NOOR AL HAYAT 61-70
Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Toh kar ki masa butulci Iman, baki san xai baki shi ba ya baki, prayer is all what ur little boy wants from you,
kiyi masa addu'a ba kuka ba Iman, if you continue like this what will be the fate of his twin, kin ga shi ma xai shiga damuwa sosai na rashin halve dinsa
and this might affect him badly.... Or did you want anything bad to happen to him also, For his sake plss ki kwantar da hankalin ki so you won't loose him
too, am telling you damuwar da shi xai shiga sai ma ya fi naki" khadijah ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "Na shiga uku don girman Allah kar ya bar
ni shi ma" yace "Then ki kwantar da hankalin ki and accept this fate" hawaye na xuba idonta tace "Toh" yace "Promise me baxa ki sake kuka ba Iman" k'in cewa
komai tayi, ya kira sunanta a hankali ta daga kai tana kallonsa, sosai gabanta ya fadi, ta kuma rushewa da kuka tace "Yanxu Sudais ya tafi ya bar ni.... Shi
fa yace min in je in kira masa Shureim he wants to tell him he is sorry, dama mutuwa xai yi baya son ya mutu a kusa da ni" Ta hade kai da gwiwa tana kuka
kamar ranta xai fita maganar Sudais na karshe na dawo mata "Anty ki ce Shureim ya xo, I want to tell him am sorry" kuka ta ke kamar ana dada tunxurata,
Aliyu ya kasa ce mata komai duk jikinsa yyi sanyi, Ta rikosa tana girgixa kai cikin tashin hankali tace "Yanxu shkkn baxan sake ganin sa ba, me yasa ya tafi
ya bar ni da Shureim" Aliyu ya kasa cewa komai wani mugun tausayinta na shigarsa, cikin sanyayyen muryarsa yace "Pls ki daina kukan nan Iman, da duk biyun
Allah ya raba ki da ya xa ki yi kenan, you neva knew why he took him so soon, be a good Muslimat plss" shiru khadijah tayi jin yace Dukka biyun, ta goge
idonta gabanta na mugun faduwa cos she can't just imagine that, Murya can kasa yace "You make the promise now, that baxa ki sake masa kuka ba sai dai
addu'a...." Ta gyada kai da kyar trying not to cry tace "I promise" yace "Add in sha Allah to the promise" a hankali tace "In sha Allah" Ya d'an yi murmushi
yace "Good" mikewa yyi ya dago ta ta mike ita ma tana goge idonta yace "Ki wuce ciki and remember the promise you make" tace "Toh" daga haka ta fara tafiya
ya bi ta da kallo, da sauri ta juyo sai kuma ta dawo tace "Ina shureim plss" da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace "Yana nan tare da mu" ta
hadiye abu da kyar tace "Ka dauko min shi plss" yace "They are people everywhere, later xa a kai maki shi" shiru tayi sai kuma ta juya a sanyaye ta fara
tafiya, Juyowa tayi ta kara dawowa idonta har ya fara kawo kwalla tace "Toh me yake yi?" Yace "Kukan xa ki fara kuma" da sauri ta girgixa kai tana goge
idonta, yace "He is just sitting down" bata ce komai ba ta fara tafiya kamar iska xai kadeta ta fadi har ta bar wajen, Aliyu ya koma a sanyaye ya xauna ya
jinginar da kansa jikin bango yana jin mutuwar yaron har cikin ransa, Tun da khadijah ta dawo compound din khaleel ke bin ta da kallo har ta shiga parlor,
sai a sannan barrister Sudais ma ya dauke idanuwansa daga kallonta, Bedroom ta wuce duk mutanen parlon suka bi ta da kallo cike da tausayinta, Umma na xaune
har lkcn duk jikinta yyi la"asar, da ido ta bi khadijah har ta dauko Hijab dinta ta sa ta xauna kan darduman dake shimfide ta jingina da bango, hawaye ya
cika Idon Umma don bata yi xaton hakan ba, tashin hankalinta ta Inda xata fara lallashin Khadijah sai ga shi taga ta ma daina kukan, Wata frnd din umma ta
dawo kusa da ita a sanyaye tace "Kiyi hakuri kinji Khadijah, Allah yayi masa rahama..." A hankali khadijah tace "Ameen" Umma taji hankalinta ya kwanta
sosai, tashi tayi ta fita da kanta taje kitchen ta hado mata shayi ta dawo, kasa sha Khadijah tayi har lkcn ta kasa yarda Her lovely Sudais is gone forever,
tana son kuka amma sai ta tuna promise din da tayi, hakan yasa xuciyarta ya dinga mata xafi sosai, kowa ya ganta sai yaji tausayinta, Umma har lkcn mamakin
karfin halin nata ta dinga yi, a haka har aka yi la'asar, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh umma ta xubo mata abinci ta xauna kusa da ita cike da
lallami tace "Don Allah ko kadan ne ki ci Khadijah, tun jiya fa baki ci komai ba" Khadijah tayi shiru bata ce komai ba, can ta dago da kyar tana kallon Umma
tace "Umma yanxu shikenan Sudais ya tafi" Rungume ta umma tayi tana kokarin ganin bata xubda hawayen dake baraxanar xubo mata ba, cikin sanyin murya tace
"Pray for him daughter, Allah yasa can ya fi masa nan, Allah ya sa mai ceton mu ne" cikin rawar murya Khadijah tace "Ameen" umma tace "Toh ki ci abincin
kadan don Allah" ta girgixa kai tace "Umma baxan iya ci ba" Umma tace "Ko cokali biyu ne ki yi" Nanny ce ta shigo dakin da kumburarrun idonta ta duka kusa
da su tace "Umma akwai baki parlor sun xo mata gaisuwa ta daure ta fito" Umma tace "Kice su shigo nan" mikewa Nanny tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo
tare da su Mumy, Baby da su seeyama da wata daban, Mikewa Umma ta yi ganin su ta shimfida masu babban darduma tana masu sannu da xuwa, Khadijah ta dinga
kallon Mumy har ta xauna, A hankali tace "Sannu da xuwa Mumy" mumy da kana ganin idanuwanta kasan ta yi kuka sosai tace "Sannu Khadijah, ya hakuri" Khadijah
ta kasa amsawa ta dakar da kanta, Su siyama ma suka mata gaisuwar a sanyaye, sai a sannan khadijah ta kara dago kanta tana kokarin ganin bata bar hawayen
idonta suka xubo ba, Kallon warce ke xaune kusa da baby ta dinga yi, ita ma yarinyar kallonta take da mamaki, Khadijah tayi karfin halin cewa "Maryam sannu
da xuwa" Maryam tace "Ashe yaron ki ne ya rasu Khadijah, Allah ya ji kansa" Khadijah tayi karfin halin cewa "Ameen" sai dai xuciyarta cike yake da mamaki,
Maryam dama yar uwar su Aliyu ce kenan, makarantar su daya a UK amma Hi kadai ne mutuncin da ke tsakaninsu kawai ta rasa me yasa bata son yarinyar, kawarsu
Vanessa ce dai. Mumy sun kusa minti sha biyar a dakin, duk tausayin khadijah ya cika don tasan rashin yaro da ciwo sosai ga uwarsa barin yaro mai shiga rai
irin sudais, bata ma samu courage din tambayar ina Shureim ba, Karfe biyar da yan mintuna tace ma umma xa su tafi, Umma tace "Toh mun gode kwarai Hajiya,
Allah ya bar xumunci" Mumy tace "Ameen, kuyi hakuri bamu xo tun safe ba kanwata ce ba lafiya tana asibiti sun yi hatsari tun shekaranjiya" Umma tace
"Subhanallah, toh Allah ya bata lafiya, ya yaye mata" Mumy tace "Ameen mun gode" hakuri ta kara ba khadijah Umma ta rakasu suka fita parlor, Sai a sannan
Mumy tace "Kanin Aliyun yana waje ya xo mata gaisuwa amma ko xuwa anjima sai ya dawo" Umma tace "A'a bari ta fito" mumy tayi convincing dinta kan ta bari
sai anjima ya dawo daga haka suka wuce Umma ta koma ciki. A hankali khadijah ta tako har cikin parlor tana sanye da Hijab dinta har kasa ta xauna kujera a
sanyaye tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yyi, ta sunkuyar da kai a raunane tunawa da lkcn da suka dinga dragging sunan da ta xabar ma sudais dinta da
shi, A hankali yace "Amira..." Ta daga kai tana kallonsa lkci daya idanuwanta suka kada, cikin sanyi yace "Keep on praying for him, Allah ya sa mai ceton mu
ne, life moves on plss, ai da baki san Allah xai baki shi ba, so kiyi hakuri ki cire sa ranki, tsakanin ki da shi yanxu addu'a, baxai ji dadi kiyi ta masa
kuka ba" Tana gyada masa kai da kyar tace "Ai na daina, Allah ya ji kansa, ya hada ni da shi a aljanna" Barrister sudais yace "Ameen, Allah ya kara maki
hakuri" Murya can kasa tace "Ameen" yace "Toh yi ma Umma magana xan mata gaisuwa" Ta mike tace "Toh" daga haka ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Umma ta fito,
da ta amshi gaisuwar sudais tana sa masa albarka, Bai dade parlorn ba yace mata xai koma gida, tayi masa Allah ya kiyaye hanya ya fita parlorn, ita dai har
ranta taji Sudais ya kwanta mata, ta kuma san har abada baxa ta mance hallacin da yayi mata ba, don ko ita yayi ma, bata kuma san da me xata saka masa ba.
Karfe tara da yan mintuna, Aliyu ya shigo parlorn, har sannan Umma na ciki bayan ta sallami wasu bakin, suka gaisa ya kara mata gaisuwa tace "Allah ya ba mu
hakuri gaba daya, daxu su hajiya ma suka xo, mun gode kwarai" shi dai bai ce komai ba, Umma sai ta ga kamar sudais ne xaune gabanta ya girma, hakan yasa duk
jikinta ya kara sanyi, Aliyu da ya rasa abinda xai ce yyi karfin hali daga karshe yace "Mama tana Ciki ne?" Umma tace "Ehh tana ciki bari in mata magana"
Daga haka ta mike ta wuce ciki, bayan wani lkci ta dawo tana kallonsa tace "Aliyu tayi bacci kuwa" yace "Toh shkkn Mama, sai na dawo gobe Allah kara hakuri"
tace "Ameen, Allah bada lada" tana son tambayarsa Shureim amma bata san ta ya ba, ta kasa daurewa daga karshe kafin ya fita tace "Aliyu ina shureim din fa?"
Juyowa yyi yace "An tafi da shi mama" tace "Can gidan ku?" Ya girgixa mata kai, Umma tace "Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya" daga haka ya fita, umma ta
san khaleel ne ya tafi da shi can gidan nasu. Ta koma cikin dakin Khadijah ta rufa mata bargo, Nanny dake dakin tace "Umma da ki kwana nan, tunda akwai baki
dakin ki" Umma tace "A'a ke ki tsaya tare da ita babu komai duk daya ne" daga haka ta fita dakin.
Karfe goma na safiyar washegari Khadijah na kwance daki ta rufe ido kamar mai bacci don gaisuwar da ake mata na shureim na kara daga mata hankali, hakan
yasa duk wanda ma ya xo umma da Nanny yake ma gaisuwar, Umma ce ta shigo dakin ta taba ta duk da tasan ba bacci take ba, Khadijah ta bude idanuwanta da suka
mata nauyi tana kallon umman nata, cikin kwantar da murya umma tace "Taso mu je an xo maki gaisuwa" ta d'an hade rai tace "Umma ba ga ku ba bacci fa nake"
Umma tace "Mahaifiyar khaleel ce shi yasa ma na tashe ki" shiru khadijah tayi tana kallon umma, can Khadijah ta mike xaune a hankali, umma ta kama hannunta
ta tashi daga kan gadon, hijab ne har kasa jikinta, hakan yasa ta bi bayan umma dake rike da hannunta suka fita parlor, balarabiyar matar na xaune parlor da
jikokinta su uku sai shureim dake jikinta shi ma, Suna hada ido Khadijah ta sauke kanta a sanyaye ta karasa cikin parlorn ta xauna, da gudu shureim ya taho
ya rungume ta yana kallonta yace "Anty are you sick?" Kallonsa Kawai khadijah take taji kamar ta fashe da kuka, Ummu dake ta kallonta da tausayi tace "Sannu
Khadijah, ya karin hakuri?" kasa cewa komai tayi da farko, can dai tayi karfin halin bude baki da kyar tace "Alhmdlh Mumy, nagode" Ummu tace "Allah yayi
masa rahama, ke kuma Allah baki dangana, ya sa mai ceto ne" Umma tace "Ameen thumma Ameen" don khadijah kasa amsawa tayi, Shureim na kallonta da damuwa yace
"Anty uncle yace min sudais travelled, why will he travel alone, why didn't we go together plss, and now I am missing him, plss I want to go to him, I
promise I will never fight him again...." umma ta jawosa jikinta tana kokarin boye hawayen idonta tace "He will be back soon sweetheart, and I am sure he is
missing you too" Shureim yace "Toh Umma I want to talk to him on phone, am missing him" Ummu dake ta kallon shureim tace "Shureim har ka gaji da wasa dasu
fadeel, ain't they ur frnds anymore" ya juya ya kalleta yace "Noo Ummu I like them, but sudais is my brother, they will like him also" Ummu tace "Toh taho
mu wuce tunda ka gaida Anty" kallon khadijah da kanta ke kasa shureim yyi ya dawo kusa da ita a hankali yace "Anty, is sudais coming back soon? I want the
both of us to be frnds with fadeel and Adeel" Ummu ta mike tace "Toh xo mu wuce Shureim, idan ya dawo xa a kawo sa wajen ka" da haka suka fita parlorn bayan
shureim ya daga ma khadijah hannu, Umma ta rakasu har bakin mota, sai a sannan taga tare suke da Khaleel dake xaune motar, ganin umma ya sakko ya gaisheta
da ladabi sannan ya mata gaisuwa ta amsa tana murmushi tace "Allah ya saka da alkhairi, ya bar xumunci" yace "Ameen" sai da suka shiga motar gaba daya
sannan Umma ta koma cikin gida, bata tadda Khadijah a parlor ba hakan yasa ta wuce daki ta ganta kwance, mamaki ya cika umma ta xauna kusa da ita da damuwa,
yanxu kuma rashin kukan nata ya fara damunta don wani lkcn gwara mutum yyi kukan da kukan xuci, Umma ta yi shiru na d'an lokaci kafin a hankali tace "Look
daughter, cry... even if it's a little so you will feel relieve, kiyi kuka don Allah bana son wannan rashin kukan naki kuma, kin dai san matsalar ki, kar
kije ki tada ciwon ki, it will be worst gaskiya idan haka ya faru" Jin bata ce komai ba umma ta mike a sanyaye ta fita, ba a jima da tafiyar mahaifiyar
khaleel ba su mumy suka xo gidan, yau kam sun d'an dade kafin su wuce kuma khadijah ta fito ta amshi gaisuwar saleem, da yamma shaheedah ta xo gidan da
sadeeq, shaheedah tayi kuka don bata ba sudais mutuwa so early ba, duk taji tausayin khadijah sosai, su Vanessa duk suka kira khadijah yi mata gaisuwar
sudais da har lkcn a xaton su kanninta ne yan biyun. Da daddare ta fito wanka Shaheedah ta mika mata wayarta da yake vibrate, karba tayi ganin Khaleel ne ta
daga ta kai kunne, cikin sanyin murya yace "Khadijah..." A hankali tace "Na'am" yace "Xa ki iya fitowa yanxu?" Shiru ta d'an yi kafin tace "Toh gani nan
xuwa" shiryawa tayi ta sa hijab ta fita xuwa dakin umma, ta durkusa kusa da ita tana kallonta tace "Umma ina xuwa khaleel na kirana" Umma tace "Toh sai kin
dawo" daga haka ta mike ta fita, cikin sanyi take tafiyar kamar mai tausayin kasa har ta isa waje, yana tsaye ya jingina jikin motarsa, kanta a kasa ta isa
gefensa ta tsaya, murya can kasa tace "Ina yini?" Kallonta kawai yake bai ce komai ba har ta dago a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa kasa daga kallonta
da yake yi, cikin sanyayyan muryarsa yace "Ya hakuri khadijah" ta hadiye abu da kyar tace "Alhmdllh" yace "Ban san me xan ce maki ba shi yasa ban kira ki ba
khadijah, I know it's very sad, it's a great lost, but don't forget ba wayon ki yasa Allah ya baki shi ba, and there is always a reason for everything, and
you knw God plans best, don haka ki sa ma xuciyar ki dangana, you have ur handsome shureim, he will act as both him and his twin to you, this is part of ur
fate, and it's already written, plss kin san condition din ki Khadijah kar ki kara sa mutuwar sudais a ran ki I know its very painful, but idan wani abu ya
same ki i will be very sad, come to think of ur only son, for my sake and his don Allah kiyi hakuri, forget about Sudais, but don't forget to pray for him
always, Allah ya hada mu gaba daya a aljanna" cike da damuwa ya kare, Khadijah tayi murmushin karfin hali tana share hawayen da ya taru idonta, tun ranan da
Aliyu yace kar ta sake kuka bata kara ba sai yanxu da take gaban khaleel, a hankali tace "In sha Allah Dr, baxan sa damuwa a raina ba, ae ban ma san Allah
xai bani shi ba, so baxan butulce masa ba, na hakura Allah ya haskaka kabarinsa ya sa can ya fi masa nan, kuma ya raya min d'an uwan sa" cikin rawar murya
ta kare maganar, khaleel ya lumshe ido yace "Ameen Khadijah, am happy with ur words" Bata ce komai ba ta dinga kallon motar da yayi parking bayan na
Khaleel, Aliyu ne ya fito cikin motar, kallo daya khaleel yayi masa ya dauke kansa, Aliyu ya iso inda suke yana kallon khaleel ya basa hannu khaleel ya amsa
amma fa da kyar, Aliyu na kallon cikin idanuwansa yace "Ya hakurin mu?" Khaleel yace "Mun gode Allah" Aliyu ya kalli khadijah suka hada ido tayi saurin
sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, cikin gidan Aliyu ya shiga, khaleel na juya wristwatch din hannunsa yace "Wajen ki ya xo?" Ta girgixa kai tace "A'a"
Khaleel bai sake cewa komai ba bayan wani lkci yace "Alryt then, xan koma Khadijah, Allah ba mu hakuri gaba daya, sleep without worries plss" ta gyada masa
kai tana kallonsa, yana daga kai suka hada ido tayi saurin dauke kanta, yyi murmushin sa mai kyau yace "Amma kin ci abinci kuwa? Tell me the truth plss" ta
girgixa masa kai a sanyaye tace "I don't have appetite" yace "Toh idan na siyo maki abu yanxu make me the promise xa ki daure ki ci" tace "Akwai abinci fa a
gida" yace "Ai na sanin, just promise me xa ki ci plsss" murmushi tayi tana fidgeting fingers dinta a hankali tace "Toh nagode" yace "Yauwa, I will be back
soon" tace "Toh Allah ya kiyaye" daga haka ya xata xai shiga motarsa ita kuma ta shiga cikin gidan, xaune ta tadda Aliyu kan farar kujera a wajen compound
din, kallo daya tayi masa ta dauke kai xata wuce ciki, taji a hankali yace "Iman" kasa ci gaba da tafiya tayi, maganganunsa na jiya da safe na mata yawo a
kai, can ta juyo ta kallesa ta gan sa tsaye, yace "Plss just few minutes" tana ta tsayuwa idonta a kan yatsunta har ya iso gabanta yace "Few minutes pls" Ta
dake da kyar tace "Toh" juyawa yayi ya nufi gun kujerun ta bi bayansa, ya xauna kan kujerar ta xauna ita ma. Kallonta kawai yake ta ki kallon sa ta hade
rai, murya can kasa ta ji ya fara cewa "Iman ba dan ni ba don Allah ina son ki mance abinda ya faru tsakaninmu six years back....." Da sauri ta dakatar da
shi tace "Toh ni nace maka ban mance bane?" Ya girgixa kai a hankali yace "I mean ki yafe min ki cire a ranki da gangan na maki hakan wllh ba da gangan
bane, it's a set up, though ba lallai ki yarda da hakan ba, amma don Allah kiyi hakuri mu dinga xumunci" Ji tayi kamar ta fashe da kuka don ya fama mata
ciwon da ya ki healing har yanxu a xuciyarta, A sanyaye yace "Kin ji Iman, ki raga min ko albarkacin daya yaron da ya rage a tsakaninmu even if I didn't
deserve it" Khadijah ta kasa cewa komai, Bayan wani lkci ta daga kai a hankali tana kallonsa ta ga kallonta yake, da sauri ta sauke idonta tace "Ni fa na
mance, ya kuma wuce a gu na" yace "Toh nagode sosai, amma xaki bani yaron?" Da sauri ta daga kai tana kallonsa, cikin rawar murya tace "I can't give you my
son, kayi hakuri..." Yana gyada kai a hankali yace "No offense, amma xa ki bari ai mu dinga xumunci da shi, I mean in dinga xuwa ina ganinsa, once in a
while kuma xa ki bari ya xo gun mumy koh" shiru tayi ta kasa cewa komai, murya can kasa yace "Kin yi shiru" a xuciyarta tace "Nasan maganin ka" a fili kuma
tace "Toh" Wani murmushi yayi yace "Toh nagode sosai, Allah ya raya sa" tace "Ameen" kamar ance ta juya taga khaleel ya shigo gidan rike da leda, mikewa
tayi da sauri ya karaso har gabanta yana kallonta ya mika mata ledan, ta d'an risina ta karba a hankali tace "Nagode" ya d'an yi murmushi yace "No thanks"
daga haka ya juya ya nufi gate, Aliyu ya bi sa da kallo ko kiftawa babu, khadijah tace "Xan wuce ciki sai da safe" mikewa yayi yace "Toh ina yake, I mean
the boy? Though ban san sunan sa ba" da kamar khadijah baxata ce komai ba sai kuma murya can kasa tace "Sunansa Muhammad, ana kiransa Shureim, sunan late
half dinsa Aliyu ana kiransa Sudais" kallonta yake ko kiftawa babu, ta gyara tsayuwarta tana masa wani kallo tace "Barrister Aliyu... Sunan sa ya ci" daga
haka ta juya ta fara tafiya fuskarta daure, murmushi Aliyu yyi ya bi ta da kallo, can yace "Ohk, wait Iman, nagane barrister Aliyu ne ba ni Aliyun ba"
tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa inda take yace "Toh yana ina yanxu, I haven't seen him since yesterday" tace "Yana gidansu Dr khaleel" shiru yyi
bai ce komai ba, can a hankali yace "Ohk good nyt" daga haka ta juya ta wuce ciki ta rufe kofa. Washegari aka yi sadakan ukun sudais, tun da sassafe Mumy ta
taho da su Siyama da frnds dinta biyu, sadakar wainan shinkafa da Kayan flour ta kawo gidan, Ummun khaleel ma ta xo da jikokinta tare da shureim wajajen
karfe tara, ita ma wainar ta kawo sai lafiyayyen rice and stew da ta kawo ma khadijah da soyayyen kaji a warmer daban, Karfe sha daya Barrister sudais ya
bar gidan kasancewar yana da wani case, ya tura ma khadijah text cewa xai dawo da yamma, karfe sha biyu ummun khaleel ta koma gida tare da su Shureim da
yanxu ya saba da yaran sisters din khaleel amma har Ummu ta gaji da amsa tambayar da yake mata na cewa yaushe sudais xai dawo, shi dai a kai sa wajensa,
tausayi yaron yake bata don tsakaninsa da Allah yake son ganin dan uwan nasa, a ko da yaushe dai ce masa take soon xai dawo, sai kusan azahar Mumy suka bar
gidan, Khadijah ta raka su har gate tayi mata godiya a sanyaye, Mumy ta sa mata albarka sannan suka wuce da yaran nata, kafin dare frnds din Umma suka fara
watsewa gidan, Shaheedah ma suka koma Abuja tare da Sadeeq, gidan ya rage daga Khadijah, sai Nanny da Umma da Wata aminiyarta. Bayan magrib khadijah bna
xaune kan darduma tana azkar kira ya shigo wayarta, a hankali ta daga ta kai kunne ganin barrister sudais ne, yace "Amira xa ki iya fitowa yanxu plss, am
outside" tace "Toh" daga haka ta mike ta fita, sai da ta fara gaya ma Umma sannan ta tafi kofar gida, fitowa yayi daga mota ganinta, yana rike da 3 years
old daughter dinsa, Khadijah ta wara ido tana kallon kyakkyawar yarinyar ta xaga inda yake ta karbeta tace "Waow ya sunanta?" Sudais ya jingina da motar
yace "Ur namesake, ita ma Amira ake kiranta, na kawo ta ne ta gaida Antyn ta" Khadijah tayi murmushi a sanyaye tuno kiran ta da mahaifiyar yarinyar tayi
mata ranan da sudais xai rasu, tana taba dogon gashin yarinyar tace "Naji dadi sosai" Yace "Sure?" Ta kallesa da sauri tace "Eh mana, ko xaka bar min ita"
yar dariya yayi yace "In dai kika shigo gidan ubanta ai taki ce ita" Wani murmushin Khadijah tayi bata dai ce komai ba, yana kallonta a hankali yace "Baxa
ki shigo ba kenan, xaro ido tayi tace " Ka ji na fada haka?" Yace "Uhmn dont forget who is standing before you" ta dauke kai tana ci gaba da murmushi tace
"A barrister" ya shafa kansa yana kallonta a hankali yace "Toh ya k'arin hakurin mu dear?" Tace "Mun gode Allah" yace "Har yanxu shureim din bai dawo gida
ba?" Ta gyada masa kai tace "Bai dawo ba" yace "Ohk, ya su umma?" Tace "Suna ciki" kamar warce ta tuna da sauri tace "Sorry na bar ka tsaye mu shiga ciki"
yayi murmushi yace "Aa bari in yi ta tsayuwa ta" ta turo baki tace "Allah na manta ne kayi hakuri, mu shiga ciki" daga haka ta nufi gate rike da Little
Amira, ya bi ta da ido kafin ya bi bayanta, kan fararen kujerun dake compound din Sudais ya xauna duk yanda tayi da shi ya shiga ya gaida umma ya ki yarda
wai sai gobe, tace "Toh bari in kai mata Little Amira ta gani" yace "Toh sai ki bar ta a can ki dawo ke kadai kar in yi rashin kunya gaban daughter na"
dariya kawai khadijah tayi ta tafi tare da Amira dake ta waigo Abbanta ya daga mata hannu yana murmushi. umma ta xaunar da ita kan kafarta tace "Maa sha
Allah, daughter na mai kyau da ita, Allah ya albarkace ki" khadijah tace "Naga kamar bata magana" Umma tace "A'a don dai bata san mu bane amma wannan ai ta
isa tayi magana" fridge khadijah ta nufa ta bude ta dau ruwa da lemo ta daura kan tray ta sa glass cup sannan tace "Umma ina xuwa" Umma tace "Toh sai kin
dawo" Har khadijah ta iso gun sudais idonsa na kanta, ta ajiye karamin tray din hannunta ta bude drink din ta xuba masa sai dai bata masa ba tace "Ya aiki?"
Ya langwabar da kai yace "Ba dadi, Amira har yanxu you didn't answer my questions..." Ya lumshe ido ya bude yace "Ohk let me leave it this way, you don't
want to answer my question" shiru khadijah tayi tana kallonsa, a hankali yace "A lot of things happened after I left you and the boys Amira, na koma
damaturu gidanmu tare da Mamina amma gaba daya na rasa kwanciyar hankali, i was always sad then, thinking about you and the twins, hankalin Mami ya tashi a
lkcn ta dinga cewa kilan asiri kika min ko kuma aljana ce ke, gashi nan abun na affecting dina, nan tasa aka tayi min rokan Allah, gradually dai na fara
kokarin ganin na mance ku, na cire ku a rai na dinga harkokin gabana... saboda ku ko da ina da aiki a Abuja to baxan je ba, gaba daya na daina xuwa Abuja,
daga Lagos, kano sai Kaduna and other States nake xuwa amma banda abj, dama ni din ba wai ina da time na yan mata bane, jiddah dai ce ita ma a Holland muka
hadu lkcn ina karatu ita kuma tana tare da yayarta dake kasar tare da mijin ta, I never knew ma ashe Mami ta san mum dinta sun yi makaranta daya though it's
not as if they are frnds, to dai a haka na fara neman jiddah har aka sa aurenmu ana saura few months bikin mu na hadu da ke ranan na fito daga gida, Amira
saboda ke nasa aka daga bikin nan har na kusan watanni shiddah, a kwana a tashi kuma na kara neman a daga cos kin kusa haihuwa lkcn, let me make things
brief, at the end fasa auren nayi gaba daya, suka maido min da lefen da na kai all because of you, and happily then Abbana supported me, but bayan rabuwar
ki sai gashi na koma mata cos I don't have any option again, at first kamar baxata yarda ba daga karshe dai a cikin wata daya aka daura mana aure, 2 years
da aurenmu da jiddah Allah yayi ma Mamina rasuwa bayan tayi fama da kidney problem, though before then duk na mata bayanin yanda aka yi na hadu dake, ban
boye mata komai ba, kuma hankalinta ya tashi a lkcn but kawai sai ta maki fatan Allah ya hada ki da dangin mahaifiyar ki, daga nan kuma bata ce min komai
ba, and gaskiya a lkcn kusan na ma cire ku a rai na daina damuwa cox I knw surely Allah na tare da ku, amma kullum sai na maku addu'a every blessed day, ba
tonan asiri ba Amira ni ba wani jin dadin aure nake da jiddah ba, fitinar ta yayi yawa she is always pestering my life, ko kadan bana son hayaniya yana daga
min hankali, bani da rest of mind idan ina gidana, ko irin weekend din nan ma ni na gwammace in tafi office in yi kallo, Amira I need a woman that i will
find peace in, I need a better life partner, ina raga ma jiddah ne kawai saboda yarinyar nan dake tsakaninmu, and divorce is totally out if it baya cikin
tsarin rayuwata, I need you plss Amira" Khadijah taji kanta ya mata nauyi sosai ta rasa abinda xata ce masa, bata san lkcn da hawaye ya dinga sakko mata ba
tana kallonsa, deep down her kuma ta rasa me yasa khaleel ya fado mata.
Shiru Umma tayi tana kallon khadijah, a hankali tace "Ko saboda me?" Khadijah ta langwabar da kai cikin sanyi tace "Umma I will be lonely all alone, I want
him to be by my side" Umma tace "Life with him there won't be esay Khadijah, karatun ki na bukatar natsuwa sosai kin sani, shureim will ba a distraction,
baxai yiwu ba Khadijah" da damuwa Khadijah tace "Umma ai shi ma makarantar fa xai dinga xuwa, plss ummata" Umma tayi shiru alamar bata san me xata ce ba
kuma, can tana ci gaba da linke kayan da take tace "Rabani da shi dai kike son yi koh?" Murmushi Khadijah tayi kunya ya kamata tace "A'a wllh ummata" Umma
tace "Gaskiya ne mana, ke gashi baki kusa da ni, grandson din ma kina son daukesa" Khadijah ta xaro ido, da damuwa tace "Allah sarki Ummata ba haka bane ba
fa" Murmushi Umma tayi tace "Toh shkkn tunda kina son tafiya da shi sai ku je, Allah ya tsare" Sosai Khadijah taji dadi, Umma ta xauna gefen gadon tace
"Yanxu ya xa mu yi da maganar sudais Khadijah, kin ga samu na yayi ya min magana...." khadijah tace "Umma ya san xan koma makaranta ai, daxu ma mun yi
magana da ya xo, kuma kinga 100k da ya bani ai saboda xan tafi makaranta ne" Umma tace "Toh ai ban ce bai sani ba, kin san dai dole sai an je katsina koh?"
Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, bata son jin sunan garin ita kam, Umma ta mike ta ci gaba da abinda take tace "Shi kuma Aliyu ai ya kamata ki sanar
masa xa ki tafi da Shureim din koh, ko kuma kije ma da yaron yayi sallama da mahaifiyar Aliyun" Khadijah dai bata ce komai ba idonta a kan wayarta. Can
gidansu Khaleel kuwa Ummu ta sa driver yyi ma Shureim siyayya da taji tare xa su tafi UK da uwar sa, Khaleel dake xaune bedroom dinta yana duba kayan yace
"Sun gode Ummu" Ummu tace "Khaleel ina son mu yi magana fa da kai, gashi gobe da sassafe xa ku wuce" ya maida hankalinsa gaba daya kanta kamar baxai ce
komai ba, sai kuma yace "Ina ji Ummu" sure ya san kwanan xancen amma yayi pretending bai sani ba, Ummu ta kwantar da murya tana kallonsa tace "Abuu kasan fa
saura wata daya kachal bikin ku da jawahir kuma naji ko magana baka yi" Khaleel ya shafa kansa yace "Ina sane Ummu" tace "Toh Alhmdllh tun da kana sane,
amma ba wani shiri da xa ku yi ne?" Shiru yyi bai ce komai ba, can ya dago ya kalleta yace "Ummu tun da ba laifi bane ina son hada su da mahaifiyar yaron
nan na aura....ina da interest a kanta" Ummu ta dinga masa wani kallo tace "Kana da hankali ma kuwa khaleel???" hade rai yayi, kan kace me ya juya xuwa
Arabiya... toh nan fa ake yin ta, don Mai typing dai ba jin yaren take ba ina laifin ma yayi turanci, tun tana d'an tsintar daddaya har ya kai ya kawo ta
ajiye takardar da Biro kawai ta dafe kai, ganin khaleel fa sai xuba larabci yake a fusace ga ummu sai kallonsa take ta kasa cewa komai mai typing tasan abun
babba ne, ba fans ba, har ita tana son jin abinda khaleel ke cewa don haka ta juya da sauri don nemo kanwarta Ilham ta mata translating, can ita ma ta
sameta xaune tana halinta wato nukurci, ashe dai ba xancen translating din larabci, rai ba dadi mai typing ta kwashi legs ta koma, nan ta ga har khaleel ya
gama jawabinsa yana danna waya amma fuska a murtuke, Ummu ta d'an yi murmushi a hankali tace "Ni na isa khaleel? What am saying in here is that, ina laifin
bayan anyi bikin naku da Jawahir sai ka auri Khadijahr babu mai hanaka yin hakan ae, hakan ma xai fi" Washegari Khadijah ta gama hada few abubuwan da xata
bukata domin komawa UK, umma kuma ta hada ma Shureim nasa kayan cike da jin kewan yaron gashi khaleel ya rabasu da shi tun rasuwar sudais, karfe takwas
saura khaleel ya taho gidan tare da shureim, Khadijah tana bedroom ta gama daukar masa kadan daga takalmansa, ganin na sudais a gun yasa lkci daya mood
dinta ya canxa ta koma ta xauna a sanyaye, tun bayan rasuwarsa dama Umma ta bada komai nasa a gidan saboda Khadijah xata fi samun nutsuwa, takalman ma
mancewa tayi bata bayar ba, Nanny ce ta shigo dakin tace "Khadijah jiran ki fa suke" a sanyaye Khadijah ta mike ta fito rike da takalman Shureim, driver ne
daga gidansu Khaleel xai kai su airport din, Shureim dake jikin Umma ya sakko da sauri ya rungume Khadijah yace "I missed you Anty" ta shafa kansa tace "I
missed you same" Umma tace "Toh kuyi maxa yana jiran ku a mota" Khadijah tace "Yanxu Shureim din ya shigo?" Umma tace "Yanxu ya shigo" Khadijah ta karasa
gun umma ta rungume ta tace "Ummata sai mun dawo" Umma tayi kokarin ganin bata fara hawaye ba a hankali tace "Toh Allah maku albarka daughter, Allah ya
tsare min ku, sannan ki kula da kanki plss" murya can kasa Khadijah tace "Nagode Umma" Nanny na rike da shureim cike da kewarsa xata rakasu bakin motar,
Khadijah na isa bakin kofa ta juyo a hankali tana kallon Umma tace "Toh Umma ba a kai sa yayi ma Mumy sallamar ba kuma, I mean shureim" Umma tace "Lah kin
ga ni har na manta, to ki yi ma Khaleel din magana sai ku fara biyawa can a gurguje ki kai sa kafin ku wuce airport" Khadijah ta gyada mata kai ta fita
parlorn, Shureim ne ya bude back seat Khadijah ta dinga kallon khaleel dake xaune sanye da glasses a idonsa yana operating wayarsa, Shureim ya shiga motar
sannan ta shiga tana daga ma Nanny hannu, gaishe da Nanny khaleel yayi ta amsa da fara'a ta masu Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ta koma ciki. Sai da
suka dau hanya sannan khadijah ta kalli khaleel a hankali tace "Good morning" yace "Morning how was ur nyt?" Ta sauke idonta tace "Alhmdlh" Wayarsa dake
ring ya daga ya kai kunne, sai bayan da ya gama wayar Khadijah tace "Umma tace plss kafin mu tafi in kai shureim wajen mum din Aliyu su yi sallama, idan
suka yi waya tana yawan tambayar ta shi...." Khaleel yace "Ohk then" daga haka ya fadi ma driver anguwar da xai fara kai su, tafiyar kusan minti ashirin
suka yi suka iso gidansu Aliyu, Bayan drivern yayi parking a inda Khaleel ya nuna masa, khaleel ya juya yana kallonta yace "Ku shiga toh" tace "Kai baxa ka
shiga ba" da sauri yace "A'a, am waiting for you two a nan" a hankali khadijah tace "Ohk," daga haka ta bude motar ta sauka tana kallon Shureim tace "Come
down" daga mata hannu yyi yace "Anty ki dauke ni" ta hade rai tace "Sakko my friend" khaleel yace "Ki daukesa mana ko baxa ki iya bane?" murmushi kawai tayi
ta dauki yaron nata ta shiga cikin gidansu Aliyu yana daga ma khaleel da ya bi su da ido hannunsa, A hankali khadijah ta murda kofar taji a bude ta shiga,
babu kowa parlorn, tana jin Shureim na ce mata gidansu wannan uncle din nan nasa ne, tana kokarin sauke sa kasa sai ga Aliyu yana sakkowa stairs, jallabiya
ce baki jikinsa tayi saurin dauke kanta bayan sun hada ido, tana ta tsaye har ya iso inda suke tsaye, ya mika hannu ya karbi shureim komawa baya tayi da
sauri don wani shock ta ji ta dalilin hannunsa da ya taba jikinta, shi kam sai kallonta yake ya maxa ya kawar da memoryn da bai son tunawa a ransa, Murmushi
Shureim yake yana kallonsa yace "Uncle good morning" Aliyu ya shafa kansa shi ma yana murmushin a hankali yace "Morning how are you sweetheart" yace "Am
fine" Kallon khadijah yayi suka kara hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yace "Good morning Iman" kame kame ta fara yi, can tayi saurin cewa "Ina kwana,
wajen mumy muka xo" yace "Ohk tana Bedroom" taki yarda ta sake kallonsa tace "Toh kayi mata magana muna sauri ne" yace "mu je up stairs" daga haka ya fara
tafiya ta bi bayansa xuciyarta na bugawa wannan tunanin da yake ita ma shi take a lkcn. A hankali ya bude kofar dakin mumy ya shiga da sallama, tana xaune
da aminyarta, ta daga kai tana kallon Aliyu, ya sauke yaron hannunsa ya tafi da gudu ya hau kanta yace "Mama good morning" lkci daya bakin cikin dake
tattare da fuskar Mumy yayi fading ta rungume yaron tana murmushi sosai tace "Kai da waye Shureim, wa ya kawo ka" Yace "Ni da Anty na" Aliyu ya juya yana
kallon khadijah da ke tsaye bayansa ta ki shigowa ya koma gefe ya tsaya, Mumy na kallon ta tace "Maa sha Allah ashe tare ku ke, toh ki karaso mana Khadijah"
kanta a kasa ta karaso ciki a sanyaye ta xauna tace "Ina kwana mumy" da fara'a mumy tace "Lafiya lau Khadijah ya gidan, ya su ummar ki?" A hankali khadijah
tace "Suna lafiya Mumy" gaishe da kawar mumy tayi sannan tana kallon mumy tace "Mumy dama xan koma karatu ne kuma xa mu je da shureim shine Umma tace in
kawo sa yayi ma ki sallama" Mumy tace "Allah sarki, amma naji dadi sosai wllh, Allah ya kai ku lafiya, ya bada abinda aka je nema" kallonta Kawai Aliyu yake
jin abinda ta ce, Mumy ta mike tace "Bari in kai sa su gaisa da Abba yana nan" daga haka ta fita, Hajiya Salma dake ta kallon khadijah cike da tausayinta
tace "Allah ya bada nasara kin ji Khadijah, sai a kula sosai" Khadijah ta sunkuyar da kai kasa tace "In sha Allah Mum na gode" Bayan kusan minti goma Mumy
ta dawo, duk khadijah ta damu saboda khaleel da ta bari a mota, Mumy tace "Toh mu je kema ku gaisa da Abban koh" khadijah ta kasa dago kanta ta mike da kyar
ta bi bayanta har xuwa side din Abba, da fara'a ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mutanen gidansu, ba su dau lkci a parlorn ba suka fito tare da mumy, Lkci
daya mood din mumy ya canxa a hankali tace "Mu shiga ki gaida iklima" Khadijah tace "Toh" daga haka ta bi mumy suka shiga dakin. Kallon iklima kawai
khadijah take ganin yanda ta rame kamar warce ta shekara tana ciwo, cike da karfin hali tace "Sannu iklima Allah ya sauwake" kallonta kawai Iklima take ita
ma ta kasa cewa komai, Mumy na kallon khadijah tace "Mu je" Khadijah ta bi bayan mumy a sanyaye, Mumy tace "Babu daman in baki turarruka tunda flight xa ku
bi Khadijah, amma kar ki damu xan tura ma Maryam kudi a can ta siya ma ki, sai tayi ma Shureim ma shopping" murmushi kawai khadijah tayi tace "Ba komai mumy
na gode" Har downstairs mumy ta rakata, Aliyu dake xaune parlorn tare da shureim ya mike ganin sun sakko, mumy tace "Toh Allah ya tsare, nagode Khadijah"
Khadijah tace "Ameen mumy" daga haka ta bi bayan Aliyu da shureim don har sun nufi kofa, a tsakar compound din Aliyu ya jira Khadijah ta iso inda suke, bata
yarda ta kalle sa ba xata wuce su ya riko mayafinta, juyawa tayi amma ta kasa kallon idonsa, murya can kasa yace "Baxa mu yi sallama ba?" Still ba tare da
ta kallesa ba tace "Mumy na xo yi ma sallama ba kai ba" yayi murmushi yace "Ohk, Allah ya kiyaye hanya, sai mun hadu a can, cos am also leaving tomorrow"
Khadijah bata tanka sa ba yana rike da shureim har suka nufi gate, kasa daurewa tayi daga karshe tace "Me ya samu iklima haka?" Da kamar Aliyu baxai ce
komai ba sai kuma yace "She is suffering from Hiv" Khadijah ta xaro ido tana kallonsa a tsorace, yace "Yea, anjima dangin mahaifinta xa su xo su tafi da
ita..." Lkci daya hawaye ya cika idon Khadijah tace "Toh Anty khadijah fa?" Yace "Tana asibiti, tot kin san tayi hatsari?" Khadijah ta girgixa kai tana
kallonsa, yace "She had accident 2 weeks back" da damuwa tace "Toh ya jikin nata?" Yace "Ni tun lkcn da na kai su mumy ban san ke komawa ba so I don't knw"
Khadijah tayi shiru duk jikinta a sanyaye, Aliyu yyi murmushi bai ce komai ba har suka fito waje, Khadijah ta bude back seat tana kallon khaleel da damuwa
tace "Don Allah kayi hakuri mun bata maka lkci" ya d'an yi murmushi yace "No problem" tun da Khalil ya kalli Aliyu sau daya bai sake kallonsa ba, Aliyu yace
"Barka da asuba" sai a sannan khaleel ya kara kallonsa yace "Good morning" Shureim ya shiga mota yana daga ma Aliyu hannu sannan khadijah ma ta shiga, suna
hada ido da Aliyu ta sunkuyar da kanta, Aliyu na kallonta yace "Allah ya tsare" Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ameen" ya rufe masu motar, driver
ya tada motar suka bar layin, shureim ya fiddo bandir din Dari biyar a aljihunsa yana nuna ma Khadijah yace "Anty wannan Papa din nan ya sa min kudin a
aljihuna, I told him no but he didn't even listen to me" Khadijah ta dinga kallon kudin, ya ciro wani kudin yana nuna mata yace "Uncle ma ya bani wannan"
Khaleel dake danna wayarsa bai dai ce komai ba, Khadijah ma ta rasa abinda xata ce.
Khaleel na rungume da Shureim suka sakko daga cikin jirgi hannunsa daya rike da trolley din yaron, Khadija na biye da su har suka iso gun da xa su hau taxi,
khaleel ya juya yana kallonta ganin yanda tayi laushi alamar ta gaji, murmushi yayi ya dauke kai, ta turo baki ta rungume hannayen ta, a Booth din taxin ya
ajiye trolleyn hannunsa, ta karaso a hankali ta ajiye nata jakar a ciki, ya xaga ya shiga back seat ita ma ta shiga ta rufe, sai a sannan yana kallon mai
taxin yace "Bridge street" har suka iso gida idon Khadija a lumshe suke, khaleel ya bude motar ya fito ya dau Shureim dake ta bacci, sai a sannan ta bude
idanuwanta yace "Ae da mai cab din ya wuce da ke" ta bude side dinta ta fito, Ya fito da jakunkunan sannan ya ba ma mai taxin kudi, na Shureim ya dauka ta
dau nata ta bi bayansa, suna isa bakin apartment dinsu, ya juya yana kallonta yace "Hope baki mance makulli ba" karamar jakar hanunta ta bude ta dubo
makulin, ya fara bude nasa sannan ya amshi nata makullin ya bude mata yana kallonta, hannu ta kai xata amshi Shureim dake bacci jikinsa yace "Hey, ai ba
gudu xan yi da shi ba hajiya" Wani kallo tayi masa ta wuce ciki ta rufe kofarta, duk yanda ta so ganin ta tsaftace ko ina kafin ta huta kasa yin hakan tayi
don wani bacci ta dinga ji, wanka kawai tayi ta sauya kaya tayi slh sannan ta cire bedsheet din kan gado ta shimfida wani sannan ta kwanta, nan da nan bacci
ya dauketa. Cikin bacci ta ji ana tashinta ta bude ido a hankali ta ga Shureim kusa da ita yace "Anty, uncle yace in tashe ki kiyi sllh ki ci abinci" mikewa
xaune tayi tana kallon agogo taga bakwai na yamma ya wuce, ta kalli Shureim tace "Have you eaten?" Yace "Ehh uncle ya siya min, naki ma yana parlor" Shiru
tayi tana kallonsa sai kuma tace "Kayi wanka?" Gyada mata kai yayi, ta sauka daga kan gadon tace "Bari in yi alwala" Ko da ta fito daga bayin bata ga
Shureim ba, tayi sllh sannan ta fara gyare gyaren gidan tun daga dakin har parlorn, ta tsaftace ko ina tayi mopping sannan ta koma daki don dauko wayarta
sanin Umma xata yi ta kiranta, mis cals biyu ta ga nata da na Barrister sudais, Umma ta fara Kira bayan sun gaisa Umma tace "Kun sauka lafiya?" Tace
"Alhmdllh Umma" Umma tace "Ina Shureim din?" A hankali Khadija tace "Yana can wajen khaleel" Umma tace "Toh Ina gaishesa, ki kula kin ji ko daughter?"
Khadija ta gyada mata kai tace "In Sha Allah Umma" Umma tace "Toh Allah maku Albarka" Khadija ta amsa da "Ameen" daga haka suka yi sallama da Umma, Sudais
ta shiga kira, bayan wani lkci ya katse ya kirata, A hankali tayi masa sallama bayan ta daga,ya amsa yace "Ina kika shiga Amira?" Ta langwabar da kai tace
"Bacci nayi" yace "Ohk, ya hanya?" Tace "Alhmdllh ya takwarata?" Yace "She's good, where is my son?" D'an murmushi tayi tace "Yana waje" yace "Waje kuma,
babu sanyi ne?" Tace "Akwai amma it's not much" yace "Ohk try and get him a lot of sweaters, the cold won't be funny from next week I guess" tace "Haka ne"
yace "Xan tura maki kudi sai ki siya masa very thick one's, kema ki siya" murmushi tayi bata ce komai ba, yace "Alryt then, sleep tight dear" tace "Toh
nagode ka gaida min Amira" yace "Xata ji" daga haka ya katse wayar, kwanta tayi a hankali ta lumshe ido tana tuna moment dinsu da Barrister sudais, tashi
tayi daga karshe duk a sanyaye ta fita parlor, abincin da khaleel ya siyo mata dake kan center table ta bude don ganin wani iri ne, ta d'an tabe baki ta
rufe ta mike ta shiga kitchen ta kunna wuta, noodles ta fiddo xata dafa, jin motsi a waje ta leka window a hankali, xaune ta gansa kan kujera yana sanye da
glass idanuwansa kan wani babban textbook yana rubutu, babban sweater ne jikinsa da neck warmer, Shureim ma dake sanye da sweater da head and neck warmer na
tsaye daga bayansa ya jingina jikinsa yana kallon abinda yake yi, a hankali khaleel ya juyo ganin ta kunna wutan kitchen suka hada ido tayi saurin dauke
kanta, mayar da dubansa yyi kan littafin gabansa yace "Xa ki fara koh?" Ta hararesa tace "Xan fara me?" Yace "Kin fi ni sani ai" Bata tanka sa ba ta bar
wajen ta shiga yin abinda ya kawo ta kitchen din. Tana gama dafa indomien ta dauka ta fita ta koma parlor. Tana xaune parlor Idonta na kan wani material din
karatun ta misalin karfe goma saura aka danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta tsaya, a hankali tace "Yes?" Muryar khaleel taji yace "Hmm koh?" Bude kofar
tayi ya shigar da Shureim parlorn ta yace "Alryt good nyt" tace "Allah ya tashe mu lafiya" juyawa yayi ya koma apartment dinsa, ta rufe kofarta ta kama
hannun Shureim ta kashe wutan parlorn ta wuce daki tana rike da shi tace "Me yasa baka yi bacci can ba" yace "I said I want to come to you" bata ce komai ba
ta rufe kofar dakin bayan sun shiga ciki. Washegari da safe Shureim na bacci ta fita xuwa supermarket, har ta dawo bai tashi ba ta ajiye duk abubuwan da ta
siyo ta fara hada breakfast, muryar khaleel taji daga waje yace "Good morning" ta yi still don bata san yana gun ba, can dai tace "Ina kwana?" Yace "Hamdan,
Ina kika je da sassafe cikin sanyin nan?" Ta d'an bude ido tace "Gadi na kake yi kuma?" D'an murmushi yyi jin bai ce komai ba ta leka window a hankali, 3qtr
ne jikinsa da sweater mai hula yana tsaye bata dai ga abinda yake ba, kallonsa kawai take, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, takowa yyi har gun
windown yana kallonta yace "Ina kika je?" Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta Sauke idonta kasa a hankali tace "Market" yace "What did you get?" Ta hade
rai tace "Ina ruwanka" yyi murmushin sa mai kyau ya sauke hular kansa yace "Ohk then" daga haka ya juya ya bar wajen, Irish ta soya da kwai sai ruwan Lipton
da ta dafa da kayan kamshi, har xata fita kitchen din ta dawo, ta fi minti biyu a tsaye kamar mai contemplating abinda xata yi, kawai daga karshe ta dau
wani warmer ta debi Irish din da kwai ta xuba ruwan Lipton din a wani karamin flask ta ajiye su a gefe ta fita kitchen din, Bedroom dinta ta wuce ta tada
Shureim dake bacci ta wuce bathroom da shi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta sa yayi alwala suka fito, sai da ta gama shiryasa sannan ta shimfida
masa darduma tace "Idan ka gama sllhn meet me at the parlor" daga haka ta fita, ba a dau lkci ba ya fito yace "Anty na gama, good morning" tace "Morning
dear" kitchen ta tafi ta dauko flask din Lipton din ta mika masa tace "Ka kai ma uncle sai ka dawo ka karbi dayan" yace "Toh" ta bude masa kofa ya fita, ta
danna bell din apartment din khaleel sannan ta juya ta koma ciki da sauri, Shureim na tsaye bakin apartment din khaleel ya bude kofar, dukawa yyi yana
kallon yaron murmushi dauke fuskarsa yace "Good morning handsome" Shureim yace "Good morning uncle, Antyna tace in kawo maka" karba yyi yana kallon flask
din sannan ya jawo yaron ciki, Shureim yace "Uncle tace it's remaining one" rufe kofar yayi yace "Kyaleta xata kawo da kanta" Khadija tayi ta jiran dawowan
Shureim amma shiru, mikewa tayi ta bude kofa ta leka waje a hankali taga kofar apartment din nasa a rufe, kiran Shureim ta shiga yi, Shureim dake xaune yana
cin bread and butter da khaleel ya basa da shayi ya mike da sauri yace "Uncle Anty is calling me" xaunar da shi yyi yace "Don't worry she will come in now"
Khadija ta gaji da tsayuwa amma Shureim bai fito ba, komawa ciki tayi ta rasa yanda xata yi da Irish da ta dibar ma khaleel, daga karshe ta wuce kitchen ta
dauko ta sa hijab ta fito waje, tsaye tayi tana kallon baturiyar dake bakin apartment dinsa, baturiyar ta mata murmushi tace "Good morning" dauke kai
Khadija tayi kamar ana tilastata tace "Morning" xata koma ciki sai gashi ya bude kofar, Kallon Khadija yayi kafin ya dubi baturiyar dake masa murmushi tace
"Good morning Dr Ayman...." Juyawa Khadija tayi ta shige apartment dinta ta rufe, Khaleel na kallon baturiyar yace "Morning Lydia, hw did u knw I am back?"
Tace "I just met with Dr Ahmad, he told me you are back" shafa kai khaleel yayi a hankali yace "Ohk, we will meet later in the day, I am about going out
now" tace "Ohk do you mind dropped me?" Ya girgixa kai yace "You get a taxi" daga haka ya rufe kofarsa, yana ta tsaye bakin kofa bayan kusan minti biyar ya
bude kofarsa ya ga ta wuce, fitowa yayi yana kallon kofar Khadija, a hankali ya murda ya ji a bude ya shiga parlorn.
Not edited.🤷🏻♀
Khaleel ya fi minti biyar tsaye parlon yana jiran ganin ta inda xata fito amma bata fito ba, karasawa yayi kan kujera a hankali ya xauna ya jinginar da
kansa jikin kujerar ya lumshe manyan idanuwansa, bayan wani lkci sai ga ta ta fito daga daki da hijab a jikinta, mikewa yyi yana kallonta amma bai ce komai
ba, Babu yabo babu fallasa tace "How may I help you?" Yana shafa lallausan gashin kansa a hankali ce "Where is.... the food?" Tace "Wani abincin? I didn't
cook with you ai" ya d'an kalleta na few seconds sai kuma ya nufi kitchen cikin takunsa na kasaita ta bi sa da ido, rike da warmer din Irish din ya dawo
yana dubanta yace "This" daga haka ya bude kofa ya fita ta bi sa da harara ta ja tsaki. Khadijah na ji suka fita gidan da Shureim wajen karfe goma, kafin
sha daya ta gama duk abinda xata yi a gidan ta kwanta duk da ta so tafiya makaranta amma ta bari gobe kawai, ganin bacci ya ki xuwa mata ta dauko kayan
karatun ta ta shiga yi, tana ta xaune har azahar yayi, ta mike daga karshe ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta kwanta, lkci daya
bacci ya dauketa. A hankali khadijah ta bude idonta bayan wasu awanni ta mike xaune cikin sanyin jiki tana tunanin mafarkin da tayi, bell taji an danna
wanda hakan sai da ya d'an tsorata ta, bayan wasu yan dakiku ta mike tsaye da kyar har lkcn mafarkin ya kasa fita a xuciyarta, jin an kara danna bell din ta
sa hijab ta fita kamar mai counting steps dinta, tana isa gun kofar ta bude a hankali, Vanessa da Angela sai Maryam ta gani bakin kofar, sosai gaban Khadija
ya fadi ganin Maryam bakin kofar, da farko kallonta ta dinga yi, sai kuma ta kirkiri murmushi tana masu sannu da xuwa ta basu hanya suka shigo parlorn,
mamaki ta dinga yi a ranta, me ya kawo Maryam gidanta, after all she isn't her course mate nor her frnd, bayan sun gaisa suka mata gaisuwar Sudais, khadijah
ta mike ta wuce kitchen don kawo masu ruwa da cakes din da ta siyo daxu da safe da ta fita, Maryam na kallonta tace "Mumy tace da daya twin din kika taho
koh?" Ba tare da Khadija ta kalleta ba tace "Ehh tare muka xo" Maryam tace "Yana Ina?" Khadija tace "Ya fita ne" Maryam bata sake cewa komai ba, Khadija
suka dinga hira da su Vanessa, sai dai hirar duk ta makaranta ce bayan kusan minti talatin suka ce mata xa su koma, har waje ta rakasu inda xa su samu cab,
wani cab ne yyi parking dai dai su, aka bude cab din khaleel ya fito tare da Shureim da wani leda hannunsa, kallonsa kawai Maryam take, ya wara ido ganinta
yace "Isn't this Maryam?" Yar dariya tayi tace "A nan anguwar kake dama Dr khaleel?" Yace "Sure, me kika xo yi nan?" Ta nuna masa Khadija tace "My frnd, mun
xo mata gaisuwa ne yaron ta ya rasu" ya kalli khadijah yace "Ohh that's nyc, a schl kika santa kenan" Maryam tace "Eh a schl na santa" yace "Good" Maryam ta
karasa gun Shureim tana kallonsa a hankali tace "Hello boy" gaisheta yayi, ta amsa tana murmushi jin muryarsa kamar na Aliyu, Su Vanessa ma suka taho gunsa
duk ya gaishe su da turanci, ita dai Khadijah na tsaye, Khaleel na kallon Maryam yace "Alryt bari in shiga ciki Maryam, sai anjima" tace "Yauwa Dr, ya
mutuniyar fa?" Har ya fara tafiya ya tsaya yace "Wai jawahir?" Tace "Ehh" yace "Haba ai ke ya kamata in tambaya, kun fi kusa" Maryam tace "Au haka ma xaka
ce" Yace "Yes, nasan yau ma baxa ku rasa waya ba ni kam bata kira ni ba" Maryam tace "Lallai ma, ita ce ma xata kira ka kenan, soon ma xa su xo hutu nan da
yayarta ar" Khaleel ya d'an kalleta yace "Really?" Girgixa kai Maryam tayi tace "Dad dina naji ya fadi haka nima" Ya dauke kai ya nufi cikin gida yana rike
da Shureim yace "Allah ya kawo su lafiya" Taxin da Khaleel ya sauka suka hau Khadija ta daga masu hannu tace "We'll meet in school tomorrow, thank ya all"
daga haka ta wuce ciki. Khadija na kitchen tana girkin lunch khaleel ya taho ya tsaya gun window yana kallonta yace "Ya kike?" Dauke idonta tayi daga
kallonsa tace "Lafiya lau" Shureim dake kusa da shi a tsaye yace "Anty I am missing you" Khaleel yace "Bude masa ya shiga" kallon Shureim tayi sannan ta
ajiye wukar hannunta ta isa gun kofar ta bude, Khaleel ya shigar da Shureim ciki sannan ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, ya jawo kofar ya rufe gam, ya
jinginar da ita jiki yana mata wani kallo murya can kasa yace "Ni kike daga ma hanci" A tsorace tace "Kaga bana son haka ka bari, ka kyaleni plss" Duk ta
kasa kallon idanuwansa da ya tsare ta da shi ga kamshin sa da ya cikata, A hankali yace "Fushin me kike yi da ni?" cikin rawar murya tace "Toh Fushin me xan
yi da kai Dr, don Allah ka sakeni" d'aga kanta yayi tayi saurin runtse idanuwanta xuciyarta na bugawa, ya dinga kallon lips dinta, a hankali ya saketa yace
"Where did you know Maryam from?" Ta shiga kokarin bude kofarta da sauri, ya rike handle din kofar yace "Au Ina maki magana xaki wuce?" Ta juyo kamar xata
yi kuka tace "Ni ban santa ba sosai fah, kawai ina ganinta ne a schl kawar course mates dina ce" yace "Ohk, don't frnd her for some reasons kin ji?"
kallonsa tayi da sauri, lkci daya tayi saurin kauda kanta xuciyarta na bugawa, his eyes are always not encouraging, d'an murmushi yayi a hankali yace "Ki
gaya min meye da idona Khadijah?" Ta hade rai tace "I don't like them" wani murmushin yyi kamar me rada yace "Xan koya maki son su" murda kofar yayi ya bude
ta juya da sauri ta shige kitchen din ta rufe kofar da makulli fuskarta daure. Shureim na cin abincin da ta xuba masa bayan magrib yace "Anty uncle yace
gobe xan fara xuwa schl, we even went to the schl, uniform din na gidansa, in je in karbo?" Khadija dake ta kallonsa tace "I didn't send you" yace "Ohk"
sannan ya ci gaba da cin abincinsa. Washegari da asuba khaleel ya miko mata uniforms din Shureim ta kitchen, rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta karba
tana kallonsa a hankali tace "Mun gode" ko kallonta bai yi ba ya wuce. Karfe takwas saura khaleel yayi dropping Shureim a makarantar da yayi enrolling
dinsa, Khadija dake xaune bayan motar ta bi Shureim dake daga mata hannu da kallo har aka wuce da shi cikin makarantar, khaleel yayi parking in da ya saba
ajiye ta a schl ya juya yana kallonta, ta bude motar a hankali ta fito,, bata ce komai ba ta kulle motar ya ja motarsa ya bar wajen, a sanyaye ta karasa
department dinsu don saura few minutes a shiga lectures. Karfe sha biyu saura Khadija ta fito daga lectures, cafeteria ta tafi ita kadai ganin Maryam na
tare da su Vanessa, tana xaune ita kadai a cafterian da lemonade a gabanta idonta a kan wayarta tana dannawa, kujerar dake kallon nata taga an ja ta daga
kai da sauri, sosai gabanta yayi mugun faduwa bayan sun hada ido, tayi saurin dauke idonta, xaunawa yayi yana kallonta a hankali yace "Hi Iman" kasa cewa
komai tayi ta kuma kasa dago kanta, bayan few seconds ta dago da kyar tana dubansa tace "Hello" Murmushi yayi yace "Ya boko?" Kasa amsawa tayi lkci daya
little Sudais dinta ya fado mata, taji xuciyarta ya mata rauni, ganin tayi shiru ya fiddo wayarsa ya fara dannawa, a hankali tace "Ya su mumy" yace "Na baro
su lafiya, how is Shureim?" Tace "Yana schl" yace "Har kinyi enrolling dinsa a nan?" Tace "Ehh" shiru ya d'an yi, kafin a hankali yace "How much did you
spend Iman?" Ta kallesa lkci daya ta hade rai tace "What about it?" ya girgixa kai da sauri yace "Ohk, I am sorry I asked" bata ce komai ba, ya mike yana
kallonta yace "Alryt, I will be on my way now Iman, my regards to Shureim" da ido ta bi sa, har ya tafi ya dawo da sauri ya sa hannu a aljihunsa yace "I
think I've got something here" Chocolate guda daya ya fiddo ya duka yana kallonta ya mika mata yace "Ki ba Shureim plss" a hankali ta sauke idonta daga
kallonsa ta karbi chocolate din tace "Ohk" yace "Thanks" daga haka ya mike ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya bace mata, kallon chocolate din hannunta
tayi ta bude jakarta ta saka a ciki, tayi tagumi tana tunanin me yasa in dai ta ga Aliyu sai little Sudais dinta ya fado mata, or is it because of the
resemblance, jin wayarta na ring ta sauke kai a hankali tana kallon mai kiran nata.
Sorry for the short chappy kilan in kara post around one na dare😦
A hankali khadijah tayi picking wayar ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren ya amsa yace "Ya kike Amira?" Khadija tace "Alhmdllh ya aiki?" Yace
"Lafiya lau, account number ki xa ki turo min yanxu" shiru ta yi na wani lkci kafin tace "Barrister.... Shureim fa yana da kayan sanyi, wllh you shouldn't
bother...." Katse ta yayi yace "I am not asking for you opinion Khadijah" a hankali tace "Toh shkkn, ya Amira fah?" Sudais yace "Tana gun ummanta" bai
karasa maganar ba ya ga jiddah tsaye kusa da dinning din da yake xaune tana kallonsa, ya dauke kansa yace "I will call you later Amira" katse wayar yayi ya
ajiye, jiddah tayi dariya tana tafe hannu tana masa wani kallo tace "Cin amanar har cikin gidana Aliyu?" Sudais bai kalleta ba balle ya tanka ta, lkci daya
idanuwanta suka kankance tace "Toh ko ma wace yar iskar ka samu wlh wlh sai tayi da ta sanin sanin ka a rayuwar ta, sai na nuna mata tayi kadan tayi kishi
da ni, ba ma xai yiwu bane, mu xuba da ita sai dai idan ba mijina take cusa ma kanta ba" mikewa yayi yana kallonta yace "Wannan da kike gani wllh ta fi ki
k'ima a idanuwana Jiddah, kuma kina nan xaki ga ta shigo gidan nan ta koya maki yanda ake kula da miji" bai sake sauraranta ba ya bar parlorn, jiddah ta
kasa tsaye gu daya, ta ja kujera ta xauna da kyar xuciyarta na tafarfasa, lkci daya tayi wani murmushi tace "Babu boka babu malam, amma kai xaka bata
shawarar ta rabu da kai, mu dai je xuwa, da kuluwa take xancen" Har khadijah ta iso gun motar khaleel idonta na kansa, shi kuma yana jingine jikin motar
yana danna waya, bai san ta iso ba kawai kamshin ta ya ji, ya daga kai yana kallonta, a hankali tace "Good evening" ya mayar da wayar aljihunsa yace "Ya
lectures?" Tace "Alhmdllh, karfe nawa su Shureim ke tashi?" Ya buda ido yace "Ke fa yarinyar nan baki da kara" turo baki tayi tace "Toh me nayi, am just
asking" yyi murmushi yace "Daga nan xa mu dauko sa, yanxu suke tashi su ma" ta karasa ta bude front seat ta shiga, shi ma ya shiga motar ya tada suka bar
wajen, har suka iso makarantar shureim khaleel bai ce komai ba ita ma haka, ya bude motar ya fita, ba a dau lkci ba suka dawo tare da Shureim, xagayowa
Shureim yayi ya bude inda khadijah take xaune ya rungumeta yace "Anty good afternoon" ta shigo da shi cikin motar ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa
da murmushi tace "How you sweetheart?" Yace "Fyn Anty, I love the schl, I wish Sudais will come here also, am really missing him" Khadija bata ce komai ba,
inda sabo ta saba, don bbu ranar da xai wuce Shureim baxai mata xancen Dan uwansa ba, he is always wishing Sudais is with him, lkci daya chocolate da Aliyu
ya bata ya fado mata, ta bude jakarta a hankali ta fiddo chocolate din ta mika masa, karba yyi cike da jin dadi yace "Waow, Anty ke kika siya min?" Girgixa
masa kai tayi tace "No" ya wara ido ya juya yana kallon Khaleel dake driving yace "Uncle kai ka siya min?" Khaleel ya kallesa yyi murmushi yace "No bani
bane" Shureim ya mayar da dubansa kan Khadija yace "Toh Anty waye ya siya min" Khadijah tace "Idan baxa ka ci ba bani in cinye" Shureim ya bude chocolates
din yace "Noo Anty ina so, ai irin wanda kind uncle din nan yake ba mu a gidansu maman nan ne, he told me his name is Dr Aliyu, Anty ina son a kai ni
gidansu a Nigeria" Ita dai khadijah kallon yaron kawai take, ya gutsura ma khaleel ya mika masa yace "Uncle taste it" khaleel yyi murmushi yana girgixa kai
yace "Noo thanks son, cinye abun, ko Anty kar ka ba" dariya yaron yayi bai ce komai ba, can ya kalli Khadija, alama yayi mata da ta bude bakinta, tayi
murmushi ta bude masa bakin ya sa mata chocolate din a hankali yana satan kallon Khaleel. Suna isa gida bayan khaleel yyi parking khadijah ta bude motar ta
fito tare da Shureim tana kallonsa murya can kasa tace "Thank you" fitowa yayi yana mimicking din muryarta yace "Thank you" daga haka ya rufe motarsa,
hararansa ta fara yi sai kuma tayi murmushi ta wuce apartment dinta rike da hannun Shureim, ya jingina da mota ya rungume hannayensa ya bi su da kallo. Tun
da Khadijah ta fito daga lectures yau take xaune cafteria ta rasa dalili, har lkcn lectures din karfe biyu yyi tana xaune gun bata tashi ba, Maryam ce ta
shigo cafterian tare da wata kana ganinta kasa yar Nigeria ce, Maryam na ganin Khadijah tayi murmushi tace "Khadijah kina nan ashe, ya lectures?" Khadija
tace "Alhmdllh ya naki?" Maryam tace "Alhmdllh" Maryam ta kalli yarinyar dake gefenta tace "Deejah meet ur namesake Khadija, tana studying pharmacy ne a
nan, she is also a Nigerian from kaduna" Warce Maryam ta Kira da Deejah tayi murmushi tace "Its nyc meeting you namesake" Khadija tayi murmushi sosai tace
"Nyc meeting you too" gun Khadija suka xauna su biyun, Maryam tace "Sun xo hutu ne nan da kanwarta shine na shigo da ita taga Cambridge" Deejah na kallon
Maryam tace "Khadijah tana min kama da Safeenah, ko ke baki gani ba" Maryam ta kalli Khadijah da kyau, sai kuma tayi dariya tace "Suna dai yanayi ba kama
ba, and the nose..." Deejah tace "Exactly, dama Ammi xata ganta cewa xata yi Safeenah ce" ita dai Khadijah bata ce komai ba banda murmushin da take yi, haka
kawai taji tana son Deejah.... drinks da snack Maryam ta sa a kawo masu su uku, Maryam na shan drink din gabanta tace "Deejah wai me yasa jawahir ta ki biyo
mu?" Khadijah ta daga kai tana kallonsu, Deejah ta tabe baki tace "Kilan kar su hadu da Dr Ayman" Maryam tace "Tab, Ayman sau biyu yake shigowa makarantar
nan a sati, Mondays and Thursdays, I think ranakun yake nasa karatun" Maryam ta kalli Khadijah tace "Kingakiwa neighbor dinsa ce Khadijah fa" Deejah ta
kalli Khadijah da sauri tace "Haba dai" Maryam tayi dariya tace "Wlh, ranan da naje gidanta tare da frnds dinmu na gan sa, yace min nan yake" Deejah tace
"Wani anguwa kenan?" Maryam ta fada mata anguwar tana cin snack din hannunta, Deejah tace "Ayya, daxu dai naji da suka yi waya jawahir ta bashi address yace
xai je anjima da yamma" Maryam tace "Gidan mu?" Deejah tace "Sure" Maryam tace "Ohk ai gwara dai ya je" Khadijah ta mike tana murmushi tace "Maryam xan
shiga lectures yanxu" Maryam tace "Haba to baki dau snack din ba ai da drink" Khadija ta kirkiri murmushi ta dauka tace "Toh nagode" daga haka ta bar
cafteria din bayan tayi ma Deejah ma sallama, Deejah ta bi ga da ido, kafin ta kalli Maryam tace "Maryam joke apart wllh kamar Safeenah, idan kin lura har
da Maimoon ma suna yanayi, Maryam tace "A coincident" wani gun Khadija ta tafi ta xauna don sun cika mata kunne da surutu ne gaskiyar magana. Tana ta xaune
nan har khaleel ya kirata bayan kusan awa daya, tana ta kallon Kiran kafin ta daga yace "Are you done with lectures Khadijah?" Girgixa kai tayi tace "No,
idan na gama xan taho gida, kawai ka tafi" yace "Karfe nawa xa ku gama?" Turo baki tayi da kamar baxa tace komai ba sai kuma tace "Anjima" yace "Toh Ina
jiran ki" daga haka ya katse wayar. Karfe hudu saura Khadijah ta isa gun da Khaleel ke jiran ta, fuskarta daure ta bude motar a hankali ta shiga, yana
kallonta yace "Ya lectures?" Kamar ana tilastata tace "Fyn" sai bayan da suka bar cikin makarantar yace "Wa ya bata maki rai?" Shiru tayi bata ce komai ba,
bai sake cewa komai ba har ya isa schl din Shureim ya fita ya daukosa ya dawo sannan suka dau hanyar gida, a waje yyi parking yana kallon Khadijah da ta
bude motar ta fita, Shureim ma ya fito, yace "Am going somewhere now, sai na dawo" Khadija ta d'an buda ido tana kallonsa tace "Gun jawahir din ne
somewhere??" Kallonta ya dinga yi da mamaki, ta tabe baki tace "Wai somewhere...." daga haka ta kama hannun Shureim suka wuce ciki, shafa kansa yayi ya tada
motar yayi reverse ya bar wajen. Da daddare Khadijah na parlor aka danna bell, ta mike ta isa gun kofar tace "who is there" yace "Somebody" bude kofar tayi
tana kallonsa ya mika mata ledan hannunsa yace "Ki ba Shureim?" Bata karbi ledan ba tace "Yayi Bacci" yace "Toh ki ajiye masa" Bata yarda ta kallesa ba ta
amshi ledan daga haka ta rufe kofarta. Washegari da sassafe Khadija ta fito apartment dinta tare da Shureim da tayi ma Shirin makaranta, ganin waje xa su
fita Shureim yace "Anty baxa mu jira uncle ba yau" hararansa tayi bata ce komai ba har suka fita ta tsayar masu da cab, sai da ta fara dropping dinsa schl
sannan ta wuce nata makarantar. Tare da su Vanessa suka fito daga lectures misalin karfe sha biyu, tun daga nesa ta hangosa da wani bature suna tahowa, har
ya iso inda suke xaune bai gansu ba yana magana da baturen Khadijah ta dinga kallonsa har suka wuce, still ta bi sa da ido, muryar Vanessa ne ya dawo da ita
tana cewa su je su ci abinci, mikewa tayi a hankali suka bar wajen xuwa cafterian da suka saba xuwa, xaune ta ga Aliyu da Baturen a ciki, suna shigowa kuma
ya ganta, ta dauke idonta daga kallonsa bayan sun hada ido, waje daya suka xauna tare da su Vanessa, Vanessa tayi masu ordering abinda xa su ci, drink kawai
Khadija ta sa aka kawo mata, duk suka gama cin abincin Vanessa ta biya bill sannan suka mike, Khadijah dai na xaune bata tashi ba, Vanessa tace "Ain't you
attending the next lecture?" Khadijah tace "I will be going home soon" Tana kallon su Vanessa suka wuce, dai dai lkcn da Baturen dake tare da Aliyu ya mike
shi ma ya fita, tasowa Aliyu yyi ya dawo inda take ya ja kujera ya xauna yana kallonta yace "Good afternoon" ba tare da ta kallesa ba tace "Same...." Ya
shafa kansa yace "Ya Shureim?" Tace "Yana schl" yace "Ohk kin gama lectures yau ne?" Girgixa kai tayi tace "Aa xan wuce gida ne" yace "Ohk, yanxu?" Sai a
sannan ta kallesa tace "Soon" yace "Alryt if you are ready mu je sai in yi dropping din ki" tace "I prefer cab" yace "Ohk then," wayarsa ya mika mata yace
"Sa min digit din ki anjima da yamma xan kawo maki sakon Shureim or I give Dr.. Ayman, Maryam tace min same house ku ke da shi, and I saw him a gidanmu
jiya" Khadijah bata ce komai ba da farko, can dai tace "Sakon me?" Yace "Shine xan bada a kai maki ai" Ta Girgixa kai ta karbi wayarsa ta na sa number ta
tace "You call me instead" daga haka ta mayar masa da wayarsa, ita ta fara mikewa kafin shi, ya bi bayanta suka
fita cafterian, sai da suka isa gun motarsa ya kalleta yace "Let me drop you Iman"
Bude mata motar Aliyu yayi yana kallonta, ta ki kallonsa tana dai tsaye kamar me contemplating ta shiga ko kar ya shiga, a hankali ta karasa gun motar daga
karshe ta shiga ya rufe, sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar. Sai da suka hau saman titi yace "Wani anguwar kike?" Ba tare da ta kallesa
ba tace "Tun da Maryam ta gaya maka gidanmu daya da Dr Ayman nasan ai baxata rasa gaya maka address da house number ba" Murmushi kawai Aliyu yyi yana ci
gaba da driving dinsa bai ce komai ba, sai da suka iso street din ya kalleta yace "I only know the street...." ta fada masa number din gidan, yana isa dai
dai gidan yayi parking yana dubanta yace "Wani schl din Shureim ke xuwa Iman?" Sai a sannan ta kallesa tace "I don't think I have to tell you" Yana shafa
kansa yace "It isn't an offense ai Iman" ta bude motar ta fita tace "Thanks for the ride" murmushi kawai yayi ta wuce ciki ya bi ta da kallo, tabe baki
Khadijah tayi ganin babu motar khaleel a garage ta fiddo makullinta cikin jaka ta bude kofar ta shiga ciki, wanka tayi sannan tayi sllh ta canxa kaya ta
fito parlor, xaunawa tayi tana tunanin abinda xata girka, can ya mike ta wuce kitchen din, shinkafa da miya tayi deciding tayi sanin Shureim na son sa
sosai, tana parboiling shinkafa taji shigowar motar khaleel gidan, da gudu ta fita parlor ta isa gun kofa ta sa makulli sanann ta koma kitchen ta ci gaba da
abinda take, bell taji an danna, ta hade rai ta tura kofar kitchen din, ba a sake dannawa ba sai ringing din wayarta dake parlor ta ji, ta bude kofar ta
fita ta dau wayar tana kallon screen din, ganin khaleel ke kiranta da har xata ajiye sai kuma ta daga ta kai kunne ta ki cewa komai, yace "Bacci kike ne?"
Tace "What about that?" Yace "Ohk, naga takalman ki kin bari a waje, and ki fito ku gaisa da jawahir" Wani kallo tayi kamar yana gabanta tace "For what?" A
hankali yace "Am waiting Khadijah...." daga haka ya katse wayar, mamaki ne ya cikata, a kan wani dalili xa ta gaisa da jawahir, tsaki tayi xata ajiye wayar
text ya shigo nasa, ya budewa tayi tana kallon content din, "Plsss" abinda ya turo mata kenan, ta turo baki sai kuma ta harari kofar, a hankali ta isa gun
kofar ta bude, tsaye ta gansa shi da jawahir din, suna hada ido jawahir tace "Sannu Khadijah ya gida?" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Lafiya lau, fatan
kin xo lafiya" Jawahir tace "Alhmdllh, ya hakuri?" A hankali Khadijah tace "Alhmdllh nagode" kallonta kawai khaleel yake, Jawahir tace "Dama Dr yace in taho
in maki gaisuwa ne" Khadijah tace "Ayya nagode, baxa ki shigo ba" khaleel na kallon jawahir yace "Shiga sai kiyi sllh" jawahir tace "Toh bari in yi" daga
haka ta shiga parlorn Khadijah, ba tare da Khadijah ta kallesa ba ta rufe kofarta fuska daure, murmushi kawai khaleel yyi yana kallon kofar. Jawahir na kan
darduma xaune parlorn Khadijah ta kawo mata abinci a plate, jawahir tace "Ayya na ci abinci Khadijah, am not hungry" Khadija tace "Haba ki ci ko kadan ne"
Jawahir tace "Da gaske bana jin yunwa ki bar sa kawai" juyawa kawai Khadijah tayi rike da abincin ta koma kitchen, tana fitowa jawahir ta mike tace "Toh
nagode bari in je" Khadijah tace "Welcm" daga haka ta fita, tana ji ta bude apartment din khaleel ta shiga, tabe baki Khadijah tayi, ta ja tsaki ta wuce
daki, mayafinta ta dauko ganin Shureim ya kusa tashi a schl, tana fita apartment dinta ta sa makulli ta nufi waje, cab ta samu ya kai ta har makarantar,
Rungume ta Shureim yayi bayan ya fito daga cikin makarantar yana kallonta yace "Anty me yasa uncle bai xo ba" Khadijah ta hade rai tace "Don't ask me that
again" daga haka ta kama hannunsa suka shiga cab din, suna isa gida ta biya mai cab din ta wuce ciki tana rike da hannunsa, sai kallon kofar khaleel take ta
tabe baki ta bude kofarta ta shiga parlor da Shureim, makulli ta sa ma kofar, ta Shiga bedroom da shi ta cire masa uniform, tayi masa wanka ta shirya sa ta
sa masa rigar sanyi sanan ta sa yayi sllh, suka fito, a plate daya ta xuba masu abincin, tana ci a hankali tana kallonsa, muryarsa taji yace "Anty yaushe
Sudais xai dawo? Umma tace min after one month, kuma ai one month yayi ai koh?" Khadijah ta sauke idonta daga kallonsa tana ci gaba da cin abincinta tace
"Nima ban sani ba, sai dai anjima idan Umma ta kira ka tambayeta" ya langwabar da kai yace "Ohk" kallon wayarta dake ring tayi taga sabon number ke kiranta,
ta dauka ya kai kunne, muryar Aliyu taji yace "Iman" a hankali tace "Na'am" yace "Fito ki amshi sakon Shureim din" kallon Shureim tayi tace "Ohk" daga haka
ya katse wayar, ta mike tana kallon Shureim tace "Mu je ka rakani Shureim" ya tashi ta dauko plate ta rufe abincin, ta dau tissue ta goge masa bakinsa
sannan ta dauko masa takalmansa ya sa suka fita, ba dai dai kofar gidan yayi parking ba, Khadijah na rike da hannun Shureim ta tsallaka xuwa side din da
yake, daga cikin motar Aliyu ke kallonsu ko kiftawa babu har suka iso dai dai inda yayi parking, a hankali ya bude motarsa, Shureim na ganinsa ya nufe sa da
gudu cike da murnar ganinsa Aliyu ya daga sa ya rungume sa ya lumshe ido, cike jin dadi shureim yace "Uncle ka kai ni wajen mama plss" Aliyu ya dago kansa
yana kallonsa yayi pecking goshinsa yace "Mama tana Nigeria ai, idan kun yi hutu sai in kai ka" Shureim yace "Uncle plss ka tafi da ni" Aliyu ya kalli
Khadijah dake wasa da ring din hannunta, a hankali yace "Thanks for coming out Khadijah" Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, jin bata ce komai ba ya
bude bayan motar ya fiddo babban leda, Shureim yace "Uncle Anty ta bani irin wannan chocolate da kake bani da Sudais..." Aliyu ya wara ido yace "Da gaske?"
Yace "Yes uncle" ya kalli Khadijah ya langwabar da kai yace "Toh Anty ki bari muje in siyo masa irin chocolates din, sai mu dawo yanxu" Khadijah bata ce
komai ba, Aliyu yayi kasa da murya yace "Ko xa ki raka mu?" Girgixa kai tayi tace "No way" daga haka ta tsallaka ta wuce ciki abun ta, Aliyu ya bi ta da
kallo kafin yayi murmushi ya xaga ya bude front seat ya xaunar da Shureim, ya dawo ya shiga driver seat ya tada motar ya bar street din. Khadijah na dai dai
apartment dinta khaleel ya bude motar ya fito rike da makulin motarsa, ganinta yace "Let me go pick Shureim, na sha'afa wllh" a takaice tace "You don't
worry na dauko sa, Ni ban sha'afa ba" daga haka ta Shiga ta rufe kofarta, ya fi minti daya a tsaye kafin ya koma nasa apartment din. Shopping mall din da
Aliyu ya kai Shureim kusa da gidan kanwar Abbansa yake, don haka yana gama masa shopping ya shiga gidan tare da Shureim, Tasowa Maryam dake xaune parlor da
Deejah tayi ganinsa ta tafi da sauri dau yaron ta rungumesa tace "Waow yau ga Shureim a gidanmu, Yaya Aliyu a ina ka samo mana shi? Jiya kuwa muka hadu da
mum dinsa a cafteria a schl" Maryam ta kalli Deejah dake parlorn tana kallon Shureim da expression na Waow a fuskarta tace "Kin tuna warce muka gani a
cafteria jiya?" Deejah ta xaro ido tace "Wai Khadijahr nan da nace maki suna kama da Safeenah??" Maryam tace "Yauwa ita" da mamaki Deejah tace "Kar ki ce
min ita ta haifi yaron nan?" Maryam tayi dariya tace "Yaronta ne mana, yan biyu ne ma, daya ya rasu" lkci daya jikin Deejah yayi sanyi ta mike tace "Allah
sarki" Aliyu dai bai tanka su ba ya wuce sama bayan ya amshi Shureim hannun Maryam don kai ma Antyn sa shi, Deejah ta bi su da kallo murya can kasa tace
"but naga yaron na kama da cousin din naki ai, I mean sosai fa" Murmushi kawai Maryam tayi sai dai bata ce komai ba, bude kofa aka yi sai ga jawahir ta
shigo, wurgar da takalman kafar tayi, ta jefar da jakar hannunta kan kujera ta xauna, Deejah dake ta kallonta tace "Ke kuma meye haka? me ya faru?" A fusace
ta fara magana tace "Wllh Anty deejah na gaji da Ayman, abinda yake min ya fara isata, am just tired" Maryam ta xauna kusa da ita tace "Toh fah, me kuma ya
hada ku?" Mikewa Jawahir tayi rai bace tace "Don rainin hankali sai yayi ta wani hada ni da yarinya da ban san meye tsakaninsu ba, I really want to know
wacece yarinyar nan, sanann ta wani dinga daga min hanci tana amsa min da kyar kamar dole.... Da yaje Nigeria gaba daya lkcn sa ita yayi dedicating ma, ashe
ma gidansu daya a nan ban sani ba sai daxu da ya fita yake gaya min, Ni kuma abinda yasa ma na sake ma yarinyar fuska tun farkon da muka hadu a Nigeria naga
tana min yanayi da Safeenah ne, ban da haka tayi kadan in ganta da saurayina in raga mata, sannan ni a tunani na matar aure ce don ina ganin yaran nan nasan
nata ne but now I am totally confuse...."
Deejah ta kamo hannunta a hankali tace "Kilan it's not what u are thinking lil sis, may be they are just frnds and neighbors, Kar ki bari shaidan ya ci
galaba a kan ki, na kuma san ki da hakuri sosai jawahir so meye nasa wannan a ran ki?" Kamar xata yi kuka tace "Anty da kyar fa take amsa min magana idan na
mata, kamar ma haushi na take ji shi kuma sai yayi ta sa ni in mata magana, to idan ba budurwarsa bace ita me yasa xata dinga haka" Deejah ta sauke ajiyar
xuciya tace "But ni dai she was very free with me da muka hadu a cafteria jiya" Jawahir ta jinginar da kanta jikin kujera cike da damuwa bata ce komai ba,
tausayinta Deejah ta dinga ji, Maryam dai na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, mikewa Jawahir tayi ta dau jakarta ta wuce sama, Xaunawa Maryam tayi,
Deejah na kallonta tace "Maryam ko dai budurwar Ayman ce Khadijah kar ki boye min?" Maryam ta bude ido tace "A'a gaskiya ban sani ba, ni ban ma taba ganinsu
tare ba ko a schl" Tare Aliyu ya sakko da Hajiya Mariya dake rike da Shureim, shi kuma yana rike da ledan na lotion da turaren yara da small mum din tasa ta
ba Shureim, Maryam na kallonsu tace "Ya Aliyu dama ba kwana xai yi ba" Aliyu ya kalleta yace "Aa" Hajiya Mariya ta xauna kan kujera tana kallon Shureim dake
gabanta tace "Ka gaida mumy ka ji boy?" Ya wara idanuwansa irin na Aliyu yace "Mumy ai tana can Nigeria, Anty xan gaida maki" Murmushi Hajiya Mariya tayi
tana shafa kansa tace "Toh ka gayar min da Anty son" Aliyu ta kalla tace "Toh yaushe Antyn xata xo ta gaisheni" Aliyu yyi yar dariya yace "Ai Antyn nan sai
a hankali ba xuwa xata yi ba" a hankali Hajiya Mariya tace "Kar ka damu, Allah xai dai dai ta ku ko don albarkacin yaron nan" murmushi kawai Aliyu yyi bai
ce komai ba ya kama hannun Shureim xa su fita yace "Toh bari in mayar da shi mum, it's getting late" Shureim ya daga ma Hajiya Mariya da ta bi sa da kallo
ganin sak mahaifinsa yana daga mata hannu, mikewa Maryam tayi ta bi bayansu, sai da suka fita waje ta kamo hannun Shureim ta durkusa tana gyara masa hular
sweater dinsa tace "Darling ni baxa kace min bye bye ba" Dariya yayi yana kallonta ya daga mata hannu yace "Byee" mikewa tayi tana murmushi ta daga masa
hannun ita ma sannan ta ce ma Aliyu sai ya dawo ta juya ta koma ciki, Aliyu ya sa Shureim mota sannan ya xaga ya Shiga ya tada motar ya nufi gida da shi,
sai da suka kusa isa gidan ya juya yana kallonsa yace "Wani school kake xuwa Boy?" Shureim ya fada masa sunan makarantar, yace "Did you like the schl?"
Gyada masa kai Shureim yayi, Aliyu yyi parking dai dai gidan yana kallonsa a hankali yace "Anty ce ta kai ka schl din?" Shureim yace "A'a uncle dina ne ya
kai ni" Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba, can ya dauko wayarsa ya shiga kiran Khadijah, Tana xaune parlor tana karatu kiran ya shigo wayarta, tana ganin
number ta gane ta daga ta kai kunne, Aliyu yace "ki d'an fito ki dau Shureim" Katse wayar tayi ta mike ta shiga daki ta sa hijab ta fito, kamar mai tausayin
kasa take tafiya har ta isa inda motar Aliyu yake, fitowa yyi daga motar ya xagaya ya bude side din Shureim ya sauko da shi, Khadijah ta karaso ta kama
hannun yaronta ba tare da ta kalli Aliyu ba tace "Sai da safe" Riko Hijab dinta yayi yana kallonta, ta juya suna hada ido gabanta ya fadi tayi saurin
sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "Sai da safe kuma? baki amshi sakon sa ba" Bata ce komai ba ya saketa ya bude bayan motar ya dauko babban leda ya dau
ledan da Hajiya Mariya ta ba Shureim ya sa a ciki da ledan da yayi masa shopping duk ya hada su waje daya ya mika mata, karba tayi yace "Xa ki iya" Bata ce
komai ba ta kama hannun Shureim ta fara tafiya, ya bi su da kallo, Shureim ya juya yana daga masa hannu, murmushi yayi ya daga masa hannun shi ma a sanyaye
har suka wuce ciki. Manyan sweaters da head warmer ke cikin ledar da Aliyu ya bata na Shureim sai kaya kala hudu, ta bude daya ledan taga chocolates,
biscuits sweets da dai abubuwan ci na yara, ta bude ledan da Hajiya Mariya ta basa taga lotions masu tsada da turare, tabe baki tayi ta mike ta wuce ciki da
kayan, sai da ta ajiye kayan inda ya kamata a daki sannan ta fito da ledan chocolates din parlor, turus ta tsaya ganin khaleel xaune parlorn, ta dinga bin
parlorn da kallo ganin bata ga Shureim ba, Mikewa khaleel yayi yana kallonta, sake ledan hannunta tayi ta juya da sauri xata koma ciki yace "Khadijah"
tsayawa tayi amma ta ki juyowa, kawai ganinsa tayi gabanta yana kallonta, tayi saurin juyo masa baya, a hankali yace "Gaya min me na maki?" Ta turo baki
tace "Toh ni na ce ka min wani abu ne?" D'an murmushi yayi yace "Saboda Aliyu kika canxa min Khadijah?" Shiru tayi ta rasa ma abinda xata ce masa, lkci daya
jikinta yayi sanyi, jin shi ma bai ce komai ba ta juyo a hankali tana kallonsa, hawaye ya cika idonta tace "Me yasa xan canxa maka saboda Aliyu?" A sanyaye
yace "Nima ban sani ba Khadijah" hawaye idonta ya xubo tace "Ko dai kai ne ka canxa min saboda budurwar ka" tana fadin haka ta fashe da kuka, kallonta ya
dinga yi shi ma jikinsa yayi sanyi, da wani expression fuskarsa yace "Why? Why will I change because of Jawahir?" tana hararensa cikin kuka tace "Toh nima
me yasa xan canxa saboda Aliyu?" Ya lumshe ido ya bude a hankali yana kallonta, rasa abin fadi yayi, har ransa yake jin kukanta, ya bude hannayensa cikin
sanyin murya yace "Can... I console you?" Make kafada tayi ta juya masa baya, ya lumshe idanuwansa a hankali ya rungumota, cikin sanyayyan muryar sa yace
"You know I love you Khadijah, and... I want you to be the mother of my kids, i want to marry you Khadijah, but you met me with Jawahir, I was with her
before you, kin ga baxan mata walakanci ba saboda ke, jawahir na da saukin kai sosai, she don't have problem, and I don't want to betray her... Beside ita
daban a rai na haka ke ma, Give me a chance to show you how much I love you plss Khadijah" kasa cewa komai Khadijah tayi, duk gaba daya jikinta yayi sanyi,
jin tayi shiru ya juyo da ita a hankali yana kallonta, Bata yarda sun hada ido ba ta sulale nan kasa ta xauna, dukawa yayi gabanta yana kallonta murya can
kasa yace "Say something plss Khadijah... Nace Ina son auren ki baki ce komai ba" Ta hade kai da gwiwa jin hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace "But
Barrister Sudais...." Sai kuma ta fashe da kuka, ya dago kanta gabansa na faduwa, da kyar ya iya cewa "what about him Khadijah?" Tace "He proposed before
you..." Shiru yayi yana kallonta ko kiftawa babu, a sanyaye tace "He said he want to marry me, and you know I can't tell him no Doctor, aure ma bai isa na
biyasa abinda ya min a rayuwa ba, he deserves more than that from me, though nasan 6 years back I will confess I was in love with him, but yanxu I only
respect him as someone that brought light to my life after my Lord, sai gashi ya dawo yace yana son aure na, baxan iya cewa bana son Sudais ba, baxan iya
cewa baxan auresa ba, but I am afraid of his wife" shi dai khaleel bai ce komai ba, kana ganinsa kasan jikinsa yayi sanyi sosai, mikewa yayi a hankali bayan
few seconds yace "Ohk then, Khadijah, Allah yasa hakan yafi alkhairi, wishing you all the best" daga haka ya juya xai fita ta tashi da sauri hawaye na sakko
mata tace "But I know I love you so much Dr, bayan Sudais you are the next in my life, da ba don kai ba da ban san abinda xai sameni ba few months back, you
made me lively once more in life, may be...." sai da ya isa bakin kofa ya juyo yana kallonta ya katse ta yace "Forget I did that to you Khadijah" daga haka
ya fita, ta bi sa da ido xuciyarta na bugawa.
Duk yanda Khadijah ta so yin kuka ko xata samu saukin xafin da take ji a xuciyarta kasa yin hakan tayi, ita ta dai san ta fadi ma khaleel haka ne don ta
wanke kanta ko da wani abun xai faru gaba wanda bata ma fatan hakan but she never expect such harsh reply from him, why will he just decide to leave? Sai a
sannan ta fashe da matsanancin kuka, ashe dama ba sonta yake ba, ashe dama playing dinta kawai yake, gaba daya ta rasa abinda ke mata dadi a ranta, tayi
kukan har ta ji babu dadi, duk jikinta yayi sanyi. Tana kwance bayan Isha ita kadai a daki, xuwa sannan ta daina kukan da take kuma ta samu relieve amma
banda xafi babu abinda xuciyarta yake mata, ji tayi an bude kofar parlor, duk da wutan bedroom dinta a kashe yake hakan bai hanata dinga kallon kofar dakin
ba, lkci daya kuma aka bude kofar Shureim ya shigo dakin, bai kunna wuta ba ya karaso ya hau saman gadon ya kwanta kusa da ita a hankali yace "Anty are you
sleeping?" Shiru tayi bata ce komai ba idonta a lumshe, tana ji yayi addu'ar bacci yayi lamo jikinta, a hankali tace "Ka ci abinci?" Ya dago kai yana
kallonta yace "Uncle ya bani na ci" Jawo sa tayi jikinta bata ce komai ba, sai da taji yayi bacci sannan ta kwantar da shi ta mike da kyar ta sakko kan
gadon tana jin kanta na sara mata ta fita parlor don rufe kofa, a kan centre table ta ga Key a ajiye ta karasa gun kofa ta murda taji a rufe, alamar ya rufe
ta waje ga Key a ajiye kan centre table, Dawowa parlorn tayi a sanyaye ta dau books din Shureim ta duba taga yayi assignment dinsa ta ajiye cikin jakarsa
sannan kashe wutan parlorn ta koma daki ta kwanta ta lumshe ido. Har kusan karfe goma na dare ta kasa bacci, bude ido tayi da sauri jin wayar ta na ring ta
mike xaune ta dau wayar tana kallon mai kiranta, A hankali ta daga ta kai kunne tayi sallama, daga daya bangaren ya amsa yace "Hope ban tashe ki bacci ba
Amira" ta lumshe ido a sanyaye tace "Ba bacci nake ba" Shiru ya d'an yi na wani lkci kafin yace "Gaya min me ya faru, what's wrong with you" Ta bude ido da
sauri cike da mamaki tace "A'a ba komai, am just tired, me ka ga?" Sudais ya girgixa kai yace "Noo, I know you well Amira, we stayed together for two years,
from ur voice, there is something wrong, ki gaya min meye plss" Tace "Lahh da gaske ba komai barrister, today was very hectic shi yasa" D'an murmushi yayi
yace "Ohk then" trying to brighten up tace "Ya Namecy na fa?" Yace "Ga ta tayi bacci" Khadijah tace "Toh a shafa min kanta" Sudais yace "Alryt, Shureim yayi
bacci?" Khadijah ta gyada kai tace "Uhm" yace "Ya kamata ya ci gaba da karatun sa a nan, I think I will be coming over next week sai inyi enrolling dinsa" A
hankali Khadijah tace "Ai ya fara ma" Yace "School din?" Tace "Ehh" yace "Shine baki fadi min ba Amira?" Ta langwabar da kai tace "Kayi hakuri" yace "Ke
kika sa shi schl din" ta girgixa kai tace "Dr Ayman ya sa shi" Sudais ya d'an yi shiru sannan yace "That's nyc" Khadijah tace "Next week din xaka taho?"
Yace "Sure, Akwai abinda xan yi, but few days xan yi, so do you need anything?" tace "A'a bana bukatar komai, Allah ya kawo ka lafiya" yace "Ameen, let me
leave you dear, it's late and kilan xa ki lectures gobe koh?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi mata sallama bayan ya tunasar da ita tayi addu'a
sannan ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta kwanta ta ja masu duvet da Shureim. Washegari kafin karfe bakwai ta gama komai, ta ba Shureim indomie da ta girka
masu a baki don kar ya bata uniform dinsa, Yana gamawa ta mike ta basa jakarsa ya goya ta dau nata jakar tana rike da hannunsa ta nufi kofa, tana gama rufe
kofarta Shureim yace "Anty yau ma tafiya xa mu yi mu bar uncle?" Ta kallesa kamar baxa tace komai ba sai kuma a hankali tace "He is still sleeping dear"
daga haka ta ja sa suka fita gidan, cab ta samar masu kamar jiya tayi dropping dinsa a schl sannan ta wuce nata makarantar duk da bata da lectures din safe,
Wani waje ta samu ita kadai ta xauna, har ga Allah mai lallashinta take nema a lkcin, she need someone to console her, ta share hawayen da ya cika idonta
trying hard to control her self, bata samu courage din kiran Umma ba har lkcn, tana ta xaune har lkcn lectures yayi bata tashi ba sai da ta ga kiran
Vanessa, ta mike jiki ba kwari ta bar wajen. Bayan sun fito daga lectures sha biyu saura, Khadijah ta wuce cafteria ba tare da ta bari su Vanessa sun lura
da ita ba, tana ta xaune nan tayi tagumi kamar ance ta daga kai ta ga Aliyu xaune yana kallonta, a hankali ta sauke kanta kasa, bayan kusan minti biyar ta
sake daga kai tana kallonsa taga wayarsa yake dannawa, mikewa tayi ta dau wayarta dake ajiye kan table da jakarta xata fita taji a hankali yace "Iman" kasa
kallonsa tayi tana tsaye, ya mike ya iso kusa da ita yace "Gida xa ki wuce?" Tana kokarin ganin bai ga hawayen idonta ba ta gyada masa kai, daga haka ta
fita cafterian ya bi bayanta, har suka yi nisa bata ce masa ba shi ma bai ce mata ba, kuma kusan a tare suke tafiyar Daga karshe yayi breaking silence din a
hankali yace "What's wrong Iman?" bata san lkcn da ta fashe da kuka ba kamar jira take, nan da nan ya rikice mata yace "Subhanallah, me ya faru Iman, plss
ki gaya min, wani abu ya faru ne" ta kasa ce masa komai sai kuka take xuciyarta na mata xafi, Har ransa ya dinga jin kukan nata, bai san lkcn da cikin tsawa
yace "Plss I don't like this Iman, ki daina wannan kukan" Tsayar da kukan nata tayi amma hawaye na ci gaba da sakko mata, wuri Aliyu ya samu ya xauna jin
kafafuwarsa sun masa nauyi ya rike kansa, lkci daya jikinsa yayi sanyi xuciyarsa yayi masa rauni don kukan nata bashi da maraba da irin wanda tayi a ranar
da kaddara ta afka masu six years back, A hankali ta nufi inda ya xauna ta xauna kusa da shi tana goge hawayen da yaki tsaya mata, Bayan kusan minti daya ya
dago, cikin sanyin murya yace "What happened Khadijah?" Ta hadiye abu da kyar tace "Should I confide in you plss?" Kallonta yake ko kiftawa babu, a hankali
yace "Sure Iman, you won't regret doing so" Ta gyada kai cikin sanyi tace "Ohk, tnx" Shiru ne ya biyo baya na 'ya dakiku.....