HABIBI DA'IMAN 201-220 END
*page 200-205*
.."Eh tapiya khadijah amma ki kwantar da hankalinki keda pretty zaku zauna kafin mu dawo ai ba Matsala ko? Nauyayyar ajiyar zuciya ta safke jin cewa pretty zata dawo gidanta su zauna kafin su sudawo yasa hankalinta ya kwanta, d'aga mashi kai tayi alamar ba damuwa
Kwance take saman cinyarshi tana karanta wani novel mai suna
...kawarta ce sanadi
Samra kenan ayayin da Muhsin yake waya da abokin nashi yana
cewa " gaskiya J nidai a tawa shawarar kada kace idan ta tashi haihuwa sai
kunje wata k'asa, in banda abinka kai da kake Abuja meye na tafiya wani wuri?
Ai akwai hospitals masu kyau"...daga can b'angaren banji abinda yace ba sai ji nayi Muhsin yace
"OK yanzu saura sati daya kadawo kenan?..
Rafeeq"
Hanging up din call din yayi sannan ya shafa kan Samra da
tayi nisa a karatunta yace "Jiddan na gaidaki..ina amsawa Ashe basu nan?
"Eh ya akayi kika Sani?..nima da mukayi waya da Islam
ne take gaya Mani don ita gida ta koma wai bata iya kwana ita kadai a
gida"
Tashi Muhsin yayi da niyyar fita yace "toh kinga
laifinta ko ke zaki iya kwana ke kadai ne" zumbura baki tafara yi shikuma
yayi saurin ficewa don kada ta shiriritar dashi zuwa massallaci
***
*3 months ago*
Alhamdulillah komai
yana tafiya Normal a yayinda b'angaren jiddan da khadijah har yanzu tana fama
da laulayin cikin domin kuwa yana wahalar da'ita dukda yafita watannin kwaikwai
amma hakan baisa ya sararamata ba
Fitowarta kenan daga bedroom ta nufi inda Jiddan yake zaune
tare da katon cikinta kamar kace haihuwa yau ko gobe saboda wani irin girma da
cikin yayi duk bai wuce wata shidda ba
Zama tayi sannan ta bude mashi tafin hannunshi ta saka mashi
wasu beat's guda ukku tana k'ok'arin yin magana
saurin cewa yayi
"Eyye bincike kikayi Mani ko hrtcon? Girgiza kai tayi
tace "a,a wallahi kawai nima bansan yadda akayi naje wurin ba kawai dai
ina mamakin yadd har yanzu suna nan"
"Toh naji ina D'an hannun yake?hannunta dake boye a
bayanta ta fiddo tare da mik'a mashi, yace "oh da b'oyewa zakiyi ko? Bayan
Ke ki ka bani.."a,ah nifa da ajewa zanyi idan na haihu insa ma baby
koh" ta k'arashe maganar cikin sigar shagwab'a
Da Sauri ya kamo hannunta ya saka mata yana cewa "toh
gashi jeki aje tunda baby khady zakisa mawa don ita kad'aice zan iya bari
asamawa
Tashi tayi dakyar ta
tafi don adanawa tana cewa "yayana da alama idan na haihu zaka daina ji
dani"... biyota yayi yana cewa "wane ni indaina ji dake princess ai
bari ma in gwada maki yadda nakeji dake...daga haka suka ida shigewa dakin
_(nace uhmm komi zasuyi da wannan tukeken cikin 🤔 dake gabanta_ )
Bayan sati d'aya da faruwar haka suna zaune yayin da
khadijah tayi pillow da cinyarshi shikuma yana shafa kanta, saidai kuma da
alamar damuwa a fuskarshi Wanda ko khadijah bata ankare ba saboda TV take kallo
Cikin muryar dake tabbatar da damuwarshi yace
"khadijah.. Juyowa tayi da sauri takalleshi saboda yadda sautin muryarshi
ya daki dodon kunnanta, sannan yaci gaba da cewa "naso ace kin yarda munje
anduba abin da zaki haifa dukda ina tunanin lokaci baiyi ba gashi yanzu zamuyi
babbar tafiya Wanda sai mun share 3 months bamu dawo...cikin murya mai kama da
ta kuka ta katseshi tana cewa
"Rabin raina kana nufin wani wuri kuma zaku?share mata
hawayen ya farayi don lokacin har sun fara zuba yace "pls khadijah nima
abin yana damuna saboda nasan baninan zaki haihu harji nake kamar na aje aiki
saboda ke saidai kuma me zan baki kici idan na'aje aikina?
Shiyasa nake son kiyi hak'uri ai matar soja itama soja ce
koh? Haka yak'arashe maganar cikin k'arfafa mata gwiwa
Da Haka dai ya samu ya lallasheta tare dayi mata alkwarin
zai kaita wajen Momy ta zauna sannan idan ya dawo za'a basu Hutu
sosai saboda aikin da zasuyi babba ne
Bayan kwana ukku da faruwar haka Jiddan da khadijah suka
rabu da juna, shi yatafi aikin da aka tura su itakuma ta koma gidansu Jiddan
Wanda lokacin da zai tafi suma ne kawai khadijah batayi ba,
kai kace idan ya tafi bazai dawo ba *_(nace wannan kuma Allah ne masani_*)
Sannu a hankali tunda Jiddan ya tafi saida suka kwashe wata
d'aya basuyi wayaba duk khadijah tabi ta damu, a b'angaren cikinta kuwa Momy na
kula da'ita yadda yadace inda ta cigaba
da zuwa awo, shima Abba yana bakin nashi
k'ok'arin ganin bata cikin damuwa
Kwance take tana kallon katon cikinta da yayi mata nauyi,
wani bangare na zuciyar ta na tunanin mijinta..
Kamar daga sama taji wayarta na ringing, dauka tayi tare da
zaro ido ganin Jiddan ne ke kiranta, ai kuwa da sauri ta dauka don taji muryar
habibin nata
"Yayana!.." Na,am khadijahtu ta ya kike? Lapiya
lau shine ka manta dani ko ka kirani"
"Haba princess ya za'ayi na manta dake damar wayarce
babu don inda muke ba service don baki San yadda nake kewarki ba keda baby
ta" Dan murmushi tayi Wanda sai da ya jiyo ta tace "muma muna kewar
ka sosai saboda Kaine ginshikin rayuwar mu" jindadin kalamata yasa ya
lumshe idanun shi kafin yace
"Allah khadijatu ina missing dinki sosai duk da allurar
da akayi mamu but kullum cikin sha'awarki nake don har na fara tunanin yadda
zan jure har 2 months nan gaba"
Saida tayi kamar zatayi kuka cikin shagwaba tace "nifa
cikina yayi kato dayawa.." Khadijah kada ki rikitani mana kina irin wannan
shagwabar kuma ai katon ciki bazai hana abani ba, ni ban San yadda zanyi ba ma
don lokacin da zan dawo nasan kin haihu ga....dariyar da take ne ya katse mashi
maganar dayake, da haka dai sukaci gaba da hirarsu ta ma,aurata cike da sha'awar juna
*After 2 months*
Zaune yake cikin mota Wanda kiris yarage su shiga Kaduna
saidai idanuwanshi a lumshe suke kamar maijin bacci Wanda fuskarshi kad'ai zaka
kalla kasan yana cikin farincikin dukda ramar da Yayi
Saboda damuwar dayake ciki narashin haihuwar khadijah gashi
harta wuce edd d'inta da kusan 3 weeks,
wannan shine abinda ya haddasa damuwar captain J wanda yasashi rama
Tun kafin ya shiga cikin gidan hancinshi ya fara jiyo mashi
k'amshin matarshi, lokacin da yayi arba da'ita kuwa ba'a magana saboda yadda
farin ciki da tausayi yakamashi don duk yadda yake tunanin girman cikin ya wuce
tunaninshi
Ko kunyar idonsu Momy baiji ba ya kama hannunta ya
rik'e yaki saki tunda ita ko tashi wuya
yake mata don ma Momy nasata tana Dan takawa kullum da safe tana zagaya harabar
gidan haka yak'arashi rashin ta ido yawuce d'aki domin yasakarma kanshi ruwa
Dare kuwa nayi ko kunya baiji ba yace ma Momy d'akinshi zata
kwana, ba yadda ta iya dashi dole ta kyaleshi tare dayi mashi gargadin kada ya
takurama
khadijar
K'iri-k'iri yau gashi ga khadijah kwance amma ya kasa biyan
bukatarshi saboda wani irin tausayinta da yakeji, a hankali ya matsa kusa
da'ita yashiga kissing d'inta duk Inda ya samu don wani irin kewarta yakeji,
itama bata hanashi ba don tasan yadda yake buk'atarta,haka ya cigaba da
wasanninshi da'ita har saida yaji yasamu natsuwa
A hankali takejin bayanta na ciwo har ya fara tsanani sai
lokacin Jiddan ya lura da yadda take ya mutsa fuska
K'ok'arin tadata yayi, sannan ya saka rigarshi yana tambayar
ta amma ta kasa bashi amsa, ganin ciwon nata kamar nakuda ce yasa ya kira Momy
suka wuce asibiti bayan Sun d'auki katin da take awo dasauran kayan data had'a
cikin wata k'aramar trolly na haihuwa
Bada b'ata lokaci ba aka wuce da'ita Labour room, bayan
kamar 2 hours khadijah ta d'auka bata haihu ba haka yasa Jiddan ya kasa daurewa
dole sai da aka barshi ya shiga Inda take kasancewar ita kad'ai ce cikin Labour
room, rik'e hannunta yayi yana karanto mata addu'oi saidai ita bata masan
yanayi ba don gaba d'aya tafita hayyacinta
Wani irin ciwo da azaba takeji nan take tafara nishi sai ga
ga jariri ya fad'o yana ta tsala kuka itakuwa bata ma San inda kanta yake ba
hakashima Jiddan baibi takan D'an ba gani khadijah na wani irin numfashi
Sai lokacin likitan
daya amshi haihuwar yagane yayan biyu ne ganin tana wata nakudar tadaban don
koda akayi mata scanning Allah yaboye baiwarshi d'aya kawai suka gani basu ga
d'ayanba
Da kyar ta bude bakinta tace "yayana ka yafe..Mani
..bazan iya ba I'm sorry..."plz khadijah kada kice haka zakiyi Mani
kidaure zaki iya..", wata dubarace tazo mashi sai ya saka mata yatsanshi
guda cikin bakinta
Jitayi an saka mata wani Abu abaki hakan yasa tayi wani irin
yunk'uri sai dai kuma kash jira take taga ta inda mala'ika zai bullo mata
Batayi aune taga wani irin duhu mai kama da inuwa yana
lullube d'akin iyayin da bakinta keson karanta Kalmar shahada saidai data kama
sai ta kasa idawa sakamako rashin sanin Inda kanta yake...
_*Mrs Abdul Sule*_
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_Ina matuk'ar ganin k'ok'arinki Zainab Yusif Kaita_ _(Zee kaita_)
_wurin ganin kin yad'a online Novel don haka wannan page d'in sadaukarwa
ne gareki kiyi yadda kikeso dashi halak
malak Mk ta mallaka makishi_
*page 205-210*
Koda Jiddan yasa mata hannu cikin baki sai yaga ta yunkura
kamar zatayi amai Wanda yayi sanadin fad'uwar d'ayan jaririn dama haka yake so
saidai kuma wani sabon tashin hankalin
daya shiga wanda bai wuce naganin khadijah bata numfashi ba, da sauri ya fara
jijigata yana kiran sunanta amma ina...
Kasancewar likitocin sun gane suma tayi yasa sukace ma
jiddan yafita, amma fir yak'i fita saima birkice masu da yak'arayi duk yabi ya
rud'asu don dole suka rabu dashi ganin in suka takura yafita kamar zai iya
shiga wata matsalar yasa suka hak'ura suka gyaleshi
Saida sukayi nasarar farfad'owar ta sannan suka dank'ara
mata allurar tsaida jini, shikuwa gogan naku sai lokacin ya samu natsuwa sannan
yabi takan yaran da aka gama gyarawa aka mik'a su wajen Momy da Abba
Kallon yaran yake cike da so da kauna duk da yaci burin
samun mace saboda har addu'a yake kan Allah yasa khadijah ta haifi mace amma
Allah bainufaba, amma dukda ba macen bace bai hanashi jin kaunar yaran ba cikin
zuciyarshi Wanda yakasa misalta son dayake masu da komi cikin zuciya da jinin
jikinshi
Ganin khadijah na bacci yasa Momy ta mik'o mashi dabino,
dama Wanda aka fara haihuwa ne hannunshi
tace "maza tauna kasa masu" ba musu ya amsa yasa musu tare dayin
addu'a
Haka suka kasance cikin farin ciki Jiddan kuwa kasa bacci
yayi daga ya lek'a yaran sai ya kalli khadijah sai ya koma yaci gaba da nafila
yana godema Allah da irin wannan ni'ima dayayi masu, kafin safiya kuwa kowa
yasan khadijah ta haihu sai farin ciki Ihsan keyi don tana mutuwar son yara
A hankali ta bud'e
idanuwanta bata sauke su kan kowa ba sai mijin nata da iyayen shi, bud'e baki
tayi da niyyar tayi magana saidai Jiddan ya Rigata yana tambayarta ya takejin
jikin, ita dai momyy tea ta shiga had'a ma khadijar, saida tasha tace ta koshi
sannan aka mik'a mata yaran Jiddan na rik'e da d'aya don wata irin yunwa sukeji
sai tsotsar hannu suke
Lokacin da ta rungume su ji tayi duk duniya ba abinda take
k'auna sama da abinda ta haifa koda kuwa kowa zai k'isu, ba musu ta shiga
shayar dasu dukda d'aurewa kawai take saboda akwai zafi idan suna tsotsa duk
Jiddan na lura da'ita
Gaba d'aya khadijah d'akin Momy ta tare tana jego shikuwa
jiddan kin komawa Abujah yayi tunda sun samu hutu gashi Momy ta kasa ta tsare
kullum Sai dare yayi yake samun ganin matar tashi da babys gashi kullum idan ya
tambayi khadijah koda sunan da takeso asa Sai tace duk Wanda yasa yayi dama tun
tana da ciki yake tambayarta
Haka akaci gaba da zaman barka ranar suna na zagayowa yara
sukaci sunan sulaiman da Jamilu Wanda hakan yayi mukar faranta ran khadijah
kuma ba k'aramin mamaki tayi ba dama abinda yahanta fada don kada jiddan yaji
kishi Sai gashi yasa da kanshi
Kwanan khadijah 27 da haihuwa jininta ya d'auke Wanda Juddan
ya lura da haka don ya shigo nemanta ya ganta tana sallah lokacin cwt S ke kuka
dayake haka suke kiransu cwt S da cwt J
Kamar kullum yau ma da dare ya shigo d'akin da take tare da
kwantar da cwt J da yayi bacci sannan ya koma kusa da khadijah ya zauna tare da
rik'e hanunta kafin yace
"Andeejana
yaushe zamu koma gida? D'ago manyan idanunta tayi ta zuba mashi su na D'an wani
lokaci tana karantarshi, shima ita yake kallo kafin tace "amma kasan sai
nayi arba'in koh?.."toh ai naga kina sallah yaufa"..."duk da
haka kasan Momy
bazata bari ba
D/an yamutsa fuska yayi alamar ana ta kura mashi kafin yace
"toh naji amma don Allah yau..sai kuma yayi shiru, kallonshi take alamar
tanajinshi
Tashi yayi tsaye tare da janyo hannunta itama ta mik'e
tsaye, k'ok'arin janta yake taja ta tsaya hakan yasashi juyawa yana kallonta,
Dan dakewa tayi tace "ina zamuje ne? Don ita ta harbo jirginshi tun
lokacin daya shigo tanazarceshi
K'ara had'e rai yayi yace "toh kina tunanin zan saida
ki ne? Daga haka ya kara Jan hannunta sai takara turjewa tana turo baki
Juyowa yayi a D'an fusace sai kuma ya kwantar da murya cikin
lallashi yace " Haba khadijah d'akina fa zamu kisan me nakeso
Haba.."toh ba Kaine kemin fad'a ba"
"Toh shikenan na daina yi hak'uri kizo muje kinji"
zare hannunta tayi daga nashi ta fara cewa "gaskiya yayana Kayi hak'uri
kofa arba'in banyi ba sannan idan Momy tagani fad'a zatayi taga kamar nice na
biye ma... Cikin fad'a ya katseta don wannan karon khadijah takaishi k'arshe
bayajin zai iya danne fushin shi
"toh shikenan khadijah kada ki biye Mani Nida nake
mijinki kinsan dai yadda laluri na yake yau kusan 4 months rabona dake amma ke
baki damuba baki tausayina kamar yadda nake maki baki son abinda nakeso kamar
yadda nake son naki koda kuwa zan cutu amma bari kiji in gaya maki baki isa
kisani aikata zina ba idan hakuri na ya k'are zan karo aure don biyan buk'ata
ta"
Daga haka ya fice daga d'akin cikin tsananin bakin ciki da
abunda tayi mashi don bata San yadda yake bacci ba kullum shiyasa tayi mashi
haka
Tsaye tayi inda ya barta tana kuka babban tashin hakalinta
bai wuce yada yayi fushi da'ita ba don bai taba yi mata haka ba har yana
ikirarin k'ara aure Wanda bata jin zata iya sharing d'inshi da wata don haka da
sauri tabi bayansa
Yana zuwa d'akinshi yayi ma k'ofar key sannan ya duke
yanajin dacin yadda khadijah tasa yayi mata fad'a yau dole ya nemi mafi...
Tunaninshi ne ya katse jin tana buga k'ofar tana kuka tare da kiran sunanshi,
tabbas bai iya yi mata dogon fushi da jure jin kukanta don yasan bata saba ba
shiyasa take kuka sosai
Bud'e mata k'ofar yayi bata jira komai ba ta rungumeshi tana
kuka duk sai yaji ya daina jin haushinta tausayinta ya kamashi itakuwa bottoms
d'in rigar shi ta shiga cirewa tana shafa mashi lallausan gashi dake kwance
saman kirjinshi har a lokacin bata daina kukan datake ba, d'aukarta kawai yayi
ya D'ora saman gado yana cewa "pls daina kuka banso kinji" shiru tayi
tare da had'e bakinsu tana kissing d'inshi tuni jiddan ya manta inda yake, nan
take ta fara aika mashi da abubuwan da tasan yafiso daga gareta, shikuwa har
wasu hawaye yake fiddawa yana mata surutai itama tana biye mashi, daga haka Na
jawo masu k'ofar Na tafi gudun kar inzama mai ganin kwammm
Bayan kamar 30 minutes jiddan ya D'an samu natsuwa sai kallonta
kawai yake, a hankali tace "yayana yaranmu fa su kad'ai ne Kayi hak'uri da
wannan kaji Na koma wajensu", d'aga mata kai yayi cike da gamsuwa yace
"ba komai tashi kije amma pls
kullum ki dinga bani 30 minutes kinji d'aga mashi kai tayi alamar ta yarda
sannan ta kama hanya
Hartaje bakin k'ofa sai kuma tajoyo tare da cewa "da
gaske aure zaka k'ara? Tasowa yayi ya rugumeta don har kwalla ta cika mata ido
yace" sorry fushi ne kawai kinsan ke kad'ai zan aura DA'IMAN don haka kada
ki damu daga haka yasamu tayi shiru sannan ta koma wajen yaran
Hamdala tayi ganin Momy har lokacin tana wajen Abba, toilet
ta shiga tayi wanka saida ta fito sannan Momy ta shigo don tayi mata saida safe
sannan ta jaddada mata ta daina tafiya toilet tana barinsu su kadai a d'aki ta
dunga kiran Afrah ta zauna da su
Tunda ga ranar kullum khadijah sai taba mijinta 30 minutes
Wanda har yanzu Momy bata Sani ba gashi tana faman gyara ta amma Jiddan na
mirjewa kullum ba Wanda yasani
Saida ana saura 3 days su koma sannan Momy ta lura da hakan
shiyasa tasa Jiddan ya tattara ya koma Abuja acewar ta yaje yasa a gyara gidan
kafin zuwan khadijah shikuwa ganin ta gane gashi saura 3 days yasa ya tafi don
kada ya bata mata rai
Haka khadijah tasha gyara har ta gaji bayan 3 days ta koma
tare da wata dattijuwa da zata tayata raino mausuna baba Ayyo
Bayan komawar khadijah rayuwa ta kasance mai dad'i da
farinciki a garesu Wanda suka shiga nuna ma juna sabuwar soyayyah kamar basu
taba shiga wani tashin hankali ba _rayuwa kenan_
*AFTER 5 YEARS*
🍊🍊🍊
Abubuwa da yawa sun faru acikin wannan lokacin ciki kuwa
harda K'arin auran Usman mijin Ashanty Wanda iyayenshi ne suka bashi wata yar
uwarshi mai suna Nafisa tunda ita Ashanty bata haihuwa sanadiyar magungunan
hana d'aukar haihuwa da tasha a baya, Alhamdulillah suna zaman lafiya don
nafisar ta haihu kuma suna zaman lafiya dukda tasan baxata tab'a kama k'afar
Ashanty ba a zuciyar Usman
A b'angaren Seema ta haihu har sau biyu Rayyan sai Ridwan,
Samra twince ta haifa itama Dinah da Daleelah, Islam d'anta d'aya tahir
Al amarin Ihsan da Rafeeq kuwa har yanzu Allah bai basu ba
dukda suje Asibiti an tabbatar da lafiyar su kuma ko yaushe zasu iya samun
haihuwa sai dai hakan bai daina sa Ihsan damuwa ba don ma Rafeeq bai barinta
don shi mutum ne mai raha bakoda yashe ake ganin damuwarshi ba
*_Mrs Abdul
Sule_*
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA'DATU ALIYU KABUGA
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
*page 210-215*
Bazata wuce shekaru 33 ba amma kai kace yar 25-26 ce, zaune
take tana shayar da wani yaro da bazai wuce shekara 1 ba aduniya
Jitayi an rugumo ta ta baya hakan yasa ta juya tana
kallonshi, shima ita yake kallo da murmushi saman fuskarshi, d'an zumbura baki
tayi tace "kai yayana cwt J fa na kallon mu" d'aga kanshi yayi ya
kalli yaron da gaba d'aya hankalinshi ba Kansu yake ba saboda cartoon d'in da
yake kallo
Sakinta yayi yakoma gefanta ya zauna tare da amsar zaid da
ke hannunta Wanda tuni yayi bacci sannan yace "wai bazaku tashi Ku shirya
ba lokaci na tafiya fa..." Nifa nan yayana shirye nake shi waccan da kake
gani tun d'azu nasa mashi kaya amma yaki sa takalmin shi ko irin murnar yawon
da yara keyi baiyi wani irin murdadden haline da shi
Dariya jiddan yayi da har sai da zaid ya motsa sannan yace
"gaskiya ki daina yi ma takwarana
haka da cwt S ne baki cewa komai don yanzu ma nasan shi kike jira
amma,...jiyayi an rufe mashi ido daga baya hakan yasashi yin shiru yana
murmushi don yasan kowaye kafin yace "lalle my boy ya tashi lafiya
tunda..sakin idon nashi yayi yace " daddy, Momy good morning"
murmushi khadijah tayi tace gud morning my son ya naga baka shirya ba ina Aunty
taka?...uhm mun shirya fa nine kwai bansa kaya ba shine tace nazo naga kayan da
J zaisa asamani irinsu "wanan karon jiddan ne yayi magana yace
"Toh ka gansu koh toh je kasanya kace mata kuyi Sauri
Ku muke jira kaji my son d'aga kanshi yayi alamar toh sannan ya kama hanya, har
ya isa bakin k'ofa kuma sai ya juyo ya kalli D'an uwanshi yace " J ko
magana bakayi Mani ba fa" ko kallon inda cwtS yake baiyi ba kamar badashi
ake magana ba sanin halinshi ne yasa S tafiya batare da ya k'ara cewa komai ba
Tashi khadijah tayi cikin fushi taje ta kashe TV d'in sannan
tace "kanajin D'an uwanka na maka magana amma koh tanka shi bakayi ba toh
tashi ka wuce kasa takalmin ka mu tafi, zuburo baki yayi tayi saurin cewa Allah
zan mangareka in baka tashi ba hakan yasa cwt J tashi ya nufi d'akinsu shikuwa
jiddan kallonta kawai yake yadda ta dage tana masifa kafin yace
"Allah khadijah ki daina yi ma yaron nan masifa yanzu
da D'an uwan nashi na nan da sun had'e maki kai" batace komai ba sai tab'e
baki da tayi ta nufi hanyar d'akinta don ta ida shiryawa don tasan halin ya'yan
nata ga kama da suke sosai sai dai shi S hakuri gareshi shiyasa Ihsan ke sonshi
gabad'aya ma gidanta yake kwana
Akasin cwt J da sai yaga dama zai maka magana haka idan bai
sanka ba toh ko zaka mutu bazai maka magana ba
Zaune take a d'akin cwt
S tunda ya tafi take nan wurin gabad'aya ta lula duniyar tunani
Rungume hannuwanshi suke a kirji yana kallonta don bata san
dawanzuwarshi a wurin ba yana kallonta, a hankali ya taka har zuwa inda take
bai jira komai ba ya rungume ta hakan yasa ta dawo cikin hakalinta
Ajiyar zuciya ta sauke yace "haba pretty meyasa haka ni
nagama kwanan kinyi kiba kodai nayi ajiya anan ne?tare da shafo cikinta, ita
kuwa murmushi tayi don tasan tsokanar ta yake don bata wuce 3 days da gama
al'adarta ba
Maganar shice ta katse mata tunani yace "yadai ko babyn
ne? D'an yamutsa fuska tayi tace "uhm my Rafeeq zuciyana ke tashi apple
nake son ci" ai da sauri ya tashi yana cewa bari na kawo maki kinji karki
wahala, ita kuwa dariya ta hauyi don haka sukeyi pretending kamar tana da ciki
shi kuma yayi ta lallaba ta kamar da gaske
Tana nan sai ga cwt S ya dawo b'ata lokaci suka shirya sai
Kaduna domin gudanar da shagalin bikin Aslam da za'a fara gobe
*****
Zaune take ayayin da kwallah suka cika idonta babu Wanda
take tunawa sai Laila, jitayi an dafata suna had'a ido ta fashe da kuka yace
"don Allah Aisha ki daina kuka ko wani abun akayi maki? Girgiza kanta tayi
tace a'a yace "toh ya akayi?.."kada kayi tunanin ina kukane saboda
rashin haihuwa hasalima godiya nake ma Allah da ya mallaka Mani miji irinka
saidai duk sadda zan tuna rayuwa ta ta baya dole nayi kuka musanman Laila da
shekararta 5 cikin kasa jiddan d'in da ta mutu kanshi yananan ya zama wani Abu
yak'ara samun girma da kud'i da Y'aya ba
kamar yadda ta Sani ba"
"Addua ya kamata ki dinga yi mata kinji? Don ba,a fidda
ran rahama ga musulmi" daga kanta tayi sannan suka ci gaba da hirar su ta
masoya
Kwanaki 3 suka share a kd ana shagalin biki sannan suka dawo
gida Wanda duk wannan hidimar da ake Ihsan bata lafiya saboda malaria da ta
kamata saidai tanajin sauki saboda magani da take sha
Bayan dawowarsu ne Rafeeq ya matsa mata dole suje sukaje asibiti ganin zazzab'in
da yatafi sai yadawo don shi bai yadda ba ace mutum baya lafiya amma kullum sai
k'ara hawa take kamar ansama pulawa yis
don har wani Dan tumbi ta aje
Zaune suke a gaban likitan suna jiran jin abinda zaice,
batare da wani shakku ba ya d'ago yana kallon Rafeeq kafin yace "ya akai
kasan tanada ciki ka bari ciwo ya kamata kuma bakuzo asibiti da wuri ba"
Da mamaki Rafeeq da Ihsan suke kallonshi,
"Ciki kuma! Shine abinda Rafeeq ya maimaita kafin
likitan ya tabbatar mashi da ciki kuwa har na 4 months, shidai Rafeeq bai daina
mamaki ba kafin yace "but doctor duka batafi 1 week da gama mesturation
d'inta ba and than babu wata alama ko laulayi daya nuna mana hakan
Murmushi likitan yayi sannan ya d'ora da cewa "tabbas
akwai mata irin wadanan saidai basu da yawa wata kila idan cikin yakai wata
shidda ta bari sannan ya kalli Ihsan yace madam ina fata baki matse cikin dai
ko?
D'aga mashi kai kawai ta iya don tanajin abin kamar a
mafarki, da haka likitan ya sallamesu
tare da rubuta masu magani sannan ya shawarce su da su rink'a zuwa asibiti akai
akai
Haka suka koma gida cikin farinciki da godiya ga Allah
sannan suka hau sheda ma mutane Wanda kowa saida yayi mamaki
Haka ihsan taci gaba da rainon cikinta har ya kai wata Tara
lokacin nan cwt S sai murna yake Auntyn shi zata Haifa mashi baby mai kyau don
har zama yake ya danna mata kafarta idan tayi kumburi, haka zalika ko laulayi
batayi sadai kumburin kafa shima sai da cikin ya tsufa
Tsaye take a kicin tana motsa girki Rafeeq na gefanta yana
mata magiyar ta tafi ta zauna shiyayi don bai son abinda zai wahalar da'ita,
haka itama ta dage akan exercise ne takeyi
Ji tayi wani irin fitsari ya matseta hakan yasa ta sakar
mashi girkin sannan ta nufi toilet
Saidai tana tsugunawa taga tayi jage jage ga kan jariri har
ya leko
Ihu ta saka saboda tsabar firgita da tayi ai da sauri Rafeeq
ya shigo toilet d'in bayan yakashe gas d'in
Ganin yanayin da take ciki yasa ya d'auketa sai asibiti tare
da cwt S da sai kuka yake ganin Auntyn shi za'a kai bata lafiya
Suna isa aka karb'eta don har kan da yafito sai lokacin
Rafeeq ya kira jiddan ya sanar dasu sannan yace suje d'akin Ihsan su taho da
kayan haihuwa
Haka kuwa akayi ko 10 minutes basu k'ara ba suka iso Wanda
yayi dai-dai da haihuwar Ihsan Wanda saida aka fara mik'o masu jaririyar sannan
suka shiga ganin Ihsan d'in
Shidai jiddan kallon jaririyar yake kawai ga wani irin kyau
tun kafin kammaninta su fito baka iya tantance dawa take kama amma masu karatu
kuyi imagining kyan d'iyar Rafeeq da Ihsan don gaba d'aya baka iya gane daga
wane b'angare tafi kama balarabiya ko bafullatana
Ihsan bata sha wuya
wajen haihuwa ba haka kuma bata koma gida wanka ba har ranar suna tazo d'iya
taci sunan...
*_Mrs Abdul
Sule_*
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI DA'IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA'DATU ALIYU KABUGA
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
🔚 🔚 🔚 🔚 🔚 🔚 🔚
Ba k'aramar bajinta da kuma surprise d'in jiddan Rafeeq yayi
ba domin kuwa d'iya taci sunan khadijah za'a dunga kiranta da kadra
Ba k'aramin farinciki sukayi ba mussaman jiddan shidai yana
so ace cikin yayansu ansamu khadijah shikuwa cwt S har rigima yake sai an Goya
mashi ita banda uban tafiyar da baya shiga harkar kowa kamar ba yaro ba don
idan cwt J nayin wani abun har tsoro yake ba khadijah gashi da k'ok'ari a
makaranta don har yafi S
****
Bayan shekara ukku da faruwar haka Ihsan bata k'ara haihuwa
ba khadijah kuwa ta haifi Khalid Wanda take goyo yanzu
Rayuwa ta zama mai sauk'i a garesu don kuwa yanzu ba yan
kananan kud'i su jiddan keda suba
shiyasa suke jin dad'insu
Sulaiman ne yayi sallama hannunshi rik'e dana kadra an sanya
mata kaya pink sai wata white d'in Teddy da ke hannunta da ta cire hular kanta
tasa ma Teddy d'in ita kuma tabar gashin sai rito yake tsakiyar bayanta
Tana shiga ta haye saman cinyar jiddan tana dariya yace
"ah babyn daddy ya akayi ne? Cikin maganar ta da bata kware ba tace"
Mami ce chace mujo muyi waca da chiwit ce jatayi bacci" dariya jiddan yayi
kafin yayi magana yaji cwt J yace "Allah daddy yarinyar nan na b'ata Mani
rai tayi ta bata Mani suna" daga haka ya wuce d'akinsu shi har yayi
#zuciya, ita kuwa sakin baki khadijah tayi ta bishi da kallo aranta tana cewa
wannan wane irin yarone ni dije
Tunaninta ne ya katse jin cwt S na cewa "my kadra kinga
ran J ya baci zo muje ki bashi hak'uri kinji" harararshi khadijah tayi
tace "toh bata zuwa ai banga abinda akayi mashi ba"
Diddira k'afa yafarayi yana cewa "pls Momy ki bari mana
kinga yanzu yana iya kuka fa...bud'a baki tayi daniyar yin magana jiddan yai
saurin cewa toh kutafi Allah yayi maku Albarka
Jan hannun kadra sulaiman yayi suka nufi wurin J, aikuwa
suna zuwa suka tarar da shi sai fushi yake shi kadai
Dafashi S yayi yace "haba bro kayi hakuri meye nafushi
bayan kasan ba laifinta bane bata iya fad'i bane ba", koda kadra taga haka
itama sai ta dafashi tace" blo kayi hakuli kaji" abinma dariya yaso
yaba cwt J hakan yasa ya saki ranshi yana dariya yana cewa "wai ita
yarinyar nan duk abinda taga kayi shi take kwakwayo fa" daga haka yabar
fushi kafin su jawo game d'insu su fara bugawa
Bayan shigewar su S d'aki Jiddan ya jawota a jikinshi yana
cewa "habibty ki daina damuwa da halin yaran can haka Allah ya halicce su
idan kika tukura masu kina iya ganin su samu wata matsala baki ganin ko ciwo
d'aya yayi sai guda yayi haka kuma basu San bacin ran junansu"
D'aga kanta tayi alamar ta gamsu kafin ya manna mata kiss a
wuya yana cewa "khadijah bazan daina gaya maki ina sonki ba kin isheni
rayuwa, ni don Allah nake sonki inso mu kasance tare har abadan"..
"Nima HABIBI... Huhhh DA'IMAN ina sonka ina tare da kai
bazan... Game bakinsu da jiddan yayi shiya hanata idawa itama sai ta shiga yi
mashi martani
Saida suka gaji don Kansu sannan suka bari saidai basu daina
kallon juna ba Wanda hakan yazama sabo a garesu domin aikawa junan su sak'onin
da kalaman bakinsu suka kasa furtawa
Kukan da Khalid ya farayi ne Wanda har yake neman tashin
zaid dake bacci shine yasa suka dawo daga duniyar da suka tafi
Tashi jiddan yayi ya d'aukoshi suka shiga yi mashi wasa tare
yana dariya...............
Alhamdulillah anan na kawo karshen wanan litafin nawa mai
suna HABIBI DA'IMAN inda nayi kuskure Allah ya gafarta Mani yasa mu karu da
abin dake ciki
****************
*_Mu kasance masu yarda da kaddara a duk lokacin da tazo
mana, basai kayi ma Allah laifi ba zai jarabe kaba don ya gwada imaninka sai
yayi ta kaddaro maka abubuwa cikin rayuwarka
kuma ba don baya sonka ba yayi hakan ba_*
*_hak'uri a duk halin da ka tsinci kanka yana kaika ga
babban rabo, don haka ka godema Allah a duk halin da kake ciki domin kafi wani,
wani kuma yafika_*
*_d'aukar mummunar dabi'a akan rashin hak'uri cikin halin da
ka tsinci kanka na jawo maka masifa a cikin rayuwa kamar yadda Jiddan ya d'auki
d'abi'ar shan giya amma sai laila ta hanashi zaman lafiya_*
*_Duk girman laifinka idan ka tuba Allah na yafe maka sannan
ya baka abinda bakayi tunanin samunshi ba idan yaso kuma ya jarebeka_*
*(Ashanty*)
*_Ko kun San soyayyar gaskiya bata tsufa kamar yadda mutane
ke ganin a kwai lokacin da soyyayya ke k'arewa, masoyin gaskiya yana sonka a
duk yadda kake ba kuma zai taba gudunka ba saboda tausayi shine ginshin
alakarku_*
*_Madallah da iyayen da basu sa ma rayuwar gidan auran yayan
su ido, suna d'aukar kaddara a duk yadda tazo masu_*
*_D'a namiji baya kad'an musamman idan ya nuna yanason auren
saboda rashin yin hakan na iya jawo b'anna da dama kamar haka:- rashin natsuwar
matashi a koda yaushe don haka bazai maida hankali akan harkokinsa ba,
shaye-shaye, zina da dangoginta, d'aukar munanar dabi'a saboda yana ganin an
tauyeshi da sauransu_*
*_Wata soyayyar idan ka rabata bakasan mazai faru ba gara a
dunga sanin abinda ya dace ayi_*
*_Babban kuskurene kice zaki bar gidan iyayenki saboda auren
dole, haka kuma yana da had'ari, ka uzura ma d'anka sai ya auri Wanda baiso
hakan na iya jawo matsaloli da Dama, wata rana zaka ciza lebe tabbas idan ka kori yarka daga gida
saboda tayi maka wani laifi_*
*_Mu kula, mu lura, mu gane rayuwar yar kad'ance idan kayi
hak'uri wata rana sai labari babu abinda yafi dad'i ga 'ya mace in banda ta
samu miji na gari_*
_It's lucky to
marry ur first love_
*_Bazan mance namijin k'ok'arinku gareni ba_*
*Halimatu Kangiwa (Aunty haliloss)*
*Aisha Ali Garkuwa*
*_Mrs Abdul Sule_*