Breaking News

NOOR AL HAYAT 71-80




Khadijah ta hade kanta da gwiwa a hankali ta ki cewa komai, ya fi minti biyu yana kallonta, can ya shafa kansa murya can kasa yace "Talk Iman..." lkci daya 


ta dago kanta ya dinga kallon jajayen idanuwanta, ta hadiye abu da kyar ta make kafada tace "I think I've changed my mind" muryar ta na rawa ta fadi haka, 


ya dinga kallonta a sanyaye yace "Why Iman??" k'in cewa komai tayi, wasu sabbin hawayen suka shiga xubo mata, da damuwa sosai yace "Why did u change ur mind 


Iman, am I not trustworthy" goge idonta tayi tana kallonsa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe idanuwansa, murya can kasa ya ji tace "Ina son xan wuce 


gida yanxu" Ya bude ido ya kalli agogon wrist dinsa a sanyaye yace "To mu je in kai ki" shi ya fara mikewa sannan ita ma ta tashi a hankali tana share 


idonta, har suka iso gun motarsa bai ce komai ba, sai da ya bude motar ya shiga sannan ita ma ta shiga, gaba daya she was absent-minded during the ride, 


idonta ne ya sauka kan wani karamin agogo mai kyau na yara cikin a cikin motar, ta kai hannu ta dauka tana kallon agogon ko kiftawa babu, agogon da khaleel 


ya taba siya ma su Shureim ne lkcn da suka xo hutu wajenta da xa su koma, ita dai ta san na Shureim na nan don da shi ma suka xo, Aliyu dai bai ce komai ba 


yana driving a nutse, ganin ta kallesa kafin tace komai murya can kasa yace "For little Aliyu...." Kasa cewa komai tayi da farko, a sanyaye tace "Where did 


you get it from?" Ya d'an yi murmushi kamar baxai ce komai ba shi ma, sai kuma yace "When he had an accident that very day agogon na aljihunsa, da muka tafi 


asibiti na cire" Khadijah ta sauke idonta bata ce komai ba, a hankali ta xuge zip din jakarta xata sa a ciki ya karba a hannunta, da mamaki take kallonsa, 


yace "Nima ina so, shi yasa na bar shi ma a mota" ta hade rai tace "Toh nima ai ina so" A hankali yace "But ai Shureim ma na da shi" bata sake saurarensa ba 


ta kai hannu xata karbe, bai san lkcn da ya sake steering ba ta fasa ihu a tsorace, parking yayi daga karshe inda ya dace yayi, ta dinga kallonsa xuciyarta 


na bugawa, yayi kokarin ganin bai yi dariya ba, dauke hannunsa yyi wajen ganin xata kwace agogon, Tace "Bana so ka bani abun yarona" a hankali yace "Nima ai 


yarona ne Iman" wani kallo tayi masa tace "A tunanin ka??" Murmushi kawai yayi yana kara kallon agogon, Mika mata yayi yana kallonta a hankali yace "Toh na 


hakura" kasa amsa tayi, ya dinga kallonta yana mika mata, dauke kai tayi ta turo baki tace "Toh na ara maka, xaka ban watarana" Murmushin sa yayi mai kyau 


murya can kasa yace "Toh ina godiya Iman" Ya mayar da agogon inda yake ya ajiye, ya juya yana facing dinta yace "But why did you change ur mind Iman?" 


kallonsa tayi sai kuma ta dauke kai, kamar baxata ce komai ba bayan few minutes a sanyaye tace "It's Dr Ayman, and it looks as if it's of no use telling 


you...." sai da gabansa ya fadi sosai, ya dake cike da karfin hali yace "What about him" ta jinginar da kanta da kujerar da take xaune, ji tayi abun ya dawo 


mata sabo, muryar ta na rawa tace "Kawai don nayi masa magana shine ya min walakanci" Aliyu ya ji komai nasa ya tsaya, a hankali yace "May be.... may be he 


misunderstood you Iman...." Ta fashe da kuka tuna abinda Dr Khaleel yace mata, ya lumshe ido ya bude yace "Toh wani maganr kika masa?" Babu abinda ta boye 


masa a maganarsu da khaleel na jiya, jin yanda take kuka Aliyu ya lumshe ido yace "Look.... pls ki daina wanann kukan I really don't like it, stop it now" a 


fusace yayi maganan ta hadiye kukan da take tana goge idonta, ya jinginar da kansa jikin kujerar motar a hankali cikin sanyi yace "He really misunderstood 


you, but ke ma ba haka ya kamata ki gaya masa ba" ta kallesa tace "Toh ya xan ce masa?" Ya d'an yi murmushin karfin hali yace "You where direct, which is 


not suppose to be so" turo baki tayi ta rungume hannunta tace "Ae shikenan" Aliyu ya shafa kai murya can kasa yace "You want me to talk to him?" Ta buda ido 


sosai tana kallonsa da sauri tace "Kace masa me?" Ba tare da ya kalleta ba yace "I will only explain to him what you meant by wat u said to him, kila..." ta 


hade rai ta katse sa tace "Noo, you don't need to, ba ruwana da shi, and am wishing him d best also" Aliyu na kallonta da kyau yace "Then forget him, kuma 


kar ki sake xubda hawayen ki" Shiru tayi tana kallonsa, a hankali tace "But I can't forget him just like that, yayi min hallacci a rayuwa" ba tare da Aliyu 


ya kalleta ba yace "Me ya maki?" Hararansa tayi da kamar baxata ce komai ba, sai kuma a takaice tace "He nursed my Heartache, he always made sure I was 


fine" Kallonta kawai Aliyu yake, "Wani irin heartache?" Tambayar da ya mata kenan har sannan yana kallonta sauke idonta tayi daga karshe tace "Ciwon 


xuciyata" da wani expression yake kallonta kafin yace "Kina nufin kina da ciwon xuciya?" Shiru tayi bata ce komai ba, jin hawayen talaici na xubo mata ta 


shiga gogewa, lkci daya jikinsa yayi sanyi, cike da karfin hali yace "I... i am the cause ko Iman?" Taki cewa komai, jin taki magana yace "Iman" sai a 


sannan ta juya tana kallonsa, sai ya rasa ma mai xai ce mata duk jikinsa ya mutu, tada motar sa yyi cike da karfin hali yace "Let me get you something to 


eat" Bata ce komai ba ya nufi wani gidan cin abinci da ita, suna isa bayan yayi parking ya juya yana kallonta a hankali yace "Mu je" daga haka ya bude motar 


ya fita ita ma ta fito, one side of the eatry khaleel ne xaune da cup din coffee gabansa ya jinginar da kansa da kujera har coffeen ya gama hucewa bai fara 


sha ba, kallonsu ya dinga yi ko kiftawa babu, ganin kujerar dake kallon nasa xa su zauna ya juya masu baya, Aliyu ya mika mata order list din da aka basa, 


kamar baxa ta karba ba da farko sai kuma ta amsa, ya dinga kallonta tunani iri iri a xuciyarsa, bata yi second talatin tana kallo ba ta mayar masa a sanyaye 


tace "Just anything" ya karba yana gyada mata kai, abinci iri daya ya sa aka kawo masu, duk da gaba daya ya ji ba ya da appetite hakan bai hanasa dinga cin 


abincin a hankali ba, ita ma haka, gaba daya suka fada duniyar tunani kowa da wanda yake, ita tana ganin yan biyunta tare da shi barin late Sudais, kuma ta 


dalilin haka har ranta tasan she is now comfortable with him even if it's not 100% unlike before, shi kuma yana tunanin in har bai auri Khadijah ba till the 


end of him baxai taba samun rest of mind ba, a hankali ya dago daga karshe yana kallon yanda take cin abincin kamar ana tilastata sai turo baki take, suka 


hada ido ta yi saurin sauke idonta, ya d'an yi murmushi yace "Naga bakya ci" a hankali tace "Ina ci mana" shi ya fara matsar da abincin gabansa jin ya 


ishesa gaba daya duk da ba da yawa ya ci ba, ta kalli abincin nasa tace "Ka koshi?" Ya gyada mata kai, yanda yayi da bakinsa kamar Shureim idon bai son cin 


abinci, tayi shiru tana kallonsa, yayi murmushi yana shafa kansa ya matsar mata da sauran abincin nasa yace "Ko xaki kara?" Wani Harara ta maka masa ta tura 


masa nata tace "Sai dai ma ka kara da nawa" sunkuyar da kansa yayi yana dariya, tayi murmushi a sanyaye tana kallonsa komai yayi wani lkcn sai ta ga exactly 


her kids, it's just too obvious, ya dau tissue yana goge bakinsa a hankali yace "Ranan Aunt dita ke tambayar ki, coz I told her a nan kike karatu...." 


Khadijah ta sauke idonta kasa tace "Ina gaisheta" lumshe ido yyi ya bude yace "Or xa ki je ku gaisa yanxu, tana son ki sosai, anjima sae in mayar da ke gida 


then u face Ur Dr Ayman.... Sai ki masa bayanin abinda kike nufi ya daina fushi da ke" ta hade rai tace "Ni ba ruwana da shi, bana son sa kuma" tana fadin 


haka ta kife kanta da table ta fara rera kuka, Aliyu ya dinga kallonta ko kiftawa babu, can yyi kasa da murya yace "Toh kiyi hakuri kar ki sake kuka, am 


sure shi ma ba har ransa ya gaya maki haka ba fa" Bata sake cewa komai ba ya biya bill din yana kallonta yace "Tashi mu je" mikewa tayi ya mike shi ma, tana 


gaba yana biye da ita Dr Ayman ya bi su da kallo har suka fita, har suka iso gun motarsa bbu wanda yace komai, ya bude mata motar yana kallonta, a hankali 


ta karaso ta shiga, ya rufe sannan ya xaga ya shiga ya tada motar ya fita eatry din, sae da suka hau saman titi a hankali yace "Mu je ku gaisa da ita Iman?" 


Shiru tayi da farko kafin murya can kasa tace "Toh" yayi murmushi yace "Thanks Ummu Shureim" har suka iso gidan babu wanda yace komai cikin su, yanxu kam ta 


daina jin xugin da take ji a xuciyarta, yayi parking yana kallonta yace "Toh fito" ba musu ta fita shima ya fita, Yana gaba tana biye da shi har suka shiga 


parlorn gidan. Maryam kadai ce parlor tana rubutu a takarda, ganinsu ta mike da mamaki tace "Lahh Khadijah ce gidanmu yau, sannu da xuwa" Khadijah ta xauna 


tana kirkiran murmushi da kyar tace "Yauwa nagode" Aliyu ya wuce sama, Maryam ta bi sa da kallo, kamar yanda Khadijah ke kallonta, tashi tayi daga karshe ta 


dauko mata ruwa da drink ta ajiye gabanta tana tambayarta Shureim, a hankali Khadijah tace "Yana schl" Maryam ta xauna tace "Ayya, kin shiga schl kuwa yau?" 


Khadijah ta gyada kai tace "Daga can nake" Maryam tace "Nima kin ga yanxu na dawo, nama yi ta jiran ya Aliyun don ya ce min xae shigo shi ma amma ban gansa 


ba...." Fitowar Hajiya Mariya ya sa Maryam ta mike tace "Anty yau ga mum Shureim gidan mu" Da murna Hajiya Mariya ta karaso cikin parlorn tace "Wlh kuwa, 


maa Sha Allah, sannu da xuwa Khadijah" Khadijah ta sunkuyar da kanta da ladabi tace "Nagode mumy, Ina yini?" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau Khadijah ya 


gidan?" Tace "Alhmdllh" Hajiya Mariya tace "Ya karatun fa?" Khadijah tana wasa da xobenta tace "Alhmdllh Mumy" Hajiya Mariya tace "Maa Sha Allah, Allahu ya 


baku sa'a, Ina Shureim din?" Aliyu da ya shigo parlorn yace "Yana schl Anty" tace "Allah sarki, ashe ya fara schl din a nan, Allah yayi masa albarka ya raya 


sa" Mikewa tayi daga haka tace "Mu je sama kiyi sallah ki ci abinci koh" kasa cewa komai Khadijah tayi ganin ta fara tafiya ta mike ta bi bayanta a sanyaye 


suka haura sama, Maryam na kallon Aliyu tace "Yaya shine ka shanya ni schl koh?" Ya shafa beard dinsa bai ce komai ba, Khadijah na haurawa sama tare da Mumy 


ta juya tana kallonsu, suna hada ido da Aliyu tayi saurin dauke kanta ta shiga dakin da Mumy ta shiga. Tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh Maryam 


ta shigo dakin rike da tray na abinci ta ajiye mata tace "Ga abinci Khadijah" Khadijah ta xaro ido tace "Wallahi na ci abinci kafin mu xo nan am not hungry" 


Maryam tace "Toh ko kadan ne dai ki ci" Khadijah xata yi magana aka bude kofar, jawahir ce ta fara shigowa, suna hada ido Khadijah ta sunkuyar da kai, 


Jawahir dake ta kallonta ta ajiye jakar hannunta ta fice daga dakin, sosai jikin Maryam yayi, ita dai Khadijah bata sake dago kanta ba, sai ga deejah ma ta 


shigo dakin, ta wara ido ganin Khadijah tace "Wow Khadijah ke ce gidan yau?" Murmushi Khadijah tayi tace "Ina yini" Deejah tace "Lafiya lau, ya lectures? 


Tare da Maryam ku ka xo?" Maryam na yar dariya tace "Ehh mana" Deejah tace "Ayya ya little shureim" Khadijah tace "Yana schl" Deejah tace "Toh maa Sha 


Allah" daga haka ta fita, Khadijah ta kalli agogon dakin don gaba daya hankalin ta yyi kan yaronta sanin ya kusa tashi a schl, ganin Maryam na sllh ta jira 


har ta idar kafin tace mata tayi ma Mumy magana xata wuce, Deejah ce ta dawo dakin tana video call ta iso kusa da Khadijah ta durkusa tana murmushi ta haska 


ta tace "Ammi ki duba fa plss basa kama??" Khadijah ta ki kallon screen din tana murmushi, Deejah tace "Khadijah ki tsaya ku gaisa da Ummar mu pls" sai a 


sannan Khadijah ta kalli screen din wayar, wata matashiyar mata ta gani gaban wayar, a hankali tana kallonta tace "ina yini?" Matar na kallon ta da fara'a 


tace "Lafiya lau yan mata, ya kike ya karatu?" Khadijah tayi murmushi tace "Alhmdllh" matar tace "Maa Sha Allah, Allah yayi maku Albarka ya bada abinda aka 


je nema, sai ayi ta kula kin ji?" Khadijah ta ji dadin addu'ar cikin sanyin murya tace "Ameen mama nagode" matar tayi mata sallama, Deejah ta mike rike da 


wayar tace "Ammi idan Safeenah ta dawo plss ku kira ni in nuna mata duplicate din ta" murmushi kawai Khadijah tayi, Deejah ta fice daga dakin tana ci gaba 


da waya da mum dinta. Khadijah ta kalli Maryam dake kallonta tace "Kice ma Mumy xan wuce" mikewa Maryam tayi tace "Toh" daga haka ta fita, tare suka dawo 


dakin da Mumy tace "Har xa ki koma daughter?" Khadijah tayi murmushi tace "Eh mum, Shureim sun tashi a schl" Hajiya Mariya tace "To maa Sha Allah, mun gode 


da ziyara Khadijah, Allah yi albarka" a tare suka sakko kasa har da Maryam, Mumy ta ba Khadijah sako a leda ta kai ma Shureim, a kunyace ta amsa tace "Allah 


saka da alkhairi mum" Deejah vata ji dadi ba ganin wucewa Khadijah xata yi, tace "Ae ko xan xo gidan ki ko gobe" Yar dariya Khadijah tayi tace "Allah ya kai 


mu" tare da Maryam suka rakota har bakin motar Aliyu don yana cikin motar yana jiranta, daga masu hannu tayi bayan ta shiga tace "Toh nagode, sae anjiman 


mu" Aliyu ya ja motar ya fita cikin gidan, sae da suka dau hanya tace "Xan dau Shureim a schl" yace "I thought as much, naga it's time" Mamaki Khadijah tayi 


ganin ya dau hanyar makarantar, ta kasa daurewa tace "How did you knw d schl?" D'an murmushi yayi murya can kasa yace "Kin raina irin bond dake tsakanin a 


son and his father?" Shiru Khadijah tayi tana kallonsa, lkci daya ta hade rai ta turo baki tace "Don't call him ur son, stop calling him that" kallonta yyi, 


A hankali yace "Ko saboda me?" A takaice tace "His father is a barrister" Murmushi yayi bai ce komai ba, he really really don't want to hurt her da babu 


abinda xai hanasa tambayar ta ko barrister ne yayi mata cikinsu, suna isa schl din bayan yyi parking ta bude motar ta fita don dauko d'an ta ya bi ta da 


kallo, ba a dau lkci ba ta dawo a sanyaye, yace "Where is he?" Ta bude motar ta shiga a hankali tace "Dr ya tafi da shi wai"


Aliyu bai ce komai ba ya tada motar a hankali ya bar premises din school din, har suka isa babu wanda yace komai, yana gama parking ya juya yana kallonta, 


ta bude motar ta fita tace "Nagode" yace "ki gaida min Shureim" ba tare da ta juyo ba tace "Ohkk" Da ido ya bi ta har ta shiga cikin gida, yayi wani 


murmushi ya ja motarsa ya bar wajen, tun da Khadijah ta shiga compound take ta kallon motar khaleel, lkci daya mood dinta ya canxa ta isa apartment dinta ta 


bude jaka ta fiddo makulli ta bude kofar ta shiga. Wanka tayi ta kwanta parlor ta fada duniyar tunani, murda kofar parlorn taji anyi ta mike xaune da sauri, 


Shureim ya shigo ya taho wajenta da gudu ya hau kanta yace "Anty we came back before you" ta rungumesa tace "How are you?" Yace "Am fyn" tace "Have you 


eaten?" Ya gyada mata kai yace "Uncle ya bani" tace "Toh mu je ka cire uniform" tashi tayi ta daga sa suka wuce bedroom, wanka tayi masa ta sa masa kaya da 


sweater ta bar sa dakin yayi assignment ta fito don daura girki. Tana kitchen tana fere Irish taji kamar mutum waje, a hankali ta leka window ta gansa xaune 


waya kare kunnensa, hada ido suka yi, ta dauke kai da sauri, ta ci gaba da abinda take cikin sanyi. Shidda da yan mintuna ta fito kitchen din bayan ta 


tsaftace ko ina, daki ta wuce taga Shureim kwance kan carpet yayi bacci, ta daukesa ta daura sa saman gado ta kwashe books dinsa ganin ya gama assignment 


din ta sa a jaka ta rufe, har xata fita wayarta dake kan gado yayi haske, ta karasa gadon ta dau wayar tana kallon screen din, alert ta gani na dubu dari da 


hamsin, a hankali ta ajiye wayar ta shiga bathroom, Karfe takwas saura Khadijah ta fito parlor da hijab har kasa, duk gaba daya ta rasa sukuni, a sanyaye ta 


wuce kitchen ta xuba abinci ta fito ta xauna, kasa cin abincin tayi ta tura plate din daga gabanta tana hadiye na bakinta da kyar, tashi tayi ta kara shiga 


kitchen ta dau warmer ta wanke ta xuba abinci a ciki ta rufe sannan ta fito, ta fi minti uku tsaye parlon kafin ta nufi kofa ta fita gabanta na faduwa, a 


hankali ta danna bell din khaleel, tana ta tsaye gun ga wani sanyi dake ta shigarta, ganin bai bude ba ta kara dannawa, lkci daya ya bude kofar tayi saurin 


sunkuyar da kanta kar su hada ido, barin bakin kofar yayi ya koma ciki ta bi bayansa kamar mai tausayin kasa ta rufe kofar sannan ta isa tsakiyar parlorn ta 


durkusa ta ajiye abincin hannunta ba tare da ta yarda sun hada ido ba tace "Good evening" Xaunawa yyi kan kujera yace "Evening ya kike?" A sanyaye tace 


"Lafiya lau" Yace "Ya lectures?" Shiru tayi bata ce komai ba, tana dai duke inda take yace "Baxa ki xauna ba" a hankali ta mike tace "Sai da safe" yace 


"Alryt, Allah tashe mu lafiya, todays cold isn't gonna be funny ki sa ma Shureim sweater and lock all the windows" tace "Toh" daga haka ta nufi kofa xata 


fita yace "And...." Tsayawa tayi bakin kofar don jin abinda xai ce, yace "Thanks for the food" bata ce komai ba ta fita ta rufe masa kofar. Abincin da ta 


xuba ta kai kitchen ta fito ta kashe wutan parlorn ta wuce bedroom, warm water ta xuba a kettle ta daura alwala ta fito ta kashe wutan dakin ta hau gado ta 


kwanta kusa da Shureim ta rufa masu Duvet, har ta fara bacci vibration wayarta ya tasheta, ta bude ido a hankali ta jawo wayar, tasan Barrister ne xai 


kirata wannan lkcn, tayi picking call din ta kai kunne tayi sallama cikin sanyin murya, daga daya bangaren yace "Amira..." Tace "Uhm Ina yini?" Yace "Lafiya 


lau, Ya Boy dina?" Tace "Yayi bacci" yace "Maa Sha Allah, kema tashin ki nayi koh?" Tace "Uhn, na dai kwanta ne, ina little Amira fah?" Yace "Tana gun Mum 


dinta" Khadijah tace "Am sorry ban kira ka ba Barrister, daxun na ga sako thanks very much we are grateful" yace "Is there any need for that Amira?" 


Murmushi tayi bata ce komai ba, yace "I think nan da 3 days xan taho ba sai next week ba" Khadijah tace "Ayya Allah ya kawo ka lafiya" yace "Ameen, daxu ma 


naje gun Umma" Khadijah ta bude ido tace "Haba dai?" Yace "Sure, kafin in taho Uk xan je can katsina" shiru Khadijah tayi bata ce komai ba, yace "Are you 


there?" Tace "Uhm ina jin ka" yace "Me yasa kika yi shiru" a hankali tace "Isn't it Early barrister" yace "It's not Amira, I want everything to be done in 


not less than 2 months plss, ba ki jin tausayina koh" jikinta yayi sanyi tace "Amma barrister ni tsoron Ummu Amira nake, plss ka sanar da ita don ya xamo da 


amincewarta kake yin komai, Ni tsoro nake ji" D'an murmushi yayi yace "Ba ruwan ki da Jiddah, beside ta san komai, ke din dai ce bata sani ba, sannan ba 


gida daya xa ku xauna ba" Ita dai har sannan bata ji hankalin ta ya kwanta ba, banda faduwa babu abinda gabanta ke yi, cikin sanyin murya tace "Toh 


shikenan, Allah yayi jagora" yace "Ameen Amira, let me allow you sleep" tace "Toh nagode" a hankali yace "Do have a nyc nyt rest" Ta d'an yi murmushi tace 


"Thanks" daga haka ya katse wayar, komawa tayi ta kwanta ta rufe har kanta da duvet. Washegari bata da lectures da safe amma saboda Shureim dole ta tashi 


cikin sanyi don shirya sa, tausayin little boy din nata take don sanyin isn't funny at all, haka dai ta shirya sa ta sa masa rigar sanyi babba da head warm, 


tea ta hada masa ta soya masa kwai sanin baya cin bread, tana xaune parlor tana jiran ya gama aka danna bell, kallon agogo tayi kafin ta mike ta isa kofar 


ta bude, khaleel ne tsaye ya shirya xai fita, shi ma kayan sanyin ne jikinsa yana kallonta a hankali yace "Good morning" ta kasa kallonsa ganin yanda ya 


tsare ta da ido, ji tayi yace "let me drop Shureim in school tunda baki da lectures yau" tace "Toh" daga haka ta dawo parlorn, yana ta tsaye har Shureim ya 


gama ta dauko masa lunch box dinsa ta mika masa, ya nufi kofa yana daga mata hannu har ya fita khaleel ya kama hannunsa xuwa gun motarsa, ta tsaya bakin 


kofa tana kallonsu har suka fita gidan. Washegari Thursday da yamma Khadijah na parlor tana goge ma Shureim kayansa da uniforms, shi kuma yana bedroom yana 


waya da su Umma, mikewa tayi bayan ta kashe iron din jin an danna bell, ta isa kofar ta bude, khaleel ta gani tsaye, ya shafa kansa ba tare da ya kalleta ba 


yace "I will be traveling to Nigeria today Khadijah" shiru tayi tana kallonsa,  yace "You take care of the little boy" tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, 


Allah ya tsare" yace "Ameen" xai shiga apartment dinsa ta fito a hankali tace "Dr..." Tsayawa yayi ya juyo yana kallonta, Kasa magana tayi, murya can kasa 


yace "Am all ears Khadijah" Jin hawaye na neman taruwa idonta ta juya ta koma ciki kawai, da ya tashi tafiya kuma bai ma ce mata ya tafi ba yayi wucewar sa. 


Tun da Khadijah ta tashi sllhn asuba duk ta rasa me ke damunta, gaba daya ta ji bata jin dadi, komawa tayi ta kwanta kasancewar friday ne, tana ta kwance 


har kusan karfe takwas, can dai ta tashi tunawa da tayi anytime soon flight din su Barrister xai sauka kasar, Ruwan wanka ta hada ta fara tashin Shureim ta 


wanke masa baki tayi masa wanka ta sa yayi alwala sannan suka fito bayin, shirya sa tayi ta shimfida masa darduma yayi sllh sannan ta wuce bathroom don yin 


wanka, tana tsaye kitchen misalin karfe goma tana tunanin abinda xata girka ma Barrister, Shureim ya kawo mata wayarta dake ring, karba tayi ta kai kunne 


hade da sallama, yace "Kun tashi lafiya Amira?" Tace "Alhmdllh, har kun sauka kenan?" yace "Sure, tun karfe tara" Tace "Toh ina ka sauka?" Murmushi yayi 


yace "Baki san ina da apartment nan ba koh?" Ta langwabar da kai tace "I never knew" yace "You now know" murmushi kawai tayi, yace "Ina Shureim" kallon 


bakin kofar tayi taga ya wuce tace "Yana parlor, barrister sorry I asked... plss mai xan girka maka I don't know what u like most" Yace "Noo you don't worry 


dear, Ni nayi breakfast ma" shiru tayi jin abinda yace, Can tace "Toh lunch fah?" Yace "Just tea may be with cake" xaro ido tayi tace "Tea da cake kuma?" 


Yace "Uhm sure" tayi murmushi tace "Toh shikenan yaushe xaka taho?" Yace "After I am done with what I am doing, may be in the afternoon" tace "Toh Allah ya 


kai mu" Yace "Ameen, bye dear" daga haka ya katse wayar, fita tayi daga kitchen din don dama sun yi breakfast da Shureim. Karfe Sha daya ta shirya tare da 


Shureim suka fita don yin shopping, sun fito daga shopping mall wayarta dake jakarta ya fara ring, ta ajiye kayan hannunta ta bude jakar ta ciro wayar, 


number Aliyu ta gani, ta d'an yi jim kafin ta daga, shi yayi mata sallama ta amsa tayi shiru, yace "Ya kike Iman" tace "Lafiya lau" yace "Ya Shureim?" Tace 


"He is fine" yace "Maa Sha Allah" shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Xan tafi Nigeria later, you need anything?" Tace "As in?" Yace "I 


mean ko kina bukatar wani abu daga Nigeria?" Tace "Nothing" a hankali yace "Ohk can I go with Shureim plss" wani kallo ta shiga yi kamar yana gabanta tace 


"Beg your pardon?" D'an murmushi yayi kafin yace "Ranan litinin xa mu dawo Iman, daurin auren Neighbor din ki xan je, it's tomorrow, so we will be back 


Monday morning" Shiru Khadijah tayi tana son apprehending abinda Aliyu ya ce mata, a hankali yace "Hello, are you there Iman?" Ta dake tace "Waye Neighbor 


dina?" Da kamar baxai ce mata komai ba sai kuma yace "Dr Ayman"


Khadijah na rike da hannun Shureim suka fito waje, tun daga nesa Aliyu dake cikin motar ke kallonta, har suka iso kusa da motar ya fito, ko ba a fadi masa 


ba yasan tayi kuka, kuma gaba daya a sanyaye take, ya duka yana kallon Shureim a hankali yace "How are you" Shureim yyi masa murmushi yace "Fine, good 


afternoon uncle" shafa kansa yyi ya mike ya kalli Khadijah yace "Thank you Iman" jakar Shureim ta mika masa ya karba ya sa bayan mota sannan yana rike da 


hannunsa ya xaga ya sa shi gaban motar ya dawo, ya bude maxaunin driver ya shiga, sae a sannan Khadijah ta juya ta koma ciki ko sallama bata yi da yaron 


nata ba, har cikin ranta take jin tsanar khaleel ynxu kam, ta ji ko ganinsa ma bata son kara yi a rayuwarta, bedroom ta wuce ta kwanta, lkci daya ta mike da 


sauri tunawa da tayi Sudais yace xai xo da rana, ta fita xuwa kitchen don daura masa ruwan Lipton, ta xuba kayan kamshi sosai a ciki, sake gyara gidan tayi 


tana juye ruwan Lipton a flask ta ji wayarta na ring ta fito parlor ta dau wayar, dagawa tayi ta kai kunne tace "Ina yini barrister?" Yace "Alhmdllh, ki 


turo min address Amira" tace "Toh" katse wayar tayi ta tura masa street da house number ta text message, ta ajiye wayar taje ta ci gaba da abinda take, few 


minutes later Sudais ya kirata yace yana waje, ta sa hijab ta fito, Tsaye ta gansa jikin mota cikin shigar da ta lura ya fi so, wato na suit, har ta iso 


kusa da shi idonta na kan sa, kamar yanda shi ma yake kallonta, yayi murmushin sa mai kyau yace "Kyau kike karawa idan kika xo Uk kenan" Tayi murmushi ta 


sunkuyar da kanta, a hankali tace "Sannu da xuwa" yace "Yauwa sannu, ke daya ce cikin katon gidan nan?" Ta girgixa kai tana murmushi tace "A'a bani kadai 


bace, mu shiga ciki Barrister" Yace "Do I have to Amira?" Tace "Why not?" Daga haka ta juya ta fara tafiya, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, yana 


shiga cikin gidan ganin fararen kujeru da table a bangaren flat dinta karkashin wani shade yace "That's all, I will prefer staying outside" daga haka ya 


nufi wajen ya xauna ta tsaya tana kallonsa, bata fuska tayi tace "Barrister mu shiga ciki mana kaga fa akwai sanyi wajen..." Yace "Ke dai kike jin sanyin, 


just get me my tea sai ki yi wucewar ki ciki tunda kina jin sanyi" murmushi tayi ta wuce ciki sai ga ta ta fito da tray mai dauke da karamin flask da plate 


din cake" ajiye masa tayi ta ja kujera ta xauna tana dubansa tace "But me yasa baka son shiga ciki Barrister?" Ya bude plate din ya dau cake daya yace "What 


did you mean?" Ta xaro ido tace "But is there anything wrong with going inside?" Shiru yyi yana kallonta, can ta wara ido da sauri tace "Ohh yes you are 


right Barrister" sai kuma tayi murmushi, murmushin yayi shima ya kai cake din baki, a hankali tace "But.... Seven years back...." Sai kuma tayi shiru, 


kallonta ya dinga yi kafin yace "Don't forget you where sick and pregnant then, I have no choice...." shiru tayi a sanyaye tana kallonsa, ya buda ido sosai 


yace "Wait... Ina Shureim din?" Ta sauke idonta daga kallonsa, cikin sanyin murya tace "Sun tafi Nigeria da Aliyu" da mamaki yace "Wani Aliyun?" Bata ce 


komai ba na few seconds kafin daga karshe tace "Aliyu dai" Sudais ya ajiye sauran cake din hannunsa yace "is he also in Uk?" Kai ta gyada masa, Bai iya ya 


sake cewa komai ba, bayan wani lkci a hankali yace "Kuna haduwa da shi kenan?" Ta sauke idonta daga kallonsa tace "Sometimes in school" Sudais bai sake cewa 


komai ba ya fiddo wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, tana ta kallonsa har ya gama wayar sanann ta sunkuyar da kanta, ya ajiye wayarsa in a very low 


tone yace "Amira?" A hankali ita ma tace "Na'am" yace "I don't want to deprive you of anything you wish for ur self, be frank plss Amira ki fada min 


gaskiya, did you want to go back to the father of ur kid?" Kallonsa ta dinga yi da wani expression, cike da karfin hali tace "Ban gane ba Barrister" Dago 


kai yyi yana kallon eye balls dinta yace "I mean, kina da ra'ayin komawa gun Aliyu ku yi aure ne?" Ta fashe masa da kuka tace "Anybody can say this but not 


you barrister, kai me tuna min irin wahalar rayuwar da na sha ta dalilin Aliyu ne, you witnessed everything, ko kuma ince tare muka sha wahalar barrister 


coz all those time you where by my side, Aliyu raped me without mercy har yau memory din na kai na very fresh, scene din na ido na, bayan faruwar hakan ya 


canxa min a gidan ya daina ma amsa gaisuwata ya daina xama duk inda nake, daga karshe he sent me away without thinking twice, with huge sum of money bayan 


yasan bani da kowa, Bai yi tunanin ko xan gane gida ko baxan gane ba" kuka take sosai, Sudais ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido ya kasa cewa 


komai, Tana ci gaba da kuka tace "Har yau ni ban ga wani prove that will convince me that ba da gangan Aliyu yayi min abinda ya min ba, ban ga prove da xan 


yarda cewar ba da gangan yayi raping dina ba, fine... Mahaifiyarsa cewa tayi it's a set up, did she have any choice? Dole ta kare d'an ta, an taba set up da 


rape dama?? Wllh dalilin marigayin yaro na nake raga ma Aliyu har nake kulasa naji kuma xan iya xumunci da shi albarkacin yaran dake tsakaninmu, of recent I 


dreamt of my little boy telling me to forgive his dad, so why will I not forgive him, nasan ya cuce ni ya bata min rayuwa but he gave me happiness at the 


same time... My boys" hade kanta tayi da table tana kuka sosai, Sudais ya bude idanuwansa yana kallonta cike da tausayin ta, cikin sanyin murya yace "Am 


sorry Amira, you misunderstood me, I know ur pain but..." Ta dago hawaye na sakko mata tace "But what?" Yyi kasa da murya pleadingly yace "I am sorry plss" 


kin cewa komai tayi, yace "Kin hakura?" A hankali ta gyada masa kai, ya lumshe ido ya bude yace "Nagode dear, do you have any plans for our wedding?" Ring 


dinta ta dinga jujjuyawa bata ce komai ba sai dai gaba daya tunaninta a lkcn ya tafi kan khaleel, a hankali yace "Kin yi shiru" wani mugun haushin kanta 


taji ganin Wanda ya fado mata a rai, d'an tsaki tayi ba tare da ta san tayi hakan ba, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace "Ke da wa kuma??" Da sauri 


ta kallesa ta xaro ido tace "Don Allah kayi hakuri barrister wllh ba da kai nake ba, ban san...." Katse ta yayi yace "Nasan ba da ni kike ba Amira, I can 


see you are lost in ur thought, tel me what u are thinking of" ta girgixa kai tana kirkiran murmushi tace "Uhn ba komai fa" murmushi yayi yana shafa kansa 


yace "Toh shkkn" flask din ya bude ta mike da sauri tace "Bari in xuba maka" daga haka ta karasa budewa ta xuba masa a cikin mug dake kife, kallonsa tayi 


taga kallonta kawai yake shi ma, ta sauke kanta kasa a hankali tace "In sa maka Madara?" Ya girgixa kai yace "Noo, I prefer it black" Komawa tayi ta xauna 


tana murmushi tace "Toh, what will you take for dinner?" Ya d'an bude ido bayan ya dau Lipton din yace "Da daddare sometimes ina shan tea with irish and 


egg" ta langwabar da kai tace "Toh da safe fa?" Yayi murmushi yace "Tea and bread" da mamaki ta kallesa tace "Toh barrister baka cin tuwo ko shinkafa ko dai 


any other food?" Yace "Ina ci idan na samu" shiru tayi bata sake cewa komai ba, lkci daya taji tausayinsa don ko bai fito fili ya gaya mata ba ta gane 


Matarasa ce bata girki kenan, d'an murmushi tayi tace "Toh xan maka tuwo anjima ka dawo ka karba" ya xaro ido yace "A'a ku mata da bakwa son girki mai 


wahala don't stress ur self dear I will take tea na riga na saba" tace "No, ba ko wace mace ce ke jin kiwiyar girki ba, I am also exceptional, ko mai kake 


so xan girka maka anjima" murmushi yayi sosai yace "Toh nagode Amira" Sai biyar saura ya bar gidan, shi ma saboda ya damu bai yi la'asar bane..." Ta rakasa 


har bakin motarsa sai da ya wuce sannan ta koma ciki. Kamar yanda ta fada masa kafin magrib har ta gama yi masa tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup, ta 


xuba masa a warmer, ganin bai kirata ba har bakwai ita ta kirasa, bayan ya dauka a hankali tace "Barrister baka dawo ka karba ba kuma" yayi kasa da murya 


yace "I really don't want to stress you dear, I learn girka tuwo akwai wahala..." Katse sa tayi tace " Ni dai ka xo ka amsa na gama, akwai wahala gun 


ragwayen mata dai" dariya yayi yace "Ohh really?" Tace "Yea, tun daxu na gama, ka taho ka amsa plss" a hankali yace "Toh gani xuwa Amira, I am proud of you" 


murmushi kawai tayi ta katse wayarta, cikin minti goma ya taho amsan abincin ya dinga sa mata albarka har ya tafi. Washegari Saturday da yamma Sudais ya xo 


ya fita da ita su xaga gari, duk da sanyin garin, the moment was just waow, ita dai ta san Sudais na sonta fiye da xaton ta but bata san me yasa ta kasa 


kwantar da hankalinta ba, he really made her day on Saturday, don babu wani damuwa tare da ita ya maido ta gida, kewan Shureim ma da take ji gaba daya taji 


babu shi yanxu. Ranan lahadi da safe tun da ta tashi ta shiga kitchen don girka masa shinkafa da miya, karfe goma ta kirasa, bayan ya dau wayar jin muryarsa 


a hankali tace "Bacci kake barrister?" Yace "Uhn am now awake" tace "Kayi hakuri ban san baka tashi ba, ka gaya min address din ka sai in kawo maka 


breakfast" ya mike xaune daga kwancen da yake kan gado yace "Noo ba sai kin ba kan ki wahala ba xan shirya yanxu in fito" tace "Toh, kayi hakuri" ya wara 


idanuwansa yace "Hakuri kuma dear" murmushi tayi ta katse wayar, bedroom ta wuce ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin kananun kaya, tana 


xaune gaban mirror tana gyaran gashinta kawai ta tabe baki ita kadai, yanxu su Maryam gaba daya sun tafi Nigeria biki kenan, d'an tsaki tayi a ranta tace do 


I have to care, turo baki tayi ta mike ta daure gashinta ta dau rigar sanyi ta sa da head warmer ta dawo parlor ta xauna.


✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨


 Ranan lahadi da safe Khadijah ta raka Sudais Airport, har ranta ta dinga jin kewarsa bayan ya tafi duk jikinta yayi sanyi, tana tsaye inda xata hau cab a 


wajen airport din kamar ance ta kalli gefenta taga khaleel tsaye alamar fitowarsa kenan shi ma daga cikin airport, farar shadda ce jikinsa sai walkiya take, 


Khadijah ta dauke kai da sauri tun kan ya kallo inda take ta karasa gun cab da ta gani ta shiga ta fada ma driver din inda xata. Suna isa gida ta fito ta 


basa kudin sa sannan ta shiga ciki da sauri ta bude jakarta tana kokarin ciro makulli, dai dai nan khaleel ya shigo gidan, bata yarda ta juya ba ta bude 


kofarta ta shige. Daki ta wuce ta tattara reading materials dinta, ta dau kayanta kala biyu da nyt wear ta fito rike da jakarta, kulle apartment dinta tayi 


ta wuce kamar warce ake jira a waje tsabar haste din, tana fita ta samu Cab ta hau xuwa gidan Vanessa. Gaba daya ranan a gidan ta yini, sai dai she was just 


uncomfortable saboda mazan turawan dake xuwa suke fita gidan, gashi ba isasshen hankali gare su ba duk ta takura, ta so komawa gida da daddare amma saboda 


sanyi ta hakura ta kwana gidan, washegari daga gidan ta shirya xuwa sch tare da Vanessa bayan sun yi breakfast, suna gama lectures Vanessa ta sake jan 


Khadijah suka koma gidanta, tana xaune parlorn Vanessa bayan tayi magrib idonta a kan takardun hannunta ta jawo wayarta dake ring, number Aliyu ta gani sai 


a sannan ta tuna da yaronta ta yi picking kiran, daga daya bangaren yace "How are you Iman" tace "Fyn, how about my son" yace "Naga kin ma mance da shi gaba 


daya" ta hade rai tace "Taya xan mance shi?" Murmushi yayi yace "Toh gobe da safe xan kawo shi don ya samu yaje schl" tace "Kun dawo ne?" Yace "Yea daxu da 


yamma" shiru ta d'an yi kafin tace "Bring him in the afternoon" yace "Alryt then" daga haka ta katse wayar ta. Ranan talata bayan sun gana lectures misalin 


karfe biyu Khadijah ta koma gida, bude kofar apartment dinta tayi a hankali ta shiga sannan ta rufe, gyaran gidan ta shiga yi, bayan ta tsaftace ko ina, ta 


bude kofar kitchen xata xubda shara suka yi ido hudu da wata yarinya da ta xo xubda sharan ita ma, yarinyar ce ta fara cewa "Sannu" Khadijah tace "Ina 


yini?" Yarinyar tace " Lafiya lau, jiya da muka xo mun duba baki nan ashe kin dawo" Khadijah ta d'an yi murmushi tace "Ehh yanxu na dawo" yarinyar tace 


"Ayya, to Sannu da xuwa" Khadijah tace "Idan na gama xan shigo yanxu" yarinyar tace "Toh sai kin shigo" daga haka Khadijah ta wuce ciki, Allah ma ya san ba 


don ranta ya so ta fada haka ba, kawai dai yarinyar ta mata kwarjini ne, and kuma sai taga kamar suna kama, toh ko dai ita ce warce su Deejah ke fadi? Tabe 


baki tayi ta wuce bedroom dinta, wanka tayi ta sauya kaya tayi sllhn azahar sannan ta linke Hijab dinta ta yafa mayafi ta fito, a hankali ta danna bell din 


apartment din khaleel, bayan wani lkci wata ta bude kofar, Khadijah tace "Ina yini" yarinyar dake ta kallonta ta bata hanya tace "Lafiya lau" shigowa 


parlorn Khadijah tayi gabanta na faduwa, few mutane ne parlorn kuma yawanci duk manya ne, ta durkusa jikin kujera a hankali tace "Ina yinin ku" amsa mata 


suka yi da fara'a, wata a cikinsu tace "Ikon Allah, ji mai kama da su Maimoon" Yarinyar da ta bude kofar tace "Wllh Anty na xata Safeenah ce ta da farko, 


haka na tsaya da mamaki Ina kallonta don nasan Safeenah na daki ai" Ita dai Khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Wata mata dake kusa da ita tace 


"Dama haka Allah ke ikon sa ai, tashi ki shiga ciki yan mata suna can gaba daya" warce ta bude mata kofar ne ta kai ta har dakin da jawahir da yan uwanta 


suke, Khadijah dai gabanta sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, da sallama ta shiga dakin bayan yarinyar ta bude mata kofa, suka hada ido da Jawahir dake 


xaune gefen gado tana danna wayarta, sosai tayi kyau sai wani glowing chocolate skin din ta yake, hannayenta sun sha lalle, kai kana ganinta ka ga amarya, 


Khadijah ta sunkuyar da kanta, Maryam ce ta fara mikewa ganinta tace "Lah Khadijah ashe kin dawo" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Ehh ban dade da dawowa 


ba" Maryam tace "Ayya, Sannu da dawowa, ga waje ki xauna" Bata kai ga xama ba Deejah ta fito daga bayi tana ganinta ta rungume ta da murna tace "Khadijah 


har na gaji da jiran ganin yaushe xa ki dawo, gashi babu mai number ki, Sannu da xuwa" Khadijah tace "Ayya ni ban san jiya xa ku taho ba ina gidan frnd dita 


ce" A hankali Khadijah ta xauna Deejah ta xauna kusa da ita tana kallonta da fara'a tace "Mun taho rakiyar amarya" Khadijah ta kalli jawahir a hankali tace 


"Sannu Amarya, Allah ya bada xaman lafiya" sai a sannan jawahir ta kara kallonta babu yabo babu fallasa tace "Ameen" Deejah sai kallon jawahir take alamar 


bata ji dadin yanda ta amsa mata ba, ita kanta Maryam dauke kanta kawai tayi, Safeenah ta shigo dakin tace "Lahh ashe har kin shigo" Khadijah tayi murmushi 


tace "Eh na shigo" ta karaso ta xauna ita ma tace "Su Anty Deejah na ta labarin ki a Nigeria sai gashi yau na gan ki, kin lura da kamar da muke yi kuwa?" 


Dariya ta ba Khadijah, Maryam da Deejah ma suka yi dariya ban da Jawahir da ta tsuke fuska, A hankali Khadijah tace "Ikon Allah kenan" Safeenah tace 


"Gaskiya ne, Ammin mu na gaishe ki" Khadijah tayi murmushi tace "Na amsa sosai" hira suka dinga yi dakin banda Khadijah da sai dai tayi murmushi idan sun 


kallota, duk a takure take ta kagu ta tashi ta wuce amma ta kasa tashi, agogo ta kalla ganin uku ya wuce tayi karfin halin mikewa tace "Xan dan shiga ciki 


ina aiki ne" Safeenah tace "Amma xa ki dawo ai?" Murmushi Khadijah tayi tace "Ehh xan dawo anjima" Rakota suka yi parlor, Khadijah tayi ma wa enda ke xaune 


parlor sallama ta bude kofa xata fita suka kusa cin karo da khaleel, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yanda ta daburce shi ma haka, yyi saurin 


bata hanya, ganin Deejah da Safeenah na bayanta tayi karfin halin ce masa "Ina yini" yace "Lafiya lau, ya gida" fita tayi daga parlorn bata ce komai ba ta 


bude apartment dinta ta shiga ta rufe, ganin la'asar yayi ta daura alwala a bayi tayi sallah sannan ta kwanta, bude data tayi da sauri tunawa da tayi daxu 


Barrister yace xai turo mata sako ta duba, ko ya bar Dubai din ma oho, ai ko tana budewa taga messages da ya turo mata da yawa, ta shiga tana kallon message 


din, kusan gaba daya hotuna ne, downloading din su ta fara yi, murmushi tayi ganin set na akwatuna ne yace ta xabi wanda take so, a hankali ta dinga 


scrolling tana duba boxes din, bbu na banxa gaba dayansu, murmushi tayi masa as reply, sannan ta tura masa message tace duk sun yi kyau sosai, daga haka ta 


kashe datan ta, bayan kusan minti goma sai ga kiransa, kuri ta kura ma wayar ido, can ta daga a hankali ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren 


yace "Amira" tace "Na'am good day" yace "Thanks, I saw ur reply, kuma ni ba tambayar ki nayi ko sun yi kyau ba" Yar dariya tayi tace "Barrister amma ai kai 


ma kasan sun yi kyau" yace "My question is wanne kika fi so" tayi murmushi tace "Uhm ni ban san wanne xan ce ba barrister" yace "Ask ur frnds then" tace 


"Toh xan tambaya" yace "Ina fa jiran ki kafin gobe, don goben xan bar Dubai" a hankali tace "Toh barrister" daga haka yayi mata sallama ya katse wayar ta 


koma ta kwanta a sanyaye, juye juye ta dinga yi tana kokarin bata ba damuwar dake neman dirar mata a xuciya space ba, can ta mike jin ta fara jin yunwa, 


kitchen ta tafi ta daura ruwan xafi don tafasa na shayi, kamar ance ta leka window taga khaleel xaune waje doing nothing, hada ido suka yi tayi saurin dauke 


kanta ta ci gaba da abinda take, tasowa yayi a hankali ya iso kusa da windown ya tsaya yana kallonta, trying her best not to look toward his direction tace 


"Wishing a happy married life, Allah bada xaman lafiya" kallonta kawai yake, can a hankali yace "Khadijah"  kashe gas dinta tayi ba tare da ta kalli inda 


yake ba ta nufi kofar fita kitchen din ya bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar. Shayin da bata sha ba kenan tana ta xaune parlor wayarta ya fara ring, 


dauka tayi ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tayi shiru, "Ki fito muna waje" abinda Aliyu yace mata kenan, ta mike a hankali ta tafi daki ta dauko 


hijab dinta ta sa ta fita, Tana isa kusa da motar ta bude ganin bashi da alamar fitowa ta fiddo Shureim tana kallonsa, xata wuce yace "Jira ki karbi sakon 


Mumy" Bata ce komai ba ta tsaya ya fito ya bude bayan mota ya ciro wani leda ya bata, amsa tayi tace "Mun gode Allah saka da alkhairi" Har ta juya xata tafi 


sai kuma ta tsaya tana kallonsa ta basa wayarta tace "Ka sa min number ta sai in kirata in mata godiya" karbar wayar yayi ya sa mata digit din Mumy ya mika 


mata, ta amsa tace "Thanks" yace "Don't forget ki tambayeta jikin Anty Khadijah idan Kin kirata" tace "Har yanxu bata samu sauki ba?" Yace "She is still at 


the hospital" Shiru Khadijah tayi, lkci daya jikinta yayi sanyi, can tace "Toh Allah ya bata lafiya" Yace "Ameen" Cike da karfin hali tace "Ya jikin iklima 


fa?" Ya shafa kansa yace "Tana can family din babanta, ban samu xuwa dubata ba coz I spent only three days kuma throughout Zaria nake ta tafiya gun Anty 


Khadijah" Khadijah tace "Toh Allah ya sauwake, idan muka yi hutu soon xan je gida sae in je in duba Anty Khadijah da Umma" Yace "Alryt" shiru ta kara yi, 


sai kuma ta kallesa tace "Ina son tambayar ka pls" yana kallonta ya rungume hannunsa yace "Ina jin ki"


✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨


 Khadijah tace "Ya dangartakar ku da su Deejah?" Ya d'an yi shiru yana tunani kafin yace "Wacece Deejah kuma?" Ta kallesa tace "Deejah ce baka sani ba?" 


Buda ido yyi yace "Ohh wai warce kika tarar gida ranan da na kai ki kike nufi, kawar Maryam" Khadijah tace "Ehh" yace "I think, noo they are just family 


frnds kawai, Dad din Maryam da dad dinsu are just good frnds, childhood frnds if I am not mistaken, that's just it" Khadijah tace "Toh Maryam fa?" Ya shafa 


kansa yace "Her mum kanwar Abbana ce, dad dinta kuma was once under my dad, so Maryam is my cousin" Khadijah tace "Ohk" yana kallonta yace "But why did you 


ask?" Wani kallo tayi masa tace "Is there anything wrong with me asking?" Murmushi yayi yace "Not at all, yaushe xa ku fara exams?" Tace "Nan da 3wks" yace 


"Ohk Allah ya kai mu" tace "Ameen" daga haka ta kama hannun Shureim dake tsinkar flowers ta nufi cikin gida, Aliyu ya bi su da kallo Shureim na daga masa 


hannu har suka shiga cikin gidan. Da daddare Khadijah na bedroom tana karatu bayan Shureim yayi bacci taji an danna bell, sosai gabanta ya fadi ta kalli 


agogo, a lokacin ma takwas yayi, ta mike a hankali ta isa gun kofar ta tsaya tace "Waye?" Jin muryar mace ta bude kofar, Safeenah ce tsaye bakin kofar tace 


"Khadijah I want to spend the nigh here if it's ok by you" Khadijah tace "Oh you are welcm" daga haka ta bata hanya ta shigo parlorn tana cewa "Su Anty 


Deejah na takura ni shi sa na yo nan, da dare bai yi ba gidansu Maryam dama xan tafi" Khadijah tayi murmushi tace "To mu shiga ciki" bin bayanta Safeenah 


tayi har suka isa bedroom dinta, Safeenah na kallon Shureim dake bacci tace Woaw brothern ki ne wannan" Murmushi Khadijah tayi bata ce komai ba, can kuma 


tace "Ki hau saman gadon" Safeenah ta hau kan gadon xuwa daya side din tace "Hope baxan takura ku ba" Khadijah ta xauna gefen gadon tace "Haba dai ba wani 


takura" Safeenah tace "Kin san har na fara ba Abban mu labarin ki" Khadijah tayi dariya tace "Haba dai" Safeenah tace "Ehh mana, Ko mijin Jawahir Dr Ayman 


ya din ga kallona jiya da muka xo, da yake bai san ni ba dama tunda ba gida daya muke da jawahir ba, she is my cousin, My father and her mother are having 


same parent" Khadijah tace "Ayya that's nyc" Safeenah tace "Ke karatu kawai ya kawo ki kasar nan kenan" Khadijah ta gyada kai tace "Na ma kusa gama wa" 


Safeenah tace "Ayya, a Nigeria wani state ku ke da parent din ki?" Khadijah tace "Kaduna" Safeenah ta gyada kai tace "Su jawahir ne ke kaduna mu a Abuja 


muke" Wayar Safeenah ya fara ring ta duba, mike tayi ta koma can karshen gado tace "Let me answer my call Khadijah" daga haka tayi picking call din, 


murmushi Khadijah tayi ta mike don dauko masu rigar sanyi, har ranta taji tana son Safeenah, she's just free minded, daya side din gadon ta tafi ta kwanta 


bayan ta ajiye ma Safeenah rigar sanyin, ta lumshe ido nan da nan bacci ya dauke ta. Da asuba bayan sun idar da sllh Safeenah ta koma ta kwanta, Khadijah ta 


fita xuwa kitchen tana tunanin abinda xata yi na breakfast ta kai ma su Deejah, Irish tayi deciding ta soya da kwai ta dafa masu ruwan shayi don ita iyakar 


abinda take ci kenan gidan sai indomie ko shinkafa... Gaba daya cimar kasar bai dameta ba shi yasa ko siya bata yi, ta fi ga abincin Nigeria, har ta gama 


abinda take a kitchen Safeenah bacci take, daukan Shureim tayi ta fita daga dakin xuwa wani dakin tayi masa wanka ta dauko Uniform dinsa ta shiryasa ta sa 


masa kayan sanyin sa sannan ta basa Breakfast, wankan tayi ita ma kafin ya gama ta shirya cikin abaya ta yafa mayafinsa ganin da sauran lokaci yasa bata kai 


masu breakfast din ba ta tafi kai Shureim makaranta, tana dawowa ta tarar da Safeenah a parlor, Tace "Har kin tashi?" Safeenah tace "Wllh Dr Ayman ne ya 


tashe ni yanxu shi ya xo neman ki" Khadijah tace "Nema na kuma?" Safeenah tace "Noo xai fita ne yace xai yi dropping brother dinki a schl sai nace kilan kin 


je kai sa" Khadijah tace "Ayya ai daga can nake ma, akwai ruwan xafi bathroom idan xaki yi wanka" Safeenah ta mike tace "A'a bari in je can inyi tunda 


kayana na can din, dama jira nake ki dawo" daga haka ta nufi kofa Khadijah tace "Toh shkkn, Amma xa ki dawo?" Safeenah tayi dariya tace "Eh xan dawo" 


Khadijah tace "in bar maki breakfast din ki a nan kenan" Safeenah tace "Da safen nan fa xa mu wuce Khadijah" Khadijah tace "Da gaske" Safeenah tace "Ehh 


amma can gidansu Maryam xa mu je, Mum dinmu na can anjima da yamma sai mu dau hanyar Naija" Khadijah tace "Ayya to shikenan, idan na fito lectures da yamma 


kila in taho gidansu Maryam sai muyi sallama" Safeenah tace "Ba wani kila, kawai ki taho ku gaisa da Ammin mu tana can gidan ai, plss ki xo wllh ni dai ina 


son ki fa Khadijah I want us to be frnds" dariya Khadijah tayi tace "Toh in sha Allah xan xo" daga haka Safeenah ta wuce, Khadijah ta dau breakfast da ta 


masu a kitchen ta kai masu, a hankali ta bude kofar dake bude ta shiga parlorn, babu kowa parlorn sai ac dake kunne duk da sanyin garin, a hankali ta 


durkusa nan tsakiyar parlorn ta ajiye abubuwan hannunta, tana tunanin shiga daki wata xuciyar na ce mata kawai ta yi wucewarta idan sun fito xa su gani, har 


xata mike sai ga Khaleel ya fito, ya shigo parlorn yana kallonta, dai dai nan Safeenah ta fito daga daki ita ma ganin Khadijah tace "Yauwa Khadijah na bar 


wayata bedroom din ki" Khadijah ta mike da sauri tace "Lah to bari in dauko maki, dama xan taho da flask yanxu" Daga haka ta fita Khaleel ya dinga kallon 


safeenah da bata yarda ta kallesa ba tace "Ina kwana Doctor" yace "Lafiya lau" juyawa yayi ya wuce bedroom dinsa ya xauna kujera yana kallon jawahir da 


shigowar ta dakin kenan ita ma, atamfa ne jikinta ta yafe jikinta da mayafi tayi kyau sosai, a hankali tace "Ina kwana" yace "Lafiya qlau dear, I want to 


ask you something, shud i?" tana kallonsa tace "Ina jin ka" yace "Safeenah naji kamar ake kiran ta koh?" Jawahir na kallonsa tace "Ehh, what about her?" 


yace "Ya ku ke da ita pls?" Jawahir tace "She is my cousin sis, My mum and her father are having same parent, me ya faru?" Kallonta ya dinga yi kafin yace 


"Where do they stay?" Tace "Abuja" yace "Ohk sorry I'm asking this dear, bayan Dad din Safeenah, da Umman ku, da Uncle din ki na Lagos, akwai wasu kawun nan 


ki da ban sani ba ko aunt din ki? ta bangaren mumy fa nake tambayar ki" jawahir ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Dama su biyar ne kawai gun maternal grand 


parent dina, kawun mu na Lagos ne babba, sai Abbansu Safeenah, sannan kawu Abdul, sai Ummata da kuma autarsu, but she is late, ta rasu" Khaleel dake ta 


kallonta yace "Since when?" Ta girgixa kai tace "I really don't know don Umma tace min muna yara lokacin, she is always talking about her younger sis til 


date, seems tana sonta sosai" Khaleel na kallonta har lkcn yace "Kuma tayi aure kafin ta rasu?" Jawahir tace "Gaskiya ban sani ba" Khaleel ya dawo kusa da 


ita yace "Plss do me a favor of asking Umma to tell you more about her" da mamaki Jawahir ke kallonsa tace "But why?" Ya shafa kansa yace "Ke dai ki 


tambayar min ita plss wife" d'an murmushi tayi tace "Toh xan tambayar maka in sha Allah" yace "Yauwa nagode sosai" Khadijah na komawa apartment dinta ta 


dauko wayar Safeenah da flask na Lipton da ta dafa ta dawo apartment din Dr Ayman, har lkcn Safeenah na parlor tana jiranta, bayan ta karbi wayar tace 


"Thanks much Khadijah, baxa ki shigo ku gaisa da su Deejah da jawahir ba?" Khadijah tayi murmushi tace "Toh ina xuwa, xan dawo yanxu" daga haka ta fita, 


tana shiga apartment dinta jakar makarantar ta kawai ta dauka ta bar gidan don bata son sake jamming da khaleel, she just can't withstand the sight of him. 


Kamar yanda tace ma Safeenah suna gama lectures karfe uku da yan mintuna ta tafi gidansu Maryam tunda ta mata alkawari, Hajiya Mariya taji dadin ganinta 


haka mahaifiyarsu Safeenah, Khadijah na ganinta ta ganeta don ita ce suka yi vid call kwanaki, Safeenah tace "Ammi kin ganta koh" Ammi tayi murmushi tace 


"Ae kam na ganta, ya iyayen naki Khadijah" Khadijah tace "suna lafiya..." Ammi tace "A kaduna ku ke da xama?" Khadijah ta gyada kai tace "Ehh" Hajiya Mariya 


tace "Ina Shureim din Khadijah?" Khadijah tace "Yana schl Mumy" shirye shiryen wucewa Airport suke, Khadijah dai na ta xaune parlor tare da Hajiya Mariya da 


Ammin su Safeenah, gaba daya hankalinta yayi kan Shureim sanin sun tashi amma ta rasa me yasa ta kasa masu sallama ta wuce, wayar ta ne yyi ring ta kalli 


Deejah dake kusa da ita tayi excusing kanta ta fita, kasa daukar wayar tayi duk jikinta yayi sanyi, gaba daya ta mance ita yake jira, ganin xai tsinke ta 


dauka daga karshe ta kai kunne a hankali tayi masa sallama, amsawa yayi yace "Uhnn it seems.... Amira ni kadai nake hauka na koh?" Da damuwa tace "Am very 


sorry barrister, I wanted calling you na mance, but kasan me duk wanda kaga ya maka kyau Wallahi ina so, I want ur choice" jin yayi shiru a hankali tace "Ka 


yi shiru barrister" yace "Ohk then..." Marairaicewa tayi tace "You are still angry koh?" Yace "Sure" tace "But nace fa kayi hakuri" yace "Amira if I am 


important to you baxa ki ce kin manta ba, am still in dubai because of you but kuma kice min kin mance" jikinta yayi sanyi tace "Don Allah kayi hakuri..." 


Yace "Nayi" daga haka yayi mata sallama ya katse wayarsa, tana ta tsaye duk bata ji dadi ba don tasan bata kyauta masa ba aka shigo gidan da mota, bin motar 


tayi da kallo har yayi parking ya fito, kallonta ya dinga yi sai kuma ya karaso inda take yace "Iman, when did you come?" Tace "Yanxu" yace "Good evening" 


tace "Same, pls kace ma su mumy na tafi Shureim yana schl har yanxu" ya kalli agogon wrist dinsa yace "Har yanxu? This is after 4" tace "Na xo sallama da su 


Safeenah ne" ya kara kallon agogo yace "Ohk to mu je ki daukesa in kai ku gida dama airport xan kai su..." Tace "A'a don't worry ka kai su airport din, 


tnxx" daga haka ta juya ta fita gidan, tana isa makarantar su Shureim ya samu an xo an daukesa, wucewa gida tayi, tana bedroom ta cire kaya ta daura towel 


xata shiga wanka aka bude kofa da sauri ta juya shureim ya shigo da sallama ya wara ido yace "Anty yau ma na riga ki dawo wa" Tace "Wa ya dawo da kai?" Yace 


"Uncle mana" jawosa tayi ta xauna gefen gado tace "Da kuka dawo mai Antyn dake gidan tace maka?" Yace "Nothing, she only gave me food with juice, shine 


yanxu tace in xo in cire uniform" Khadijah ta tabe baki tace "Shi uncle din me yake?" Ya buda ido yace "Yana daki..." Ta kuma tabe baki ta cire masa uniform 


dinsa ta fara yi masa wanka tasa yayi alwala suka fito ta shirya sa sannan tace yayi sallah, wanka ta shiga tayi ta fito ita ma ta shirya, Shureim na 


assignment dinsa kan gado ta dau wayarta, text ta shiga rubuta ma Barrister na ban hakuri tana gama rubutun ta tura masa, dai dai nan aka danna bell ta mike 


ta dau gyalenta ta fita.


Khadijah na kwance bedroom dinta waya kare kunnenta tana sauraren Umma dake mata magana, bayan wani lkci ta turo baki a hankali tace "Umma ni ce masa nayi 


ko wanne, I don't have choice..." daga daya bangaren Umma tayi murmushi tace "You know ur problem Khadijah?" Khadijah ta girgixa kai a hankali kamar tana 


ganinta, Umma tace "Kin ki kwantar da hankalin ki to know what's best for you, sure ni na san kina son khaleel but he is married kin sani, me yasa har yanxu 


xuciyar ki ke yaudarar ki?" da mamaki Khadijah ta dinga sauraren Umma, can dai tace "Umma how did u knw he is married?" Umma tace "Ya xo gida ranan 


Saturday, he told me about his wedding" Khadijah taji hawaye ya taho mata ta kasa cewa komai, Umma tace "Ke da bakin ki kika ce masa barrister... to don me 


kuma baxa ki kwantar da hankalin ki da Barristern ba, it's not as if Khaleel isn't good, but I think barrister Aliyu is the best for you, Kuma khaleel daga 


aure ai baxai fara xancen auren ki ba kuma, Khadijah as a mother nake gaya maki ki kwantar da hankalinki ki ba barrister chance you won't regret it, idan 


kuma kinga khaleel din ke xuciyar ki to sai ki tanadi kalaman da xaki gaya ma barrister but count me out kar ma ki nuna masa na san komai" Hawaye na sakko 


mata cikin sanyin tace "Ni ai ban ce ban yarda da barrister ba Umma, his wife is my greatest fear Umma lkcn a clinic da Sudais bai da lafiya I didn't tell 


you she called and warned me to stay away from her husband" Sake baki Umma tayi tace "Ehh lallai Khadijah da alamar rako mata kika yi, ita kishiyar xaki 


fara tsoro tun baki shiga gidan ba, ita kishiyar Khadijah?" Turo baki tayi tace "Umma ni ba tsoronta nake ba kawai dai tashin hankali ne bana so, I don't 


want anything that will make me sad" Umma tace "Toh ai ba gida daya xa ku xauna ba" Khadijah tayi shiru bata ce komai ba, cikin kwantar da hankali Umma tace 


"Kiyi ta addu'a daughter, Allah ya maki xabi mafi alkhairi" a hankali Khadijah tace "Ameen" Umma tace "And one more thing Khadijah in har ke a tunanin ki 


saboda kawai Barrister Aliyu ya taimake ki a rayuwa kike son aurensa to pay him back toh gaskiya you are making a mistake kuma kin cucesa kin cuce kan ki 


indai sabida haka kika amince da aurensa" Hawaye Khadijah ya dinga yi sosai duk jikinta yayi sanyi, cike da karfin hali tace "Umma ba haka bane" Umma tace 


"Are you sure Khadijah" tana gyada kai da kyar tace "Ehh" Umma tace "Toh am happy to here that, ke dai kiyi ta addu'a kawai, and make sure yanxu ki kirasa 


ki ce masa ga wanda kika fi so a akwatunan" Khadijah na share idonta tayi kasa da murya tace "Wanda kika ce ya fi koh?" Umma tace "Ehh" A hankali tace "To 


bari in kirasa yanxu nagode Ummata" Umma tace "Welcm dear, Shureim yayi bacci koh?" Kai ta gyada tace "Ehh yayi but kamar yana son yin mura fa Umma, his 


voice is even cracky" Umma tace "Wannan kuma ke kika sani, least I forget nasan halin ki Khadijah tsakanin ki da matar khaleel mutunci kada kiyi amfani da 


cewa kina son mijinta ki dinga daure mata nasan ba hankali ya ishe ki ba" turo baki Khadijah tayi tace "Umma ni da ma mun kusa hutu in taho gida abuna ina 


ruwana da su" Umma tace "Khaleel dai ba abun walakanci bane a gun ki, though baku dade da sanin juna ba but he is always there for you, kuma duk da yasan ke 


wacece ya nuna yana son ki yana yaran ki, am reminding of all this ne don naga kamar kina da saurin mance alkhairi, dubi fa mahaifiyar Aliyu ba don nayi da 


gaske da ke ba ita ma ba raga mata xaki yi ba" jikin Khadijah yayi sanyi sosai, Umma tace "Sai da safe" daga haka ta katse wayarta, Khadijah tayi lamo kan 


gado, can ta bude idonta a hankali ta shiga kiran barrister a sanyaye, bayan sun gaisa a hankali tace "Barrister ka fara bacci ne?" yace "Noo ina wani aiki 


ne, how r you?" Tace "Lafiya lau, I now have a choice my barrister" Ya d'an buda ido yace "Really?" Tana murmushi tace "Sure" yace "Then which is ur 


choice?" Ta langwabar da kai tace "Ka hau Whatsapp in nuna maka yanxu" yace "Ohk then" daga haka ta katse wayar, bayan ta nuna masa akwatin da take so tayi 


masa text din sai da safe, daga haka ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. washegari da safe Khadijah na sa ma Shureim shoes dinsa na makaranta aka danna 


bell, ta kalli kofar kafin ta mike ta dau jakarsa ta goya masa a baya ta dau lunchbox dinsa tana rike da shi ta nufi kofar ta bude, khaleel ne tsaye bakin 


kofar, bai yarda ya kalleta ba yana kallon Shureim da murmushin sa mai kyau yace "How are you son?" Shureim yace "Good morning uncle" khaleel ya duka ya 


kamo hannunsa yace "The morning isn't good son, cold everywhere..." dariya Shureim yayi da ya bayyana white set of teeth dinsa, Khaleel yyi murmushi yana 


kallon kyakkyawan yaron ya fito da shi ya mike, gyara rigar sanyi sa yyi still bai yarda ya kalli Khadijah da ta hade rai ba yace "Plss do u use salt?" 


Khadijah na kallonsa tace "Meye shi?" Sai a sannan ya kalleta yace "Gishiri" sauke idonsa yyi daga kallonta, ta tabe baki kamar baxa ta ce komai ba sai kuma 


can tace "I don't know, let me check" daga haka ta juya a hankali ta koma ciki, Shureim yace "Uncle Aunt din nan tana nan" khaleel ya shafa kansa yana 


kallonsa yace "Tana nan" Shureim yace "Ae yau tace xata bani puzzle irin na su fadil..." khaleel yace "Tana bacci yanxu, ka bari sai ka dawo school xata ba 


ka" Shureim yace "Ohk can I tell her good morning now so as she will remember my puzzle?" khaleel ya duka yana kallonsa a hankali yace "No she is sleeping 


son, idan ta tashi I will remind her for you" Shureim yace "Ohk tnx" Khadijah ta dawo rike da container din Gishiri ta mika masa, ya karba yace "Thanks I 


will bring back the remaining now" Kamar jira take tace "Noo na ba ku" kallonta yayi da sauri yace "Noo ni xan yi amfani da shi ai" Wani kallo Khadijah tayi 


masa tace "Did you hear me mention name?" Khaleel ya sauke idonsa daga kallonta, a hankali ya juya xai koma ciki sai kuma ya juyo da sauri yace "I am coming 


inyi dropping dinsa a schl" Khadijah tace "Xan kai sa yanxu, you don't worry" yana kallonta da kyau yace "I insist Khadijah" daga haka ya juya ya wuce ciki, 


Khadijah tafi minti biyar tsaye a wajen can ta juya ta koma parlor ta xauna shureim ya biyo bayanta, tashi tayi daga parlorn gaba daya mood dinta ya canxa 


ta kalli Shureim tace "Ka jira sa a nan" daga haka ta wuce bedroom ta kwanta, ta rasa dalilin da yasa ta ji tana son yin kuka, ta kife kanta da pillow 


trying hard not to cry, ta fi minti goma a haka aka bude kofar dakin, Shureim ya shigo yace "Anty uncle yace in kira ki" A hankali ta mike xaune ta runtse 


ido jin xuciyarta na mata xafi, ta kalli agogo taga takwas saura, da kyar ta tashi ta bi bayan Shureim, tsaye ta tadda khaleel parlorn har ta karaso cikin 


parlorn bai yarda ya kalli inda take ba, ta tsaya tana kallonsa, kama hannun Shureim yayi yace "Plss Khadijah I need hot water, or rather lipton kafin in 


dawo" daga haka ya fita tare da Shureim dake daga mata hannu ya rufe kofar, juyawa tayi ta koma daki tayi kwanciyar ta. Bayan kusan minti ashirin aka danna 


bell, kin tashi tayi daga kwancen da take, Jin an sake dannawa ta daure ta dake, cike da karfin hali ta tashi ta fita, bude kofar tayi tana kallonsa, ledan 


hannunsa ya mika mata yace "Drugs din Shureim naga he is having cold" karba tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Thanks" daga haka ta juya xata wuce yace 


"Khadijah ruwan lipton din fa?" K'in juyowa tayi tace "Ni bani da ruwan Lipton" daga haka ta rufe kofar ta, daki ta wuce ta fada kan hado tayi kukanta mai 


isarta Kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ita kanta bata san me yasa take kukan ba, ta fi minti talatin kwance, ta mike a hankali jiki ba kwari daga 


karshe ta fito parlor, kitchen ta shiga ta kunna gas ta daura ruwa ta xuba Lipton da kayan kamshi ta dawo parlor ta xauna, tana ta xaune parlorn har taji 


alamar ruwan ya tafasa ta mike a hankali ta shiga kitchen din, cikin flask ta juye ruwan Lipton din gaba daya ta sa hijab ta fita, danna bell dinsa tayi, 


tana ta tsaye bayan wani lkci ya bude kofar, Mika masa flask din tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Yanxu na dafa" Ya karba a hankali yace "Thanks 


Khadijah" Bata ce komai ba ta juya ta koma apartment dinta, sai kusan sha biyu ta fita gidan duk da karfe goma take da lectures, da wuri ta fito schl don 


daukar Shureim ta samu har khaleel ya xo ya dauke sa, har ta fito wanka tayi sllh tana ta jiran ganin shigowar Shureim amma bai shigo ba, throughout ranan 


babu wani abin kirki da ta ci kuma gaba daya taji bata jin yunwa, a hankali ta dau wayarta don kiran Barrister taji ko ya isa gida lafiya, har ya katse bai 


dauka ba ta sake kiransa, nan ko yana xaune parlorn sa Little Meerah na jikinsa tana ta masa surutu da pure English dinta, Jiddah kuma na durkushe gabansa 


tana xuba masa dafadukan taliya da ta dafa sanin ranan xai dawo, kallon taliyar kawai yake don he is not a fan of it kuma sarai tasan baya ci, ya girgixa 


kai ya dauke kai daga abincin, ajiye serving spoon din hannunta tayi ganin alamar ana kiran wayarsa da ke jone a caji, ta mike ta nufi inda wayar yake, tana 


isa ta dauka tana kallon screen din "Ameerah" sunan da ta gani kenan jikin screen din, ta dinga kallo xuciyarta na bugawa, picking call din tayi kafin ya 


katse ta kai kunne tayi shiru Khadijah na jin an daga ba a ce komai ba tayi shiru ita ma don it's unusual of him kuma tana jin muryar little Amira a wajen, 


Kamar ance Sudais ya daga kai ya ga jiddah tsaye har lkcn wayar na kare kunnenta fuskar nan nata a murtuke, ajiye Amirah yyi kan kujera ya mike da sauri 


yace "What's that u are doing Jiddah?" Ba shiri Khadijah ta katse wayar ta ajiye ta tabe baki ta yi kwanciyar ta. Jiddah na masa wani kallo tace "Wato dai 


da gaske aure kake shirin yi saboda baka da tsoron Allah ko Aliyu?" Ya warce wayarsa  a hannunta yana mata wani kallo yace "Don't you ever dare pick my call 


again malama" daga haka ya bar parlorn ya wuce sama, Xaunawa gefen kujera Jiddah tayi lkci daya hawayen takaici ya shiga sakko mata, ai da ta sani kawai 


guduwa daki tayi da wayar tayi pick din call din ta sussurfa ma shegiyar dake kiransa xagi, to Wai wacece wannan Amirar? Sai yanxu taji tana mugun son sanin 


wacece ita, ta kalli Yar ta dake xaune tana kallon tv, lkci daya lkcn da ta haifeta ya dawo mata, ranan sunanta bayan ya sa sunan mahaifiyarsa babu yanda 


bata yi da shi kan cewar da Khaleesat xata kirata ba yace inaaa bai san xance ba sai dai Amirah, da ta tambayesa me yasa sai ce mata yyi sunan wata frnd 


dinsa mai muhimmanci a rayuwarsa ce kuma yana ji da ita sosai shi yasa xai kira 'yar sa da haka.... Jiddah ta mike da sauri xuciyarta na bugawa ko dai ita 


ce wannan mai kiran nasa yanxu, ita fa dama tun lkcn taji ta tsane koma wacece Amirar nan, shi yasa har yanxu da kyar take kiran Yar ta da Amirah, a bayan 


idonsa dama kiri kiri Khadijah take ce mata, wayarta ta dauka ta shiga dakin da ke parlorn ta kulle kofa ta shiga neman number Dr Yusuf tasan duk yanda aka 


yi baxai rasa sanin wacece Amira ba, bugu biyu ya daga bayan sun gaisa yana tsokanarta wai ta sa abokinsa ya mance shi gaba daya, ta xauna gefen gado tace 


"Dr dama tambaya ce na kira in maka don Allah..." Dr Yusuf yace "Toh Ina ji, Allah sa na sani dai" tace "Uhm nasan ka ma sani, wllh in gaya maka abokin ka 


ne duk ya ishe ni da wata Amira nayi nayi ya gaya min wacece ita ya ki, har cewa yayi idan na cinka wacece ita to xai bani kyautar mota, toh ni dai duk iya 


tunani na rasa gane wacece amma na fi tunanin frnd dinsa ce kilan da yake ji da, shine yanxu na kira ka bani satar amsa, dama wllh motata ta isheni sabuwa 


dal nake so, Kuma kasan barrister baya saba alkawari plss Dr ka taimaka" dariya sosai Yusuf yayi yace "Wai Amira?" Gabanta na mugun faduwa tace "Ita fa 


Dr..." Yace "Yasan baxa ki taba sanin wacece ita ba, Kuma xancen gaskiya babu wani mota da yake da niyyar baki don yasan ko xa ki shekara kina naxari baxa 


ki san wacece ita ba, it's not even possible, Ni kuma yanxu idan na gaya maki kika fada masa he will suspect ni na gaya maki don duk abokansa babu wanda 


yasan ta sai ni...." Jiddah tace "Haba Doctor, shi kansa yasan ai alkawari yayi baxai saba ba, Ni dai fa damuwata mota, don Allah ka gaya min ai bai san ina 


da number ka ba he won't suspect anything" Yusuf yyi murmushi yace "Toh xan gaya maki indai sabuwar mota kike ma" ta baxa kunne tace "Yauwa nagode sosai Dr" 


nan Dr Yusuf ya fara bata labarin Khadijah tiryan tiryan babu abinda ya boye a duk labarin har ranan da Mami ta rabasu na karshe. Gaba daya xufa ya dinga 


karyo ma Jiddah taji cikinta ya hautsine, Jin Yusuf yace "Hello" cike da karfin hali tayi dariya tace "Ikon Allah, Allah sarki, to nagode Dr Allah saka da 


alkhairi Allah ya barka da Amina, sabuwar mota kam dole a ban" daga haka tayi masa sallama ta katse wayar dai dai lkcn da aka bude kofar dakin kafin ya kai 


ga shigowa tayi saurin boye wayar hannunta, ya shigo yana kallonta yace "Files da na bari kan dinning kafin nayi tafiya, Ina kika ajiye min?"


✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨


 Shiru Jiddah tayi ta tallabi chin dinta tana kallonsa lkci daya kuma tana murmushi, Sudais ya hade rai yace "Magana fa nake maki jiddah?" Ta tabe baki tace 


"Amira na ba ta kai maka daki, kaje ka tambaye ta" wani kallo ya dinga mata yace "Amirar xaki ba files jiddah?" Cikin halin ko in kula tace "Ita, ko bata 


isa aike bane, Beside if they are that important ai baxa ka bar su yashe a dinning area ba" Girgixa kai yyi ya juya ya fice daga dakin, tayi wani murmushi 


mai sauti tana girgixa kafarta, lkci daya murmushin yayi fading a fuskarta, da ajinsa, da kyansa, da iliminsa da kudinsa duk fadin duniyar nan ya rasa warce 


xai kawo mata matsayin kishiya sai warce ta taba cikin shege ta haife yaran... Wani dariya ta kwashe har da kyakyatawa ta mike tana wani murmushi tace 


"Abomination" daga haka ta fice daga dakin, sai dai fa jin ranta take fess. Har khadijah ta fara bacci Shureim ya shigo dakin, ta dinga kallonsa har ya iso 


inda take yace "Anty cire min uniform" mikewa xaune tayi ta shiga cire masa uniform din jikinsa tace "Have u eaten?" Ya gyada kai yace "Uncle ya bani 


cornflakes" Khadijah na kallonsa tace "Are you okay with it?" Ya wara ido yace "Ehh Anty, ai da yawa ya bani, shi kuma ya sha tea" Khadijah bata ce komai ba 


ta dinga laluba aljihun wandon sa jin akwai abu a ciki ta fiddo Chocolate tana kallonsa tace "Wa ya baka?" ya karba da sauri yace "Aunt din nan ce ta bani, 


tace min xata siya min puzzles amma bata siya ba she is sick, she is even sleeping at the room" Khadijah ta ajiye kayan bata ce komai ba, ya kamo hannunta 


yace "Anty will you go and check her?" Wani kallo ta dinga masa strictly tace "If I should slap you...." A hankali ya koma baya yace "Anty kiyi hakuri" tana 


hararansa ta nuna masa bayi tace "Wuce kayi alwala" ba musu ya wuce da sauri, ta mike don fiddo masa kayan da xai sa, magungunan sa da khaleel ya siyo masa 


daxu da safe ta basa sannan ta ce yaje parlor yayi assignment dinsa, ta hada socks dinsa xata shiga bayi ta wanke wayarta yayi ring ta dawo tana kallon 


wayar taga Barrister ke kiranta, ta karasa ta dau wayar ta xauna gefen gado sannan tayi pick din call din ta kai kunne, a hankali yace "Am sorry you called 


bana kusa Amira" tace "Ba komai, ka isa lafiya?" Yace "Lafiya Alhmdllh dear" tace "Ya Amira fah?" Yace "She's fine, how about my son" tace "Yana assignment" 


yace "Ohk ba shi mu gaisa" mikewa tayi ta fita parlor ta ba Shureim wayar tace "Abba yana son maka magana" ya karbi wayar yana kallonta yace "Anty waye 


Abba?" Harara ta watsa masa tace "C'mon answer ur call..." ya kai kunne a hankali yayi sallama, Barrister dake jin su yayi murmushi yace "How you boy?" Yace 


"Am fine Abba" Barrister yace "Ka je schl yau?" Ya gyada kai yace "Ehh na je" yace "Good, always aim good grades sai in siya maka Bicycle" ya wara ido yace 


"My two uncles sun ce xa su siya min bicycle, kaga am having three now, sai in ajiye ma Sudais daya, in ba su fadeel daya, Ni kuma..." Khadijah ta kwace 


wayar hannunsa ta koma daki, ta kai kunne a hankali tace "You need rest barrister, ya kamata ka huta, hope ka ci abinci?" Yace "Me yasa kika amshe wayar?" 


Tace "He is talking off hook" yace "Baki son dai in san two uncles din nasa" ta wara ido tace "Aliyu da Dr Ayman yake referring as two uncles fah?" 


Barrister yayi murmushi yace "Alryt then" ta langwabar da kai tace "Toh ka ci abinci?" Yace "Eh yanxu xan ci" tace "Toh shkkn, kaje ka ci, a shafa min kan 


Namecy na" yace "Ohk, will do that in sha Allah, thanks love" daga haka ya katse wayar, tayi murmushi ta ajiye ta kwashi socks din Shureim ta shiga bayi don 


wanke su. Washegari gaba daya bata da lectures ranan, da wuri ta shirya Shureim ta tafi kai sa makaranta don bata son khaleel ya xo yace xai kai sa, tana 


dawowa ta rufe kofar ta ta wuce bedroom ta kwanta, sai kusan sha daya ta tashi daga baccin da tayi, yunwan da take ji yasa ta wuce kitchen don neman abinda 


xata ci, ta kunna gas ta daura ruwa ta dauko indomie da kwai taji kamar motsi a baya, ta isa gun window ta tsaya kafin ta leka a hankali, tsaye ta ga 


Jawahir... khaleel na bayanta ya rungumota fuskarsa dai dai nata, yana d'aga karamin weight da hannu daya, Khadijah ta sauke idonta a hankali ta juya ta bar 


wajen, kashe gas din tayi ta fice kitchen din gaba daya ta wuce daki ta kulle ta fada kan gado. Ta fi awa uku a haka, har lkcn sllh yayi ta kasa tashi, cike 


da karfin hali ta mike daga karshe tana runtse ido ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta sa hijab ta dau karamar jakarta da waya 


ta fita, tana kokarin rufe apartment dinta Khaleel ya fito, bata kalli inda yake ba ta gama rufewa ta juya xata wuce yana kallonta yace "What's wrong with 


you Khadijah, are u sick...." da kyar tace "No, i am okay" daga haka ta wuce waje ya bi ta da kallo, cab ta tsayar a waje ta shiga, kawai gani tayi ya ajiye 


ta schl, ita dai bata san ya aka yi ta ce masa can xata ba, ta fito ta basa kudinsa ta wuce ciki, cafteria ta nufa direct tana shiga ta xauna ta hade kai da 


table jin numfashinta na sama, ba a dau lkci ba Maryam ta shigo cafterian da frnds dinta xa su ci abinci, tana ganin Khadijah ta gane ta duk da kanta a kife 


yake har lkcn, ta isa kusa da ita tace "Hi Khadijah are u okay?" Da kyar Khadijah ta dago kanta, Maryam ta dinga kallonta ganin yanda idonta ya kada tace 


"Subhanallah baki da lafiya ne?" Kasa bata amsa Khadijah tayi, kana ganinta kasan she is in pain, Maryam ta fiddo wayarta a jaka da sauri ta shiga kiran 


Aliyu sanin yana within area din makarantar, Yana dauka tace "Ya Aliyu kana kusa ne plss, yanxu na shigo cafteria naga Khadijah kamar bata da lafiya, and 


she is not even responding, ko xaka taho yanxu plss...." Bata gama maganar ba Aliyu ya katse wayar, ta ja kujera ta xauna kusa da Khadijah tana kallonta da 


damuwa tace "Sannu Khadijah" frnds dinta turawa sai sannun suke mata su ma, Aliyu ne ya shigo cafterian ya karaso kusa da ita da sauri yana kallonta yace 


"Iman.... what's wrong, are you okay?" Tun Khadijah ma ganinsa bibbiyu a gabanta har daga karshe ta daina ganinsa kwata kwata, Bata sake bude ido ba Kuma 


sai can kusan magrib ta ganta kwance kan gadon asibiti, dafe kirjinta tayi ta dinga bin dakin da kallo, a hankali idonta ya sauka kan Aliyu dake xaune kusa 


da ita ya jinginar kansa da kujerar da yake kai idonsa a lumshe, kokarin tashi ta shiga yi hakan ya sa shi bude ido, da sauri ya mike ya dawo kusa da ita da 


damuwa yace "Stay still Iman kinga ruwa ne a hannun ki, how are you feeling now?" ta kalli drip din hannunta har sannan tana rike da kirjinta da kyar tace 


"It's hurting me" yayi kasa da murya yace "Kiyi hakuri xai daina Iman you are still under medication, koma ki kwanta plss" taki kwanciya ta hade kai da 


gadon, hawaye ne ya shiga sakko mata, a hankali yace "Iman?" Ta ki dagowa, hakan yasa ya tsaya yana kallonta cike da tausayi, cike da karfin hali ya ji tace 


"What about shureim...." Yana kallonta murya can kasa yace "I went to pick him in the evening na tarar neighbor din ki ya je ya dauke sa" Bata ce komai ba 


kuma bata dago ba yace "Let me call a nurse... Ina xuwa" daga haka ya fita dakin, ita dai har sannan bata dago ba hawaye kawai take kamar an bude tap, tare 


da wata baturiyar nurse ya dawo, ta duddubata ta fita, a hankali Aliyu yace "Iman kukan me kike plss?" ta kallesa hawaye na ci gaba da sakko mata ta kasa 


cewa komai, rikicewa yayi ya dawo kusa da ita sosai, yace "Don Allah Iman tell me whats wrong, me ya faru, me ne ke damun ki? Ur Bp isn't encouraging, ur 


condition don't need this, Tell me what ur problem is Plsss, ko an maki wani abu ne" ta goge idonta a hankali bata ce komai ba, Bude kofar ward din aka yi 


Maryam ta shigo tare da mum dinta, Hajiya Mariya ta karaso da damuwa tace "Sannu Khadijah, ya jikin naki yanxu?" a hankali cikin sanyi tace "Da sauki Mumy, 


Ina yini" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau, Ina Shureim din" Aliyu yace "Neighbor dinta ya dauke sa schl daxu" Maryam ta ajiye basket din abincin hannunta 


tana kallonta tace "Allah ya sauwake murya can kasa Khadijah tace "Nagode Maryam" Hajiya Mariya tace "Nan xata kwana, ko xa su yi discharging dinta?" Aliyu 


yace "Sai gobe da safe" Hajiya Mariya tace "Toh shkkn sai Maryam ta kwana tare da ita" Shiru Aliyu yayi ya rasa me xai ce don bai so haka ba, Hajiya Mariya 


ta ja kujera ya xauna ta bude basket din don debar ma Khadijah abinci, sai kusan karfe takwas ta bar asibitin tare da Aliyu ba don ya so ba, suna fita babu 


dadewa wayar Maryam ya fara ring, dauka tayi ganin Jawahir ke kiranta ta d'an wara ido ta daga kafin ta ce komai taji muryar khaleel, xaro ido tayi tace 


"Ina yini Dr?" Yace "Lafiya lau ya kike, I want to ask plss Maryam, Kun hadu da Khadijah schl yau?" Maryam tace "Gata nan  ai muna asibiti bata da lafiya, 


she collapsed daxu a cafteria but da sauki yanxu she's recovering" khaleel bai san lkcn da ya mike ba, jawahir dake kwance Shureim a gefenta dai sai 


kallonsa take, ya jira har Maryam tayi shiru kafin a hankali yace "Wani asibitin ku ke?" Ta fada masa sunan asibitin yace "Toh xan xo yanxu" daga haka ya 


katse wayar, yana kallon jawahir yace "Xan je duba Khadijah clinic yanxu she is sick, I will be back soon" jawahir dai bata ce komai ba ya nufi kofa, 


Shureim ya sauka daga kan gadon da sauri yace "Uncle ni xan bi ka" jawahir ta jawo sa jikinta tace "Don't worry yanxu xai dawo" a parlor khaleel ya dau 


makullin motarsa ya bar gidan ya nufi asibitn da Maryam ta gaya masa, yana parking a haraban hospital din ya fito ya kira Maryam don da wayar jawahir ya 


taho, Maryam na daga kiran yace "Ina waje Maryam" ward number ta fada masa yace "Thanks" daga haka ya katse wayar ya shiga asibitin, ya fi seconds talatin a 


bakin kofar ya kasa budewa, can ya murda a hankali ya shiga ward din, Kwance Khadijah take idonta lumshe, Maryam ta mike ganinsa tace "Sannu da xuwa Dr" 


yace "Yauwa Thanks" karasowa yayi bakin gadon yana kallonta, Maryam tace "Ina jin ta koma bacci" shiru yayi bai ce komai ba yana kallonta har lokacin don 


yasan ba bacci take ba, he really want Maryam to excuse them but he don't know how to make the approach, kamar kuwa Maryam tasan abinda ke ransa ta mike ta 


dau wayarta tace "Doctor bari inyi making wani call in dawo yanxu" ya kalleta yace "Alryt" daga haka ta nufi kofa ta fita ta rufe kofar, ya lumshe ido ya 


bude ya xauna gefen gadon ya kamo hannunta  ya kai fuskarsa dai dai nata a hankali yace "I know you are awake Khadijah, look at me plss"


Khadijah bata yarda ta bude ido ba, ya dinga kallonta, a hankali yace "Baxa ki kalleni ba Khadijah" dauke kanta tayi ta juya masa baya, mikewa yyi ya koma 


kujera ya xauna yana kallonta, bayan wani lkci yace "Shkkn since you don't want to see me bari in tashi inyi wucewata" a hankali ta juyo tana kallonsa, 


tausayinta ya dinga ji har ransa ya taso ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Ki gaya min ko na maki wani abun ne Khadijah, bana 


son wani abu ya same ki saboda ni, tell me ur mind plss..."  Tana kallonsa da kyau tace "What is in my mind da xan gaya maka?" A hankali yace "Noo, ai ke 


xaki fada I don't knw what you are thinking of me... Say out ur mind Khadijah" ta hade rai tace "Kana tunanin saboda kai nake rashin lafiya a nan?" Ya buda 


ido sosai yace "Noo ba abinda nake nufi ba kenan" Tace "Toh ciwo ne kawai Allah ya sakko min, so I just have to say Alhmdllh" Ya langwabar da kai yace "Toh 


Allah ya sauwake" tace "Ameen" yace "Kin ci abinci?" Kai ta gyada masa tace "Su Maryam sun kawo min" Wayarta dake ajiye yyi haske alamar kira khaleel ya 


dauka ya mika mata ta karba, ganin barrister ke kiranta ta daga ta sa a handsfree ta kai kunne, da damuwa yace "Ina kika shiga Amira, I have been calling 


since but no response" ta koma ta kwanta a hankali tace "Kayi hakuri plss, yau tun da na tashi nake jin ciwon ciki, sai bayan da naje schl sai ya matsa min 


aka taho dani clinic.... Am even stil at the clinic" Sudais yace "Subhanallah, wani irin ciwon ciki ne haka?" Ta d'an buda ido tace "Aa ni ma ban sani ba, 


kawai dai ciwon ciki" yace "Ko dai... Ko dai na period ne?" xaro ido tayi don ita har mancewa take akwai wani abu wai shi al'ada, tun da ta haifi su Shureim 


ta daina, sai dai tayi bai fi sau daya ko biyu a shekara ba shi ma na kwana biyu, Amma fa tana shan axaba sosai don wani lkcn har tunani take kila mutuwa 


xata yi, yace "Uhm shine koh?" Yar dariya tayi tace "Ae ni bana yi" yace "Bakya me?" Tace "Uhm abinda ka fada mana" yace "Are you serious?" Tace "Ehh" yace 


"Maa sha Allah, kice doubling sadaki xan yi kenan" Boye fuskarta tayi da gado don ba karamin dariya da kunya ya bata ba ga khaleel a xaune, shi dae Khaleel 


idanuwansa na kan wayar hannunsa da yake dannawa yana saurarensu, ta dago a hankali tace "Koh?" Yace "Ehh mana, ai ku special ne cikin mata, and you are 


rare...." tace "Uhmm" lkci daya khaleel ya mike ya nufi kofa ta bi sa da Harara har ya fice, Barrister yace "But hope ciwon cikin da sauki sosai yanxu?" Ta 


gyada kai tace "Naji sauki amma sai gobe xa ayi discharging dina" yace "Toh wa ya kawo ki asibitin?" Da har xata ce Aliyu sai kuma tayi shiru, da sauri tace 


"Maryam da na baka labari ranan, ita ce ta kawo nii, luckily ta shigo cafteria lkcn ta gan ni kawai muka wuce clinic" Yace "Toh Allah ya kara lafiya, how 


about shureim ko tare ku ke a asibitin?" Ta girgixa kai tace "Noo yana gun neighbors dina" Barrister yace "Ohk, I will send the hospital bill yanxu kin ji" 


da sauri tace "Nooo, 'yan gidansu Maryam sun biya ma, don't bother plss my barrister" yace "Toh idan na turo sai kiyi pepper soup da yawa ke da Shureim ku 


ci, clear?" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace "Yea, sai da safe dear, Allah ya kara lafiya" a hankali tace "Ameen nagode sosai" lumshe ido yayi ya 


katse wayar, Khadijah ta mike xaune a hankali, gaba daya taji ta samu relieve kamar an cire mata ciwon, Maryam ce ta dawo ward din tace "Ashe kin tashi 


Khadijah" d'an murmushi Khadijah tayi tace "Ehh" Maryam tace "Ohk, Dr Ayman yace in fada maki ya wuce sai da safe" Khadijah tace "Ohk, I was making call ya 


fita" sosai Khadijah ta sake da Maryam suka dinga hira a ward din har Maryam ta dinga mamaki ganin ashe dai tana magana haka, sai kusan karfe sha daya duk 


suka kwanta. Washegari karfe bakwai na safe Aliyu ya xo clinic din, Khadijah na bathroom tana wanke baki da sabon toothbrush da Maryam ta kawo mata da 


paste, Maryam suka gaisa da Aliyu yana kallonta yace "Ya jikin nata?" Maryam tace "Ai kam taji sauki sosai" dai dai nan Khadijah ta fito ta karaso tana 


kallonsa a hankali tace "Good morning" yace "Morning Iman ya jikin?" Tace "Naji sauki sosai, thanks for ur care" yayi murmushi har ransa yaji dadin yanda ya 


ganta unlike yesterday, ya ajiye breakfast da Hajiya Mariya ta bada ya kawo masu, Khadijah ta xauna gefen gadon tana kallonsa tace "Plss ina son kaje can 


gida I don't want to inconvenience anybody sae ka dau Shureim kayi dropping dinsa schl" Yana shafa kansa yace "Dr Ayman din baxae kai sa ba?" Tace "Toh ni 


bari in je in daukesa in ajiye sa schl idan baxa ka je ba, Kuma ai nasan da Dr Ayman din" murmushi yayi yace "Aa ae bn ce baxan je ba malama" turo baki tayi 


ya juya ya fita ward din din Maryam ta bi sa da kallo, Mikewa tayi daga karshe ta hada ma Khadijah shayi da ya kawo ta bata da kwai, Khadijah ta amsa tace 


"Nagode" daga haka ta fara shan shayin da spoon, bayan kusan awa daya Aliyu ya dawo ward din, kujera ya ja ya xauna ya jinginar da kansa da kujerar yace 


"Dama kawai don ki bani wahala ne kika ce in tafi koh?" Tana kallonsa tace "Me ya faru" murmushi kawai yayi ya dago yana kallonta, ta ci gaba da Shan 


shayinta, mikewa yayi yace "Anyi discharging din ki yanxu, we can leave" tace "Toh bill din fah, am not with money, ko idan mun je gida sai in baka, nawa ne 


kudin?" Ya fi minti daya yana kallonta kafin ya juya ya fita ward din, Maryam ta d'an yi murmushi tace "Haba dai ya biya ai Khadijah...." Khadijah ta sakko 


kan gadon ta dau mayafinta da wayarta da jaka tace "Toh nagode" Maryam ta dau kayan shayin da ya kawo suka fita waje, a haraban asibitin suka tadda shi yana 


jiransu cikin mota, Maryam ce ta shiga gaban motar Khadijah ta shiga back seat suka bar asibitin, da Khadijah ta daga kai sai su hada ido da Aliyu yana 


kallonta ta madubi, ta daga kai yayi sau uku sai su hada ido, ji tayi gaba daya she is uncomfortable, ta matsa a hankali ta koma can karshen motar tana 


kallon waje, dai dai gidanta yayi parking ta bude motar ta fito ta xagayo ta inda Maryam take tace "Nagode sosai Maryam, ki taya ni yi ma Mumy godiya in sha 


Allah xan shigo anjima da yamma ko gobe, Allah saka da alkhairi" Maryam ta d'an yi murmushi tace "Ba komai, sai kin xo" kallon Aliyu dake ta kallonta tayi, 


da kamar baxa ta ce masa komai ba sai kuma tace "Thanks" daga haka ta juya xata wuce ciki, a hankali yace "Anjima xan kawo maki drugs din ki Iman" tace 


"Ohk" tana fadin haka ta shiga gida ya ja motar suka bar street din. Tun daga wannan rana gaba daya Khadijah ta ajiye khaleel da jawahir gefe daya, 


tsakaninta da su gaisuwa faram faram ita kanta tayi mamakin yanda har ta sake ma jawahir yanxu duk da ita sai wani daure mata take, Lkci daya Khadijah ta 


yakice khaleel gaba daya a ranta, ko don tashin dare da take yawan yi tana rokon Allah ya cire duk wani connection dake tsakaninta da shi a xuciyarta ne, 


yanxu tun safe in ta fita gidan dama sai yamma take dawowa kuma duk ta dawo xata tarar khaleel ya dauko shureim, wani lkcn basa ma sanin ta dawo, yanxu kam 


ita kanta tasan ta rage damuwa sosai, jarabawarta kawai ta sa gaba, duk bayan kwana biyu ta kan je gidansu Maryam gaida Hajiya Mariya, kuma duk taje sai sun 


hadu da Aliyu, wani lkcn ta amince ya maido ta gida wani lkcn kuma tace baxata hau motarsa ba shi dai kam sai dai yayi murmushi baxai ce komai ba, sai ta 


tafi tayi ta tausayin sa bata san dalili ba, har xuciyarta take ganin Aliyu kamar little Sudais dinta cos the little boy have all his fathers quality, Kuma 


tasan saboda Aliyu yasa ta sa ma kanta dangana haka, Wani rama khaleel yake da shi kansa bai san dalilinsa ba, gaba daya ba shi da sukuni, yanxu kam sure 


yasan Jawahir and Khadijah are cousins daga binciken da yayi but bai san ta inda xai billo ba, gaba daya kansa ya kulle, bai taba xaton haka ba, they are 


very close relatives, dauke masa wutan da Khadijah tayi ya fi komai bata masa rai, in har ta gaishesa a gidan to tare ta gansa da jawahir, in ko just haduwa 


suka yi su biyu ko kallon inda yake bata yi, sai ma saurin barin wajen da xata yi, shi dai yasan har sannan bai cire rai da ita ba ko don nuna mata iyakarta 


kan walakancin da tayi masa but how will that be when they are cousins  with his wife Jawahir?? sure it's not prohibited, but Uhm... A can Nigeria kuwa 


Sudais ya gama hada lefen sa tsaf, komai ya siya sai ya nuna ma Khadijah ta WhatsApp ko yayi mata, Yana gama hada lefen dama ya kai ma jiddah kayan fadar 


kishiya, tun da taga akwatunan hankalinta yayi mugun tashi, ya sanar da ita ko na meye bai tsaya saurarenta ba ya fice, Ta fashe da matsanancin kuka tana 


kallon kayan, yanxu har auren nan ya matso bata samu damar daukar number Khadijah a wayar Barrister ba gaba daya hakan ya faskara duk iya kokarinta, Nan ko 


bata san duk Barrister ya lura da take takenta ba ya canxa yanda yyi saving number Khadijah daga Amira ya mayar Ummu Shureim, Xaunawa jiddah tayi kan kujera 


wata dubara ta fado mata.... Murmushi tayi tana share hawayen ta a hankali tace "Allah ya kai mu ranan auren, ai dai Amarya xata tare koh? Toh a daren 


farkon ta gidan ka xan maku abinda ita xata yi da ta sanin auren ka, kai Kuma xaka gwammace baka aureta ba" wani murmushin ta kuma yi ta wuce daki xuciyarta 


fess, har Allah Allah yake ranan ya xo ta cika aikinta, ta tabbata Khadijah baxata kwana gidan ba Kuma har karshen rayuwarta xata ji baxata iya yafe masa 


ba, ba boka ba malam. Ana saura sati daya Khadijah ta taho hutu Barrister Sudais yaje katsina gun Kawunta bayan Umma ta basa address, ciwon kafa kawu jibril 


ke fama da shi sosai sai dai hakan baya hanasa tafiya, duk yaransa biyu da ya aurar na xaune gida da ya yansu auren ya mutu,  gashi yanxu duk kudin sun ja 


babu komai sai motoci biyu da gidan da yake ciki, kawu na jin abinda ya kawo Sudais bayan sun shiga parlorn sa, ya dinga masa wani kallo yace  "inaaa, you 


are mistaken don bani da wata ya wai Khadijah, ka dai koma ta kai ka gun dangin ubanta amma ba ni ba, tashi ka ban waje malam" Sudais dake ta kallonsa yace 


"Amma dai ka santa koh?" Kawu yace "Toh meye amfanin sanin nata, Yarinyar da rabon da na sa ta ido yau xai yi shekara goma sha, tana can tana yawon duniya 


da kishiyar babarta" Sudais ya san xa ayi hakan shi yasa ma ya fara xuwa shi kadai, bai taho da kowa nasa ba dama Kuma bai sa ran Kawunta xai yarda ya daura 


mata aure ba" Sudais yyi murmushi yana kallonsa da kyau yace "Kawu dama ba wai lallai sai kai xaka daura mata aure ba, Kar ka mance babu abinda kudi basa yi 


a duniya, kawai dai dama an sa na xo ne don a fita hakkin ka a matsayin ka na wan mahaifinta, bayan haka Kuma kawu yanxu xaka iya damka ma Khadijah gadon ta 


na mahaifinta tunda ta mallaki hankalinta?" Da mugun mamaki Kawu Jibril ke kallonsa baki bude, can ya mike da kyar yace "Kai a uban wa xaka xo min da xancen 


gadonta??" Mikewa Sudais yyi ya tako har gabansa ya fiddo Id card dinsa yana masa wani kallo yace "Ni a lawyer mai xaman kansa.... Barrister Aliyu Umar, don 


haka nake maka gargadi kawu kar ka yarda magana ta kai mu ga shiga kotu baxai maka kyau ba... 10 years kamar yanda ka fada is enough.. hand over her 


properties to her" Daga haka Sudais ya juya ya fita kawu ya bi sa da kallo cikinsa na kara baki sake.... Yau Khadijah ta gama exams tana bedroom tana ta 


shirye shiryen kayan da xata koma Nigeria da, Shureim kuma na parlor ta bar sa yana bacci taji kamar an bude kofa, juyawa tayi da sauri don bata ma san 


kofar a bude yake ba, tayi saurin daukan hijab xata fita suka kusa cin karo bakin kofar dakin.


Komawa baya khadijah tayi tana kallonsa, ya shigo xai rufe kofar ta xaro ido tace "Meye haka Doctor" rufewa yyi ya yana tahowa kusa da ita yace "Tell me why 


you are avoiding me Khadijah" wani kallo tayi masa tana komawa baya tace "Avoiding din ka kamar ya, bayan gaisuwar da nake maka me kuma kake so daga 


gareni?" Ganin ya kusa isketa ta juya da sauri xata shige bathroom, yyi hanxarin rikota ya juyo da ita yana kallonta, wani kara tayi ya matseta jikinsa yana 


mata wani kallo, lkci daya jikinta ya dau rawa tace "Stop it plss Dr, meye haka don Allah ka bari ni bana soo..."  yace "Is it a crime don nayi aure?" Sake 


baki tayi tana kallonsa, can ta hade rai tace "Ban gane ba?" Yace "Ehh tunda nayi aure kika kara dasa min rashin mutunci a kan na da, I showed interest in 


marrying you kika yi shunning dina, me kuma kike son in maki Khadijah? Tell me me kike so?" A hankali tace "Let go of me now!" ba musu ya saketa yana 


kallonta, juyowa tayi tana facing dinsa da kyau tace "Ai da kana so na kamar yanda kake ikirari ko me xan ce maka baxai hana ka abinda ke a ranka a kai na 


ba, kuma abinda yasa baka wani damu ba shine saboda kana da warce kake so da aure... so don't tell me dat Ayman" Ya shafa kai yana mata kallon mamaki, bude 


kofar parlorn suka ji aka yi, a tare suka kalli door din dakin, ya nufi kofar ya bude ta bi bayansa, tsaye suka ga Jawahir a parlorn ta rike waist da hannu, 


Khaleel ya karaso kusa da ita kamar mai tausayin kasa ya tsaya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba ta taka ta tafi gun Khadijah dake tsaye bata karaso 


cikin parlorn ba, wani kallo Jawahir ta dinga mata kafin tayi wani murmushi tace "Khadijah kike kowa? Let me warn you first before taking any action...." 


Strictly tana mata wani shegen kallo tace "Stay Away from my husband, I repeat my self stay away from him you bitch, idan ma kina da wani kuduri a kansa a 


ranki ne to kiyi maxa ki goge don wllh ya fi karfin ki nesa nesa ba kusa ba, shi ba sa'an ki bane, shi ba sa'an auren ki ba ne, and let me advice you as a 


lady.... idan aure kike so ki rufa ma kanki asiri ki koma gidan uban 'ya yan ki wllh hakan kadai ne rufin asirin ki, ke bari ma kiji abinda baki sani ba, da 


Khaleel ya aure ki a matsayin kishiyata gwara ya auro min budurwa kamar ni mu goga, banda naci da ba kai wahala Ina ke ina Khaleel kina baxawarar, ragowar 


wani???" Tsawa Khaleel yyi mata ya isa kusa da ita lkci daya idanuwansa suka sauya xuwa ja yace "Kina da hankali Juwairiyya? Kin san wacece ita kike fadi 


mata wannan maganan gabana?" Wani kallo ta masa ta daga masa hannu tace "Spare me Malam ba da kai nake ba da sa'ata nake, keep ur mouth shut... ban kuma 


damu in san wacece ba, tunda ta shanye ka ni bai gagareni in kwatar maka yan cin ka ba" Fincikota Khaleel yyi a mugun fusace yace "Did you knw I can give u 


a dirty slap now?" Jawahir tayi dariya tace "Wllh ka mare ni in rama a kanta, wai ma a kan shegiyar mai makale ma maxajen mutane xaka ce xaka mareni 


Khaleel?" Kasa ce mata komai Khaleel yyi, can ya runtse ido ya turata yace "Ina guje maki ranan da xaki ji kunya Jawahir, ranan da xaki kasa kallon idanuwan 


warce kike ma rashin mutunci yanxu, Kuma bayan kin san ta kina ji kina gani xan aureta in hada ku...." Khadijah tayi wani murmushi bata ce komai ba ta juya 


a hankali ta koma daki ta rufe kofar ta sa key, tafi minti goma kwance kan gado, ita kanta ta rasa me ya hanata yin kuka, kalmomi hudu suka tsaya mata a 


lkcn, Bitch, Baxawara, ragowar wani, mai makale ma maxan mutane, yanxu jiddah ma kallon da take mata kenan koh?? wani murmushin tayi ta kai hannunta 


fuskarta jin abu na sauka taji hawaye ne, cikin pillow ta cusa kanta bata sake dagowa ba sai kusan karfe dayan dare shima ta dalilin sanyin dake neman mata 


illa, da kyar ta mike jikinta na rawa ta fiddo kayan sanyi ta sa, Shureim ya fado mata ta fita parlor da sauri, kwance ta gansa kan kujera ya takure waje 


daya yana rawar sanyi duk da kayan sanyin jikinsa, ta isa kusa da shi ta daukesa ta rungume sa ta karasa gun kofa ta sa key sannan ta kashe wutan parlorn ta 


wuce daki, kwantar da Shureim tayi ta rufa masa duvet ta wuce bathroom ta sa ruwan dumi tayi alwala ta fito, sai kusan karfe biyu da wani abu ta kwanta 


bacci me nauyi ya dauketa. Tun da tayi sllh asuba take ta shirya sauran kayansu, tana gamawa ta tada Shureim ta shirya sa ta basa tea da sauran cake dake 


gidan, ita ma ta shirya, wayarta ta dauka ta shiga scrolling call log a hankali tana neman number Aliyu duk da bata yi saving ba amma tasan number, ta fi 


second goma tana kallon number can tayi dialing, bugu biyu ya daga, a hankali yace "Iman, hope all is well?" ta gyada kai kawai tace "Ina kwana" yace 


"Lafiya lau, Ina Shureim" ta kalli Shureim dake gefenta a xaune, murya can kasa tace "Airport xaka xo ka kai mu pls, if we won't inconvenience you"

Aliyu yace "Sure, yau xaku tafi Nigeria din?" Tace "Ehh" yace "Toh gani xuwa yanxu" daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti sha biyar tana xaune ta 


rungume Shureim kai kana ganinta kasan she is just weak, duk ta xama kamar mara lafiya alhalin babu inda ke mata ciwo, da ta tuna maganganun da Jawahir ta 


gaya mata jiya da yamma sai tayi murmushin takaici, mikewa tayi ganin kiran Aliyu ta dau karamin jakarta suka fito bayan ta tabbatar komai na gidan ta kashe 


ta kulle kofar apartment din, ta nufi waje rike da hannun Shureim, Kayan sanyi ne jikinsa shi ma yana jingine jikin mota ya rungume hannunsa, yana ganin 


Shureim ya isa kusa da shi ya daga sa ya rungumesa a hankali yace "Good morning sweetheart" murmushi yaron yayi yace "Good morning uncle" kallon khadijah 


dake kallonsu Aliyu yayi ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "Good morning" ta ce "Morning" xagawa yayi ta bi bayansa ya bude motar ta shiga ya mika mata 


Shureim ta xaunar da shi gefenta sanann ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver, driving din some minutes yayi suka isa airport yyi parking waje duk 


suka fito, Daukar Shureim yayi da damuwa yana kallonta yace "Iman kin bari sanyi ya kama sa da yawa fa" ta kalli Shureim dake tari, sauke idonta tayi tace 


"And I am very cautious about that, Ni ma ban san yanda aka yi ba" yace "ko yana shan ruwa me sanyi ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" Ganin yanda yake 


tarin tace "Ka ajiye sa kar ya maka amai a jiki" Bata rufe baki ba ya kwarara masa aman shayin da ya sha a jikinsa, Aliyu ya dinga shafa masa bayansa yana 


masa sannu, da damuwa khadijah tace "Toh ina xa mu samu ruwa yanxu, gashi ya bata maka jikin ka" Aliyu na kallon direction da motarsa yake yace "I think I 


have table water a mota" tace "Toh bani makullin in dauko" mika mata makullin yayi ta koma motar da sauri, ba a dau lkci ba ta dawo da ruwan ta mika masa ya 


karba, ya sauke Shureim ya ciro handkerchief dinsa ya shiga goge masa bakinsa da jikinsa da ya bata, tana kallonsa tace "Baxa ka wanke masa bakin da ruwan 


ba?" Yace "Noo, akwai sanyi..." yana gamawa ya mike ya shiga kokarin cire sweatern jikinsa, ganin goran ruwan hannunsa ta xaga bayansa a hankali ta taimaka 


masa ta cire sweatern, sai ta ganta yar karama kusa da shi don ya fi ta tsayi sosai, lkci daya ya juyo yana kallonta, ta sauke idonta ta saita wajen aman a 


sweatern ba tare da ta kallesa ba tace "Xuba min ruwan" yace "But it will be very chill kawo in wanke" tace "A'a ni ka xuba min" bude ruwan yayi ya shiga 


xuba mata tana wanke wajen har ta gama ta shiga kakkabe sweatern, da sauri ya sake ruwan hannunsa ya nufi gun Shureim ganin yanda ya jingina da wani mota, 


he looks so sick, ya daukesa ya rungumesa yace "Sorry son" Khadijah na kallonsu a hankali tace "Toh kar yaje yana min amai a jirgi" Aliyu ya juyo yana 


kallonta yace "Noo baxai yi ba, mu je in siya masa drugs mu dawo yanxu" daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa. Sai da ta fara shiga motar sannan ya xaga ya 


mika mata Shureim ya rufe motar ya dawo ya shiga maxaunin driver ya tada motar, drugs ya siya masa na mura da xaxxabi, bayan yyi reversing motar murya can 


kasa yace "Can I accompany you two Iman, because of his condition, I will postpone my schedules for today..." Khadijah da ke rungume da Shureim tayi shiru 


bata ce komai ba, ganin ya dau hanyar airport ta kallesa a hankli tace "Ai baka shirya ba, you can't just go without preparation" yace "I will only drive 


home yanxu inyi dropping motar, mu dawo airport and make the traveling process" Tace "Toh amma ai su Mumy ba su sani ba" ya kalleta a hankli yace "I will 


explain to her, she will understand" khadijah ta d'an yi shiru, can tace "Toh shkkn" gida ya nufa yayi parking a waje yace "Kilan baki shirya shiga ku gaisa 


da Mumy ba, beside it's too early, let get a taxi sai ku shiga ku jirani saboda sanyi" ita dai bata ce komai ba ya fita ya tsayar masu da taxi bayan ya fada 


masa xai d'an jira sa ya shiga gida ya fito, kayansu ya fara transferring xuwa taxin sannan ya xaga ya bude motarsa Khadijah ta fito ta shiga taxin, ya dau 


ledan maganin Shureim ya bata ta amsa, ya shiga motarsa ya shiga gidan yyi parking. Bayan few minutes ya fito ya hau taxin suka wuce airport, sai kusan 


karfe tara jirgin su ya tashi. Aliyu na kallon ladyn dake kusa da Khadijah bayan sun yi boarding plane din xai yi magana ta gane abinda yake nufi, tace "Ohk 


then" daga haka ta koma seat dinsa ya xauna wajenta yana rike da shureim ya kalli Khadijah da ta lumshe ido yace "Ke kin ci abinci kafin ku fito?" Ta bude 


ido tana kallonsa ta gyara xamanta tace "Na sha shayi" Bai sake cewa komai ba, bayan wani lkcn Shureim yayi bacci yana rungume da shi, da farko kawai lumshe 


ido tayi ita ma, amma after sometimes bacci ya dauketa, kallonta kawai Aliyu yake, ko ba a fada masa ba yasan she is disturb, there is something eating her 


but he won't even dare ask what it is, ya lumshe ido tuna farkon ranan da aka fara kawo khadijah aiki gidansu da yanda ta dinga kallon TV bata ma san abinda 


ake ce mata ba, lkcn da ta taka masa kafa xata kitchen and how she said she is sorry, tun daga sannan dama yasan kaddara ce ya kawota gidansu, bude ido yayi 


a hankali ya sake kallonta, Khadijah is just beautiful in many ways....  A hankali ya sauke idonsa kan Shureim ya ga babu abinda ya dauko nata sai pink 


coloured lips, kanta ya ji a shoulder dinsa, ya daga kai yana kallonta, bacci take me nauyi, bai taba ta ba kuma bai tasheta ba ya bar ta a haka. Sai kusan 


magrib suka sauka Abuja a Nigeria,wani flight din suka sake boarding xuwa kaduna, Adai daita sahu ya kawo su har kofar gidan Umma, Aliyu ya fito Aliyu yana 


dauke da Shureim, ita ma fito ya dauko mata jakarta ya mika mata ta amsa yace "Ki kai ciki sai ki dawo ki amshe sa" ba musu ta wuce ciki 


yana kallon mai napep din yace "Kayi hakuri xaka kai ni Gra yanxu" Bayan wani lkci khadijah ta fito ya isa gabanta ya mika mata yaron dake bacci ta karbesa 


tana kallonsa tace "Mun gode sosai" d'an murmushi kawai yayi, can yace "Idan ya ci abinci sai ki basa magungunan sa" tace "Toh" yace "Alryt xan wuce gida a 


gayar min da Umma" daga haka ya shiga adai daita, mai adaidaitan ya ja suka bar wajen ta bi su da kallo, juyawa tayi a sanyaye xata shiga gida suka kusa cin 


karo da Nanny da ta amshi Shureim hannunta suka wuce ciki, ruwan xafi Nanny ta hada masu bayi, ta ma Shureim wanka sannan khadijah ta shiga, Umma na ba 


Shureim abinci ta fito, Umma ta kalleta tace "Ni nasan sai sanyi ya kama yaron nan kawai salon ki ja masa kika tafi da shi tunda kin san lkcn sanyi ne" 


khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi...