HABIBI DA'IMAN 21-40
*Page* *21*
*~* *25*
Wani farin dogon
saurayi na gani wanda bazai wuce shekara 23 ba, amma baya da k'iba, fuskarsa
d'auke take da dogon hanci kamar biro, sai girarshi da take a cike, gashin
kansa kamar na larabawa ga fuskarshi sumul ba alamun yana da saje.
Yana isa ya lallab'a ta bayanta, tare da dafa hannayenshi,
Hakan yasa khadijah ta juyo da sauri da niyyar yin ihu
Kawai saiya kama yi mata dariya, hakan yasa tafashe da kukan
shagwab'a tana cewa
"wallahi yaya sai na rama" biyo shi tayi da niyyar
ta buga mashi book d'in dake hannunta
Kamata yayi tare da zaunar da ita ya had'e hannayenshi 👏🏻
yace "i'm sorry, ke d'ince ai baki da k'iba shiyasa nike maki wasan
yara"
"uhmmm amma dai ba ramamma bace"
Yace "shiyasa nake ce maki everthing about you is
moderate"
Kallanshi tayi tace "ya exam"
"fine, kefa?"
Nima lfy lau
Yace "my princess yakamata in tashi in tafi inshirya,
don inason la'asar tayi mani a kaduna"
Raurau tayi da ido alamar kuka tace "Allah ya kiyaye
hanya"
Tsugunnawa yayi agabanta yace
"pls khadijah menene na kuka gobe kamar yanzu kema kina
kaduna.
Pls dan Allah karkiyi kuka kinsan bana so yana tada mani
hankali"
Yadda taga duk ya birkice mata yasa taji tausayinshi tace
"toh yayana na daina" tare da
yin Murmushi"
Saida yakama hannun ta ya murza zoben hannunta tare dayi
mata kiss sannan suka tafi.
Washe gari da wuri su khadijah da Mama suka wuce, safwan ne
yayi driving d'insu, don Baba baya gari sai ranan d'aurin aure xaije.
Ihsan dake gaban motar ta ishi ya safwan da surutu yace
"idan bakiyi mani shuru ba zan sauke ki a daji kura ta
cinyeki"
Aikuwa shuru tayi bata k'ara magana ba har bacci yayi gaba
da ita.
Suna isa kaduna
khadijah ko abinci bata tsaya ciba, ta fito da niyyar zuwa wurin Maman su
Jiddan, cin karo tayi dashi shida muhsin suna tahowa, hakan yasa muhsin ya wuce
yana "cewa taje ta dawo akwai labari"
Ita kuma da Jiddan suka wuce wurin Mama.
Ummi ce zaune a
palour, s.s yayi sallama ya shigo
Tace "yauwa dama suleman kai nake jira don kasan gobe
da wuri zamu wuce kaduna"
Dama nima nazo ince maki ku shirya k'arfe 8:am zamu tafi don
haka su seema suje su kwanta da wuri"
The following day,
bayan antaso daga sallar juma'a dubanan mutane suka shaida daurin auren Saudat
Aliyu da Inspector Kabeer k. Mashi.
Su muhsin da Jiddan ne suka k'araso inda mutane suke suna
gaisawa daidai lokacin da Jiddan ya mik'ama s.s hannu ya dago suka hada ido,
hakan yasa Jiddan yayi wani kala, Batare da yanuna ba yabasar sai bayan suntafi
ne yake cema
"Muhsin nida naga wancan guy d'in wallahi hakanan naji
gabana ya fad'i, i don't no why"
Muhsin yayi Murmushi yace "kada kadamu dama sometimes
mutum najin irin haka.
Amarya Saudat ansha kyau angaji su Asiya da Rabi'atu duk sun
zo, khadijah kuwa sai hidimar biki akeyi, amma abinda ke damunta bai wuce yadda
kowa yake ganin kamar tana korar samari bane wai don ta auri mai kud'i, don
taga tana da kyau, ita kuwa a ganin ta bazata tab'a soyayya da kowa ba sai
Jiddan don akanshi tasan so kuma akanshi zata k'are
Yanzu gashi ana bikin Saudat kowa na cewa ita tak'i aure.
Haka akasha shagalin biki, da dare kuma aka wuce Arabian
nyt.
In tsaya fad'a maku kyan da Amarya da ango sukayi zai d'auke
mu lokaci bamu gama ba, amma sunsha kyau ba k'arya.
An k'awata wurin da komai white and black inda maza sukayi
shigar white d'in dress da black d'in hula, mata kuma black gown and white
shoes.
Can na hango s.s ya keb'e shi kad'ai yana latsa phone
d'inshi, 'yan mata kuwa sai kallon shi suke don sunga hansome guy "ni
halima nace to fah!!"
Ihun Rabi'atu dasu mimie naji shiyasa na juya don ganin me
suke ma ihu
Jiddan da khadijah ne suka shigo, ni kaina dana ke d'auko
maku rahoton saida na firgita saboda kyau da dacewar da sukayi ga wani red
lipstick da khadijah tasa, sunyi kyau kamar wasu couple.
Hakan yasa s.s ya d'ago don ganin me akema ihu!!!
Kawai sai ganin khadijah yayi da wani kyakyawan saurayi
wanda kamar yasan face d'inshi, Aikuwa baisan sadda yamik'e cikin fargaba da
faduwar gaba ba yace "what"
Hakan yasa nai saurin Kallanshi nace toh 😳, shi kuma
wannan lafiya????
Mrs Abdul
Sule
[1/17, 10:46 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI* *DA'IMAN*
*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*
*DEDICATED* *TO* *SA'ADATU* *ALIYU* *KABUGA*
DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION
Page 26
~30
Gani nayi kwashi
keys d'in motarsa da wayoyinshi ya fita a fusace ba tare da ya kalli inda suka
khadijah suke ba, hakan yasa na maida kallona gunsu Jiddan dan kada abani
labari
Jiddan nagani yana jan habibatin tashi, ita kuma tana
turjewa yana cewa
"yau sai kinyi rawa"
Hakan yasa yajanyo ta jikinshi tare da rik'e mata hannu
d'aya yana rawa da ita a hankali
Ita kuwa sai faman sunne kai take alamar jin kunya.
Can na hango 'yan group d'in Mk na mata xallah suna ta
kwasar shoky💃🏻, su mairo Usman sai tura take away ake cikin
jikka, birchi ko cewa take banshi haka ana kallanmu, ke basu ganin mu shoky
suke kwasa😜
Haka aka sha shagalin arabian nyt
Anyi biki ank'are lafiya anci ansha, gobe ne za'a kai amarya
gidan mijinta domin itama a katsina zata xauna sannan ta ida karatun ta.
Washe gari haka su khadijah da sauran k'awayen amarya suka
shirya tare da amarya sai katsina ta dikko d'akin kara kunya gareku badai tsoro
ba.
Jiddan kuwa baiji dad'in tahuwar ta ba, saboda shi sai hutu
yak'are zaidawo
Direct gida su Mama suka wuce da saudat kasancewar sai bayan
ishsha'eh zaa kaita
Mama da ummi ce dasauran yan uwa suke ma amarya nasiha kan
zaman takewar rayuwar aure da abinda ya k'unsa
Shikuwa s.s bayan fitarsa daga wurin dinner, tafiya yayi
masaukin su, shigarsa d'akin baixarce ko ina ba sai toilet yasa karma kanshi
shower tare da tunanin meyasa yakejin haushi don yaga khadijah da wani
Hakan yasa the following day da safe yakoma katsina
Su khadijah dare nayi Misalin k'arfe 8:00pm suka kai amarya gidanta
Saidai kuma a can gida s.s yaje yana neman khadijah ta dafa
mashi abinchi bai tadda taba hakan yasa ya biyota gidan saudat
Sukawa bayan sun aje amarya, ita dasu Asiya suka fito da
niyyar amaidasu gida
Sai kawai taga motar s.s, shikuwa da yaganta saiya fito tare
dayi mata alama da tazo,
Tana zuwa taga ya shiga cikin motar tare da bude mata gaban
motar alamar tashi ga
Hakan yasa ta shiga Batare da musu ba
Jan motar yayi suka tafi
Tafiya suke amma ba wanda yace ma d'an uwansa komai
Can ya daure yace "waye naganki dashi jiya?"
"tace ina?" harararta yayi yace "wurin
dinner"
Murmushi tayi tace "au ya Jiddan"
Kallanta yayi "dama kina da wani yayan bayan
safwan"
Kallan mamaki tayi mashi sannan tayi fari da ido tace
"Aishi wannan na daban ne"
Batare da ya kalletaba yace "kamarya"
Batayi shayin komai ba tace "saurayi na"
Bata ida fad'in maganar taba dai-dai lokacin sun iso kusa da
k'ofar gidan yaja wani mugun birki, cikin tsawa yace
"fitar man a mota"
Hakan yasa ta fita tana kuka, wai yau itace na miji yacima
mutunchi Batare da tayimashi komai ba!!
Haka ta shiga gida tana kuka,
Yana daga cikin motar yana hangeta da yadda take kuka sai
yakejin bai kyautama zuciyar shiba da yayi mata haka
Toh amma shima baisan dalilinshi nayin Hakan ba
Abinchi da baa dafa mai ba kenan ya koma gida ya kwanta
cikin tsananin damuwa
********
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya s.s kullum yana cikin
tunanin har abokinshi Adnan ya gane sannan ya tabbatar mashi da son khadijah
yake shiyasa yake shiga duk wani hali idan yaganta da wani
Take yafara tunanin ta ina zaifara shiga rayuwar ta bayan ya
fahimci tana da wanda take so
Sannan shibai masan ta yaya zaifara tunkararta ba, hasalima
baitab'a soyayya ba
Baisanma yadda akeyima 'yan mata ba gashi baison abinda take
so da wanda bataso ba
Kuma bama yajin zai iya kaskantar da kanshi wurin ta yace
yana sonta gudun kada tarenashi.
A bangaren khadijah
kuwa bata k'arasa s.s a idon ta ba tunranda abin ya faru, sau d'aya ya shigo ya
gaida Mama, tana jin sallamarsa tayi sauri ta shige d'aki dan wani irin haushin
shi da tsanarshi takeji, kuma tayi alwashi sai ta rama abinda yayi mata duk
daran dad'ewa
s.s da Adnan kuwa sungama shirya yadda zasu billoma
al'amarin domin shi s.s yace bayason a cutar da kowa ko Jiddan ko ita khadijah
Hakan yasa suka fara bincike akan yanayin soyayyar tasu
Mrs
Abdul Sule
[1/17, 10:46 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI* *DA'IMAN*
*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*
*DEDICATED* *SA'ADATU* *ALIYU* *KABUGA*
DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION
Page 31~35
*Wannan* *shafin* *naki* *ne* *my* *lovely* *sis Asiya Mk*
*Allah* *ya* *jib'anci* *lamuranki*
Sannu sannu abin yaci gaba da damun S.S hakan yasa ya kasa
jurewa yaje ya samu safwan da maganar yanason ya bashi number muhsin yayan
saudat
Safwan yayi mamaki ya akayi ya sanshi? Amma sai ya share
yace "lafiya dai ko?"
No ba wani abu bane kawai na hadu da yaron ne a wurin bikin
saudat kuma nayi mantuwa a wurinshi"
Batare da wani tunani ba yabashi number
Bayan S.S yakoma gida ne yazauna a d'akinshi yayi dialing
number muhsin saida yabashi 2 miscall, ana ukkun ne yayi Receiving call d'in
tare dayin sallama
Sannan S.S yace mashi "zaka iya tuna wani wanda kuka
gaisa a ranan daurin auren saudat?"
Shuru muhsin yayi na d'an wani seconds sannan yace mashi
"gaskiya a'a"
Da farko suna na Dr suleman shehu matazu mune neigbour
d'insu khadijah"
Muhsin yace "am sorry kasan bansaka a face ba saidai
labarinka nakeji a wurinsu safwan"
S.S yace "alright ba damuwa, amma mungaisa dakai ranan
daurin auren saudat.
So dama nakiraka ne inji when are you free inzo muyi wata
magana da kai"
"No problem dama ranan saturday Mama zata aiko ni
katsina so in nazo sai muyi maganar inba damuwa? "
S.S yace "Ok nothing" tare dayin hanging up
Daga ranan wednesday zuwa saturday S.S jiyayi kamar
anshekara saboda k'agara da yayi su hadu da muhsin don jin abinda yakeson sani
game da khadijah
Amma saboda tsabar miskilanci bai yadda wani ya gane halin
da yake ciki ba
Ranan saturday kuwa da wuri yagama duk wani abinda zaiyi
gudun kar muhsin ya kirashi yana busy
Da misalin k'arfe 2:15 pm muhsin yakira shi yace su had'u
soli centre
Batare da b'ata lokaci ba ss ya isa wurin, bayan sun gaisa
ne yayi gyaran murya sannan yace
"dama akwai wani guy fari sosai wanda naganku tare
ranan daurin aure ance neigbour d'inku ne, shine nakeson naji miye alak'arshi
da khadijah?"
Cikin mamaki muhsin yace "amma lfy kake tambaya
akanshi?
"No bakomi kawai dai yadda naga ya rik'eta ne ranan
dinner hankalina bai kwanta ba, so kasan Yaran wannan zamanin sai a hankalina,
a matsayina wanda nake ganin tamkar yayanta wanda suka fito ciki d'aya"
Muhsin yace "kuma fa haka ne, amma da kasan tarihin su
bazaka ce wani abu bane duk da wannan ma abun dubawa ne"
S.S yace "inason kagaya man waye Jiddan don hankalina
ya kwanta?
Tun anan muhsin ya harbo jirginsa saidai ya share yace bari
ya tabbatar sannan
Sunan mahaifin Jiddan Abubakar sai mahaifiyarshi Fatima
wanda auren zumunci ne shida ita, Jiddan shine d'a na biyu a wurin su
Soyayyar Jiddan da khadijah tasamo asaline tun muna da
shekara 9 lokacin ita kuma tana da 5 years
Wata rana muna zaune a k'ofar gidanmu suka fito da gudu ita
da yara suna wasa, ganin muna k'ofar gidan zaune ita kuma ba kallabi akanta
yasa ta koma ta d'auko kallabinta, sanadiyar hakan ne yasa yaji ta burgeshi
tunda daga ranan yake mutuwar son khadijah don akwai wani lokaci data dad'e bata
zo hutu ba har rashin lfy ya kwanta
Lokacin da yakai kan gab'ar balagarsa da khadijah yafara
mafalkinshi wanda ni kad'ai nasan da haka saboda bama boye ma junan mu damuwar
mu
Saboda haka ina da linking akan Soyayyar su domin ni na
rink'a tusa ma khadijah sonshi a ranta tun bata son kowaye ba"
Asirtacciyar ajiyar zuciya S.S yasaki tare da fad'in
"Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi"
Sannan yatashi cikin mutuwar jiki yayi mashi sallama sannan
ya wuce gida
Shikuwa muhsin a lokacin ya tabbatar da zarginsa akanshi
saboda yadda ya hango tsananin son khadijah da kishin ta fuskarshi, hakan yasa
ya tab'e bakin shi alamar shiya sani, sannan yatashi ya tafi.
"nikuma nace oh ni Mk haka zakuyi ma ss 🤔
Bayan komawar ss gida yakira Adnan yake fad'a mashi yadda
sukayi da muhsin
Sannan yake ce mashi "ni gaskiya bazan iya raba wannan
Soyayyar ba domin zan shiga hakk'insu, saidai inshi Jiddan ne yajanye da kanshi
Don haka zanyi kok'arin b'oye abinda ke raina har lokacin da
Allah zai yaye mani sonta"
Take Adnan ya goyi bayan shawarar abokin nashi tare da mashi
fatan alkhairi.
Mrs Abdul
sule
[1/17, 10:47 AM] Halima Mk: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*HABIBI* *DA'IMAN*
*WRITED* *BY* *HALIMA *Mk*
*DEDICATED* *SA'ADATU* *ALIYU* *KABUGA*
DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION
Page 36~40
A yanzu hutun su khadijah yak'are sun cigaba da zuwa school
Tana zaune a class ita kad'ai kasan cewar damuwa tayi mata
yawa, sai ga Iman da zee sun shigo da yake a hostel suke zaune
Ganin khadijah cikin damuwa yasa Iman ta dafa ta tace
"Aminiyata miye damuwarki"
Nan take tagaya masu abinda Mama tace mata
Zee tace "toh me zai hana idan Jiddan yazo kigaya
masa"
Nima shi nake jira ya fito daga class kinsan yau ya dawo
kuma bamu haduba"
K'awaye nagari suke baka shawara maikyau nan take suka fara
kwantar mata da hankali akasin mimie da Rabi'atu suna iya yi mata dariya,
shiyasa bata cika gaya masu damuwarta ba
Da yake iman da zee iyayensu masu kula ne basu barin su yawo
shiyasa ko bikin saudat basu jeba saidai fatan alkhairi dasuka yimata
Jiddan na hango yana ta sauri yaje wurin hrtcon d'inshi bcos
tun bikin saudat raban shi da'ita
Ya kuwa yi sa'a ita kad'aice don su zee suntafi nan suka
barta a class
Tun kafin ya k'arasa inda take ya fuskanci tana da damuwa ga
wani Haske da tak'ara
Ita kuwa shuru tayi ta kura mashi ido tanajin sabuwar
k'aunarsa nak'ara ratsa tah
Zama yayi tare da rik'o hannunta yasaka mata wata leda yace
"canko menene anan ciki"
Kallonshi tayi tare da fad'in "yayana ya za'ai nasani"
"Ok bari na bud'e kila ki tuna"
Kwance ledar yayi tare da zazzage abinda ke ciki sai gawasu
beads guda ukku sun fad'o
Dasauri naga khadijah ta d'auko su tana cewa
"yayanah ai banmata lokacin da suka cire daga kitsona
ba nace kamaida mani kace baka iyaba nace toh ka aje mani ashe haryanxu suna
nan"
"khadijah kenan ai duk abinda ya shafeki ina mutuwar
sonshi kamar!!!
Bai ida fad'in abinda zai fad'a ba ya dafe saitin zuciyar
shi"
Ita kuma hakan da yayi kawai sai yasa tafara dariya
Hakan kuwa yayima Jiddan dad'i ganin ta fita daga damuwarta
Saida yabari tagama dan kanta sannan yace
"khadijatu" yanda taga ya kirata yasa ta maida
natsuwarta kanshi
"Na'am"
"menene damuwarki?"
Nan take wasu hawaye suka zubo mata, tare da gaya mashi
yadda sukayi da Mama
Shuru yayi na wani lokaci Batare da yace mata komai ba
"kada kidamu khadijatu nasan iyayenki bazasu bari har
saina gama karatu nasamu aiki ba sannan muyi aure, musamman yadda suke son suga
kinyi aure da wuri
Amma karki damu zan fad'ama Mama halin da ake ciki domin
tayi mani alk'awarin aurenki"
Da haka yasamu ya kwantar mata da hankali
Da Jiddan ya fad'ama Mama tace "kabari zanyima
mahaifinka maganar"
Bayan tayi mashi maganar yace shi baisan da wannan xance ba
saboda shi yafi son d'anshi yayi ilmi mai zurfi
Sannan idan ma ya aure ta dame zaiciyar da yarinyar mutane
don shi bazai yima d'anshi auren gata ba
Kuma yarinyar da yakeso ba wani nisa ke tsakanin suba
ballantana ta jirashi don haka ni banyadda da ba.
Haka Jiddan yayi ta Damun Mama data taimaka mashi da jari
yafara sana'a kafin lokacin da zai gama makaranta ya auri khadijah
Mama kuwa tunani take tabashi ya fara kasuwanci kafin
lokacin auren koko tabi shawarar mijinta?
Duk da dama yace bai amince da auren ba
Take ta yanke shawarar goyon bayan mijinta shiyasa ma tacema
Jiddan yayi hak'uri
Tundaga wannan al'amari da yafaru Jiddan yashiga
matsananciyar damuwa daga shi har khadijah karatunsu yaja baya saboda tsananin
damuwa da tayi masu yawa kullum cikin neman mafita sukeyi amma abin ya gagara
A b'angaren khadijah kuwa kullum Mama fad'a take mata data
dunga kula samari ga wani faisal abokin safwan da yadad'e yana sonta amma tak'i
kulashi harya hak'ura ya fara neman wani auren
Sakamakon haka khadijah ta k'udir ta aranta koma wa yazo
zata fara kulashi don ta fidda kanta
daga zargi
Duk wannan wainar da ake toyawa ss baisani ba
Amma yakasa fidda son khadijah aranshi gashi ummi da daddy
sun isheshi da maganar aure
Jiddan kuwa duk wata sana'ar hannu da yasan zaiyi ya samu kud'i
yanayi saidai yasan bazasu isheshi ya auri khadijah ba balle yarik'eta
Shiyasa yake ce mata tarink'a bin maganar Mama kila hakanne
yafi zama alkhairi.