sa ido zagin mutane da shawarar da wata aminiyar momy ta bata na janye Sameer ta kyautata masa yanda shima zai taso sai abinda tace dashi,ta hakan zata Æ™ara samun Alhaji bukar a tafin hannun ta,hakan kuwa tayi idan ba momy ba sameer bai san kowa ba har sanda yayi aure ita yake gani kamar mahaifiyar sa,ko auran sa ma,Allah ne ya Æ™addara za'a É—aura dan sai bayan auran ma su hajiya fatima suka sani.




*CIGABAN LABARI📖*



       "Ko da zee tayi É“arin su Sameer ki ciÉ“us sukayi da Sameeha ta fito daga É—aki, zuru zee tayi tana kallon Sameeha,itama Sameeha ta kalle ta,da mamaki zee ta furta,,""yaya ita da aka ce tazo ta duba ko Sameeha ta wula,zata tarar kamar yanzu ta diro duniyar ba shiri ta juyo tayi É“angaran momy da sauri har ta Æ™arasa ta kutsa dakin kai tsaye ta na""""


""Momy ga baƙin labari,ido momy ta zubawa zee tana soraron abinda zata faɗa daga zaune,zee ta ƙaraso ta na"""


"Momy garau yarinyar chan take na rantse da Allah kamar babu abinda ya sameta,a tsaye fa naje na same ta.


Anya kuwa ba gizo take yi miki ba Zainabu,yarinyar da ko motsin kirki batayi na baro ta.


wallahi zo mije kigani da idanun ki anya kuwa aikin nan yayi.


gaskiya bana shakku akan aikin mu amma muje dai nagani da idanu na,momy ta miƙe da sauri,da miƙewar momy da shigowar Alhaji bukar ɗakin kusan atare ya ƙaraso yana.


   "Maza maza É—auki mayafi ke da zee muje kuga gidan da Sameer zai zauna,yanzu akayi min waya nazo nagani ko yayi na basu kuÉ—in su,shine nace bari mutafi tare idan yayi muku to yayi mun nima sai abiya akarÉ“i takardun ku hanzarta Zainabu.


Amma Alhaji dakaje kai kaÉ—ai idan yayi maka muma yayi mana babu wani abu a ciki.



Aa tare nake son muje mu gani nasanku ku mata da ƙananan magana,dakuce nan yayi chan beyi ba,sai chan yayi kaza da kaza ku wuce kawai muje mu dawo.


Alhaji kaje mana.........Nace ku wuce muje ko sai na ɓata miki rai ne Asma'u.


kutumar..........abinda momy ta furta a zuciyar ta kenan ta ƙarasa da.


lallai ma Bukar ni zakayiwa tsawa kamar ƴarka,hmmmm laya bakya kusa amma,tayi kwafa,zan rama,"duk daga cikin zuciyar momy take maganar a fili ta zari hijabinta ƙato suka fito ita da zee suka shiga mota,sai da Alhaji bukar yazagayo mazaunin direba tukunna momy tasan shi zai tuƙa motar ba sameer ba, da tayi kamar zatayi magana sai taji an ɓame mata baki,tayi shiru har Alhaji bukar yaja motar da kaɗan ya rage su fita daga cikin gidan ta hangi Sameer yayi nashi ɓangaran da Sameeha take,haka kawai taji gaban ya faɗi suka fita daga gidan.



*IN DA RAI DA RABO,IN ALLAH YASO ABU BABU WANDA YA ISA YA HANA,SAMU DA RASHI DUK DAGA ALLAH YAKE,ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CHARA KO ANA SHAWO KO ANA MUZURU SAI YA KAI.*


"A wannan rana a dai dai lokacin Allah yayi ikonsa akan,Sameer da Sameeha,a nan fallon nasu shi kansa bai san taya ya hakan ta kasance ba tsintar kansa kaÉ—ai yayi cikin wata duniya me wahar fassaruwa.












_*By*_

_*Maman Dr*_