HABIBI DA'IMAN 141-160
*PAGE141~145*
"Uhm khadijah kenan yakamata ki gane ni ban can-canci
zargi a wurinki ba, kwata-kwata kwana biyun nan kinfita lamarina, baruwanki
dani ko abinci baki girka mani saidai nafita na saya naci, kanki kawai kike
dafamawa, duk miyayi zafi da zaki horar
da ruhinmu haka"
Ak'ulaface take kallonshi tace "mizai hana kaje wajen
karuwan naka su dafamaka kaci" daga haka ta tashi ta Ruga d'aki saboda
kukan da taji ya taho mata
Fita yayi daga gidan don bazai iya jure jin kukanta ba, ita
kuma tanajin tashin motarshi ta kara fashewa da kuka tana cewa"yayana ka
cuceni ka yaudareni ina danasanin saninka da nayi a rayuwata"
Girki suke ita da Mama a kitchen babu mai magana can ihsan ta katse shirun tace "wai Mama
meyasa Baba yasa akayi ma Yaya khadijah Jere a Kaduna bayan Abuja suke
zaune?"
"Saboda insun zo gidan su zasu rink'a sauka ba gidan
iyayenshi, don haka yanxu kiyi sauri ki karasa Mani girkin nan ni zanje in
shiga wanka Babanku ya kusa dawowa" toh Mama shine abin da ihsan tace
Tana gama girkin itama ta wuce d'aki don tayi wanka,
wayartace ta d'auki ringing da sauri ta d'auka tana cewa "eye amaryar nan
da 2 month's" daga can bangaren Islam tace "ai harda ke ni wallahi
gani nake ansa abin kusa sosai ko dayake angwayen ne suka matsa ba kamar Rafeeq..."
"kema kinsan
wanan sai dai Mujaheed ni su samra ma gani nayi ba ruwansu abin ta masu
dadi"
Islam tace "ke ni bawan nan ba, dama na kirakine ince
maki kawai Ku fidda duk ankon da yayi maku keda twince duk yadda kukayi kin
sanar dani kawai"
"Ok toh ba damuwa sai kinjini" daga haka suka aje
wayar
*****
A cikin kwana biyun nan laila duk ta gama had'a yadda plan
d'inta zai kasance shiyasa take farin ciki saboda gobe ne zata ai watar da
nufinta, kallonta Ashanty tayi tace
"Uhm laila a gaskiya kina shirin aikata babban kuskure
Wanda bai kamata ace na zuba maki idanu ba ina gudun abin da zakizo kina da kin
Sani, yakamata kituba tun kafin lokaci ya k'ure ma...."
saukar Marin da taji ne yasa tayi shiru tana kallon Laila da
mamaki tace "ni kika mara?.."
"eh an mareki kuma daga yau idan kisan wanan zancen
zakiyi Mani kada k'afar ki ta sake takowa
inda nake" hawayen da suka cika ma Ashanty ido ne suka zubo mata,
bawai dan zafin marin da Laila tayi mata ba sai don tausayin Laila da takeji, tare
da d'ago kai tace
"Kada ki damu bazaki sake ganina ba dama naso ace kamar
yadda muka shigo bariki tare mu fita tare sai dai Allah bai k'addara haka ba,
Don Haka ina maki ban kwana dafatan alkhairi, gobe da safe zan wuce Kano in koma wurin
iyayena in nemi gafararsu kema ina fatan Allah ya shiryeki da sauran masu hali
irin naki"
Daga haka ta fita tana tunanin yadda zata kubutar da Jiddan
daga tarkon Laila, don ta tabbatar bazai tab'a
yimata abin da takeso ba
Itakuwa Laila tsoki ta buga tana cewa "aini ba kanwar
ubanki bace da zakice mutuba tare" nan ta zauna tana zumudin gobe tayi
donta aiwatar da k'udirinta
Zaune take a palour tana kallo tana jin alamun shigowarshi
amma ko daga kai ta kalleshi batayi ba shima bai cemata komai ba ya wuce d'aki
don yayi wanka amma tunani yake a ranshi idan
ba khadijah ba'ai yi macen da zatayi mashi haka ya kyaleta ba, har ya
fito tana nan Inda take zaune, zama yayi bisa cushion d'in da take tare da aje
mata take away na abinci don haka yakeyi yanzu tunda bata dafa mashi amma idan
ya bata bataci sai dai yaci da dare domin tana dafa nata taci
Tashi tayi da niyyar ta bar mashi wurin yayi saurin rik'o
hannunta yace
"pls zauna magana zamuyi" ba musu ta zauna tare da
juya mashi k'eya, yace "aww bazaki kalleni ba?" Bata cemashi komai ba
hakan yasa yace "toh naji dama inaso ince ki shirya anjima zamuje muyi
sayayya kinga bikin mutum hudu ke gaban mu gashi ko Ihsan banga kin siyo mata
komai ba..."indai da kud'inka ne bani so kuma ban zuwa"
tashi tayi da niyyar barin wurin, saurin jawota yayi taf'ada saman kirjinshi
don bayajin zai iya d'aurewa, kiciniyar kwace kanta tashiga yi amma takasa, don
yasamata k'arfi dabazata iya kwantar kantaba,
shinshinarta ya shiga yi daga baya kuma ya Dora da kiss, tana jin haka
ta bare mashi baki tana kuka da sauri ya d'ago yana cewa "menene?"
Cikin kuka tace "bana so kabari" yace "toh
shikenan na bari amma sai kin yarda zamu fita" da sauri ta shiga daga
mashi kai tare da kokarin tashi, yayi saurin kamota yace"haba andeejana ko
kadan ne" saurin fizge hannunta tayi, tashige d'aki, dafe
kanshi yayi a hankali kuma ya furta "ina sonki andeejanah"
Suna gama sallar Asr suka fita sayayya sukayi sossai don
gaskiya ko kayan da khadijah zata sa a bikin ba kananan kudi ya kasheba har sai
da khadijah tayi mashi magana, lokacin da suka dawo sun gaji sosai don har
d'inki sai da suka bada don haka kowa ya shige wanka
A bangaren Laila kuwa tana jin baccin jiddan soldier ne
gidanshi akwai tsaro sosai daba abin da zai hana akai mashi hari cikin daren
nan saidai zata bari har zuwa gobe idan ya fito kamar yadda ta tsara
Al'amarin da ya hana Ashanty bacci shine ta sama ma kanta
mafita akan cewa gobe da sassafe zataje ta gaya masu Jiddan komai tun kafin ya
fita, da wanan shawarar bacci ya d'auketa
Da wuri yau ya gama shirinshi don yana so su tattauna da
General akan tafiyar da zasuyi gobe saboda an turasu Lagos sai dai ba wani
dad'ewa zasuyi ba duka 3 weeks zasuyi kuma lokacin da zasu dawo saura 5 weeks
bikinsu Rafeeq, shiyasa Rafeeq ketajin
haushin tafiyar
Har yaje bakin k'ofa sai kuma yadawo saboda yadda yakejin
gabanshi na fad'uwa, wurin khadijah ya nufa ya durk'usa gabanta tare da riko
hanunta yace
"bakiyi Mani addu'a ba" a hankali tace "Allah
ya kiyaye hanya" saboda yadda takejin gabanta na fad'uwa, kiss ya manna
mata a goshi tare da fad'in "thanks" sannan ya fita da sauri
Abin tsautsayi motarshi na hawa bisa babban titi suka sha
gabanshi tafiya yake ba tare da tunanin komai ba dai-dai lokacin da yashiga
wata kwana suma suka shiga, duk bailura da yadda suke binshi ba, shigarshi
kwanar daba kowa ke bin wurin ba kawai sai gani yayi ya buge mutum kamar daga
sama
Da sauri ya fito yana salati, bai k'arasa Inda Wanda ya kad'e yake ba sai
jin saukar icce yayi akanshi nan ya...
_*Mrs Abdul Sule*_
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITTEN BY*
_*HALIMA
Mk*_
DEDICATED TO
SA'ADATU ALIYU
KABUGA
*Page136~140*
*D'*auke da ciki, tunanin tane ya katse da taji Laila na
cewa "idan yazo ki bashi sannan ki gaya mashi bazan zubar da cikin nan ba
saidai in ya aureni ko kuma na haife mashi abinshi
Murmushin yak'e khadijah tayi wanda yafi kuka ciwo tace
"aidama yasanar dani komai a kanki, batun aure ma kicireshi a ranki dan
bazai tab'a auren kamar kiba marar kamun kai wanda tarabarma guys darajarta a
waje, don haka inkin haihu zaki iya kawo mana d'anmu mu rik'e"
Kallon baki isa ba Laila tayi mata tace "kece zaki iya
rik'e mani d'ana, uhmmm airik'on d'a sai uwarshi balle ke asuwa dazan baki d'a
mafi soyuwa ga ubanshi, wanda duk wanda za'a haifa mashi a bayanshi yake"
"uhmmm ni a matarshi ke kuma karuwarshi, don Haka zaki
iya fitar mani daga gida tun kafin nasa a fiddaki"
Tashi Laila tayi ta nufi bakin k'ofa sannan ta juyo tace
"zaki san kinyi da Laila" sannan ta banko mata k'ofar ta fita
Laila! Laila!! Khadijah ta shiga nanatawa yanzu abinda
Jiddan zaiyi mata kenan lalle zaizo ya sameta wata kuma zuciyar tace kada ta
yadda da abinda wannan k'adan garuwar bariki tafad'a tana sone kawai ta had'aki
da mijinki dukda dai Namiji ba tabbas gareshi ba, haka dai tayi ta tunani har
Jiddan yadawo
Tunda yadawo ta lura dashi a dirice yake itadai bata nuna
mashi komai ba amma shi yak'osa su tashi kwanciya ya kwashi shokinshi san
ranshi
Har ta kwanta yace ta tashi tayi alwala zasuyi sallah, bata
mashi musuba taje tayo, yajasu jam'i, saida suka gama yayi mata tambayoyin da
yasan bazasu caza mata kwakwalwaba tunda tana da matsala
Naman talo-talon da yayi mata alk'awari shi zasuci ranan
daren farkonsu shi ya d'auko da niyyar ya bata, dandanan kwakwalwarta ta shiga
rud'ani gani take kamar antab'a yimata irin haka a rayuwarta, lura da yanayin
da take ciki yasa yamaida komai inda yake sannan yajata saman gado yana mata
fira harya samu tamanta
Lokacin da yafara Romancing d'inta duk yarud'e dan ak'agare
yake ita kuwa abinda Laila tafad'a shike mata yawo cikin kunne kamar lokacin
abin yafaru, jitayi takasa d'aurewa hakan yasa ta tureshi ta tashi tsaye tana
jada baya
Cikin tashin hankali yafara cewa "don girman Allah
karyi mani haka, ba haka mukayi dake ba don Allah kitaimaka mani pls.....
Kinji..... Koyaya ne kitaimaka mani kinsan ina k'aunarki sosai"
Girgiza kanta take tace "k'arya kake bazan iyaba bansani
ba ko kana d'auke da wata cuta" daga haka bata k'ara cewa komai ba taruga
da gudu ta shige d'akinta ta kulle
Maimaita kalamanta yake aranshi don yagaza gane inda
zancenta ya dosa, tashi yayi yaje bakin k'ofar d'akinta yana kwankwasa mata
amma tanajinshi yak'araci magiyarshi, ganin ba bud'ewa zatayi ba yasa dan
dolenshi ya hak'ura yatafi
Da safe ma haka yayi-yayi da'ita ta bud'e amma tak'iya
saidai aje mata break fast d'in da yahad'a mata tare dayimata rubutu a pepper
sannan ya wuce d'akinshi don d'aukar key d'in motarshi, har zai wuce ya hango
wata takadda bisa dress mirrow, d'aukarta yayi ya karanta, nan ya fuskanci inda
fushin khadijah ya dosa, don ko yaga sunan Laila ajikin takardar, watau ita ta
haddasa zargi a tsakaninshi da khadijah, kwafa yayi na inyaga Laila baison wane
irin hukunchi zai d'aukar mata ba ta kuma gaya mashi yaushe ya kwanta da ita
har yayi mata ciki
Tanajin tashin motarshi ta fito ta nufi dinning don tayi
break fast, note d'in dataga ya aje mata ta d'auka takaranta _don Allah kici
abinchi karki horar mani da kanki da yunwa_
tab'e baki tayi tace
"yo dama saboda kai zank'i cin abinci ne, kuma wallahi
bazan yarda dakaiba har sana tabbatar da zargina, haka kawai kaje kasa mani
cuta"
Saida tagama taje ta zauna palour tana tunanin abinda zatayi
mashi ta bata mashi rai, wani Murmushi naga tayi daza'a iya kiranshi da na
mugunta, tashi tayi ta shiga gyaran gidan tana gama ta wuce kitchen ta d'ora
tuwo miyar kuka don tasan Jiddan baya son tuwo, saida tagama ta gyara kitchen d'in
sannan taji ana knonking, lekawa tafarayi ta window taga Laila ce, komawa tayi
kitchen ta d'auko muciya tana cewa "yau zakici ubanki karuwar banza mai
bibiyar mazan mutane"
B'oye muciyar tayi a bayanta, ta bud'e k'ofar, yauma kamar
jiya tana bud'e mata tashige ciki kamar gidan ubanta
Bata ankaraba taji saukar muciya bisa kanta nan take tafad'i
sumammiya, igiya taje ta d'auko ta d'aureta sosai yadda bazata iya kwancewa ba,
d'auko ruwa masu sanyi tayi ta watsa mata ajiyar zuciya tasaki ganin ta d'aurene
yasa tacika da mamaki, bari tayi saida tadawo cikin hankalin ta sannan
Ta d'auko sessiors ta datse duka k'arin gashin dake kanta
saida taga tamaidata kamar Namiji sannan ta kyaleta tace
"wallahi ina warning d'inki idan kika k'ara shigo mani
gida saina illataki don gabama kaciya zanmaki inkika yi kuskuren k'ara shigowa
gonata"
Duk wannan abin banda kuka ba abinda Laila keyi, shewa
khadijah tayi tace "ashe ke iskancin naki k'arami ne tunda d'an wannan abu
danaimaki yasaki kuka, kad'an ma kika gani don ni nan dakike gani nafiki iya
hatsabibanci, don haka karna k'ara ganin maikama dake wannan layin bare kiyi
kuskuren shigowa nan"
Kai tad'aga mata da alamun bazata sake haka ba tace
"don Allah kiyi hak'uri kibarni natafi"
"zanbarki kitafi amma saina k'ara yimaki tabo"
daga haka tashiga jibgarta kamar tasamu jakka saida tafasa mata baki sannan
takira maigida ya fidda ta
Saida tagama hucin dukan da tayima Laila tace "saura
kaima zakazo kasameni nasan yadda zanmaka" d'aki ta shige tayi wanka
sannan ta zauna kwalliya sai lokacin ta lura da yad'auke takkardar, Murmushin
mugunta tayi tace "uhmmmmm kenan dagaske ya santa"
Wani d'an k'aramin mini siket tasaka da wata 'yar
bingilallar riga wace za'a iyacewa da ita da babu duk d'aya sannan ta feshi
jikinta da turare ta tafi palour ta zauna
Har suka tashi office Rafeeq na lura da yanayin shi saida ya
bari bakowa inda suke sannan yace ma Jiddan
"meke faruwa kodai jikin khadijah ne?" shuru yayi sai kuma ya
zaro takkada daga cikin aljihun wandonshi yamik'a mashi
Zaro ido Rafeeq yayi yace "kasani a duhu kayi mani
bayanin da zangane"
Iyakar abinda yasani yagaya mashi yak'ara da cewa
"nidai nasan bantab'a zina ba ballantana kuma Laila dako birgeni batayi" Nisawa yayi yace "da'ace
nasan inda zansameta wallahi dasai nasa ankulleta amma bakomai indai kare na
yawo zabo na yawo wata rana za'a had'e"
Dafashi Rafeeq yayi yace "insha Allah nima zan tayaka
nemanta kaidai kayi k'ok'arin wajen shawo kan mutuniyar taka"
Tana zaune taji k'arar shigowar motarshi, tashi tayi ta duba
ta window don ta tabbatar dashi ne, fitowa yayi daga cikin motar taga damuwa
k'arara a fuskarshi, Murmushin mugunta tasaki akaro na ba adadi, kwanciya tayi
saman 3seater tayi wata kwanciya ta d'aukar hankalin wanda zaiyi arba da'ita, duk
tabaza gashin kanta sannan ta rufe idonta kamar mai bacci
Yana shigowa yaji ba alamun motsinta sai tv dake aiki,
tunanin tana d'aki ne yafad'o mai, saida yashiga cikin palourn sosai ya ganta
kwance tana bacci, tsaye yayi yana tasbihi ga Allah daya azurtashi da mace
abociyar kyau da kamala, Kallonta kawai yake yakasa koda motsawa sai had'iyar
yawu yake Jiyayi k'afafunshi sunkasa d'aukarshi duk'awa yayi dai-dai saitin
k'irjinta da yafi d'aukarmai hankali
Itakuwa duk tana ganin abinda yake, hamdala kawai yake
furtawa cikin ranshi a hankali yakai bakinshi dai-dai k'irjinta yafara kissing,
zumbur tamik'e tace
"malam menene haka kada kasake tab'ani katafi wurin
karuwanka kayi dasu bani ba" dasauri yajawota ta fad'a k'irjinshi don kada
ta gudu yafara cewa
"Pls... Pls.... Kada kiyi mani haka wallahi bantab'a
kusantar wata ba balle har nayi mata ciki" fizge kanta tashigayi tana cewa
"Ni zakayi ma dad'in baki wallahi banyardaba"
Ganin yak'i sakinta yasa ta gartsa mashi cizo sannan ta
tashi tashige d'aki ta kulle, cikin rantako cewa take "nasan idan harda
gaske kake baka neman mata zangani, don nasan inkanayi dole kafita kabiya
buk'atarka"
Duk 'yan mitina tana lek'ashi taga ko yafita batare da yasan
tana hakan ba
Shikuwa bayan sha'awa yunwa ta isheshi don yasan da gayya
tadafa abinda baici tashi yayi ya fita yaje restauranat ya siyo abinci yadawo,
fitartashi ya tabbatar mata da zargin nata yazama gaskiya, wani irin kishi
yataso mata zuciyarta na harbawa, harbata lokacin da hawaye ke silalowa daga idon
ta
***
Tana fita wurin Ashanty ta wuce, kuka take gaban Ashanty
tamkar ranta zaifita kyaleta tayi mai isarta sannan tace
"Laila yana ganki haka meyafaru?" kuka laila keyi
tana gayamata abinda yafaru
"kema Laila nace ki hak'ura ni kinga tunda naga mutuwar
da silly tayi naji tsoron duniya da abinda ke cikinta,, wallahi na tuba nakoma
ga Allah nadaina sab'a mashi ta wannan hanyar yakamata kema ki tuba mukoma ga
Allah
Kallon bazan tayi mata tace "amma Ashanty baki da
hankali in tuba fa kikace, ai wallahi sai naga abinda yaturema buzu nad'i tunda
tayi mani haka saidai murasa J d'in dagani har ita saina maidata bazawarar
k'arfi da yaji"
Girgiza kai Ashanty tayi tace "Allah yashiryeki
Laila"
_*Mrs Abdul
Sule*_
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
*page 146~150*
*J*iddan na tafiya kamar da 3 minutes sai ga motar Ashanty,
parking tayi ta fito tare da gaida maigadi sanan ta tambayeshi ko matar gidan
na nan yace mata "eh tana nan" kaitsaye ta shiga cikin gidan batare
da tsoron komai ba
Tana nan zaune Inda yatafi ya barta, gaba d'aya tarasa me
yasa takejin fad'uwar gaba duk tabi ta
damu sai jitayi ana knocking
Tashi tayi duk jikinta a mace taje ta bud'e k'ofar, murmushi
Ashanty tayi tace "sannu mun tashi lpy" hakan yasa khadijah tadan
saki fuskarta tace "lpy lau sai dai ban ganeki ba" cikin ranta ko
tace wannan ina kuma ya kwasota
"Eh toh sai dai da zaki Mani izini mu shiga daga ciki sai nayi maki bayani"
"ba matsala" khadijah tace, shiga sukayi suka zauna sannan Ashanty
tace
"Nasan baki sanni ba kuma kina mamakin yadda nazo maki
gida da sassafe haka" daga kai khadijah tayi alamar haka ne sannan Ashanty
taci gaba da cewa
"Toh gaskiya dole ce tasa nidai sunana Aisha k'awa ga
Laila wacce tazo tace maki tana d'auke da cikin mijinki sai dai k'arya take
kawai tana so ta biya buk'atar ta ne" nan Ashanty tayi ma khadijah bayanin
duk abin da ya faru tun daga had'uwarsu da jiddan har yanzu da Laila ke shirin
aiwatar da nufinta, sanan ta k'ara da cewa
"Ni yanxu daga nan Kano zan wuce na koma wurin iyayena
sai dai nace Allah ya k'ara sada fuskokin mu da alkhari don haka kada ki bari
jiddan ya fita idan ba haka ba d'ayan cikin biyu zai faru kodai ya biya mata
buk'atarta ko ta kashe shi Ku rasa baki d'aya"
Bazan iya rubuta maku irin tashin hankalin da naga khadijah
ta shiga ba, nan take jikinta ya d'auki rawa, muryarta na rawa tace
"Na shiga ukku wallahi yazun nan ya fita don Allah ki
taimakeni" duk cikin rud'ewa take fad'in haka don bata ma San me yakamata
tayi ba, da sauri Ashanty da itama ta shiga firgici jin jiddan d'in ya fita
tace
"Yi sauri ki
kirashi ya dawo tun kafin yayi nisa" cikin kyarma don har wayar na neman
fad'uwa khadijah ta d'auki wayar ta shiga kiranshi
***
Dafe kanshi yayi dai-dai Inda yaji an bugeshi hakan yasa
yaji duniyar na juya mashi, ba tare da yayi wani yunkuri ba yaji an d'aureshi
tare da cire bindigar dake sakale a aljihunshi
Cikin juwa yake kallon k'attin mazan majiya k'arfi da sukai mashi wanan
illar sai dai ya kasa magana, basu tsaya b'ata lokaci ba sukayi saurin sakashi
cikin motar su sanan sukaja zuwa bayan gari Inda Laila ke jiransu
Zaune take ta sako k'afarta d'aya daga cikin motar, wasu
arnakun kayane a jikinta Wanda ko a bariki bakowa ke iya saka irin kayanba sai
kad'a key d'in motar ta take tana jiran isowar su
Ba b'ata lokaci sai gasu sun iso suka gurfanar da jiddan a
gabanta, murmushi tayi ta kad'a idanuwanta sanan ta d'ora hanunta saman
fuskarshi tana shafa sajenshi da yake mutukar birgeta cikin wani salo tace
"J meyasa kake son ka dinga wahalar dani, yanzu da ka
bani had'in kai ko sau d'aya na d'an-d'ani zumarka da yanzu mun wuce wurin" abinka da soldier
sai ya kalleta a wulak'ance babu alamun tsoro a tattare dashi yace "ke
jahilar ina ce da har kike tuna nin zan'iya had'a jikina da k'azamin jikinki,
ni ban tab'a ganin jarababba irinki ba ko kina tunanin da kikasa aka kamoni
shizaisa ki samu abi da kike so? Uhm ki guji ranar da zan kamaki"
Wata irin mahaukaciyar shewa Laila tayi sanan ta daure fuska
tace
"Kana tunanin zan barkane, ita kanta wadda kake
wulakantani a kanta saina maidata abin tausayi don haka tsaya ka gani"
tana fad'ar haka ta zaro desire tablet tare da wani poison cikin kwalba sanan
ta kalli Jiddan tace"dole ka sha kuma ka biya Mani buk'atata ko kuma in
kashe ka"
"Toh ki kasheni mana sai me ko angaya maki ina tsoron
mutuwa ne? Aiko da ban zama soldier ba, don nasan kona biya maki bukatarki ba
barina zakiyi ba matata kuma baki isa ki mata abin da Allah bai nufeta da shi
ba" ran Laila ne ya soma baci nan tasa wadanan k'attin suka shiga dura
mashi desire tablet d'in
***
General ne ya kalli Rafeeq cikin mamaki yace "ina
mamakin yadda har yanzu captain J baizo ba bayan jiya da kanshi yace Mani zai
shigo da wuri anya lpy?"Rafeeq ya Dan kad'a kai sannan yace "Nima
abin da nake tunani kenan but bari in kirashi inji"
Rashin dace aka samu dai-dai lokacin da yake kiranshi itama
khadijah tana kiranshi hakan yasa ya
kasa samunshi itama haka, koda yaga ya kira sau biyar bai samu ba sai yace ma
General
bari yaje gidan yaga ko lafiya, har ya je bakin motarshi sai
kuma ya tsaya yana kiran no d'in khadijah yaga ko ita zai samu but still bai
samuba saboda itama lokacin shi take k'ok'arin kira ta gaya mashi gashi ta kira
Mujaheed but switch off sai Ashanty ce tace tak'ara kiran Jiddan d'in
Duk cikin tashin hankali take kiran sai dai yanzu tayi sa'a
tana ringing, amma ba'a d'auka ba
Mujaheed ne ya karaso Inda Rafeeq yake yace "har yanzu
J baik'arsoba?, gashi inta kira dagashi har khadijar amma ban samu ba, ko kai
ka sameshi?"
"A'a ni wayata kashe ma take but mu tafi
kawai"cewar Mujaheed, daga haka sukaja motar suka tafi
Idanunshi har sun canza kala saboda maganin ya fara mashi
aiki, koda Laila taga haka sai ta fito daga cikin motar fuskarta dauke da
murmushi ta tsugunna gabanshi tana shafa fuskarshi, cikin wani salo ta furta
"J"
Aiko dagowar da zaiyi ya watsa mata uban miyau a fuska, da
mamaki take kallonshi sai kuma tayi murmushi tare da goge fuskarta tace
"kusa Mani shi cikin mota"
Duk da k'arfi irin nasu amma sun kasa sa jiddan cikin motar
saboda yadda yatirje kuma hannuwanshi a d'aure suke ganin ya k'iya yasa sukayi
niyar d'aukar shi gaba d'aya amma sai ya shiga cizon su
Cikin fushi babbansu ya zaro bindiga zai harbeshi, Laila
tayi saurin dakatar dashi sanan ta dauko wanan poison din ta mika masu tace
"ba sai kun harbeshi ba"
Suna k'ok'arin d'ura mashi sai wayar shi ta hau ringing,
Laila ce ta d'auki wayar taga ansa PRINCESS murmushin keta tayi tace zakayi ban
kwana da matarka kafin ta biyo ka, tana fad'in haka tayi receiving call din
tare da sa mashi a kunne
Cikin wahalaliyar murya yace "Khadijah...sai Laila tayi
saurin janye wayar, ta fashe da dariyar da ta k'ara tada ma Khadijah hankali
sanan tace
"Kina magana da Laila don haka zaki iya zuwa ki d'auki
gawar mijinki" tare da siffanta mata wurin daga haka ta kashe sanan suka
shiga d'ura mashi poison din
Saida suka tabbatar yasha sannan suka tafi suka barshi,
dukda basu Sani ba Dan kad'an yasha amma
nan take ta fara mashi illa saboda gubar mai k'arfi ce
Tashin hankali Wanda ba,a sa mashi rana, jin abin da Laila
ta fad'a batasan sadda ta saki wayar ba ta fad'i k'asa tare da tarwatsewa
Da gudu ta fita Ashanty na tayi mata magana amma ina batasan
tanayi ba, Allah ya taimaka Riga da wando ne na Pakistan a jikinta kuma
mayafinsu na bisa kanta
Tattara wayar Ashanty tayi ta had'a tare da kunnawa sanan ta
aje saman center table ta fita, gate man ta tambaya ko yaga Inda Khadijah tayi
Yace eh yaga ta fito da gudu ta tsaida taxi amma baisan Inda
ta tafi ba, godiya tayi mashi ta shiga
motar ta takama hanyar Kano aranta tana cewa
"Nasan idan wani Abu ya samu Jiddan ko Khadijah ni za,a
tuhuma Inda Laila take bayan ni taimako nayi " haka ta tafi tana fatan
Allah kada yaba Laila nasara
Mai taxi d'in take cemawa ya k'ara sauri but gani take kamar
ba tafiya yake ba, wani irin birki taji yaja sakamakon go slow din dake gaban
su, sanadin wani accident da akayi da sauri mai taxi din ya fita don gane ma
idonshi
Ganin babu hanyar da zasu wuce gashi sun kusa isa yasa ta
fito da gudu batare da tabi takan kowa ba
Gudu take sosai tana kuka ba abin da take tunawa sai lokacin
da suna yara yanayi mata wasa, yana dagata sama tana dariya a hankali ta fara
tuna wasu maganganunshi cikin kunnuwanta kamar haka:
"Kinsan bazan tab'a cin amanarki ba ..." Meyayi
zafi zaki rinka horar da ruhimmu haka?.. Aw bazaki kalleni ba?.., ina sonki har
gaba da abada...
Takalminta ne ya katse hakan yasa ta ta tsaya sanan ta cire
taci gaba da gudun ita dai burinta ta isa Inda Jiddan yake
Jitayi ta taka wani Abu hakan yasa ta tsaya sai taga Ashe
wata katuwar kwalbace ta taka gashi taji mata ciwo sosai amma saboda tashin
hankali ko zafin bataji ba sai cire kwalbar tayi taci gaba da gudun
Ganin duk Inda ta taka sai yayi sawun jini yasa mutanen da
take wucewa suke mata magana amma Sam bata San sunayi ba saboda saura
k'iris ta isa Inda yake
Haka taci gaba da gudu kamar ranta zai fita, sai dai kash!
Tana zuwa ta tarar da Jiddan ...
*_Mrs Abdul
Sule_*
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA Mk*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
*PAGE 151-155*
*S*una isa gidan Jiddan Rafeeq ya danna horn maigadi ya
bud'e masu suka shiga ba tare da sun tsaya tambayarshi komai ba
Parking sukayi tare da shiga cikin gidan, tsaye sukai sunata
sallamma amma shuru, ganin shurun tayi yawa yasa suka shiga cikin palour
Tunda Rafeeq yaga k'ofar a bud'e take bayan yasan Khadijah
kullewa takeyi saidai ayi knocking sannan tabud'e, yasan ba lafiya
Ganin suna takiransu ita da Jiddan shuru alamun ba mutum
cikin gidan yasa Mujaheed yace su shiga bedrooms su duba sugani ko suna ci,
saida suka fara k'wank'wasa wa sannan suka shiga amma ba kowa a ciki
Haka suka zagaye ko ina na gidan amma ba kowa, mai gadi suka tambaya ya gaya masu iyakar abin da
yasani, nan Rafeeq da Mujaheed suka tabbatar daba lafiya, amma abin da ya
d'aure masu kai wacece wadda maigadi yace tazo da safe haka?
General suka kira suka gaya mashi halin da ake ciki da kuma
abinda suke zargi sannan suka shiga motarsu
Maimakon su biyo ta hanyar da sukazo sai suka bi ta wata
hanyar wadda itace Jiddan yafibi, basuyi tsammani ba sai sukaga motar Jiddan a
kan hanya gashi wurin ba kowa
Da mamaki suka fito daga cikin motar don su tabbatar ma
Kansu, wayar Rafeeq ce tahau ringing, dubawa yayi yaga general ne hakan yasa ya
d'auka da sauri
A d'ayen b'angaran general kema Rafeeq bayanin cewa shima
yakira wayar Jiddan and'auka amma ba'ayi magana shine sukayi tracing sungano
inda yake yanzu haka antura soldiers suje wurin
shima Rafeeq nan yake sanar dashi inda suka ga motar Jiddan
amma suma yanzu zasu nufi wurin tunda kusa suke
Suna katse wayar Rafeeq yaja motar, shi kuma Mujaheed ya
d'auki waya don k'ara kiran jiddan
***
Tana isa ta tarar da Jiddan kwance dukda bai mutu ba amma
har miyan bakinshi ya tsinke don gab yake da yarasa rayuwar shi, da sauri ta
ruga ta rungume shi tana kuka tare da cewa
"Don Allah yayana ka tashi Kada ka barni don..."
Wayar Jiddan dake gefece ta d'auki ringing cikin kyarma ta kai hannu ta d'auka
duk da irin jirin da takeji
"Hallo! Hallo! Jiddan..."Mujaheed..
Mijina..ya.." Sai kuma ta sume saboda tashin hankali ga kuma jini mai yawa
da ta zubda
Mujaheed da yaji abin da Khadijah ta fad'a kuma yagane itace
amma sai dai yaji shuru, katse kiran yayi yasake kira but ba'a d'auka ba sai ya
kalli Rafeeq yace
"Duk yadda akai Khadijah da Jiddan suna tare, saidai ga
dukkan alamu akwai babbar matsala a tare dasu" take Rafeeq yak'ara speed
d'in motar domin isa inda general yayi mashi bayani
Suna isa Rafeeq ya fito da sauri ko rufe k'ofar motar baiyi
ba ganin Khadijah da Jiddan kwance a k'asa, left hand d'insu da ke d'auke da
zoben su rik'e da juna, ga alamun zubar jini a wurin
Bai San sadda ya isa wurin su ba ya fara girgiza su yana
cewa "Jiddan! Jiddan!! ..Khadijah!!! Khadi..."dai_dai lokacin wasu
bak'ak'en Hilux suka iso, sojojin dake ciki su fifito, Mujaheed da zuciyar shi
ta gama karaya yayi saurin ce masu
"Kusa su mota mu tafi asibiti" da sauri suka Sara
mashi tare da cewa "OK Sir" daga haka suka kwashesu sai asibiti
Da hanzari aka karb'esu ba bata lokaci suka gano matsalar
Jiddan na take suka shiga tsotso gubar ta tare dayi mashi wasu allurai hatta
hancin shi sai da suka rink'a samashi wani Abu yana fiddo da gubar tare da jini
Saida suka d'auki lokaci mai tsawo akan Jiddan sannan likitocin suka fito, sai d'aya daga cikin su
ne ya tsaya yi masu Rafeeq bayanin cewa
"Shi jiddan poison yasha saidai ko wacce guba da irin
illar da takeyi ma mutum, k'arshe ma Ana iya rasa rayuwa indai ba'ayi hanzarin
d'aukar mataki akan haka ba, toh amma shi Jiddan Alhamdulillah babu abinda ta
lalata mashi ko'a cikin shi komai lafiya lau yake saidai zai Dan dad'e kafin ya
farfad'o, koda ya tashi ba lalle bane ya iya motsa ko ina na jikinshi sai a
hankali zai warware"
Numfashi Rafeeq ya sauke sannan yace "ita macen da aka
kawosu tare fa?.."eh ita ba Wata babbar matsala bace ba, taji ciwo ne
sosai a k'afarta Wanda yayi sanadin zubar jininta mai yawa ga alamun tashin
hankali a tattare da'ita don haka yanxu anyi mata dressing sannan akwai wasu
blood tonic dazamu bata insha Allah zatayi replace blood d'in data zubda"
Daga haka doctor d'in ya tafi shi kuma Rafeeq ya kira
general ya sanar dashi abinda yasamu Jiddan
Yayi matuk'ar girgiza najin cewa Jiddan guba yaci, take
Abinka da babban soja military ta aiko da soldiers don bada tsaro ga Jiddan,
musamman jin cewa poison aka bashi
***
Adaidaita sahu ce wato keke napep tayi parking a k'ofar
gidansu Khadijah, fitowa sukayi su ukku tare da sallamar mai napep, kayane da
yawa suka siyo daga kasuwa ga alamun gajiya a tattare da su, Ihsan ce tafara cewa
"Toh kun wani tsaya Ku d'auka mu shiga gida ko"
Samra da tafi kowa nuna gajiya tace "keni wallahi gida zan wuce kawai kije
da kayan ajima sai mu shigo mu tattauna"
"Toh uwar son jiki wlh Yaya muhsin ya bani dake, ita
kuma waccan ta wani yi shuru sai tunani take "cewar ihsan dake k'ok'arin
d'aukar kayan ta shiga gida, girgiza kai Seemah tayi tace "uhm Allah sarki
yaya SS dayana nan nasan bazamu sha wannan wahalar ba" jikinsu ne yayi
sanyi kafin ihsan tace
"Kuyi hakuri mu daina wannan tunanin addu,ar mu yafi
bukata" Samra dakeda saurin kuka har idanun ta sun ciko tace "naso
ace Yaya yaga ranar auran mu amma Allah bai nufa ba, gashi kuma yanxu aure zai
rabamu" dafata ihsan tayi tace "kiyi hakuri Seemah ai muna tare"
cewar Ihsan
"ki daina kuka ni yakamata nayi tunda ku duk Kaduna
za,a kaiku Niko ina nan katsina ni kadai don haka zan gaya ma ummi sai na raka
Ku sannan indawo akaini" Samrah tace "lalle Seemah toh munji amma ai
itama d'auketa Rafeeq zai dungayi yana tafiya da'ita Abuja"
Ihsan tace "toh saiki bimu" daga haka hirar tasu
ta koma wasa kafin kowa ya shige gida
Da sallamar ta ta shiga gida saidai tayi turus ta tsaya jin
wayar da baba keyi ga Mama dake gefe ta kuka, hawayene suka shiga zirarowa daga
idanta, aranta kuwa cewa take yanzu kuma meyasamu yaya Khadijah, kullum suke
nan cikin jarabtar ubangiji, saurin istigifari tayi ganin tana neman jafa kanta
cikin halaka
Babane ya ida wayar dagaya ma Rafeeq cewa lnsha Allah yau
zasu biyo jirgi su taho sannan ya aje yana kallon Ihsan da tasaki kayan hanun
ta tana hawaye yace
"Haba Ihsan ba kuka zakiba keda baki tabbatar da kome
ya samesu ba" a hankali tace "meya faru?" saida ya kwantar mata
da hankali sannan yayi mata bayani, itakuma ta d'auki kayan da ta shigo da su
ta nufi d'aki
Kallon mama yayi yace "ji don Allah yadda kike hawaye
duk kin tada ma yarinya hankali, yanzu je ki d'auko Mani passports d'inku"
zuwa tayi ta d'auko sanan tayi mashi Allah ya kiyaye kafin ya fita
K'arshe dai basu samu tafiya ba sai k'arfe 7:30pm, jirginsu
yad'aga zuwa garin Abuja
***
General ne ke gaya ma Rafeeq cewa tafiyarsu ta gobe tana nan
sai dai an cire Jiddan kuma za'a cigaba da bashi tsaro har ya warke, shidai
Rafeeq komai ya dagule mashi kanshi kawai ya iya d'agawa sannan ya fita
Asibiti ya nufa dayake Mujaheed nacan, yana zuwa Mujaheed yaja hanunshi yace zauna muci
abinci, ba musu ya fara ci don yunwar dayakeji saboda tun safe rabonshi da
abinci, daga shi har Mujaheed d'in hakalinsu ba kwance yake ba
Da misalin k'arfe 8:15pm su Ihsan suka iso Abuja lokacin
iyayen jiddan sun dad'e da zuwa harda Islam
Kowa ka gani fuskarsa da damuwa, sai lokacin allurar baccin
da akayi ma khadija ta saketa ta tashi
Koda ta ganta a gadon asibiti gasu Mama kusa da'ita, sai ta
fara hawaye momy ce ta shiga lallashinta, a hankali saboda yadda take jin
bakinta yayi mata nauyi tace "ina ya Jiddan?.. "Yana Nan lafiya lau
bacci ma yake" cewar momy "toh Ku kaini in ganshi"
Sai lokacin Mama tayi magana tace"ki bari kici abinci
mana" shiru tayi batace komai ba, sai Ihsan ce ta had'o mata abinci
itakuma Islam ta taimaka mata ta zauna
Saida ta gama cin abincin tayi sallolin dake kanta sanan aka
kaita wurin Jiddan, da yake duk mazan suna can koda aka shiga da'ita sai ta
sadda kanta k'asa tana hawaye
Abba ne yayi mata bayanin abin dake damun Jiddan d'in tare
da kwantar mata da hankali, sannan itama tayi masu bayanin duk abin da ya faru
har taje inda Jiddan yake, nan kowa ya shiga jimamin abinda ta fad'a
Rafeeq ne yayi gyaran murya yace "Abba kada Ku damu
muna nan munsa ana bincike da yardar Allah za'a kamota, Baba yace "toh
Allah ya taimaka" nan Rafeeq yayi masu bayanin tafiyar su ta gobe, sannan
kowa yayi masu fatan alheri
Washe gari tunda safe kafin su Rafeeq su tafi sai da suka zo
asibitin sukayi ban kwana da kowa Wanda har yanzu Jiddan baifarka ba
Har bakin mota ta rakoshi fuskar ta cike da damuwa, dakewa
yayi don kada taga tashi damuwar yace "haba my pretty ki daina damuwa haka
insha Allah duk zasu warke kuma nima 3 weeks ne kwai zanyi in dawo don haka
Dana samu dama zan kiraki kinsan ruwa zamu shiga"
Dago idanun ta tayi suka had'a ido sai kuma ta Sadda kanta
k'asa tare dayi mashi fatan alkhairi
takoma cikin asibitin
Girgiza kai yayi yace "Ihsan kenan" daga haka
shima ya shiga mota Yana jiran Mujaheed ya gama ban kwana da Islam
_nace su Rafeeq kenan bacin damuwa da yanzu ya farayi ma
Mujaheed sharri_
Kwana d'aya da tafiyar su Mujaheed, zaune take bakin
gadonshi amma ta tafi duniyar tunani, da yake ita kad'aice a d'akin
Jitayi kamar ana shafa hanunta da sauri ta juya ta kalli
jiddan sai taga....
*page 156-160*
*T*ana juyawa sai taga jiddan ne ke shafa hannunta yana
murmushi, da sauri ta rik'e hannun nashi, kwalla cike da idonta tace
"yayana katashi? yaka..." girgiza mata kai ya shiga yi alamun kada
tayi kuka
Bata iya hana hawayen da take tarewa zubomata ba, bayan
hannunta tasa tana sharewa, k'ara matse hannunshi tayi tare da cewa "na
daina yayana, mekake so yanzu?" Dan k'aramin murmushi yayi tare da d'aga
hannunshi na Dama ya shafi gefan fuskarta ba tare da yace komai ba
Rik'e hannun nashi tayi tace "bari in kira doctor"
bai musa mata ba ta tashi taje kiran
doctor, yana lura da k'afarta datake d'angyashi, nan take yaji wani iri don
yana da tabbacin ta silarshi taji ciwon,donkuwa koda yabaro gida yasan lafiya
lau k'afarta take
Bayan doctor ya gama dubashi ya kalli Khadijah yace"
komai yana tafiya normal sai dai wasu jijiyoyin jikin shi da suka rik'e, suma a
hankali zasu warware sannan yanzu ki had'a mashi madara da da d'an ruwan d'umi
a bashi yasha" daga haka ya fita ita kuma ta shiga had'a madarar
Zaunar dashi tayi jikin gadon tare da sa mashi pillow a
bayanshi amma hakan bai mashi ba sai da ya kwantar da kanshi saman kafad'arta,
ba yadda ta iya a haka ta fara bashi madarar yanasha
Abba ne da Momy suka shigo don doctor ya fad'i masu tashin
shi, jitayi kamar ta nutse don kunya shikuwa Jiddan dad'in hakan yakeji
Gaidasu tayi ta fara kokarin tashi daga jikinshi amma duk
yabi yak'ara langab'e mata
Abba ne yalura da atakure take ganin suna cikin d'akin gashi
shikuma gogan sai wani k'ara kwantawa yake jikinta, Kallonta Abba yayi yace
"eh zamanki cigaba dabashi" hakanan tacigaba
dabashi, ganin duk a takure take yasa su Abba suka fita sukabar masu d'akin
Jitayi Jiddan na k'ara shigewa jikinta hakan yasa ta
kalleshi ta gane bacci yake ji, d'an murmushi naga tayi sannan ta gyara mashi
kwanciyar tana shafa kanshi har yayi bacci
Yau kimanin kwana biyu da farfad'owar Jiddan amma bai iya
aiki da hannunshi na hagu ,tafiya ma da kyar yakeyi duk Khadijah ce ke taimaka
mashi duk da itama ba wani iya taka k'afarta take sosai ba
Sukuwa su Mujaheed da Rafeeq tun tafiyarsu basu kira ba
A b'angaren su Ihsan suma sun koma katsina, saboda gobe ne
za'a sallami Jiddan daga Asibiti don jikin nashi yayi sauk'i, su Abba ma gobe
zasu wuce kaduna
Fitowar shi kenan daga toilet sai ga Khadijah ta taho da
sauri don ta rik'eshi, dariya ma abin ya bashi yace "lalle Khadijah mai
kika maida nine? Kuma idan fad'uwa zanyi ni dake wa zai rike wani" turo
baki ta shiga yi sannan tace "yo kaima kasan yanzu na fika k'arfi"
yace "Allah ko! Kamar haka?" Saiji tayi ya jawota
da k'arfi zuwa jikinshi, da sauri tace
"Na yarda wlh ka fini k'arfi yi hakuri" tayi
maganar cike da shagwaba da salonyin kuka, bai saketa ba sai yaci gaba da kallon
cikin idonta, itama shi take kallo
Hannuwanta duka biyun tasakalo saman wuyanshi tare da yin
tantad'o saboda ya fita tsawo, bata daina kallon cikin idonshi ba shima haka,
tace
"Yayana pls kayi hakuri da abin da........shihhhhh!
"bakiyi Mani laifin komai ba andeejah na nidai fatana Allah ya barmu
tare" " toh amma ya.." Bata ida ba saboda ganin yadda ya tsure
bakinta da ido yana k'ok'arin had'awa da nashi
Da sauri ta sakeshi hakan yasa ta dira ma kafarta mai ciwo
ayayin da hannunshi mai lafiya yake bayan kanta saboda yayi niyyar kissing
dinta
Zafin ciwon da taji ne yasa ta tapi zata fad'i, roko rigar
jiddan tayi batare data Sani ba, shi kuma bai lura da fad'uwa zatai ba gashi ba
wani kwari jikinshi ke akwaiba, Kawai sai ya bita
Lokacin da ta isa k'asa ta d'auka zataji ta bige, amma sai
taji sab'anin haka saboda hannun Jiddan dake bayan kanta
A bangaren Jiddan kasa tashi yayi sai wani kallon kwayar
idonta yake har hacinsu na kokarin gogar na juna, itama haka take kallonshi
dake nuna kauna da tausayi a tsakanin su
Sun d'auki kusan 3 minutes a haka, a hankali ta sauke idonta
k'asa shiyasa Jiddan ya dawo cikin hankalin shi, dakyar ya samu ya tashi don
shi hannunshi Wanda ya tareta yadan bugu amma bai bari ta gani ba
Ganin jikinta yayi sanyi yasa yajata saman gado ya shigayi
mata wani salo nadaban, neman zasu fita wata duniyar yasa khadijah ta ankarar
dashi
Waya ta gama yi da
Islam cikin damuwa ta kalli su Samra tace "itama Mujaheed bai kirata ba
Allah dai yasa lafiya" Seemah tace "lalle pretty kamar bakece soyayya
take ba haushi ba ke da zaki rinka wata ukku nan gaba baki ganshi ba"
hararar ta Ihsan tayi, Samra tayi saurin cewa "kyaleta addu,a zamu rinka
yi masu"
"Ni ba dad'ewar bace damuwa ta at lease kasan halin da
mutum yake ciki," sai Seemah tace "haba matar sojan ruwa sorry"
tare da kama kunnuwanta
***
"Aikin banza! kuma kunsan fad'i kawai kuke, taya zakuce
na biya Ku kud'in Ku bayan kun kasa
kashe shi da anyi magana kuce sojoji ke tsaron shi, bakusan
idan Jiddan ya tashi ba na kad'e, bani kad'ai ba harda ku" tare da binsu
da wani wulak'antaccen kallo
Wani daga cikin yaran yace "toh mu ina ruwan mu, bayan
munyi niyyar kasheshi kika hana"