HABIBI DA'IMAN 181-200
*page 180-185*
Allah sarki HABIBI DA'IMAN har wani tsinkewa yakeji jinin
shi nayi baya son abin da zai dunga wahalar da Khadijah, shi kanshi bazai iya
misilta irin yadda k'aunarta ke gudana a cikin jinin jikinshi ba
Da Sauri ya iso wajen, har kyarma yake ya rungume ta a
jikinshi yana jijigata, kuka yafarayi kamar ba namiji ba yana kiran sunan tah
da k'arfi
Bai tsaya bin takan su Adnan ba ya d'auketa sai asibiti,
suma bayanshi sukabi bayan Adnan yace ma
mai motar ya tafi ba komai
Yana zuwa aka karb'eta, saida sukayi nasarar farfadowar ta
sannan suka dank'ara mata allurar bacci saboda sumbatun da ta farayi
Kafin wani lokaci kowa ya hallara a asibitin, likitan da ya
duba Khadijah yayi masu bayanin ba wani problem kawai don ta tuna komai na
rayuwar ta ne amma zata tashi normal don haka da ta farka zasu sallame ta
Da misalin k'arfe 7:15pm a yayin da kowa ke haramar tasowa
daga masallaci Khadijah ta farka da surutai a bakinta wanda yayi dai-dai da
dawowar Jiddan daga masallaci
Tun kafin ya shiga yake jin surutun ta hakan yasa yayi
saurin shiga, saidai kuma yana zuwa bakin k'ofa ya tsaya saboda jin abin da take cewa
Kuka take tana cewa Mama yanzu Yaya SS ya mutu kenan da
gaske Kuna nufin kuce narasa cikinshi dake jikina, wayyo Allah ka jikan mijina
ka kai rahama a k'abarinsa saida nace mashi banason zuwanshi Kano ba amma ya
tafi.... To gashi abinda jikina kebani ya afku
Shigowar Likitan baisa ta daina surutan datake ba, duba ta
yayi sannan ya bata hak'uri kafin ya tambayi Mama ina mijinta hakan yasa
Khadijah ta tuna da Jiddan kawai sai wasu sabbin hawayen suka shiga k'ara zubo
mata saboda kaunarshi gareta da ta tuna
Ta tabbatar ba zata taba samun masoyi kamar Jiddan ba
mussaman ita data hango girman kaunarta cikin kwayar idonshi wanda bako wane
namiji bane zaiyi abin da Jiddan yayi akan bazawara ba Mai kuma curin kwakwalwa
ba
Tana sane Yaya SS zai iya hak'ura da'ita depending da
situation d'in da ake ciki amma tana da yakinin Jiddan ba zai iya barinta ba no
matter how d situation is
Don ko lokacin da tana gidan Yaya SS tana yawan tuna Jiddan
saboda zuciyarta na bugawa tare da tashi, kawai dai tana kukan rabuwa da Yaya
SS saboda ya kyautata mata a zamantakewar su kuma shi bai tab'a nuna yana kishi
da Jiddan ba don ko zoben dake hanunta yasan na Jiddan ne
Tunanin ta ne ya katse jin likitan naba safwan sallamar ta
ita kuma Mama harta fara sallah don lokaci har ya tafi
Kallon ta safwan yayi yace "toh tashi kiyi sallolin
dake kanki sai mu tafi ko? Ba musu ta fara k'ok'arin tashi saidai da kyar ta
tashi har safwan na rik'eta sannan ta wuce donyin alwalla tai sallah
Al'amarin Jiddan koda ya gama jin abin da khadijah ta fada
sannan yaji doctor nacewa ina mijinta kawai sai ya fita ba tare da kowa ya ganshi ba
Zuwa yayi jikin motar shi ya jikingina yana tunanin irin
soyayyar da ya gwada ma Khadijah tun tana k'arama amma cikin wani dan k'aramin
lokaci wani yayi awon gaba da'ita, ya ta tabbatar da Sulaiman yana Raye ba abin da zai hana
Khadijah taki zabarshi _(nace anya jiddan?)_
Tana gama duka sallolinta suka fara haramar tafiya don Dama
ita suke jira
Jitayi bata iya d'aurewa shiyasa ta fidda kunya tace ma Mama
"ina Yaya Jiddan? "Nima ban San Yaya akayi bai dawo ba daga tafiya
masallaci" safwan yace "nasan wani babban abune ya tsareshi kawai mu
tafi gida na mashi ma waya yabiyo mu" ita dai Khadijah bata iya cewa komai
ba har suka ga abinda suke suka fita
Jiyayi ciwonshi na Neman tashi, abunda rabon da ya tashi har
ya manta, d'aga kanshi yayi yaga had'ari ne sosai a garin wanda da Gani zai
zubda ruwa sosai, shiga cikin mota yayi ya zauna saboda iskar da ta fara yawa,
yana tuna sadda suna makaranta idan suna zaune da Khadijah aka fara ruwan sama
shiga take ciki tayi ta rawa k'arshe shima sai ta jawoshi cikin ruwan hankali
ta zai kwanta...
Tunanin shine ya katse saboda hango su da yayi sun fito amma
sai suka tsaya alamun magana suke, shiyasa shima ya fita da niyyar yaje wurin
su
Mama ce tace "anya safwan mun tafi cikin hadarin nan?
" toh mama in banda abinki idan bamu tafi ba tsayawa zamuyi sai ruwan ya
safko wanda bamu San ranar tsayawar shi ba ga dare nayi" shikenan mama
tace sannan suka nufi wajen mota
Back seat Mama ta zauna shima safwan ya shiga mazaunin
driver sai Khadijah da har ta bude kofa zata shiga sai kuma ta juya saboda
bugun zuciyar ta da take jin ya k'aru kuma tanajin kamar Jiddan na kusa da ita
Karaf idanun su suka had'u dana juna, hakanan taji ta kasa
d'auke idonta a kanshi shima haka, safwan da sai magana yake mata saboda taki
shigowa jin tayi banza dashi yasa ya duba abin da take kallo sai yaga Ashe
Jiddan ne, rufe k'ofar yayi yaja motar ya batta nan tsaye, sai da ya isa inda
Jiddan yake yace "Dama kai muke jira toh sai gaka ka taho da'ita"
d'aga mashi kai kawai Jiddan ya iya yi don hankalin shi nakan Dijee...😜
A hankali ta fara takawa saboda yadda zuciyar ta ke fizgarta
zuwa wajen wanda bata da kamarshi wanda yayi ma rayuwar ta rumfa tako ina,
wanda duk girman laifi zata iya yafe mashi don ko da taji cewa Jiddan ne ya
banketa wanda yayi sanadiyar zubewar cikinta bata k'ara maganar ba
Shikuwa Jiddan kwayar idonta yake kallo so yake ya gano idan akwai sauran soyayyar shi ko kuma babu
SS ne kawai aranta..
Baifi taku ukku ya rage tsakanin su ba, ruwan sama ya kufce
kamar da bakin kwarya, tsaye Khadijah tayi don ta kasa motsa koda k'afarta sai
Jiddan ne ya ida takowa inda take tare da jawo ta zuwa jikinshi
Sun d'auki kusan 2minutes suna kallon juna ga ruwan
saman dake dukan su amma in banda kallon
juna ba abin da suke
D'aukarta yayi yasa cikin motar sannan shima ya shiga, bai
zarce ko ina ba sai hotel d'in da ya kama, har yanzu babu wanda yace komai kowa
da abinda zuciyar shi take sak'a mashi
D'aukar ta yayi kamar wata jaririya, yasa k'afarshi ya rufe
k'ofar ya nufi cikin hotel d'in da'ita, saida ya shiga daki sannan ya direta
saman gado
shiga toilet yayi ya
had'a ruwan dumi sannan yafito, baice mata komai ba ya hau cire mata kaya itama
bata hanashi ba, saidai badan k'aramin tada mashi hankali surar jikinta yayi ba
Sharewa yayi ya kaita cikin ruwan ya aje sannan shima ya
shiga har yanzu ba wanda yace komai cikin su
Sun d'auki kusan 10 minutes sannan Jiddan yasaka bath rope
ita kuma ya nadeta cikin towel, saida sukayi alwalla sannan suka fito, dayake
akwai kayanta a dakin saboda jiya nan ta kwana, shiyasa ta d'auko hijab d'inta
shikuma yajasu sallah kasancewar har yanzu
ruwa ake sosai
Knocking d'in da akayi ne yasa Jiddan tashi yaje ya bud'e
Dama yasan room service ne ya kawo abinci, amsa yayi yazo gurin Khadijah ya
zauna
Ruwan Lipton mai zafi ya fara bata shima ya shiga sha sai da
suka gama sannan suka hau cin abincin
Suna gamawa yajata saman gado suka kwanta tare da rungume ta
tsam a jikinshi
Sun Dad'e shiru ba wanda yace komai, karo na farko Jiddan
yace "I luv u.." Nima yayana bani da kamar ka" sai da ya goga
hancinshi saman fuskarta sannan Yace "har SS?..."eh har shi
mana" ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "toh me yasa kikayi ta kuka
kamar nine na mutu? D'an murmushi tayi don ta gane kishi ne ke d'awainiya da
Jiddan tace "saboda a zaman mu ya kyautata Mani sannan bai tab'a nuna yana
jin haushinka ba, amma ba hakan na nufin d'aya kuke ba shi masoyi na ne amma na
wucin gadi kai kuwa na har gaba da abada ne shiyasa wasu lokotan zakaji ina
kiranka da HABIBI DA'IMAN ma,ana MASOYINA HAR ABADA
K'ara rugumeta Jiddan yayi tare da manna mata kiss yana cewa
"wlh ina son ki sosai Khadijah yadda ni kaina ban iya misiltawa Allah ya
bammu tare, da haka dai har bacci yayi awon gaba da su
Su Mama ina isa gida suka ci karo da baba zaije asibitin,
ganin su kad'ai ne batare da khadijah ba yasa shi tambayar ina suka barota Mama
ke mashi bayanin tana wurin mijinta d'aga haka baice komai ba ya shiga gida don
shima yasan suna bukatar lokaci, a wani bangaren na zuciyar shi yana tausaya
masu saboda yadda sukaga jarabawar rayuwa su duka.
_Mrs Abdul
Sule_
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
_Amarya shalele,Amarya bakya laifi ko kinkashe d'an masu
gida_ _*Aisha Aliyu kabuga*_ _Allah
yabada zaman lfy Allah yasa next year muzo musha bikin suna wannan shafin naki
ne ke kad'ai kisha shagalinki amarsu ta ango_
*page 186-190*
Zaune take tayi shiru batace komai ba yayin da jirginsu yayi
nisa cikin sararin gajimare, abubuwa biyu ne suke addabar zuciyarta, na farko
kunyar Ammi da takeji kasancewar basu
tab'a had'uwa ba sai da biki yazo gashi seat d'inta tare yake dana Ammi,yayinda
Rafeeq shikuma yana wajen Abbu sai Rafeeqa dake zaune ita da wata Mata
Dukda kunyar Ammi da Ihsan keji bai hana tunaninta tafiya
wajen halin da yar uwar ta take ciki shiyasa ta k'osa su isa Egypt tayi waya
da'ita
Kamar an tsikareta ta tuna data manta wayarta gida saboda
abubuwan da sukayi mata yawa sai yanzu ta tuna, Ammi dake lura da ita tace
"'yata ya akayi ne? Sadda kanta tayi tana kallon yatsun
hannunta da yasha lalle tace "waya ta na tuna da na Manta ban d'auko
ba" tak'are maganar cike da girmama, D'an murmushi Ammi tayi irin nasu na
manya tace "kada ki damu idan munje sai a siyo maki wata" d'aga kanta
tayi tace "toh Ammi nagode"
Ayayin da Ammi take yaba hankalin Ihsan cikin zuciyarta
dukda kasancewarta yarinya shiyasa take godema Allah da yaba d'anta irin matar
da take fata yasamu gashi tafito gidan tarbiya ga kuma natsuwa data fuskanchi
yarinyar nada ita, bugu da k'ari gata kyakyawa don har tafi khadijah kyau duk
da tsanani kamarsu don ita Ihsan tana da beauty point Sab'ani khadijah da bata
dashi, shiyasa most of people kece mata pretty
Suna isa sai ga Yusuf mijin Rafeeqa yazo d'aukar su, shima
balarabe ne dayake yana da wani aiki a
gabanshi shiyasa bai samu zuwa bikin Rafeeq ba
Shaddad D'an Rafeeqa da bazai wuce shekara goma ba ya rugo
wurinsu yana farin cikin ganinsu dayake ba'a tafi da shi ba saboda makaranta
saida ya gama tsalenshi na murna ganin mum d'inshi da granma gakuma uncle
d'inshi da sabuwar aunty daya yakawo masu sannan suka shiga mota suka nufi gida
A cikin motar ne yake tambayar Ammi wannan ce sabuwar Aunty
d'inshi matar uncle Rafeeq, Ammi ta amsa mashi dukda bai iya Hausa ba cikin
larabci yake maganar bai hana Ihsan fahimtar wasu kalaman nashi ba tunda ba
laifi ana koya masu a islamiya
Zuwansu gida keda wuya kowa ya kama bacci saboda gajiyar da
suka kwaso, gashi dama saukar dare
sukayi ma k'asar, gashi washe gari za'a
fara shagalin da Ammi ta Shirya masu na murnar biki
Da misalin k'arfe 8:00am na Egypt Wanda yayi dai dai da 7:00am na Nigeria, Ammi ce ta shigo d'akin da
Ihsan ta kwana don ta duba ko ta tashi,
saurin gaida ta tayi kafin Ammin tayi magana sai da tayi murmushi sannan ta
amsa tare da cewa "toh kiyi sauri ki shiga toilet kiyi wanka ga break d'inki
can ga kuma kayan da zakisa nan bisa gado don har mutane sunfara taruwa"
amsa mata Ihsan tayi cikin ladabi sannan ta shiga toilet
Saida ta gama yin breakfast sannan ta d'auko kayan da Ammi
tace tasa, mamaki ne ya kusa kasheta saboda yanayin kayan baxata iya sakasu
tafita cikin mutane ba duk da rigar lafiyarta lau hannun ne aka tsaga kamar
wata tantabara amma siket din duk a tsatsage yake har wurin cinya, shigowar
Rafeeqa ne yasa tayi saurin juyawa
Dafa kafad'ar Ihsan tayi tace "sister dama nasan kina
nan kin kasa saka kayan shiyasa nazo ince maki kada ki samu damuwa babu na
mijin dake shigowa ko ango sai idan da dalili zaki ganshi, da wannan zacen na
Rafeeqa ne yasa tasamu kwarin gwiwar saka kayan duk da tanajin kunya sannan ta
Dora alkebba data gani had'e da kayan
Haka akayi shagali tare da al'adu irin na
larabawan misra (cairo) ita dai Ihsan taga yadda akai ta dura mata
karanfani dayi mata wanka da ruwan madara sannan aka koma b'angaren kamshi, sai
kusan k'arfe 11:00am aka gama sannan tasa wata doguwar Riga mai hula ta zauna a
d'aki ayayin da mutane keta kai kawo cikin gidan
Rafeeq ne ya shigo cikin parlour ya tambayi Ammi yana son
ganin Ihsan don ya bata waya ta gaisa da yar uwarta, sai lokacin Ammi ta tuna
daba waya hanunta shiyasa ta yarda Rafeeq ya shiga d'akin da take tare da gaya
mashi ya kama ta ya siyo mata waya itama idan mutane sun lafa ta kira su Mama
taji ya jikin khadijar
Sallamar da Rafeeq yayi ita ta katse mata tunanin gida da
take, zama yayi dab da'ita sannan yace "pretty ya kike? Lafiya lau ina
kwana? D'an murmushi yayi sannan ya amsa tare da cewa "dama zuwa nayi mu
gaisa inji mikeke buk'ata" shiru tayi sai kuma tace "ina son gaisawa
da mutanen gida...toh yanzu wa kikeso a kira Mama ko khadijah? Sai ta d'ago ta
kalleshi sannan tace "a fara kiran Mama sannan ya khadijah" yace
"uhm autar Mama kenan ai yanzu kin zama tawa" ita dai batace komai ba
don a tsorace take, ganin su kad'ai ne a d'akin
***
Ranar da ta haska window d'in d'akin har ta samu ratsowa ta
gefen labulan ta dira har bisa gadon baccin su, haskenta ne zai tabbatar maka
da baza'a wuce k'arfe 10:00am ba amma har yanzu baccin su suke cikin kwanciyar
hankali don ko sallar asuba yau tare sukayi saboda sun so su makara kasancewar
sun Tara bacci mai yawan gaske a idanunsu
Jiddan ne yafara bud'e idonshi bai sauke su ko ina ba sai
kan fuskar khadijah dake dab da shi tana baccinta, lumshe idonshi yayi ya bud'e
yana k'arema fuskarta kallo, gaba d'aya tun ranar da ya ganta anyi mata Kunshi
lokacin da yace ta dauko mayafi ta Ruga yaga ta canza sosai amma sai yau ya kara
lura da canzawar tata duk da gyaran da tasha amma yana jin canji Dan gane da
ita ga kyau da take karawa don hatta kirjinta yanzu a cike yake...
Motsin da tayi ne ya ankarar da shi zata tashi shiyasa yayi
saurin rufe idonshi kamar mai bacci
Kamar yadda yayi itama haka ta zuba mashi ido tanajin
kaunarshi da tausayinshi na ratsata, jikinshi ta kalla taga yadda duk ya murde
sai ta tuna lokacin da suna makaranta ba haka yake ba amma yanzu duk ya canza
saboda yawan exercise... "Kallon fa? Da sauri ta kalleshi sannan ta tabe
baki kamar zatai kuka tace "dama ba bacci kake ba kana kallona"
rugumo ta yayi yana cewa "haba hot milk ni asuwa in kalleki" mutsu
mutsu ta farayi sai kuma ta tsinci kanta da son jin kamshin jikinshi shiyasa ta
shiga tusa kanta shikuwa hakan da take mashi na Neman jawo mashi abin da
yakeson,dama ya d'aga mata sai ta ida warwarewa sannan yakoma bakin aiki ya
d'aura daga inda yatsaya
D'ago kanta yayi yace menene? Kwanta bari in shiga wanka,
bare baki tayi da niyyar d'ankara mashi kuka sai kuma wayar shi ta d'auki
ringing
Yana dubawa yaga MY R ne sai da ya kada kai tare da yin
murmushi sannan ya d'auka ita kuwa khadijah tuni takoma jikinshi ta lafe
"A'a aboki kace Mani kun tsufa Egypt..."toh
handsome ina zaka sani tunda jiya soyayya tasa ka manta damu" gashin
khadijah ya shafa sannan yace "Allah ban San wulakanci kasan indai batun
kyau ne kafini" karaf Rafeeq yace "haka kuma matata tafi taka sai dai
matsala daya daka fini zama smart" yatsina fuska Jiddan yayi yace
"zan baka time nasan d'okin amarcine ke damunka yanzu ina pretty take mu
gaisa inji dai baka yi mata komai ba ko?...."ah ni su Yaya manya gata nan
so take Ku gaisa don tabar wayar ta nan gida"
Amsa tayi tare dayin sallama, sai da suka gama gaisawa
sannan yasa ma khadijah wayar a kunne sai lokacin ya lura Wai bacci take,
mamaki ya kama shi amma sai ya share ya tada ta ta gaisa da Ihsan sannan ta
koma
Tashi yayi yaje ya siyo masu abinci ya dawo har lokacin
bacci take hakan yasa ya tada ta, da kyar ya samu taci abincin kad'an ta kuma
cigaba da baccin
A b'angaren su Ihsan da Rafeeq tana gama wayar ta tashi da
niyyar tafiya yayi saurin rik'o hanunta, a tsorace ta waigo tana kallon shi
yace "pls bamuyi fira bafa..a hankali tace " toh ka sakeni sai muyi
firar" sakinta yayi amma kafin kace kabo ta ruga da gudu, mai Rafeeq zai
idan ba dariya yana cewa duk yawonki saina sha zumar yarinya kin gama guje
gujenki kizo hannu tare da barin d'akin
***
Waya yake da wani abokin aikinsu da za'a d'aura aurenshi
gobe dayake kano yake shine yake sanar da shi Rafeeq yana Egypt don haka bazai
samu zuwa ba,
Daga can b'angaren
Usman yace " haba ba damuwa dama Mujaheed yace yana nan tahowa yau toh kai
sai yaushe?.. "Dama tunda karfe 2:00pm za'a d'aura auren shiyasa Nace gobe
da safe zan taho...bai ida wayar ba ya kashe saboda jin khadijah ta tashi tana
kyara amai
Rik'eta yayi harta gama sannan ya gyara wajen duk jikinshi
kyarma yake saboda yadda yaga tana amai ga jikin ta ya d'auki zafi dama ba tun
yauba yake lura da yadda ta canza ba
Saida ya samu ta d'ansha ruwan tea kad'an sannan ya shiryata
don zuwa Asibitin Allah bamu lafiya dayake mai asibitin abokin uncle d'inshi ne
don yana son aduba mashi ita nan take
A gurguje ya tafi da ita asibitin kuma kamar yadda yaso haka
ya samu aka duba ta batare da b'ata lokaci ba
Zaune suke shi da khadijah yayin da Dr Yusuf ke gabansu,
shidai Jiddan ya k'osa yaji mai xaice...mik'o mashi takadar Dr yusuf yayi ita ta katse mashi tunani,
sannan yace....
*_Mrs Abdule
Sule_*
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
*page 176-180*
*Y*au saura 3 days a fara biki, amare sunsha kyau har sun
gaji, Khadijah kuwa har wani yellow yellow fatarta keyi ga kirjinta da yak'ara
cika yayi fam, saidai tun ranar da sukazo har yanzu Jiddan baisamu ya ganta ba
Don kullum idan yaje gidan sai ace batanan shi kuma bazai
iya tambayar Mama inda ta tafi ba haka zaigama 'yan kewaye kewayenshi yatafi
batare da yaga ta inda zata fito ba yakuma kasa tambayar koda Ihsan inda taje
ba
Ita kuwa khadijah tana sane take guje mashi don tasan cewa
zaiyi ta bishi masaukinshi al halin ga 'yan uwa tana Gani harda wad'anda ta
Dad'e bata Gani ba kuma ai akwai kunya aga tabi miji hotel shiyasa ta kashe
wayarta don ma karya dameta da magiya
Zaune suke palourn ba kowa daga mai k'unshi saimai gyaran
jiki tare da su Ihsan sai khadija dake
zaune gefe don ita an gama mata na k'afarta har ta wanke yanzu ma na hannun da
akayi take jira ya bushe
Seema da ake cikin yi mata kunshi tace "Allah Yaya
Khadijah bakiga yadda Jan k'ushin nan yayi maki kyau ba" tace "kedai
Seemah ko zagina kike? Sai ga Iman tafito daga kitchen tace "toh uwar kuri
an yabeki madadin ki gode kin tsaya kina wata magana gaskiya Jiddan na fama
dake" tak'arshe maganar tana dariya
"Wallahi ba wani fama kedaice za'ace kina fama da
mijinki tunda har yau bamu taba gaisawa ba kullum baya gari halinsu d'aya da
mijin saudat" duk tana maganar ne cikin tsiwa shiyasa Iman tace
"Oh ni nashiga ukku da Khadijah sha kuruminki ranar
d'aurin aure zaizo Ku gaisa ni kuma in huta da gori, zabura Khadijah tayi kamar
wadda aka tsikara, Iman da har ta tsorata tace "lafiya?
"Allah wani irin fitinannen fitsari nakeji kamar yazubo
mani wallahi ban iya rik'eshi" Iman tace "toh ai sai ki sakeshi a
gaban k'annanki tunda baya rik'uwa"
Jiddan da yazo shigowa palourn yaji abin da khadija ke cewa
sai ya tsaya yana sauraranta
Ihsan ce keyi ma Khadijah dariya, khadijah tayi saurin
kallonta tace "ke ni tsararki ce shekara nawa na baki? Ihsan tace "yi
hakuri 6 years kika ban.."toh gara ki shiga hankalinki"
Sai kuma ta tabe fuska tace "ya zanyi bari in tafi
toilet d'in can baya in wanke don gaskiya ban iya rik'e fitsarin nan har lallen
nan ya bushe" tashi tayi Iman na mata dariya sai, tashin ta keda wuya
kallabinta ya fadi k'asa kallon Iman tayi
Tace" Iman don Allah d'auko ki d'aura mani" tace
"haba yariya sai dai ki tafi haka" tsoki ta buga sannan takama hanyar
fita
Shi kuwa jiddan yanajin inda zata tafi sai yaje wurin ya
boye yana jiranta, tana zuwa ta durk'usa zata bud'e famfo saiji tayi an rik'e
mata kugu tabaya, da sauri ta bud'e baki zatayi ihu yayi saurin rufe mata baki
da hannunshi
Shiru tayi tana kallon shi, baice mata komai ba ya jata zuwa
toilet d'in sannan ya tartare doguwar rigar jikinta
Tsaye tayi tana kallon miyake nufi, ganin kallon datake
masa yasa ya d'aure fuska kamar bai
tab'a dariya ba yace "tsuguna mana kiyi! Ba musu ta tsugunna tayi, tana
ganin ya debo ruwa zai mata tsarki tai saurin rufe idonta aranta kuwa cewa take
ai wannan iskanci ne ba tsarki ba....
Tunanin ta ne ya tsaya saboda jin yadda tsigar jikinta ke
tashi, haka ta d'aure har ya gama suka fito, shima tsarkin da yayi mata ba
k'aramin tada mashi hankali yayi ba d'aurewa kawai yayi
Saida ya tattara natsuwar shi sannan yace "Khadijah
guduna kike ko? Tace "a'a"
"toh ina kallabinki..."yana parlour"
"jeki d'auko mayafinki ki rakani idan munje kin wanke
k'unshin acan" d'aga mashi kai kawai tayi, saida ta bari tayi nisa da inda
yake sannan ta juyo tace
"Nizakayi ma wayau toh ba inda zan bika" sannan
taruga da gudu cikin palourn, lips d'inshi ya d'an lasa yace "yariyar nan
ta raina ni but zanyi maganin ta soon
Haka yaja mota ya tafi cikin fushi, washe gari ma da akayi
kamu baije ba don fushi yake da Khadijah, itako harkar gabanta kawai take
The next day ya kama
ranar dinner, zaune suke kowa ya shirya suna jiran azo d'aukar su ita
dai Khadijah tayi shiru tana sauraron Iman dake ce masu Ihsan wai bayan aure
idan kuka d'an saba da namiji yanaso wani lokacin mace ta nuna tana buk'atarshi
amma a cikin kissa....
Motocin da suka fara zuwa ne yasa suka fita ita dai Khadijah
ta manta da tayi ma Jiddan laifi
Suna zuwa kowa ya kama gaban shi suka bar khadijah nan tsaye
a tunaninsu sunsan Jiddan ne zaizo d'aukarta, sai ware idanu take taga ta inda
zata ga Jiddan amma bashi ba alamarshi har amare suka gama tafiya bata ganshi ba
Daga can baya ta hango shi zaune shi kad'ai cikin mota,
murmushi tayi ta nufi wurinshi saidai yana ganin ta ya d'auke kai
Bud'e motar tayi ta shiga tace "sorry nabarka kana ta
jira, bansan nan kayi parking ba" banza yayi mata baitanka mata ba, ganin
yashare ta ne yasa ta tuno laifin ta wanda ita bata d'aukeshi da wani abuba
balle haryayi fushi, kallonshi tayi cike da kissa tafara bashi hak'uri amma
still yayi banza da'ita, har suka isa wurin da za'a gudanar da dinner d'in
Biki yayi biki mawak'a kowa sai baza basirarshi yake don ya
kwashi rabonsa kamar daga sama zazzafan muryar mawak'in nan Nura M. Inuwa
yafara kiran sunan Jiddan yana wasashi yana fad'in soja marmari daga nesa,
hakan yasa Jiddan tashi ya nufi cikin
taron yana b'arin kudi
Dandanan idon yan mata yayi kanshi, shi kuwa mai wakar sai
wasashi yake tare da kiran sunan uwar gidanshi
Khadijah ko ganin yadda 'yan matan wurin sukayi mashi ca sa
ido yasa wani azabeben kishi ya gama cikata, tashi tayi taje cikin taron tare
da rik' e hannun Jiddan, gudan kuma ta Dora saman kafad'arshi
Ganin yadda take taka rawa jikinta na wani irin juyi duk sai
shima yaji kishi ya dameshi, Jan hannunta yayi bai zame ko ina da'ita ba sai
cikin mota
A back seat ya aje ta shima yaza gayo ya shiga, kamota yayi
zai rungume tace "yayana lafiya bafa gida Muke ba" kwalla ce ta taru
cikin idonshi yace "so kike in maki kuka sannan ki bani hakkina? Sati
d'aya kenan rabona dake amma guduna kike, Ko kin manta annabi yace ko akan
dabba ne miji ya....bata bari ya ida ba ta had'e bakinsu wuri guda
Har sassarfa Jiddan keyi saboda yadda yayi missing d'inta
saida ta lallabeshi sannan ya kira d'aya daga cikin soldiers d'in dake wurin
yayi driving d'insu donshi baida kuzarin driving
Suna zuwa hotel d'in ya shiga nuna mata yadda yayi missing
d'inta, har sunyi nisa sai wayar shi tafara ringing don ita khadija tata na
gida
D'auka yayi yaji Rafeeq wai su Ihsan ke Neman khadija shine
ya kira yaji ko suna tare don basu ga lokacin da suka fita tare ba, amsa mashi
Jiddan kawai ya iya yi don baya cikin hankalinshi sosai don ba k'aramin canza
mashi Khadijah tayi ba ga kirjinta da ya k'ara cika
Washe gari jama'a suka shaida d'aurin auren Rafeeq da Ihsan,
Samra da Muhsin, Seemah da Abdul Jabar, Mujaheed da Islam dukda amaryar Islam
na Kaduna amma kawu yace a d'aura anan don a rage ma mutane wahala
Lokacin kai amare nayi aka kai Ihsan wajen Ammi don tace
Egypt zasu wuce washe gari don akwai bikin da ta had'a can saboda 'yan uwanta
Motarshi yayi parking a gaban gidan su Seemah sannan ya
kalli Khadijah yace "kiyi sauri don Allah" toh tace dashi ta fara
k'ok'arin bud'e k' ofar saiga Iman, gaisawa tayi da Jiddan sannan take ce ma
Khadijah tazo su gasa da Adnan gaya can tsaye dasu Seemah hakan yasa ta nufi
inda suke
Seemah ce ke kuka sosai Adnan na lallashinta, cikin kuka ta
fara cewa "dole inyi kuka wlh mutuwar Yaya SS ta dawo Mani sabuwa saboda
yadda yaci burin ganin ranar nan...
Dai-dai lokacin khadijah ta iso, jin abinda Seemah ta ambaci
SS yasa ta shiga tariyo kamanin mai sunan, bakin ta har kyarma yake tace
"S..S.." Adnan da baisan da'ita a bayanshi ba saijin maganar ta yayi
shiyasa ya juya
Shima tana ganin shi ta tuna inda tasanshi, ja da baya ta
farayi har ta hau saman center din bata sani ba,
Ba abin da take furtawa sai "S..S..SS...S.S wata mota
ce ta shigo layin batareda mai tukin ya kula da Khadijah ba ji kake........
*_Mrs
Abdul Sule_*
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
*page 191-195*
"Uhm su Jiddan
kenan an kusa zama manya..." Haba! Don Allah likita bokan turai kada kace
Mani zargina dai-dai ne" d'aga kai Dr yayi sannan ya mik'o mashi takkada
tare da cewa" a kallah cikin dake jikinta yayi sati biyar har yashiga na
shidda don haka kada ka damu kanka akan laulayin datake da zaran cikin yayi
kwari zata daina insha Allah, amma kafin nan bari na rubuta Makan maganin da zata dungasha
insha Allah zasu taimakamata wurin kuzari da lafiyar abinda ke cikinta"
Shidai Jiddan gyad'a kai kawai yakeyi kamar k'adangare yana
kallon khadijah data sadda kanta k'asa
Ita kuwa rayuwarta ta bayace ta dawo mata sabuwa saboda
tunawa da tayi da wancan cikin nata da SS,wanda
yaci burin idan ta haifi namiji zaisa sunan Jiddan saboda farin cikin
ta... Tunanin ta ne yakatse jin Jiddan ya kama hannunta da niyyar su tafi
Har suka isa mota ba abin da tace, kafin kuwa su isa 🏨 d'in yayi mata tambaya takai goma ko tana son
wani abu, amma batace komai ba
Suna zuwa ta shiga wanka shi kuma ya tafi sawo masu abinci,
bayanta gama shirya wane ta zauna zaman jiran dawowarshi, Bai d'auki lokaci
matsawo ba sai gashi ya dawo, zama yayi ya bud'e abincin da niyyar ciyar da'ita
sai gani yayi tafara kakarin amai
Da sauri ya rik'eta ayayin da take mashi nuni da ya rufe
abincin, bayan yarufe sannan ta samu natsuwa, kallonta yayi yace "baki ci?
D'aga mashi kai tayi sannan tace "batason k'amshin miya ko kallonta ma
batasoyin..."
"Toh yanzu mi kike son ci? d'aga kanta tayi sama alamar tunani sannan
tace "danyan mango" yace haba khadijatu ai wannan ba abinci bane sai
yayi maki illah" d'an shagwabewa tayi kamar zatayi kuka,take ya diririce
yace "toh naji zan samo maki amma
ki fad'i harda abinci kinji? Shuru tayi na wani lokaci sannan tace "toh shinkafa da mai sai
gishiri kada asa magi da yaji"
Da tausayi ya kalleta jin irin abincin da zataci kuma ita
nan shiyafi mata dadi, da sauri ya fita don samo mata abincin, ita kuwa tunanin
shashshakar da Ihsan ta tab'a had'a mata lokacin da tana da cikin SS take
kwad'ayinta yataso mata, wani miyau ta had'e sakamakon tasshin tafarnuwa data
tuna Wanda ya lullub'e shashshakar da taji manja a wancan lokacin, amma ba
yadda ta iya haka ta hak'ura don tasan zatayi ma Jiddan wuyar Samu,gashi
bayadda zatayi ta had'ata a inda take
Wayar tace ta d'auki ringing saida ta k'ara a kunne sannan
tace" my Iman kin kyauta ai ..."haba khadijah nafaje gida akace kina
gurin mijinki toh ko hotel d'in kikeso na biyo Ku? "Toh bani kikazo gani
ba?.." Eh hakane amma ina tunanin notinki ya kwance ko"
Dariya khadijah tafarayi tana cewa "ni ba k'usa bace
balle ace ina da noti saidai ke" a b'angaren Iman d'in itama dariyar tayi
tace "Kinga ni kira nayi inyi maki congract shine kika tsareni da
d'umi..." Uhm kedai bari Wallahi ina ma kan tunanin wancan cikin na ya
SS"
"Sai hak'uri Allah bai hukunta jini SS zaitaka doron
k'asa ba" nunfasawa tayi ta cigaba da cewa "wai kuwa ya kikaji
lokacin da kika farfad'o na d'auka baki San anyi auren Ku da Jiddan ba..."
"a'a ko d'aya don wallahi dana farka da tunani rasuwar SS natashi
saidai ina jin ance mijina sai naji komai yak'ara dawo Mani kamar a mafarki
harda zuwan mu india duk ina sane wallahi"
Tun tana wayar Jiddan ya shigo in banda kallonta ba abinda
yake, saida ta gama wayar sannan ta kalleshi tare dayin murmushi tace"
sannu my dear kadawo? D'aga mata kai yayi ya aje abincin yana k'ok'arin bud'ewa
don shi burinshi bai wuce taci abincin ba
Saida ya bari ta gama cin abincin sannan yace "kin
k'oshi d'aga mashi kai tayi tana k'ok'arin kwanciya shima sai ya kwanta tare da
shafa cikinta Wanda hakan yayi mata dad'i
Ganin tana lumshe idonta yasa yaci gaba dayi mata haka har
bacci yayi awon gaba da'ita sannan ya tashi don had'a kayansu
Wanka yafara sannan ya had'a kayanta daban, nashi daban
saboda gida zai barta, Inyadawo kano sai ya dawo su wuce Abuja saboda yanayin
datake ciki
Lokacin data tashi taga abin da Jiddan yayi sai tahau
tambayarshi ya akai yaware kayanta daban danashi batare zasu tafi ba, bai
tunanin komai ba yagaya mata gida zai barta, aikuwa ta bud'e mashi shafin
rigima harda kukanta, tun yana kwatanta mata har ya gaji ba yadda ya iya dole
ya yarda zai tafi da'ita tunda baya son abin da zaisa mata damuwa.
A Daren ranar sukayi bankwana da kowa don har gidan Samra
saida sukaje da gidan Iman sai a lokacin Iman ke gaya ma khadijah itama ciki
gareta, sannan rabi'atu ta haihu, da wannan farin cikin sukayi sallama da juna
Washe gari tunda safe suka kama hanyar kano shiyasa k'arfe
10:00am tayi masu a kano
Hotel Jiddan yakama masu kasancewar kwana d'aya zasuyi,
saida ya tabbattar da mutuniyar tashi taci abinci kafin ya shige wanka
Yana fitowa ya ganta saman gado bacci ya kwasheta da k'irin
d'anyan mangwaron ta a hannu, d'an murmushi yayi duk da bayason tana sha amma
yaya iya dole yakyaleta tunda yanayi ne yasata shanshi, agurguje ya shirya ya
fita
Koda ya isa wajen abokin nashi Usman yafara mashi tsegumi
wai yadade bai iso ba, saida Jiddan ya bari ya kai aya sannan yace "toh
naji sarki mai Aisha bada kanka asare kaje gida kace ya fad'i,nima da hrtcorn
d'inna nazo shiyasa kaga na Dade don Kasan...uhm"
"nasan me? cewar Usman, saida Jiddan ya k'ara shakar
iska da kyau don yaji dad'in koro da bayani sannan yace "nakusa zama
babafa..."kai captain banson k'arya fa!" kallon ukku saura kwata
Jiddan yayi mashi kafin yace "na tab'a Maka k'arya ne? Ka bari anjima
da'ita zamuzo dinner saika tambayeta tunda ni nazama mak'aryaci"
"rufaman asiri shegen gora ni rashin kunyata baikai nan
ba"
"na'aza ka wuce nan tunda ni baka yarda dani ba,
badamuwa in munzo sun gaisa taga Kuma
amaryar, tunda yau dai Allah yayi Usman ya auri Aisha" dariya sukasa baki
d'aya sannan sukaci gaba da yadda zasu tsara shirye-shiryensu har zuwa lokacin
da aka D'aura Auren
Jiddan bai samu damar komawa wajen khadijah ba sai gabda
la'asar, yana zuwa ya tadda ta tana karatun novel na Hausa na fitacciyar marubuciyar nan _zarah
surbajo_ Wanda tauraruwarta ke haskawa a
duniyar yanar gizo mai suna Ummu Aymana, duk sai yaji ta bashi tausayi don
yasan kad'aici ma kadai ya isheta shiyasa baiso zuwa da'ita ba
Tana ganinshi ta tashi ta rungume shi, zaunar da'ita yayi bakin gado sannan yace
"kad'aici ya isheki ko? Bata bashi amsa ba tahau ragemashi kayan jikinshi
tana cewa " yanzu kazo kayi wanka kafin lokacin sallah don nasan ka kwaso
gajiya sosai" shidai kallonta yake yana murmushi saboda yadda yaga ta
warware ta samu
sauk'i sosai
Aikuwa kamar yadda yayi niya Ana gama sallar la'asar yajata
suka fita yawo harda siyayya yayi mata da wata purple din gown me kyau da zata
saka anjima idan zasu dinner tunda shima purple din kaya zaisa, basu suka samu
dawowa ba sai gabda magrib don haka jiddan ya wuce massallacin dake cikin hotel
d'in bayan ya aje khadijah ta wuce room d'in dasuka Kama
***
Shikuwa Rafeeq bil hakk'i yakeson kebewa da pretty amma
gudunshi takeyi haka kuma Ammi ta kasa ta tsare bata bari yana samun damar ke
bewa da'ita, donshi harya farajin haushi shiyasa ya k'osa su koma Nigeria
Zaune suke a parlour shida Ammi yayin da Ihsan ke zaune gefe
guda tana saurarsu duk da ba duka abinda suke cewa takeji ba amma su a zatonsu
Bataji maisuke cewa ba
Duk zance bai wuce son abashi matarshi dayake ba, saida kyar
ya samu Ammi ta tashi ta barshi da Ihsan, itama kuwa Ammi na fita tayi niyarfita
Saurin shangabanta yayi yace "haba ina zaki?tace
"Ammi nakeson bi" zaro ido yayi yana kallonta saboda cikin harshen
larabci tayi maganar
"Pretty dama kin iya larabci? Kice kinajin abinda Nace
ma Ammi..girgiza kanta tayi tace "a,a
ina dai gane kadan " d'an murmushi yayi yace " OK zamu dungayi
tare har ki kware kafin ki Haifa Mani babies masu kama da.... Bai ida ba ta
shammace shi ta ruga ba yadda ya iya dole ya hak'ura
***
Dinner tayi dinner,Amarya da Ango ansha kyau, inda fasihin
mawak'in nan Ali jita yana ta suburbud'a masu jitarshi, su khadijah da jiddan
suma sunsha kyau da sauran Wanda suka halarci Wurin liyafar kowa kagani sai
wallai niya yake don kyau
Mamaki bai kama khadijah ba saida taga Amaryar Don tabbas
bazata taba mantawa da fuskar Ashanty ba duk da sau d'aya ta tab'a ganinta a
bisa tsautsayi, dasauri ta is a inda Ashanty take hakan yasa Jiddan yabita da
sauri
Tun kafin khadijah ta iso Ashanty ta hangota itama sai tayi
saurin isa inda take tare da rungumeta tace "khadijah!...." Aisha!
Cewar khadijah da mamaki sukuwa Usman da Jiddan harma da Mujaheed dayake wurin
kallonsu suke suna mamakin dama sun San juna?
Tunaninsu ne ya katse jin Ashanty na ambatar ina Laila? Ai dan danan fuskar Jiddan ta canza,
kur ya kura ma khadijah ido Don sonjin wacece Ashanty Don duk yadda akai tana
da alaka da Laila.....
_*Mrs Abdul
Sule*_
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
*page 196-200*
Juyowa khadijah tayi tana kallon Jiddan tana k'ara nazartar
yanayin da yashiga daga ambatar sunan Laila da akayi, wani kallon tuhuma ya
cigaba da aika mata nasan sanin ya akai tasan Ashanty da kuma miye alakarta da'ita,
bata wani b'ata lokaci ba ta hau yi mashi bayanin yadda tasan Ashanty da kuma
taimakon da tayi masu
Jikinshine yayi Sanyi da irin namijin k'ok'arin datayi
naganin yakubuta daga sherrin Laila yana kuma godema Allah da yashiryar da'ita
kafin lokaci ya k'ure mata, bakamar Laila da tayima duniya zuwan wohi ba,
kallon b'angaren da Usman yake yayi yana k'ara jinjina mashi na jajircewa
dayayi ga abinda yakeso, Don shi shaida ne akan irin son da Usman keyima
Ashanty duk da kasancewar basu San juna ba da'ita
Kuka Ashanty ta fashe dashi jin cewar Laila tarasu, bayan ta
nisa da kukan ne takama hannun khadijah tana cewa "khadijah kamar yadda
kika sani sunana Aisha, Usman kuma d'an uwana ne, kasancewar mahaifin mu baya
bari muyi karatu gaba da secondary yasa yake zab'a mana mijin aure domin duk
yayye na mata haka yayi masu mazan ne kawai ke cigaba da karatunsu har inda
suke son sutsaya, toh nima haka ta kasance a kaina sai dai ni gaba d'aya Allah
baisaman son Usman araina ba,domin nafi kwad'aitar da incigaba da karatu ganin
bazan iya auren shiba bama shiba kowa ne namiji yasa nagudu nabar gida da zumar
na tafi karatu saina gama in dawo nasan lokacin zasu gane amfanin
hakan..."
Nisawa tayi sannan taci gaba da cewa "Ashe abinda ban
sani ba na tafka baban kuskure a rayuwata tunda ba kud'i gareni ba, haka naci
gaba da rayuwa ta a garin Kaduna ba Wanda na sani har Allah ya had'ani da Laila
wadda itama auren dole ne ya korota shine mukaje gidan wata magajiya karuwai,
itace silar samu a hanyar bariki har takai da munzo munfi k'arfinta saboda da
manyan Alhazai bariki muke harka.
In takaice maki labari daga baya ma sai muka tattara muka
koma Abuja Don babu abinda bamuyi har Allah ya had'amu da Jiddan Wanda shine
mutum na farko da ya fara gagarar mu duk dani bazai iya shaida fuskata ba
kasancewar bamu tab'a had'uwa saboda wani sab'ani da muke samu, amma nasan
fuskarshi tawa ce kawai baisani ba, har hakan ta kasance..
Lokacin da na dawo gida kuwa da kyar nasamu iyaye na suka
yafe Mani sannan na fara Neman tuba wurin Allah haka dangina ma na nemi gafarar
su kafin daga baya Usman ya dawo yace zai aureni Don har lokacin baiyi aure ba
Daga farko mahaifina yak'i amincewa nima haka don ina ganin
ban cancanci ya aureni ba dukda kasancewar bani d'auke da wata cuta amma ai da
kunya saida nagama yawon tazubar ace namiji kamili kamar Usman ace zai aureni
amma ganin yadage yasa nayi istibira'i
wata ukku, shine har Allah yanuna mana wannan lokacin toh kinji abinda yafaru
bayan rabuwarmu
Kallon Jiddan khadijah tayi cike dajin tausayin Aisha sannan
ta kalli Usman tana jinjina mashi kai alamar yayi k'ok'ari kafin Jiddan yace
"shine Wanda nake gaya maki shima saboda soyayya yasa ya tafi soja"
khadijah tace "dama akwai masu iyayin abin da kayi? Sai Ashanty ta bata
amsa da cewa "gara ke aure kikayi amma nifa kedai Allah ya rufa
asir....bata ida ba Usman ya kama hannunta yana cewa
"Kunga fa mutane sun taru wurin nan ya kama ta mubar
zancan nan" jiddan yace "kaide ko sauri kake akai maka matarka ai da
Rafeeq na nan da kasha tsiya "dariya Usman yayi yace "dad'in abunma
kokai baibariba balle kayima wani tsiya"
Daga haka suka cigaba dayin abinda ya kawo su, anci an sha
sannan ango da amarya suka wuce gidansu
saidai muyi masu fatan alheri
A gajiye suka koma masaukinsu, don haka wanka kawai khadijah
tayi ta kwanta shima yana gama yan danne dannenshi a waya yayi wankan sannan ya
kwanta tare da rungumota
Tanajin yadda ya rungumeta tasan abinda zaiyi mata, tunanin
gajiya da yadda take jin jikin ta take saidai tasan dole Jiddan ya nemeta don
rabonshi da'ita kusan 4 days kenan
Juyo da'ita yayi yafara manna mata kiss ako ina nasak'on
jikinta, k'ok'arin cire rigar baccin kawai yake saidai ganin bata mashi yadda
yakeso yasa ya d'ago yana kallon cikin idonta da kyar yace
"kin..gaji..koh? Girgiza mashi kai tayi don badan
k'aramin sonshi da tausayinshi takeji ba, rugumeshi tayi tana shafa mashi kai
kamar yadda ta saba mashi Wanda hakan na mashi dad'i sannan tace "I luv
u.. Ko amsa bai iya bata ba ya shiga k'ok'arin nema ma kanshi natsuwa a inda
yafi daukar mashi hankali kafin ya fara tona mata asirin zuciyarshi da yadda
sonta ya raunanata shekaru masu yawa bak'aramar k'ara tara mata gajiya yayi ba
don Saida yaji tana neman yi mashi kuka yasa yasarara mata badan yagaji ba sai
don tausayinta don baik'i ya kwana saman ruwan cikinta ba yana kwasar gara
Washe gari suka kama hanya sai Abuja Wanda ba abinda
khadijah keyi cikin mota daya wuce bacci shidai Jiddan mamakin baccinta yake
saboda bata d'aukar lokaci sai kaga ta bingire da bacci kamar wata jaririya don
yanzu hours din da take tana bacci yafi yawa akan Wanda take farke ita dai haka
nata cikin yazo dashi kenan ganin shi k'adai ke zancen zuciya yasa yak'ara
maida hankalinshi kan driving tare da ambaton Allah abakinshi
Suna isa lokacin ta
tashi daga bacci, Jiddan yake nuna mata
gidan Rafeeq Wanda kana hagenshi daga nasu gidan sannan suka shiga gida
Sakin baki khadijah tayi da suka shiga tace" yayana
waya gyara gidan? Rumgumo ta yayi ta baya tare da d'aura kanshi saman
kafad'arta yace "tun kafin mutaho nakira maigadi yasa matarshi ta gyara
don nafison da mun dawo ki bani...bai ida ba ta b'anb'are hannunshi dake saman
kugunta da yunk'urin rugawa
Saurin rik'eta yayi yace "haba khadijah wannan ai
wautace sai kija Mani asara, don Allah koda wasa kada kice zaki ruga kinji? Ita
harga Allah mantawa take tana da ciki don haka tasaki yar dariya tare da cewa
"toh aini mantawa nake fa" sugummar ta yayi kamar wata yarinya sai
kad'a k'afafunta take, bazarce ko ina da'ita ba sai bedroom d'insu yana cewa
"Toh ai shiken bari kigani d'aukarki mazanyi
princess" dariya ta kamayi tana cewa "ai kuwa yau har tawai nakeso
kayi Mani.. Harda ma.....
Ban ida jin abinda suke cewa ba sakamakon banko k'ofar
d'akin da sukayi ni kuma ban bisu ba saboda Biro ta da ta k'are sai na tafi
sayen wata
***
A yaune su Rafeeq suka dawo don haka Jiddan bai samu zama ba
tunda dagashi har Rafeeq din ranar Monday zasu koma aiki, yoh Alhamdulillah sun
dawo saidai mu baro ma pretty da Rafeeq fili don shan amarci
A gajiye ya dawo gida, khadijah na ganinshi tazo ta rungume
shi, kumatunta ya girgiza kamar yadda suka saba tun suna yara itama tayi mashi
kafin su fara zuba soyyayar su yadda ya dace
Kwaci tashi asarar mai rai cikin khadijah har ya shiga wata
ukku iyayin da take samun kulawa mai kyau daga wurin Jiddan
Dawowar shi kenan daga wajan aiki, sallama yayi khadijah ta
amsa mashi batare da ta taso tayi mashi oyoyo ba kamar yadda ta saba saboda
abinci da ta tusa gaba tanaci
Zuwa yayi ya tsugunna gabanta yace "an deejah na abinci
akeci? Daga mashi kai tayi, shi kuma kallon abincin yake ba wani Abu bane illa
taliya da manja
A hankali yace "idan iceprncess ta yarda zanje gidan
Rafeeq naci abinci" don shi yagaji da cin komai jalof ace kwata kwata ba'a
son ko kamshin miya
A b'angaren ta itama tausayinshi takeji don tasan dole ya
gaji shiyasa tace "me zai hana idai ba za'ayi Mani tsarabar kamshinta
ba"
Yar k'aramar dariya yayi sannan ya tashi yayi wanka ya wuce gidan Rafeeq
Koda yaje saida Rafeeq ya gama sharranceshi sannan suka
gaisa tare da fara cin abincin tare
Hira suke sama-sama Jiddan yace "Rafeeq kasan wani Abu?
..a'a sai kad'i cewar Rafeeq sannan Jiddan yace so nake idan khadijah ta haihu
insa sunanta" dariya Rafeeq yayi yace "toh kai wayace maka mace za'a
haifa idan aka haifi namiji fa? "sai in bata zab'i idan namiji aka haifa,
d'an k'aramin murmushi Rafeeq yayi yace "toh dame za'a rinka kiranta?kasan
bazamu kirata da khadijah kai tsaye ba
Plate d'in daya gama cin abinci ya ture tare da gyara zaman
shi saman cushion din sannan yace "wannan kuma naba abokina zabi", da
farin ciki Rafeeq ke cewa "ai kuwa naji dad'i kuma zan bata suna Wanda ya
dace da ita Allah dai ya safki khadijah lafiya..." Ameen wai ina pretty
take ne ? "Uhm wlh fushi take don na gaya mata batun tafiyar mu shine ake
fushi, shiyasa kaganni zaune parlour ni kad'ai, saita d'an huce sannan in gaya
mata yanayin aiki ne kasan ita ba sabawa tayi ba"
Mikewa Jiddan yayi yana cewa "kaga ni banma gaya ma
khadijah ba gashi jibine..mstww ni wlh ban son tafiyar nan saboda yanayin da
khadijah ke ciki akwai had'ari in barta ita kad'ai"
Tafiya suka farayi Rafeeq na d'an taka mashi yace "ai
sai hak'uri amma ni da ka barta ita kad'ai tunda ga yar uwarta kusa a kulle
gida daya mana basai su xauna wuri d'aya tare ba" gyada kai jiddan yayi
alamar gamsuwa yace "hakan kuwa yayi sai a kulle nan ita pretty taje can
" da wannan shawarar sukayi sallama da juna sannan jiddan ya wuce gida
Yana zuwa ya tarar da ita ta gama cin wani abincin shima da
manja, kusa da ita ya zauna sanan yace "wai khadijah baki gajiya da cin
wannan abincin shifa na barki kinaci.." Toh yayana ya zanyi bakina ne ba
dad'i"
"Toh khadijah kema dai ko nama bakici don Allah ki
dinga ci kinji? D'an shiru tayi sannan tace "naji zan dinga ci amma nakan
rago.."badamuwa zansa a dinga kawo maki duk bayan kwana biyu saboda an tura mu aiki zuwa Cameroon amma ba dadewa zamuyi ba don bazamu
wuce two weeks ba"
Tun kafin ya gama maganar khadijah tayi sake da baki tanajin
shi hakan yasa kwallah taruwa cikin idonta Baice komai ba sai don tunanin yadda
zai tafi ya barta ita kadai bayan tana da laluri kuma tana buk'atar shi kusa
da'ita.. Girgiza mata kai ya farayi alamun kada tayi mashi kuka
Itama kanta da girgiza tare da cewa "tafiya fa kace!...