WAYAFI SONTA 5
p5
Kasancewar bbu nisa dg Gurin zuwa gdnsu zainab....hakan yasa ,gidajen 2 suka Sami labarin abinda ke faruwa"gaba d'aya mama d Inna Basu ahaiyacinsu.....cike da tashin hankali suka d'unguma cikin motar baffa sule, zuwa asibitin da aka sanar musu ankai Umar da zainab.... yyinda goggo haule tayi zamanta gd... emergency aka nufa dasu su duka"yyinda wadanda suka kawosu suka tsaya jiran
tsammani! Saiga su baba ,Abba,baffa sule ,mama,Inna sunnufo Gurin cikin tashin hankali.... adedenan likitoci 2 suka fito suna share gumi, fuskarsu kad'ai zaka kalla kasan bbu lfy" guda yadube su yace Ina iyayensu suke?"abbayace gamu" dr yace pls kibiyoni office....Bbu Wanda yazauna acikin baba
d Abba da Baffa Sule! Dan su Inna na waje..Dr yyi gyaran murya kafin yace kusan
ita k'addara da jarabawar rayuwa bbu Wanda yawuce ajarabesa ko ak'addaresa da
Mai kyau ko akasanin haka! Cikin tashin hankali suka ce eh hakane kasanar Mana
meke faruwa ne dasu?" Dr Kai duk'e yace KULLU NAFSIN ZA'I KATUL MAUTE.... ALLAH ya karb'i ran wannan
namijin....kuyi hakuri kuyi Masa addua hakan shi yafi" dabai mutuba gsky
akwai matsala! Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un su baba suka furta atare!!
abba yace ALLAHU AKBAR! Yah
ALLAH ka jik'an Umar kayimasa rahama ,halinsa nagari yabisa....Yana fad'a
kwallar daya rik'e tana zuba....baba kansa aduke yake yyi shiru shida Baffa
Sule...can baba yakalli Dr Ido jawur yace ita zainab wane Hali take?"
Cike da tausayinsu Dr yace
gsky itama tana cikin had'ari sbd kwakwalwarta t juya sosai zuciyar ta ta buga
sbd abin yafirgitata Ina zaton agabanta akayi,tayi doguwar suma sai anjima zata
farfad'o...saidai da wuya ta farfad'o tana mgn gsky....cikin tashin hankali
abba yace banganeba likita?"
Dr yace kuyi hakuri! gsky irin k'arar datayi
ta wuce tunani har abin yashafi mak'ogwaronta dole amata aiki "saidai
damuwar gudace "gsky kudin aikin sai sunkai kusan miliyan 2 da rabi sbd
ak'asar waje za'a matashi..k'asar waye??" Suka maimaita atare...Dr yace eh
gsky insha ALLAH da ammata zata Sami lfy....Amma dukda haka zata iya farkawa
kuji tayi mgn abun ALLAH Amma Ni abinda muka gani bayan mun binciki lafiyarta
kenan...Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un kawai suke maimaita wa Dan sunsan
basuda wannan kud'in aikin ko baffa sule dayafisu wadata "agdn uban gdnsa yake a kabasu part guda sbd gdn nada
girma.... sannan Kuma motar dayazo da ita" batashi bace...Abba yace
mungode Dr "abamu gawar Umar muje amasa suttura"ita Kuma zainab
abarta ta farfad'o muga yanayin jikin nata"Dr yace to shikenan muje...nan
suka fito,suka Sami su Inna d mama duk atsatstsaye" nan abb yajasu agefe
cikin fahimta yasanar dasu abinda ake ciki',
amma be Fadi ,suncezainab
bazata iya mgn....
Da k'arfe 6 na marece akayi
zana'idar Umar"Wanda yasami shaida sosai aunguwarsu da abokansa na skuul....Inna da mama sunsha
kuka ,gefe guda Kuma suna tausayin zainab akan babban rashin datayi....bayan
sallar magarib aka cigaba da karban gaisuwa yyinda , saratu (k'awar zainab) da
anty uwani k'anwar mama suke asibitin
gun zainab da har sannan bata farfad'o ba andai Mata allurai ansaka Mata
drip".....gefe guda Kuma goggo haule har cikin zuciyar ta a taji dad'in
mutuwar d Umar yyi kodan kada ya auri zainab yakula da ita...tana nan zaune ana
karban gaisuwa da ita....
Gab da sallar asuba zainab ta bud'e Ido"ta kalli d'akin
"ta kalli su saratu da anty uwani dake gyangyadi....atake abubuwan dasuka
faru suka dawo a brain d'inta" azatonta Kobe mutuba.... Wasu hawaye masu
zafi suka zubo mata...k'ok'arin kuka take Mai shashsheka Amma saitaji hakan
yagagara! saita bud'a Baki da nufin yin salati ,sai taji kamr anrufe bakin
,yyinda bakin ke motsi " cikin k'idima take salati had'e da bud'e Ido
sosai ko azatonta mafarki take....Amma Ina ,gashi Baki na motsi Amma batajin
maganar ta ta fito,Amma kunnenta najin k'arar fankar dake d'akin...motsi
tahauyi ... adedenan Kuma anty uwani ta farka....da sauri ta nufi zainab tana
cewa sannu zainab! Ya jikin,Ina ke Miki ciwo,Kona Kira nurses ko
Dr???"" kallonta kawai zainab keyi" tanajin metake cewa Amma ita
takasa mgn" yyinda takejin tamkar antokare Mata mak'oshi....hawaye ke
sintiri afuskarta,ita bama wannan ba Ina Yaya Umar nata?"
Zainab kinyi shiru ko
jikin?" Muryar anty uwani ta katse Mata tunani....anan Kuma saratu ta
farka sbd maganar anty uwani....nan taje tanawa zainab sannu ! Nanma zainab
batayi mgn sunjiba sungadai bakinta na motsi ,ga Kuma hawaye na zuba
afuskarta....nan anty uwani ta je ta Kira Dr...bayan yagama dubata yace kiyi
hkri zainab wannan abin daya faru dake jarabawar ki ce "ALLAH ya Baki ikon
cinyewa kinji?" Insha ALLAH zamu sallameki zuwa anjima inhar iyayenki
sunbada kudin yimiki aiki to zaa tafi dake misra"Amma nasan kinajina
saidai Baki iya mgn!kuka sosai zainab keyi ,ita bama tataba Ina Yaya
Umar?"
Kallon Dr din tayi taga biro
gaban aljihun cot di'nshi ta nuna Masa yamiko Mata... yyinda anty uwani da
saratu ke kukan tausayin zainab jin tazama Benita"zainab ga tafin hannunta
ta rubuta Ina yah Umar Dina?" Yaya jikinsa?"
Zama Dr yyi kan kujerar gaban
gadon " yafara mata wa'azi kafin yasanar Mata.... girgiza Kai take tana
kuka had'e da furta Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un! kasancewar Dr din
nada ilimin addini sosai ,yyimata nasiha akan tadage tayita ma Umar
addua"kuka kawai zainab keyi tana tuna maganganun dayata mata Wai tayafe
Masa Kuma ta Masa addua....nanma su saratu da anty uwani suka k'ara Mata
k'arfin gwiwa,akan komai zatayi bazai dawoba,abinda zatayi t nuna tsantsar
k'aunarta agareshi shine yimasa addua....
Anty uwani ta Kira abba akan
anjima zaa sallamesu, Kuma zainab ta farfad'o....d sauri Abba yace tana mgn?anty
uwani tace ah ah... had'e da sanar Masa anyiwa zainab nasiha akan ta rage
damuwa....kafin suyi sallama....duk abinda suke bukata a asibitin da abinda aka
kashe,mlm ne yabiya ( kakan zainab) kafin abasu sallama Gurin k'arfe 2 na
Rana,suka hau adaidai ta....tun farkon shiga layin aka ajiyesu.... zainab
gabanta nata faduwa duk yadda tazo daurewa takasa ,hawaye kezubo Mata,idanunta
harsun kumbura" anty uwani na rik'e d hannun ta " suka nufi k'ofar
gdn su zainab" da akayi rumfuna mak'il d jama'a agurin"d'agowa zainab
tayi tagasu baba gefe,gasu Hamza d Ido,abokan Yaya Umar na unguwar duk sunyi
jigum jigum alamar dukda ankwana dayin mutuwar suanjinta har yanzun...cikin gd
suka wuce,anty uwani ta nufi d'akin mama da zainab duk dangi da Yan uwa
tausayinta sukeji,abakin k'ofar d'akin suka hadu da anty mariya(matar baffa
sule) zainab ta fad'a jikinta tasaki kuka dukda bbu sauti" cike da
tausayinta anty mariya tayi bed room din mama da ita tana Bata Baki sbd suna
shiri sosai da zainab...inhar sunzo garin kaduna to suna tare da ira..sai
rarrashinta akeyi ,wasu na Mata gaisuwa.....
Bayan sati d'aya da rasuwar
yy Umar "zainab dukta rame batason cin abinci ga Bata mgn ,Dan yanzun
harta fara koyon maganar bebaye dukda ita keyiwa mutum nuni da body language ,
yyinda suk wanda zai Mata mgn toyimata take sbd ansan tanaji... yyinda aka
zauna akayi meeting da yan'uwa akan laluran zainab kowa ybada abinda yasawaka
,baba duk kadarorinsa yasiyar Amma abin sai hakuri"sai Dr yabasu shawara
akan afara kaita asibitin zariya d Kano ko andace...shine aka tsaida maganar
sati na sama za'a kaita...
Zaune zainab take kan kujera
Yar tsigunne da wayar yah Umar ahanunta ,spack 2,tana kallon wayar tana tunawa
dashi ,hawaye nazubar Mata, goggo haule dake tsintar wake,ta kafeta da Ido tana
cewa uhumm duk Wanda yamutu yafamutu kenan y'ar nan baya dawowa,kinbi kintakure
Rai haka.... tafad'a tana tabe baki.... adedenan wani yaro yyi sallama had'e da
cewa Wai ance zainab tazo inji Hamza(abokin Umar)
Zaro Ido goggo haule ta yi
had'e da cewa ohni Naga abinda ya isheni Wai yarinyar data nakasa ake aikowa
tazo tad'i?" Wani kallo zainab ta d'ago tanawa goggo haule....uhum...
ALLAH sarki nagodewa ALLAH daya jarabi y'ata ,dansai Mai Imani ake jarabta,wasu
sbd duhun Kai da jahilci Basu tunanin kosu Basu wuce ALLAH yyimusu jarabawar
datafi tamuba"insha ALLAH sai zainab ta Zama abin kwatance da koyi Kuma
sai mutum yazauna a inwarta,bama yiwa kowa mugun nufi ko hassada Amma duk Wanda
yyimana sai yaga abinsa.... mama tafad'a tana yiwa goggo haule wani mugun kallo,kafin
ta dubi zainab tace tashi kije , ALLAH yasan dake....
Share
