HABIBI DA'IMAN 41-60
Page 41~45
(abinda wasu iyayen basu sani ba Namiji baya kad'an Na Aisha
Ali Garkuwa)
Ita kuwa khadijah tana ba samari dama saidai duk wanda yazo
bada niyyar aure yake zuwa ba
Duk wannan hali da suka shiga ba abinda ya ragu daga soyayyar Jiddan da khadijatu don koda
yaushe suna mak'ale a waya tare da ba junan su kulawa da manta damuwar su
🌷🌷🌷🌷
Ummi ce zaune tare da ss tana mashi nasiha tace
"kaga yanzu kagama ginin gidanka don haka wannan ce
magana ta tak'arshe da zan maka akan aure
Kallonta yayi cikin girma mawa yace
"Ummi na baki zab'i ki nemo mani Matar da kikaga tadace
dani"
Murmushi tayi tace "ko kaifa suleman kuma insha Allahu
zakaji dad'in zab'in da zan maka"
Bai k'ara cewa komai ba yatashi ya nufi part d'in shi yayi
wanka ya fita zuwa majalisarsu duk da ba fira yake ba yana zuwa su gaisa sannan
ya shiga gidan su khadijah
Ita kuwa Ummi harta kira Mama a waya ta shaida mata yadda
sukayi da d'an nata da ganin dacewar a had'asu da khadijah
Mama tace zata tambayi khadijah taji ko akwai wanda take so
idan babu? sai in fad'a mata yadda mu tsara dake"
Ummi tace bada muwa ko mai ake ciki kingaya mani"
Tare da hanging up d'in call d'in
Bayan fitar ss majalisarsu ya zaune yake jin gulmar dasu
Nazeer keyi akan khadijah na cewa
Yarinyar gidan su safwan d'incan tacika wulak'anci, wani daga
cikin su yace "ai wani d'an iskan saurayi ta lik'emawa ya hanata aure
Allah kad'ai yasan abinda suke aikatawa"
Ss jiyayi zuciyarsa na tafasa, yasa yatashi Batare da yaji
k'areshen zancen ba ya shiga gidan su khadijah
A dai_dai lokacin da Mama kema khadijah maganar in akwai
wanda ta tsayar toh ta fad'i, dai-dai lokacin ss yayi sallama ya shigo hakan ne
ya haddasa ma Mama yin shuru tare da amsa sallamarshi
Bayan sun gaisa, Mama ta tashi da niyyar shiga toilet
tabarsu su biyu
Kallonta yayi yace "ke baki iya gaisuwa ba"
"Ina yini"
"lafiya, dama inason inyi magana dake ne"
Kallonshi tayi da kyau don har yanzu tana jin haushin korar
ta da yayi a motarshi
Shikuwa bai kulataba ya cigaba da cewa
"dan Allah idan Jiddan sonki yake yakamata ya fito ya aureki
kinga mutane sun samaki ido"
Idon tane ya ciko da kwalla tad'ago cikin takaici da jin
haushin maganar shi tace
"to yaya ya akeson nayi, duk wanda yazo ina kulashi
amma bada niyyar auren suke zuwa ba!
Toh koni zance azo a aure ni, ko kuwa kai zaka aure
ni?"
Duk wannan maganar tana yinta cikin kuka da tsantsar b'acin
rai!!!!
Batare da tsoron komai ba yakalleta cikin ido yace
"yes I will marry you and i promise to love you, take
care of you till the end of my life"
Cikin firgici da kalamanshi khadijah ke Kallonshi tana
girgiza kai
Duk abinda ss yace a kunnen Mama saboda ta dad'e tsaye
batare da sunsani ba
Al'amarin da yasa Mama cikin farin ciki marar misaltuwa
Khadijah kuwa tashi tayi ta ruga d'aki tana wani irin kuka
wanda nakasa gane ko na minene shi?
Ss jiyayi kamar yabita ya lallasheta amma kunyar idon Mama
bazaisa yayi hakan ba
Mama zama tayi tace "dama suleman kanason khadijah shine baka fad'aba kayi
shuru"
Mama don naga tana da wanda take so shine yasa banyi maganar
ba, kuma ko yanzu bana son kurabata dashi,
Shiyasa nace ma ummi tazab'a mani mata"
Murmushi Mama tayi tace banda abinka aishi wanda takeson
iyayen shi sunce bazasu yi mashi aure yanzu ba
Kuma dama Ummi tayi mani maganar, har mun yanke shawarar
had'aka da khadijah
Toh sai gashi fad'uwa tazo dai-dai da zama kaima kana
sonta"
Ss yace "But Mama she can wait for him tunda naga she
is 20 years"
Ajiyar zuciya Mama tayi tace
"suleman baka ganin bakin mutane, saudat na gidan mijin ta ai itama yakamata
tayi auren"
Kiran sallar magrib ne yasa ss yayi mata sallama ya wuce
masallaci
Ko ss zai Auri
khadijah 🤔?
Ina Jiddan? Wane hali yake ciki?
Mrs Abdul
Sule
[1/17, 10:47 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI* *DA'IMAN*
*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*
*DEDICATED* *SA'ADATU* *ALIYU* *KABUGA*
DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION
Page 46~50
Bayan kwana biyu da yin haka
Mama takalli khadijah
dake yankan a kaifa tace"yakamata kije gidan saudat kinga tun d'azu tayo
waya bata jindad'i"
Hakan yasa tayi saurin gamawa tare da shiryawa cikin wata
yellow d'in gown sai kwalar wuyan rigar ne bak'i don haka tayafa black d'in
veil sai takalmi hills suma black sai wata k'aramar pose yellow
Tayi kyau sosai saidai wata rama da tayi
Har tafito zata tafi Mama tace ta shiga ta gaida ummi sannan
ta wuce
Tana shiga gidan ummi dayake gidan babba ne saika wuce
parking space sannan kashiga main palour gidan
Tana shiga taga ss zai shiga motarsa da alama fita zaiyi
D'auke kai tayi tamkar bata ganshi ba tare da sauri ta shige
palour
Shiko ganin hakan yasa yafasa tafiya tare da zama cikin
motar batare da yatafi ba
Tana shiga taga ummi cikin palour, sallama tayi sannan ta
gaisheta
Bata wani jima da shiga ba tayi mata sallama zata tafi
Ummi tace "tun yanzu zaki tafi bazaki bari sai zuwa
yamma kitafi ba"
Ummi gidan saudat zan wuce dayake batajin dad'i shine Mama
tace inje na dubata da jiki"
Assha kice ina gaisheta da jiki Allah yabata lfy"
Ameen ummi zangaya mata
Rakota tayi har
harabar gidan, hango suleman tayi tace
"ashe kai baka tafiba mekake jira"
Shuru yayi dan baisan mezai ce mata ba
Ummi taci gaba da cewa "toh aishikenan saika aje
k'anwarka gidan saudat"
Dama haka yakeso cikin ranshi batare da b'ata lokaci ba
yayima motar key, ita kuwa khadijah bata iya yima ummi musu hakan yasa ta shiga
Bayan ta shiga ne yakalleta yace "fauziyya estate ko?
Tace "eh"
Hakan yasa yafara driving batare da kowa yai magana ba har
suka isa gidan
Kama murfin k'ofar motar tayi ta bud'e da niyyar fita sai
taji ta a lock hakan yasa tayi saurin kallon shi
Murmushi yasakar mata sannan yace "khadijah meyasa kike
gudu nah"
Kallon banza tamashi "meyasa zaka auri ne,? Kodan ka
cutar danine, wanda bansa darajar mace ba shine za'ace mijina, don haka ina mai
shawar tarka tun wuri kaje kace masu baka son wannan auren don ba zaman lafiya
zamuyi ba"
"Ni bazance bansan abinda iyayena keso ba saidai ke ki
fad'a masu bakya son zab'insu,
Kuma da kike cewa bansan darajar mace, ni kuwa nasan darajar
mace don bantab'a wukanta wata 'yan mace a rayuwa tah ba"
Murmushin takaici tayi tace
"shiyasa ranan nan da kad'au koni ka ajeni ahanya
lokacin kuma gashi dare yayi"
Jiyayi gaba d'aya baida amsar da zai bata yasa yayi unlock
d'in k'ofar
Ita kuwa ganin hakan yasa ta fita batare da tak'ara cewa
komai
Saida yad'auki kusan 15 minute baitafi ba yana tunanin ita
batason kishi ne yasa yayi mata hakan ba
Kuma batason yana maturk'ar sonta ba har take tunanin
yajanye don shi yana ganin kamar Allah yahanata auren Jiddan ne don shi ya aure
ta, saboda shi kad'ai yasan lokacin da yafara sonta
Amma yayima kanshi alk'awarin zai koya mata yadda zata soshi
Tana shiga gidan saudat taganta kwance akan kujera bayan
tayi mata ya jiki ta tashi ta gyara mata gidanta tsab ta kunna mata turaren
wuta har tad'auko roomfreshner zata saka, saudat tayi saurin hanata tace
"kada kisaka amai yake sani"
Murmushi khadijah tayi tace "kufa masu ciki tsiyar ku
kenan"
Saudat tace "kema kin kusa zuwa lokacin"
"Dama nasan haka zaki fad'a, baki kojin haushin yadda
aka rabani da Jiddan"
"ba haka bane kuma Jiddan iyayen shine keda matsala,
ina mai tabbatar maki da nafi kowa jin zafin hakan"
Nan take kwalla ya cika idon khadijah, saudat na lallashinta
suna cikin haka ne
Wayar khadijah ta fara ringing ganin Jiddan ne yasa ta
dai-dai ta natsuwarta tare da pickin call d'in
"hello" Jiddan yace "khadijah meke faruwa
naji muryarki kamar kinyi kuka"
Tace "bakomai"
"pls don Allah meyafaru" tace wallahi ba abinda
ya...........................
Tarinda da yafara ne yasa bata idaba ta tsaya tana mashi
sannu, sai kuma taji shuru nan take ta fara cewa
"yayana! yayana!! yayana!!! gashi kuma baiyi hanging up
ba sai ta fara kuka"
Ita kuwa saudat sauri karbar wayar tayi takashe da niyyar ta
k'ara kira.
Ko miyasami Jiddan?
Mrs Abdul Sule
[1/17, 10:47 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI* *DA'IMAN*
*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*
*DEDICATED* *TO* *SA'ADATU* *ALIYU* *KABUGA*
*IQRA* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
page
51~55
Wannan shafin na kune masoyan *habibi* *da'ima* ina
jindad'in comment d'inku domin shike k'arfafa mani k'warin yin rubutuna #Ana
tare#
Tana fara ringing aka d'aga sai naga tayi Murmushi sannan
tamik'ama khadijah, ita kuwa har kyarma take don takarb'a tana sawa akunne taji
Jiddan nacewa "lafiya" Ajiyar zuciya tasauke tace "yayana
meyafaru naji muna waya kayi shuru? "Network ne saboda ni inajinki"
Murmushi tayi tace "ilove you" yace "llove you too, ki kwantar
da hankalinki babu abinda zai sameni don nasha gaya maki insha Allah atare zamu
mutu koda kuwa bama tare" "toh yayana Allah ya yarda, amma fa wannan
tarin naka yakamata kafara sha masa magani " " insha Allah"
cikin ranshi kuwa yana cewa don baki san yadda nake jin tarin nan ba.
Bayan two weeks da faruwan haka akasa bikin khadijah da S.S
abinka da masu hannu da shuni two month kawai akasa bikin
Tunda akasa ranan bikin khadijah tafara ciwo domin jin abin
take kamar a mafarki, a b'agaren Jiddan kuwa saidai muce Allah yasawak'e don
kullum cikin lissafin kwanakin yake iyayen shi kuwa basu da masaniyar abinda ke
damunshi ba alhalin ciwo na nan nacinshi cikin rai
Sannu - sannu lokaci na k'ara tafiya kwanaki suna raguwa
inda bikin ke k'ara kusantowa a yayinda zuciyar masoyan guda biyu sukejin kamar
mutuwarsu ke tahowa, shikuwa ss har yana tunanin kamar baiyima masoyan adalchi
ba musamman yadda yaga khadijah tarame ko kallonshi bata sonyi ga rashin had'in
kan da bata bashi saidai dasu Iman suke ta shirye-shiryen su.
Su miemee ne sukayi sallama suka shigo tare da ankonsu da
suka amso wurin d'inki da sauran kayan khadijah, zama sukayi miemee tace
"amarya ga kayanki" shuru tayi
bata ko kalletaba sai Rabi'atu ta amsa tasamata cikin wardrop sannan tace
"Ni ina mamakin khadijah ace nice na samu handsome guy kamar ss ga kud'i
ai wallahi sai kunga k'arya" mimie
tace "ai ita kinsan bata wayeba shiyasa kikaga tana haka" Ita dai khadijah har suka k'araci surutunsu
suka tafiya batace masu komai ba don ita abinda ke damunta ya isheta, ihsan ce
ta shigo tana cema khadijah "yaya khadijah ina d'inki na? ko kallanta
batayi ba ballantana ta amsa mata, hakan yasa taje wurin Mama tana gayamata,
Mama tace "taje yana d'aki ta dauko harda nasu seema da samrah da yake kusan a can gidansu take yini saboda
sune k'awayenta gashi yanzu sunfara zama 'yan mata don yanzu jss two suke.
Yau takama wednesday inda ake ta shirye-shiryen bridelshower
amma amarya tana cikin d'aki zaune tayi shuru kamar wata kurma, iman ce keta ta
lallashinta tund'azu da tatashi tayi wanka amma tak'i suna cikin haka ne saiga
saudat tashigo cikin ta kuwa har yatasa don yanzu yashiga five month, ta kalli
khadijah tace "Mama tace kitashi kiyi wanka kafin tazo ta iskeki a
wurin" jin hakan yasa ta tashi taje tayi wanka, kafinta fito iman ta fiddo
mata kayan da zatasa, nan take naga tayi kyau tun kafin tayi kwalliya, koda
yake bakasafai tacika yin kwalliya ba, haka aka gama bridelshower zuwa yamma
kowa ya tafi gida duk abinda akeyi khadijah kallon kowa take don ko magana bata
sonyi sai dole, dare nayi ta wuce d'aki ta kwanta tana tunanin Jiddan saboda
yanzu Mama ta kwace wayarta ballantana ta kirashi taji sanyi aranta
Tana cikin tunanin haka maman salma tashigo ta zauna tace
"khadijah kinga har yanzu baki ida shan magungunan kiba kuma gashi yanzu
nadafa maki kaza don Allah kiyi kokari kiciyeta tunda mazan yanzu kinsan dole mace ta had'a da
gyara
Tashi tayi batare da tace komai ba saboda ita duk wannan
abin da ake mata kallansu kawai take domin ba gyaran bane agabanta, aranta kuwa
cewa take "Dama ace Jiddan ne da sainasha abinda yafi wanda kuke
bani" amma yanzu data sha da kokartasha wannan ba damuwarta bane
Haka ta zauna taci kazar badan ranta nasoba, harta gama
sannan maman salma tasa tashiga cikin toilet tayi wanka yaji had'in turaruka
masu sanyi qamshi, dama tunjiya aka gama mata dilka sai wani kyau dafatarta
tayi sai sheki take da laushi tare da wani irin sihirtaccen kamshi dake tashi
daga jikinta.
Bayan angama tayi shirin kwanciya saiga ihsan da waya a
hannunta tashigo tacemata "gashi ya muhsin nason magana dake inji Mama,
har kyarma take ta amsa saboda a tunanin ta Jiddan ne tana d'auka taji muhsin
ne nacewa "hello khadijah"
"Na'am ya muhsin ina jinka"
Dama sonake muyi wani sirri dake" "Ok" "wallahi khadijah Jiddan yana cikin wani
hali kuma gobe naji Mama nacewa zamu taho, toh shima yace gobe tun k'arfe
7:00am zai taho kuma yace yana son yaganki ko ta halin k'a-k'a" fashewa da
kuka tace "ya muhsin tayaya zai ganni bayan gobe kamu za'ayi duk da sai
k'arfe biyar na yamma amma nasan ba wanda zayabarni na fito" "pls khadijah kitaimaka sannan kuma
inason kigaya mani inda zai jiraki sannan ki kiyaye ki kula da kanki pls"
"toh kace ya jirani a GRA bayajidda road misali k'arfe
11:00am zansan yadda zanyi in fito"
Yace "toh amma ki kiyaye" "to yanzu babu yadda za'ayi
mugaisa" "aibamu tare
dashi" "Ok"
Bayan sun gama waya ta kwanta da tunanin yadda zatayi ta
fita
Washe gari da misalin k'arfe 10:30am tace ma Mama tana so
taje shagon da akayi mata saloon ta manta wasu kayanta da kud'i aciki Mama tace
"ki aika ihsan da driver su amso maki mana"
"ai baxata basu ba saboda sai na mata bayani kuma kinga
ni tasani batasan ihsan ba"
"toh aishikenan, amma ihsan tarakaki" toh amma
bada musa zamu fita ba don naji d'azu abba ya aike shi kuma bana tunanin
yadawo" to aisaiku hanzarta, cewar Mama", zuwa tayi tayima ihsan
magana suka tafi,suna fitowa get suka hango su samrah sun taho, "yaya
khadijah kinga su samrah sun biyo mani muje wurin kunshi ko" khadijah tace
"kutafi kawai amma inkun dawo kijirani gidansu seemah idan nadawo zankiraki"
suna tafiya itama khadijah ta shiga napep, misalin k'arfe 11:20am ta isa wurin
batasha wahala ba ta hango motarshi yayi parking a wurin wata bishiya dayake
Unguwar shuru take sai akashe ma mutum batare da ansani ba bakajin motsin komai
sai kukan tsuntsaye dake ta shawagi sararin samaniya saboda yanda area take
shuru
Tana zuwa taganshi back seat ya d'an kwanta, ganin k'ofar a
lock take yasa tad'an fara yima shi knocking ashe bacci yafara ita kuma bata
saniba saboda yasa eyeglesses mai duhu saida tak'ara knocking sannan yatashi ya
bude mata ta shiga
Tana shiga ta zauna tare da rufe k'ofar tace mashi
"miyasa kazauna a backseat?"
"gajiya nayi da zama shine nadawo nan bansa sadda bacci ya d'auka
ni ba" eyeglass d'in dake idanshi
tacire tare da kama kumatunshi duka biyun ta girgiza, sannan shima yakama nata
ya girgiza sukayi Murmushi domin wannan itace d'abi'arsu insun had'u sukeyinta
sannan tace "daga gani baka bacci shiyasa" Hakan yasa ya matso kusa
da ita yana rik'e hannunta d'aya yana murzawa tare da d'aura gudan saitin
zuciyar shi sannan yakalleta cikin ido yace "toh khadijah ya xanyi inyi
bacci, yanzu dagaske rabuwa zamuyi?" cikin muryar kuka tace "toh ni yayana ya
xanyi........................bata k'arasa fad'in abinda zata ceba sanadin tarin
da yafara ba kaukautawa
Mrs Abdul Sule
[1/17, 10:47 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI* *DA'IMAN*
*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*
DEDICATED TO SA'ADATU ALIYU KABUGA
Page 56~60
Kuka tafarayi sosai ta fad'a saman kirjinshi tana buga-buga
bayanshi, a hankali tarin yafara raguwa saidai ita takasa barin kukan da take
kuma takasa tashi a saman kirjinshi, gashi har veil d'in da tayi rolling kanta
dashi ya cire, hakan yasa Jiddan baisan lokacin da yasa hannun shi ya fara shafa
gashin kanta ba musamman yadda yasha
gyara ga wani sihirtaccen kamshi dake tashi daga jikinta
D'agowa yayi da fuskarta yafara lashe hawayen da ke zuba
daga idaniyarta
Ita kuwa jin abinda yafara matane yasata daina kukan da take
ta shiga duniyar tunani, batayi aune ba taji ya had'a bakunansu yana tsotsa
kamar yasamu sweet, da kyar tayi nasara zare nata bakin daga nashi
D'ago idonta tayi a fusace da niyyar yima shi magana kallo
d'aya tayi mashi ganin yadda idanuwanshi suka koma sai taji tausayinshi sosai
Shikuwa ganin ta kwace bakinta yasa ya fara shinshinar wuyan
ta sanadin doguwar rigace jikinta shiyasa yakai hannu ya zage zip d'in rigar,
baisan sadda ya k'ara rikicewa ba duk ya fita hayyacinshi wani irin romancing d'inta yake sosai
Kamar a mafarki yake jin kukanta hakan yasa yadawo cikin
hankalinshi tare da rufe mata jikinta yakuma
yimata rolling veil d'inta
K'ara rungumeta yayi tare da sauke numfashi a hankali sun
d'auki kusan 5 minute babu wanda yace komai
Jiddan ne yayi k'arfin halin cewa "khadijatu kiyi
hak'uri wallahi bansan sadda hakan tafaruba kuma kinsan wannan ba hali na
bane"
D'agowa tayi da niyyar yima shi magana sai ganin hawaye tayi
a fuskarsa tace
"yayana miyasa kake kuka" yace
“khadijah
abubuwa da yawa gashi gashi zan rabu dake ga kuma abinda nayi maki yanzu ina
zansa kaina"
"yayana nasan ba halinka bane harda zafin rasa ni da
zakai ne" yace
"kinyarda badan sha'awa yasa nayi maki haka ba?"
"eh yayana" zoben dake hannunsu suka jera yatsun
dake jikin zoben, ya kalleta yace "khadijatu inasonki har gaban
Abada"
Lokaci d'aya suka sake fashewa da wani kuka nazafin rabuwa
da abinda kakeso sun d'auki lokaci mai tsawo a haka
Da kyar suka lallashi junansu sanna khadijah tayi mashi
sallama zata tafi, har ta bud'e murfin motar da niyyar fita ya k'ara jawota ya
manna mata kiss sannan yace
"Khadijatu promise me kada ki manta dani"
Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace "I promise you
yayana" yanzu bazan sake ganin kiba ko khadijatu?
Ganin kamar zaiyi kuka yasa tace "a'a munanan tare har
Abada, kuma da anbani waya ta zankira ka"
Bud'e k'ofar motar tayi ta fita batare da tak'ara kallanshi
ba domin bata son taga yanayin damuwar da zaishiga
Haka takoma gida bayan ta kira ihsan suka shiga gida, tana
zuwa d'aki ta k'ara fashewa da wani kukan saboda yadda ta tuna Jiddan da kuma
halin dayake ciki na rasata da zaiyi dakyar tasamu ta tsagaita kukan gudun kar
asan halin da take ciki domin 'yan biki ne cike da gidan
Maraice nayi aka fara kamun amarya a zanbrush inda akayi
decorating d'in wurin da komai ash and yellow sai chairs d'in white, suma
'yanmatan amarya yellow d'in kaya suka sai head ash
Amarya naga anshigo da ita cikin hall d'in tasaka wata
had'ad'iyar gown yellow sai sharar k'asa take, da yake akwai layi layin white a
jikin gown d'in sai tasaka white head tare da wani white d'in mayafi da ya rufe
duk jikinta harda fuska
Can naji 'yan group d'in Garkuwan fulani nacewa "Ina
ango yake yazo ayi bud' ar kai ko munga fuskar amarya" Aikuwa kamar dama jira yake suyi magana, saiga
S.S da abokanan shi anshigo suna ta washe baki
Nan take bada wani b'ata lokaci ba abokan ango suka sayi
fuskar amarya akan naira dubu d'ari sannan aka fesheta da turare kafin ango ya
bud'e fuskar amarya
Muguwar fad'uwar gaba ss yaji a lokacin da yabud'e fuskar
khadijah saboda baiyi tunanin kyanta yakai haka ba amma ba wannan ne yafi
damunshi illah yadda yaga khadijah ta k'ara ramewa ga damuwa a fuskarta
Matso wa yayi dai-dai kunnanta yace "pls khadijah ki
d'aure ki saki fuskarki kada mutane su fahimci wani Abu" kwalar dake cikin
idonta ta had'iye sannan tayi Murmushi da yafi kuka ciwo batare da tace komai
ba
Ganin haka ne yasa Iman tayi saurin tahowa wurinta don bata
nan aka fara bud'ar kan tana can wurin ba 'yan group d'in pherty novel's
seveniors gudun kada suyi rigima lol 😜
K'ara sauri take taga ta isa wurin khadijah jitayi tayi karo
da mutum taiyi baya zata fad'i shi kuma yayi saurin rik'ota da sauri gudun
karta fad'i
Tace "am sorry banganka ba ne" daga haka bata sake
cemai komai ba ta wuce shikuwa ganin hakan yasa ya bita
Tana zuwa, ahankali tace ma khadijah "don Allah karkiyi
kuka kinji" d'aga mata kai kawai
khadijah tayi, saiga Adnan da yabiyo bayan Iman sallama yayi Iman ta amsa mashi
yace "baiwar Allah wurin ki nazo"
"amma ai nabaka hakuri"
"ba shine damuwa taba"
"to ina jinka"
"taimako ne zakiyi mani kidaina tafiya da sauri don
gudun kada wata rana kiyi mani asara, sannan kuma inaso kibani number
wayarki"
Murmushi Iman tayi tace "bani da waya" daga haka
ta tafi bata kara cewa komai ba, shikuwa ss binsu kawai yake da kallo
Haka aka gama taro aka tashi lafiya, amma Adnan saida yasan
yadda yayi ya amshi number Iman
Ana dawowa daga kamun wani irin zazzab'i mai zafi ya rufe
khadijah har saida Mama ta kira ss tagaya mashi
Bayan ya dubata ne yace ma Mama "malaria ce, data sha
magungunan nan insha Allah zata sauka"
Anty fa'iza ce tace gaskiya a sanar da mutane gobe ba wata
dinner da za'ayi abarta ta huta
Bayan sallah juma'a,dubun nan jama'a suka shaida d'aurin
auren Dr Suleman Shehu Matazu da khadijah Usman Abdallah akan sadaki naira dubu
hamsin, wanda manya yan kasuwa da k'usoshin gwamnati suka halarta
Ango nata gaisawa da mutane ya hango muhsin hakan yasa
yamatsa suka gaisa sannan ya mik'ama na kusa dashi hannu d'agowar da zaiyi sai
yaga ashe da Jiddan ne suka gaisa baisani ba
Jiddan ne yayi k'arfin hali yace "ina tayaka murna
Allah yasa alkhairi"
A yanayi da yayi maganar da kyar ya ida shiyasa ss yaji
matukar tausayinshi, dafa kafad'arshi yayi yace
"Jiddan kayi hakuri bawa baya samu sai rabonshi, don
har ga Allah banso rabuwarku ba kuma nasan harna mutu bazan daina zargin kaina
akan rabuwarku ba"
Da kyar Jiddan yace "Na sani kuma ina godema Allah da
khadijah ta fad'o hannunka don nasan kai mutunan kirki ne, abinda zan rokeka
shine ka rike khadijah amana pls, don Allah kayi hak'uri da ita kada kabata
mata rai nasan zaka sha wahala kafin ka shawo......................bai ida
maganar ba tarin shi ya sark'eshi ss ne da muhsin keyi mashi sannu sada yalafa
da tarin sannan ss yace
"nayi maka alk'awari insha Allah zanrik'eta amana"
Kiran da akayi mashi ne yasa ya tafi shikuwa muhsin yaja
Jiddan suka shiga mota, sai kuma tarin shi yatashi har yana zubda jini cikin
rud'u muhsin yace "Jiddan kaga abinda nake gaya maka kaje asibiti kak'iya
yanzu gashi nan" don haka da sauri yaja motar zuwa Asibiti