Breaking News

SAMEEHA P

🧕SÂMÊÊHÂ🧕_*

            (P)

""Do so tabarmar dake cike da maza dam sukayi a ɗan risine momy ta shiga gaisawa da jama'a haɗe dayi musu gaisuwa gaba ɗaya jama'ar suka amsa suna mai yiwa Sameeha gaisuwa da ban baki akan haƙurin rashin abba da kowa yayi,ban da kuka babu abinda Sameeha keyi har wani shassheƙa take hawaye na ambaliyi daga idanuwan ta har suka nufi cikin gidan kai tsaye.

      Mona na É—akin Umma taji an É—auki yiwa Sameeha gaisuwa da gudu mona ta miÆ™e ta fito ta rungume Sameeha gaba É—aya suka kuma dasa wani sabon kuka a tsakar gidan gida ya kuma kicimewa da koke koke musamman da ita umma ta fito gaba É—aya suka rungumo ta suna kuka suna kiran Abba umma dake basu haÆ™uri ita ma ta fara share hawaye wani na kuma sako mata Momy ma da ke gefe matsa Æ´ar Æ™wallar take dafe da kafaÉ—ar sameeha tana""


""Dota haÆ™uri a ke yi ana yiwa mamaci Addu'a kowa da haka zai tafi duk jiran lokacin mu  muke kuyi haÆ™uri Addu'arku Abba ke buÆ™ata ba kuka ba kinji ke ce babba kiyi haÆ™uri dan Allah ki dena kukan ya isa haka nan É—iya ta.


nan jama'a suka amshi batun aka shiga lalaÉ“a su Sameeha da mona da Æ™yar mona ta iya haÉ—iye kukanta amma idanuwan ta basu fasa fitar da Æ™walla ba Sameeha kuwa jin momy ta ce tayi shiru taja bakin ta tayi tsit sai mis mis da baki takeyi azumar Addu'a bata ma san me take furta wa ba idon nan ya kumbura yayi jajir dashi😫 


*INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJU'UN,Allah a baki a zuci kuma babu Allah kwata kwata momy aranki😓*


Mona ce riƙe da hannun Sameeha kamar wace zata gudu ta barta duk inda momy tayi Sameeha zata bita haka mona ma har umma tayiwa momy iso zuwa ɗakin da take zaune da sauran ƴan uwa da abokan arziƙi,momy ta dubi umma ta ce"


   "Æ´ar uwata ayi haÆ™uri rashin zuwan Sameer wlhy bashida lafiya amma insha Allah.........Umma ta dakatar da momy da"Haba momy nasan bashida lafiya maimuna duk ta faÉ—a mana halin da yake ciki a yau É—in nema Abba yake faÉ—in in yadawo zamu zo mu dubashi ashe ma Abba ba mai dawowa bane,Umma ta share Æ™wallar data cika mata ido momy ta karÉ“i maganar da"



Allahu Akhubar kana naka Allah na nashi kai duniya Allah yasa mugama dake lafiya.


É—akin ya É—auka da.



"Amin.


Har kusan yamma Momy ta kai a gidan ana amsar gaisuwa da ita duk wasu kayan abinci da nasha ruwa komai sai da momy tasa aka aje a gidan su Sameeha a cewar Sameer ne ya kira ta yace gasu nan ya turo a kawo, kowa yayi mata godiya banda yaya jummai da ko kallon kirki bata dubeta dashi ba sai wata harara dake haɗasu da zaran sunyi ido biyu da momy gaba ɗaya hankalin momy ya koma kan yaya jummai har yaya jummai ta ƙosa da kallon da momy ke nata ta zarowa momy ido haɗe da miƙewa tsaye ta bar cikin ɗakin gaba ɗaya.

    momy ce ta buÆ™aci ko zasu koma da sameeha gida a ranar mona ta fashe da matsanancin kuka haÉ—e da roÆ™on momy ta bar mata yaya sameeha ta har ayi bakwai sai ta koma idanun mutane yasa momy amincewa tayiwa kowa sallama haÉ—e da miÆ™awa sameeha kuÉ—i ko za'asiya wani abu,hankalin umma ne ya koma kan Sameeha ganin wata muguwar rama da tayi gashi gaba É—aya ta chanja a yanda take a da ko magana batayi daga umm sai aa ta takure kanta kamar bata san kowa ba har yaya jummai sai da ta lura da hakan ta ja sameeha gefe ta tambaye ta yaya zaman nasu sameeha tayi shuru duk juyin duniyar da ya jummai tayi ta magantu abin yaÆ™i tira a dole yaya jummai ta barta ta zuba mata ido tana kallon ta.


     momy na barin gidan da wasu awanni zazzaÉ“i me zafi ya rufe sameeha har karkarwa take tana sambatu maganin zazzaÉ“i aka siyo da sauri aka É“alle aka bata,sameeha na haÉ—iyewa ta dawo dashi nan fa amai yace bisimillah gaba É—aya hankali ya tashi asume aka kwashi sameeha aka nufi asbiti mafi kusa da gidan ya jummai ce a riÆ™e da sameeha sai yaya asabe da mona dake ta faman kuka tana Addu'ar Allah yasa ya Sameehan ta ba mutuwa tayi ba.



  cikin kulawa likita ya karÉ“e su gadan gadan aka shiga bawa Sameeha taimakon gaggawa da fari likitan ya tambayi dalilin faruwar abin daga bisani ya sake dawowa ya tambayi ya jummai sameeha budurwa ce ko kuma matar aure ce?


jiki a sanyaye ya jummai ta ce"


"Amarya ce ko wata biyar batayi ba.


likitan ya saki É—an murmushi haÉ—e da""



""Masha Allah ku É—in ya ya kuke da ita?


kaga malam sai tambayoyi kake mana har da wani murmushi kasan me yake damun mu zaka ringa mana dariya shin dariya mukazo kayi mana ko,ko duba mana yarinya?


gaskiya ne ya jummmai ko farfaɗowa bamu ga ƴarmu tayi ba sai yaƙe mana haƙora kake yi kana mana tambayar rainin hankali kamar wasa mukazo yi asibiti,cewar ya Asabe.

 




"Dan Allah kuyi haƙuri akan aikina nake banyi hakan da wata manufa ba,sannan tambayoyi danake muku dole ce tasani dan sanin ta inda zan faɗamuku matsalar ƴar ku kuma Alhamdulillah naji daga bakin ku ƴa take a wajanku to albishir gareku ƴarku ba wani abu bane yake damun ta ilah *JUNNA BIYU* dake tare da ita.


yo ba sai ga murmushi daga fuskokin su ya jummai ba mona kuwa rungumo Sameeha dake kwance tayi ta kuma sakin wani sabon kuka Aunty asabe ta ce da likitan.


"Dan Allah kayi haƙuri bawan Allah duk hankalin namu ne atashe ga mutuwa ga kuma rashin lafiyar Sameeha.


likitan yayi murmushi akaro nabiyu ya ce""



babu komai hajiya muna fuskantar irin haka har finsa kuma a halin da kuke dole ku furta haka sannan zaku kula da ita sosai a kan abinci masu gina jiki da ƙarin lafiya da abinsha kar kuma abata ko wane irin magani indai ba likita ne ya rubutashi ba naji kunce kafin ku zo kun bata na zazzaɓi (feaver),dan Allah aringa lura za kuma ta farka insha Allah lafiya lau laulayi sai a hankali komai zai koma dai dai (Normal).



in sha Allahu za akiyaye mun gode likita.


    yaya jummai da Aunty asabe suka furta atare kamar haÉ—in baki,ba aÉ—auki dogon lokaci ba Sameeha ta farka daga dogon barcin karku so kuga kulawa da lallama da nan nan da kowa ke mata yaya jummai ce ta sheda mata abinda likita ya furta sai gashi ma yazo ya Æ™ara duduba sameeha da wasu shawarwarin ga masu ciki da magunguna ya bada sallama bayan sun biya duk (chajis)É—in da akayi musu sukayo gida,Alhamdulillah ana jimamin mutuwa ga kuma Æ™aruwa an samu *KAÆŠAN DAGA IKON ALLAH*,inji umma kowa yayi farin ciki yabi Sameeha da Addu'a umma ma taji daÉ—i tabi É—iyarta da Addu'ar Allah ya sauketa lafiya ya bata zuri'a É—ayyiba,yaya jummai ce ta kasa ta tsare sai an kira momy an faÉ—a mata umma ta ce Aa ba ayi haka ba cikin fari ai a karanta idan Sameeha ta koma gida sa gani ko suji daga gare ta nan rai yaso ya É“aci ta inda yaya jummai ke shiga bata nan take fita ba da kanta umma tasa saratu ta kira momy asanar da ita,hakan kuwa akayi an kira momy an faÉ—a mata murna kamar zata fito daga cikin wayar har kuka tasaka wai Allah ya kawo mata abinda ta jima tana jiran gani ta Æ™ara da a kular mata da É—iyarta sosai abata duk abinda take so kar kuma abari ta kuma zubar da hawaye dan Allah.


Saratu ta katse wayar kowa na yaba irin hali na momy suruka me kirki da mutunci ga sanin ya kamata Addu'a da fatan alkhairi momy tasha shi har ta gaji a ranar.


       a É“angaran momy kuwa tana kashe wayar ta doka Æ´ar banza da Æ™asa tsabar baÆ™in cike tambayar kanta, ta shiga yi da""



""Me yasa ban murje banza na nuƙashi da kaina ba?



me yasa har na bari shashashan mutanan nan suka farga da cikin?


me yasa me yasa tunani na bai kawo haka zata iya faruwa ba kai cona na zama banza na zama shashasha,menene abinyi,ta daki jikin durowar ta sai zagaye É—akin ta ke tana furta""



bazaka zo duniya ba in sha Allahu ko komai nawa zasu ƙare na rantse da wanda ya halicce ni bazaki haifi abinda ke cikin ki ba Sameeha ko duk duniyar nan zasu taru akan ki sai inda ƙarfina ya ƙare zaro layar ta tayi ta danneta da ƙarfin tsiya rai a ɓace sarkin hatsabibai ya bayyana,sun ɗauki tsawon lokaci suna tufka da warwara har suka ƙula abinda suka ƙula ya ɓace daga ɗakin momy ta ɗauki gyale da mukulin mota ta fita.







……………………






Allahu Akhubar,har an yi bakwai É—in Abba Sameeha na gida Æ´an uwa da abokan arziÆ™e duk an cika ana Æ™ara jimantawa,har Sameer a ranar sai da yazo sakamakon da momy ta tasoshi a gaba da uban kayan sha tara na arziÆ™e ya ware tas  dashi kamar bashiba har Æ´ar tsokanar junna sukayi da mona abin ya bala'in bata mamaki har umma sai da ta kuma tara da maganar,umma ta ce sauÆ™i ya samu da kansa ya nemi Sameeha ta koma a yau momy ta É—an saka baki wai ya barta ta kuma kwana biyu bai furta komai ba sai da momy ta zura hannunta a wayence ta matse Æ™awarta dake cikin jaka da sauri Sameer ya ce.



"Hankali na ne baya nan baya gida Umma ayi haƙuri idan na takura,yana faɗi yana sosa ƙeyarsa kamar munafuki mona tayi charf ta ce"



"aiko sai dai yayi ta yawo a sararin samaniya ya sameeha sai ta sauke.


"Haba ƙanwa ta haka zamuyi dake to ai shikenan zan saka ki cikin layin manyan..........,momy ta amshi zanchan"



""kama isa mona É—in tawa guda kaje zan tawo da ita insha Allah.



Sallama Sameer yayi musu haɗe da ajiye kuɗi masu nauyi yayi kuma alƙawarin kulawa da Umma da mona kamar yanda zaiwa momy,Addu'a kam yashata sai da yatafi yaya jummai ta ƙaraso sunyi saɓani da aka faɗa mata abinda ya wakana,ta dubi momy da ita ma momy ke duban ta tace""



""Mun gode bama buƙatar taimakon kowa sai na Allah.


ya jummai ta bar É—akin kowa yayi tsit a É—akin saboda kunya,koda dare yayi jalolo yazo É—aukar su momy da sameeha kuka sosai sameeha da mona suka dinga yi duk da rashin sanin wace ce ita amma hakan ya taÉ“a zuciyar sameeha sai kallon Umma da mona take tana kuka wiwi kamar bazata sake ganin su ba da Æ™yar momy ta janyota tana bata haÆ™uri da ban baki har ta tusa ta mazaunin baya ita ma  momy ta shiga jalolo ya ja suka É—auki hanyar gida.




   Ko da suka iso gida jalolo ya danna (horn) baba me gadi ya fito da sauri ya buÉ—e (get) É—in gidan suka shigo chan gefe É—aya jalolo ya tsaida motar momy ta buÉ—e Æ™ofar motar ta fito ta zagayo ta buÉ—ewa Sameeha ma ta fito baba me gadi yayi shiru yana duban sameeha bayan yaiwa momy san da zuwa,sallamar su momy tayi cikin tsawa da É—aga murya kowa yayi inda yake momy ta kamo hannun Sameeha suka nufi É“angaranta suna shiga fallon momy na hankaÉ—a sameeha ta tafi taga taga zata faÉ—i kamar wace aka riÆ™o ta ta tsaya gam ta haÉ—e da saka kuka,zee dake kwance a kan kujera ta miÆ™e tsaye a hankali ta tako É—as É—as har daf da gaban Sameeha hannu ta É—aga ta wankawa Sameeha mari masu zafi har sau biyu sameeha ta dafe kumatun ta da sauri haÉ—e da sakin Æ™ara me razanarwa zee ta kuma sa Æ™afa ta kaiwa cikin sameeha duka,wani wulwula akayi da zee aka yarÉ“ar jikin kujerar dake fallon ta faÉ—i a kan Æ™afar da ta kaiwa Sameeha har wani Æ™ara Æ™afar tayi tsabar bugun da zee ta sha momy ta nufo inda zee ta baje a Æ™asa tana ihu da kiran momy!!! momy!!! momy!!…………………………





*Alhamdulillah,nasan fan's yau zakuji daɗi anwa zee ƙafa ɗaya😆*







_*By*_

_*Maman Dr*_